Showing 51001 words to 54000 words out of 104857 words
Chapter 18 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
matuƙar zafi na furzar daga bakina ina jingina kaina ajikin kujerar motar.
Lumshe idona nayi ina hango fuskar Habib lokacin da likitan ke faɗamasa ina ɗauke da juna biyu,irin farin-cikin daya taso masa lokaci ɗaya.
Banji shigowar saba saijin ƙarar rufe murfin ƙofar motar danaji saurin cusa kaina nayi cikin tafukan hannuna ina ɓoye fuskana,murmushi ya saka mai sauti kana yace"Hibba nagode wannan farin-cikin dakika sani a cikinsa yau Allah yamiki tukwuici da aljannarsa maɗaukakiya,Allah yasa wannan cikin ya zamto sanyin idaniya agaremu".
A zuciyata amsa sannan ya tada motar tunda muka fara tafiyar idanuna suke runtse,ban buɗesu ba sai lokacin danajin motar ta tsaya ganin inda muke yasa na kallo shi da sauri.
Ɗaga min gira ɗaya yayi yayin dayake ƙoƙarin since bal ɗin motar dake jikinsa sannan ya fita,wata zuciyar tace min"Mutumin nan yau kawai so yake kirasa inda zakisa kanki saboda kunya,inba hakaba meyasa daga barinmu asibiti zai kawoni gidan Ummi?".
Jidanayi har ya zagayo ya buɗe min ƙofar motar yasa ya dawo daga tinanin dana lula,a hankali na sauƙo da ƙafata na fito muka nufa cikin gidan.A falo muka tarar dasu hadda Daddy Sayyid ma lokacin yazo gida.
Sai da muka zauna sannan muka gaishe da Ummi da Daddy suka amsa,kafin Ummi ta ɗaura ta tambayata ya jikin nawan dan Habib ya faɗa mata kwana biyun nan banajin daɗin.
Tun kafin nakai ga bata amsa Habib yayi saurin cewa"Ai Ummi kedai kam kin kusa samun jika"ya ƙarishe maganar yana miƙo mata takardan da likitan ya basa.
Nidai kam da kunyar Daddy da Ummi yana nasara inda zan sakaye kaina,na tashi da sauri na nayi ɗakin Yasira na kwanta abini.koda Ummi ta karanta takardan godiyawa Allah ta shiga rabzawa ɗaya nabin ɗaya sannan tamikawa Daddy takardan dubawa yayi jikin tsanaki kana ya tsaki guntun murmushi tare da faɗin"Allah ta raba lafiya"duk suka amsa da amin.
Nikam tun dana shiga ɗaki ban fitoba sai da zamu tafi,kaina a ƙasa hakana fito muka tafi Yasira sai dariya takemin,muna isa gida na wuce toilet na sakewa kaina ruwa sannan na ɗauro alwala na fito doguwar rigata marar nauyi na zira na tada sallan Asr daka fara ƙira ina iddarwana fito falo na zauna na tunna TV tashar Manara Tv nakai naci sa'a kuwa sun saka karatun al-qur'ani hakan yasa na ƙure volume kamar yanda Ummi ta umurce ni kafin tahowar mu akan cewa inyawaita sauraron karatu saboda neman tsari daga dukkan abin cutarwa.
Ina zaune Habib ya shigo ya dawo daga masallaci yana tafe yana waya da Granny yana labarta mata zancen cikin ko zama baiyi ba ya katse wayar ya ƙira Baffa shima ya faɗa masa inajiyo guɗar da Inna tarangaɗawa,sallama sukayi sannan yazo ya zaune.
Harara na cilla masa ina cewa"kowa kaikam sai ka ƙirashi ka sanar dashi nifa nafiso kawai sai dai aji na haihu".dariya maganar yaso ya bashi ya mazge yace"Kinsan aka cewa wai abokin kuka ba'a ɓoyewa mutuwa duk waɗanda kikaji na ƙiransu Granny nece,Baffa sai kuma Bashir sukuma masu farin-cikin ne akan wannan abun bakiji yanda Inna tayi murnan jin wannan abunba,shiyasa gobe zamuje asibiti mu taimkawa masu buƙata don mununawa Rabbi godiya akan wannan arzikin daya bamu".
"Allah ya kaimu Hamma"na faɗa ina akai masa da murmushin yaƙe,yace "Amin".
Hajara kam tun lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata lokacin da Baffa ke faɗawa Inna maganar nasama ciki,ta kasa tsaye ta kasa zaune duk ranta ya jagule mata hijabinta ta saɓa a ƙafaɗarta ta fita ta nufi gidan Adda barira.
Ganinta da Adda barira tayi haka ya tabbatar mata daba lafiya,miƙewa tayi tana tsame hannunta daga cikin ruwan wankin datakeyi ta nufeta tace"Ƴar-uwa lafiya kuwa?".
"Ina kuwa lafiya Adda wallahi ni nafara tinanin malamin nan kawai cin kuɗinmu yakeyi"ta faɗa hawayen takaicin nabin gefen kuncinta.
Jan hannuta Adda Barira tayi suka shiga ɗaki"Ki nutsu kimin bayani yanda kwakwalwata taza fahimta Hajara meya faru?".
Share ƙwallar dake kai kawo a fuskarta Hajara tayi da bakin hijabinta kafin ta shiga labartawa Adda labarin cikin dake jikina,salati Adda ta saka tana tafa hannu kafin ta riƙe haɓarta tana cewa"kai!gaskiya wannan abun da mamaki yake,amma kinsan abunda zamuyi bari muje wajensa kawai muji ba'asi dan zama bai ganmuba".ta faɗa tana jawo hijabinta dake maƙale samar ƙofar ɗakin sannan suka fito
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
Page 3⃣5⃣
__________________________________
Suna tafe suna surutai kamar sabbin zararru haka har suka isa gidan boka Iro kamar yanda tsarin shiga gidan yake,ba sallama haka suka shiga suka zauna akan buzun dake yashe a ɗakin nasan.
Ɗan muzgutawa Adda Barira tayi kana ta shiga faɗa masa komai,kamar yanda Hajara ta faɗa mata sannan ta ɗaura da cewa"Allah gafarta malam mudai yanzu burin mu shine a ɓarar da cikin dake jikinta sannan a ɗaure bakin mahaifar ta yanda bazama ta ƙara samun wani cikinba,sannan koma buƙata ta biyu munason shi mijin ƴar-uwar tawan daga shi har mahaifiyarsa a mallakesu sai yanda Hajara ta juyasu kamar raƙumi da akala"
Wani dariya mai sauti boka Iro ya saka wanda ya karaɗe ilahirin ɗakinnasan kafin ya shiga faɗin"Sai yanzu na ganu matsalar da aka samu tun farko,watau ita yarinyar babu wani haƙƙinku tada tauye zaluncine kawai irin na mutum mai ƙafa biyu,sannan dazaku raɓeta to zata zamto muku katangar sugari zata zamo alkhairi gareku".
Kallo-kallo Hajara da Adda Barira suka shiga aikawa junansu kafin Hajara tace"Malam dan Allah ba wannan ne ya kawo muba mudai ayi yanda mukace inkuma kanaga bazaka iya bane saika faɗa mana munema wani".ta faɗa cikin sakewa da aikin Boka Iro.
Wani kallon daya watso mata da rikiɗaɗɗun idanunsa yasa hanjin cikinta haɗawa"Ta gama ƙona aljanin damuka tura mata da ayoyin Allah,kuma ta kasance tana yawaita zama da alwala zaiyi wuya aikin dazamuyi ya cita domin mijinnatan ma ba haka kawai ya zauna akan cikinba yana addu'o'i".
"Allah gafarta malam yanzu meye abunyi?"tambayar da Adda ta jefa masa tana tsaida ƙwayar idonta akansa domin jin amsarta.
Ƙasar dake gabansa ya shiga bugawa yaɗau lokaci ahaka kana yace"babu abunda zai gagara kunkawo kukanku inda za'a share muku hawaye,cikin zai zube kamar yanda kuka buƙata kuma ita da haihuwa saidai ta gani awani wajen anayi,amma kuma ana buƙatar azubda jini ga aljanu domin aga biyan buƙata".
"To malam godiya mukeyi zakaga aike in sha Allah"cewar Adda.
Tsawar daya daka mata yasata rikicewa yace"ki kiyaye bakinki ba'a ƙira mana Allah anan".
"Zan kiyaye".
Tashi sukayi muka tafi suna ayyana inda zasu samo kuɗin abin yankan da Boka Iro ya faɗa,kowa tayi gidanta.
Tun dana sama cikinnan nake samun kulawar Granny da duk wani masoyin Habib yayi farin-ciki da hakan,Sosai na dage da addu'a gami da sallan dare har wani makarantar almajirai dake kusa da makarantarmu naba wasu sadaka nace suna tayani da addu'a.
Ranan nadawo daga makaranta a gajiye ga wani azababben yunwar dana kwaso,ina shiga nayi wanka nayi salla sannan na fito zan shiga kitchen,hakan yayi dai-dai da turo ƙofar falon da Hajja tayi ganin wacce ke biye da ita yasa na ruga aguje na rungumeta tsam a jikina inacewa"Anty Amina yaushe kikazo ya akayi kika gane gidan?".
Sai data rabani da jikinta kafin tace"kin mantane kin taɓa min kwatance gidansu Habib nan naje aka haɗoni da driver yakawoni,danazo bakyanan shine na zauna awajen Hajja".
Riƙo hannunta nayi muka zauna sannan naje na ɗauko mata ruwa da abun taɓawa gaisheta nayi ta amsa,sannan nashiga yiwa Hajja bayanin wacece Anty Amina a gareni.
Nan mukayi hirarmu sosai sosai hadda Hajja sai yamma lilis sannan Anty Amina tafara shirin komawa daura,Habib na ƙira awaya na sanar dashi zuwarta inzai sama dama yazo su gaisa kafin ta tafi ya shaida mini dazai zo ɗin.
Muna zaune a falon nida Anty Amina izuwa lokacin Hajja ta tashi takoma sashinta,Anty Amina tace"Hibba yanzu dai ina fatan babu wata matsalar ko?".
Sai dana numfasa kafin nace"Anty Amina yanzu nema nake cikin babbar matsala dan samun cikin nan danayi ji nake kamar shi zai zamto dalilin yankewa farin-cikin rayuwata gabaɗaya".
Saurin katse ni Anty Amina tayi ta hanyar faɗin"Subhananlahi!mekike faɗi haka Hibba?ki zamto mai kyautata zato akan komai sannan ki dogara da Allah kinji?"Kaina kawai na gyaɗa mata ina mai sunkuyar da kaina ƙasa zuciyata cike take da fargaba acikin kwanakin nan danji nake ina dab da rasa duk wani farin-cikina.
Ƙara shigowar motar Habib danaji ya sanyani ɗago kaina bai ɗau lokaci ba ya turo ƙofar falon ya shigo yayin Anty Amina ke gyara mayafin dake jikinta tana ƙara lulluɓe jikinta dashi.
A ƙasa ya zauna irin zaman kan yatsun ƙafa yana gaida Anty Amina ta amsa tana ƙara tayashi murnar ƙaruwar damuka samu tare da addu'ar Allah yakawu masu albarka,da Amin ya amsa mata dashi.Sannan ta miƙe muna ƙarayin sallama da ita har harabar gidan muka rakota na rakata ta shiga sashin Hajja ta mata sallama.
Goma sha tara ta arziki Habib yayiwa Anty Amina sannan yasa Driver yakita har gida tare da mata alƙawarin shima zai kawoni cikin kwanakin nan kafin nayi nauyi.
Sai mukaga ficewarsu daga cikin gidan sannan muka koma ciki,ƙirar sallan magrib da aka farayi yasa Habib fita masallaci kamar kullum sai da akayi sallan isha'i sannan ya dawo.
Bayan munci abincin daya sayo mana dan bana iya yin girki muka kwanta,ciki baccin dayaci ƙarfina na farajiyo Muryar Habib a hankali na fara ware idanuna da ba komai acikinsu face bacci,Akan sallaya na hangoshi ya ɗaga hannayensa dukka sama bayan ikirarin danaji yana zubowa Ubangijin talikai ya ɗaura da faɗin"Ya Allah kaine ka bani farin-ciki a lokacin daban tsammata ba,Ya Allah ka ɗaurar dashi acikin sauran kwanakin dasuka ragemini a cikin duniya,ka azurta mu da samu ƴaƴa na gari wanda addinin musulumci zaiyi alfahari dasu dan girman zatikan ka tsawaita rayuwata a duniya nima naga jinina".
Yana kawowa nan addu'ar yashafa komawa nayi na kwanta lamau yayin danaji wani kibiyar tausayinsa ta harɓi zuciyata har ta sama damar tarwatsata.
Ban rutsa ba sai wajajen ƙarfe uku Habib dazai fita masallaci ya tadani nayi salla.
Sannan na shiga kitchen na harɗa mana breakfast tea ne kawai sai irish potatoe dana soya mana,ina jeresu akan dinning Habib ya shigo lokacin har gari ya fara haske da hanzari ya iso gareni tare da karɓan flask ɗin tea ɗin take hannuna ya ajiye yana cewa"Haba!bana hanaki wannan aikin ba meyasa baki bari na dawo nayi ba?".
Shagwaɓe fuskana nayi kana nace"Kawai nagaji da zaman ne shine nayi".
"To banaso kina wahalar mini da Baby,wai yaushe zaki fara zuba awo ne?"yafaɗa yana ɗaura hannunsa a ƙasan marata dan lokacin cikin ya fara fitowa.
Sai dana ɗaga kaina kamar wacce ke tinanin wani abun kafin nace"jiya dai Anty Amina tacemin wani sati ya kamata na fara zuwa tunda yayi sati ashirin da uku yanzu".
"Allah yanuna mana"ya faɗa na amsa da Amin sannan muka zauna cin abinci nace"Hamma sunan wa zakasa in aka haifa cikin nan?".
Murmusawa yayi yana sipping tea ɗin dake hannunsa yace"In macece zansa sunan mahaifiyata Zainab kenan,inkuma namijine zansa masa sunan Abbanki".
Dariya nasa mai sauti nace"Allah ya kawosu lafiya"yace"Amin".
Da haka muka gamacin abincin muka kimtsa wajen,sannan kowa yayi ɗakinsa yafaɗa bathroom shiryawa nayi cikin ɗanye les mai launin ruwar hoda ɗinki rigar bubace mai faɗi wanda najini nasake sosai acikinta,haka nan nabar fuskata daga lip gloss sai ɗan hodan dana murza na lulluɓa mayafita na ɗauki wayata na fito bayan naɗan murza ƴar humrata dan bana saka turare inzan fita,tun nadaji malamai nacewa haramune sanya turare ga ƴa mace yayin fita.
Ganin Habib bai fitoba yana nazauna a falon ina jiran fitowarsa,ban jima da zama ba ya fito cikin shigar manyan kaya kamar yanda ya saba farar shaddace sol!tsayin rigar ya tsaya dai-dai gwiwarsa gajeren hannun gareta sai kuma hular kansa mai launin ruwan ƙasa tunin falon ya cika da ƙanshin turarensa na Laylatul sahara.
Hannuna na ɗaga masa alamar yayi kyau ina kashe masa ido ɗaya,da murmushi ɗauke fal!akan yalwataccen fuskarsa ya nufo ni ya riko ni yayi muka fita domin zuwa asibitin bada taimako.
Sai dana shiga sashin Hajja na mata sallama sannan muka tafi,Asibitin farko damuka fara zuwa asibitin gwanatine dake cikin garin funtua sosai Habib ya ware bakin aljihunsa yana bada taimaki ga marasa lafiyan dake kwance a asibiti,wata mata data kuka akancewa kwanan ta biyar a asibitin tare da ƴarta dake naƙuta har ɗan yamutu acikin cikinta amma a waje suke kwana saboda ƙarancin ishashshun gadaje a asibitin.Da taimakon Habib likitan ya rubata mata resing zuwa wani asitibin na kuɗi yayin da Habib ya ɗauki nauyinsu.
Tunda muka baro asibitin nake ƙara godewa Allah akan ni'imar lafiya daya bamu,har muka isa gida ranar Habib zaije office ba tare muka wuni dashi cikin unguwa kawai suka fita tare da Malam Idi suka ƙara raba kayan abinci ga gajiyayyun cikin unguwa saboda watan azumin ramadana da yake gabatowa a wannan lokacin.
Tunda muka dawo daga asibitin gabana yake faɗuwa narasa dalili yayin da zuciya take rayamini cewar wannan farin-cikin danakeyi ayau kamar shine ƙarshe a rayuwata saurin kawar da wannan mummunar hasashe na zuciyata nayi. har Habib yadawo ya same ni a haka komai a suƙure nake aikata shi inajin yanda gabana yake tsinkewa kamar wani mummunar abu na dab da faru dani.
Koda Habib ya tambaye ni cemasa nayi gajiyace kawai,haka mukayi dinner na wuce ɗaki nabar Habib a falo yana aiki a laptop ɗinsa tsananin fargabar da zuciyata take ciki ranar yasa na kwanta ba tare danayi alwala kamar yanda nasaba kullum ba.
Cikin baccin daya fara saɗɗata nayi mafarkin wai cikin dake jikina ya zube,firgigi na farka ina toshe bakina saboda ihun danaji na shirin kubce mini ba shiri sannan na shiga karanto addu'o'in neman tsari.
Yunƙurowa nayi zan tashi najini cikin jini tsamo-tsamo bedsheet ɗin gadon yajiƙe jaƙaf yazama jajir nan fa naji wani azababben ciwon mara da ciki da kuma baya ya karyo mini,dam!na faɗu daga kan gadon nahau juye-juye a ƙasan wanda har izuwa yanzu jini bai bar zuba daga jikina ba.
Numfashina na fuzga da ƙarfi da nufin kwalawa Habib ƙira sai kuma naji kamar an ɗaure min maƙoshina,irin azaban danakeji a jikina na gama saddaƙarwa ajalinane ya riske ni,kofin dake ajiye akan site drawer na jawo na dugashi da kan tile's dake malale ko'ina a ɗakin.
Jiyo ƙarar fashewar kofin yasa Habib shigowa ɗakin da hanzari yana ƙiran sunana ganina dayayi cikin halin danake ciki yasa ya nufo a matuƙar gigice.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________
Page 3⃣6⃣
Ɗago kaina yayi lokacin har nafita hayyacina ya ɗaukeni ya fito muka nufi mota zaburar motar yayi da ƙarfi yayin da Malam Idi ya fito buɗe masa gate ɗin yana tambayar lafiya?ya faɗa masa abunda ya faru.
"Subhananlahi!ai kuwa dai bari na taso Hajja ku tafi tare da ita"cewar Malam Idi yana nufar sashin nasu har daɗan gudunsa,sannan suka dawo tare da Hajja tashiga motar muka tafi.
Koda muka isa asibitin Emergency aka shiga dani ɗakin ƴan ɓari,wankin ciki akami sannan aka ƙara mini jini leda uku sakamakon jinin danayi asararsa kafin zuwarmu.
Lokacin da likitan yake shaidawa Habib batun zubewar cikin ba ƙaramin tashin hankali ya faɗa ba,ganin kamar shima ɗin yana buƙatar kulawar likitocin yasanya Hajja ƙiran Malam Idi ta sanar dashi,ta gidan su Ummi ya biya ya sanar dasu sannan suka garzayo asibitin dukkansu.
Ganin su Ummi yasa Habib saurin miƙewa ya nufesu yana faɗawa jikin Ummi kamar jira yakeyi ai kuwa nan yasaki kukan dake ƙasan maƙoshinsa.
"Habib kasama kanka nutsuwa kasani ba wayonku ko kuma dabararku ne A'a Allahn daya baku shi zai ƙara baku".Daddy ya faɗa yana ɗago Habib ɗin daga jikin Ummi,sannan suka ƙarisa suka zauna.
Tunda mukaje bansan waye akaina ba haka nan na daɗe dabarin cikin hayyacina tun lokacin da akamin wankin ciki,sanyin asubar da'ake busawa shiya sanyani wangale idanuna dasuka kumbura tsimtim.
Robar jinin dake saƙale a hannuna na fara kai kallona gareshi,kafin nafara ƙarewa mutanen dake cikin ɗakin kallo.Yasira ce ta fara lura dana tashi ta matso kusa dani tanamini sannu,sannan Ummi ma dake kan sallaya tataso ta fara jero nata sannun sai kuma Hajja itama ta ɗaura danata.
Dai-dai lokacin da Habib da Daddy suka dawo daga masallacin dasuje domin gabatar da sallan asuba,da sauri suka iso gareni Daddy yana cewa"Hajiya ta farka kenan"Ummi tace"E yanzu ta tashi".
Tsuguwana Habib yayi ya zuba gwiwoyinsa a ƙasa sannan ya riƙo ɗayan hannuna saboda ɗayan har yanzu jinin bai ƙareba balle acire mini shi.
"Hibba kinga wani ikon Allahn ko?munata farin-ciki sai kuma Allah ya zartar da hukuncinsa,dole mu karɓa ƙaddararmu hannu bibiyu Allah yabamu wasu masu albarka"duk ƴan ɗakin suka amsa da Amin.
Nikam kallo na tsuramasa cikin mamaki meyake nufi kenan babu ciki kome?daga nan kuma ban ƙara tantance abinda yake faɗaba sai dai ganin bakinsa yana cigaba da motsawa hakan ya tabbatar maganar yacigaba dayi.
Bana tausayin kaina a wannan lokacin kamar yanda nake tausayin Habib yanda ya ɗaura buri akan cikin nan daga shi har danginsa mussamman Granny.
Hawaye kawai nake fiddawa yana sauƙa har izuwa saman wuyata,Ummi da Hajja keta mini nasiha zuwa ƙarfe ɗayan rana su Inna da yaya Fawas sukazo daman tun daren jiya Daddy ya sanar da Baffa tare da Sayyid sukazo danshi ya taho dasu.
Ina ganin yaya Fawas hawayen dana keyi ya tsananta yunƙuruwa nayi na tashi yayin daya iso gareni shi kuka ni kuka haka nan ma Inna sai faɗin"Ya Allah ka dubi rayuwar wannan marainiyar ka haskaka matashi dan soyayyarka ga annabinka Muhammadu (S A W)"take su Ummi na amsawa da Amin.
Duk yanda naso nayi magana jinayi bakina yamin nauyi nakasa furta koda kalma ɗayace kuka kawai nakeyi kozanji sanyi a sashin ruhina danakejin kamar ana watsamini garwashin wuta.
Ganin irin kukan danakeyi yasanya Daddy yiwa likitan magana akamin allurar bacci,tare muka yini dasu a asibitin har Hajja bata koma gidaba malam Idi ne dai yakoma amma har Daddy nan ya wuni.
Zuwa yamma kuwa Granny da Iya suka iso ganinta yasanya Habib sakin wani kukan tamkar ƙaramin yaro lallashinsa ta shigayi saidai itama kanta kasa kashe wutar tausayin jikan natan mafi soyuwa agareta acikin zuciyarta,wanda hakan ya sabbabar da fitar hawaye daga idanunta.
Sai bayan isha'i sannan na farka da wani masifaffan ciwon jiki,Granny ta matso tana min sannu kaina kaɗai nake gyaɗa mata,sannan ta gabatar mini da abinci a wannan lokacin banacin koda ƙwayar shinkaface zata iya wuce daga maƙoƙaruna har ta iya zaman acikin cikina.
Ganin duk sunyo kaina yasa na ɗaure daɗan zuƙa tea