Showing 69001 words to 72000 words out of 104857 words
Chapter 24 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
mazauninsa nada.
Daddy yayi gyaran murya"Haƙiƙa rayuwa cike take da jarabawa,sannan dukkanin mu munyi imanin cewa ƙaddarar bawa bata wuce kan mai ita.mu kasa jure jarabawar da Allah ya jarabci Hibba dashi na lalura tsawon watanni har sai da Haƙurinmu ya gaza muka haɗasa aure da ƴar-uwarsa.Tabbas haƙuri nasara ce babba kuma duk wanda ya rungumeta baya taɓewa wannan alƙawarine na Allah,Hibba ta kasance daga cikin mutanen dasuka karɓa ƙaddararsu hannu bibiyu,har gashi yau taci ribar wannan haƙurin datayi ba kowacce mace bace tazayi halalcin da kikayi kin danne duk wani kishi yayin auren Habib da Yasira kuma bayan auren baki canza su daga matsayin dasuke a da ba hatta mu muma kina bamu girman mu madalla dake Hibba Allah yayi muku albarka".
Da Amin duk muka amsa dashi sannan Ummi ma ta ɗaura da nata nasiha haka nan ma Granny da Iya.
"Kar wannan jarabawar tasa kiyi fatali da tauhidin ki na kaɗaita Allah duk abunda ya sama bawa daga gareshi ne sannan kuma rubutacce ne daman tun fil-azal acikin ƙaddarar rayuwarsa,karki bari zuciyarki ta zargi kowa akan faruwar wannan alamarin kisani babu wanda ya isa ya miki abunda Allah bai miki ba"furcin Granny kenan wanda naji sun ƙara sanyaya mini sashin ruhina kuma ya wanke duk hashashen da zuciyata kemin akan sihirin da Iya tayi magana akai na ƙara kawar da tinanina akan cewa wani ne yamin hakan amma zamu ƙara tattaunawa da yaya Fawas.
Daddy dasu Habib suka fita masallaci domin sallan isha'i muma muka miƙe mukayi namu,ina zaune akan sallayata a ɗakin Ummi Yasira ta shigo kusa da inda na miƙe ƙafafuna ta zauna,tace"Anty kinga lamarin Allah ko?"kaina kawai na jinjina tacigaba dacewa"Wataƙil dasu Granny sunyi haƙuri har izuwa yanzu da Allah ya baki lafiya basu haɗa wannan aurenba".
Ƙwayar idona na tsayar akanta"Yasira meyasa kike irin wannan tinanin kamar bamai ilmin addini ba?,kinsan fa ƙaddara bata wuce lokacinta koda wannan lalurar data faɗa mini ko babu ita idan Allah ya ƙaddara zaman aure a tsakaninki da Habib babu makawa sai hakan ya faru".
Leɓɓanta ta fara motsawa alamar bakinta nason furta wani abun,nayi azamar kamo hannunta na riƙe gam!cikin nawa nace"Muci muci abinci duk mu suke jira".sannan muka jera muka fito Ummi da Sayyid suka tarar suna sauƙar da abinci suna ajiyewa akan babbar gardumar da aka shimfiɗa a wajen.muka ƙarisa muka tayasu sauƙarwa.
Nida Yasira mukayi serving ɗin kowa sannan muma muka zuba namu a plate ɗaya muka faraci,Sayyid ya kallomu ya saki murmushi ƙasa-ƙasa yana maida kansa da plate ɗin abincin dake gabansa.
Yasira ta ɗan harare sa tace"Faɗi karta kashe ka".
"Naga kun ware min ɗan-uwa a gefe kun zuba abincinku ku biyu,shi kuma shi ɗaya gaskiya wannan ba adalci bane".
Lokaci ɗaya muka bushe da dariya Habib kam murmushi kawai yasaka ya ɗauke kansa kamar yabajin abunda mukeyi.
Granny ta gyara zaman tanakai lomar wainar masan farar shinkafar daka ɗebo cikin bakinta tace"Nima dai haka nagani ana nuna masa wariyar launin fata ƙiri-ƙiri,mijina ai ba gata ka rasa ba bari nazo muci tare ina baka a baki".ta miƙe ta dawo kusa da Habib dariya mai sauti muka saka nida Yasira hadda Sayyid wannan lokacin har Ummi da Daddy da Iya sai da suka murmusa,ganin Granny ta zage tsakaninta da Allah ta ɗebo lomar tana bawa Habib a baki shi kuwa ya wani sha kunu yana taunar abincin kamar an masa dole.
"Lalle Hajiya kice yau ƙaunace ta motsa keda mijin nakin"furcin Ummi wanda yasa muka ɗan tsagaita da dariyar muka baza kunne don jin amsar Granny.
"Ke dai Habiba bari yo banda yaran zamani ma dame suka fimu soyayyar ko kuma kula da mijin?".Muka ƙara tuntsirewa da wata dariyar.
Da haka muka gama cin abincin cikin nishaɗi da tsantsar ƙaunar juna a matsayinmu na ahli guda,nida Yasira muka tattare wajen sannan muka dawo falo.
Granny kam da Iya ɗakunan su suka wuce,Daddy da Ummi ma basu daɗe ba suka tafi ɗaki bayan mun musu sai da safe.
Daga ni sai Yasira da Habib muke zaune a falon muna kallo wani series film ɗin da'ake haskawa a tashar Tauraruwa TV,Sayyid kuwa tunda aka ƙira wayarsa ya fice.
Sai danaga ƙarshen film ɗin sannan na tashi na kashe kayan kallon nayiwa Habib sai da safe na wuce ɗakin Yasira.
Koda daban juyoba jikina yabani irin kallon da Habib kebina dashi har kusan tuntuɓe da matattakala nayi.
Na wuce ɗaki wanka nayi koda na fito na iske Yasira ta shigo har ta kwanta,dan daman a gidan zamu kwana.na wuce gaban mirro ina murza mai sama-sama a jikina wayata ta hau ruri gabana ya faɗi ras!ina juyayin abunda zaisa Habib ƙirana cikin daren nan dan bamu fiye yin waya da daddare ba ko lokacin dayake neman aure na.
Na ɗauka tare da manna wayar a kunne na"Me kikeyi har Yanzu bakiyi bacci ba?".
"Wanka nayi yanzu nake shirin kwanciyar"nakai ƙarshen maganar ina ɗan zame wayar daga kunnena na duba agogo wanda yake nuni da ƙarfe shaɗaya da mintuna arba'in,lalle na daɗe a banɗakin maganar daya somayi yasa na maida wayar kunnena.
"Inason ganin ki yanzu please".
Na gyara ɗaurin towel ɗin dake jikina kana nace"Yanzu dare yayi fa sosai sannan ga Ummi dasu Granny ina kunyar suka fitana na shiga part ɗinka".ya katse ni dacewa"To ni bari nazo"kafin nace wani abun ya kashe wayar.
Zuciyata ta harba da ƙarfi na miƙe na ciro doguwar rigar bacci na nasaka,dan nasan tunda ya furta to babu makawa zai aikata inagama gamawa na ɗaura hijabi na akai sannan na ɗauka wayata na fito daga ɗakin.
Saɗaf-saɗaf nake tafiya ina duba inda zan jefa ƙafata dugun kar nayi wani ƙwaƙwƙwaran motsin da zai tashi wani.
Nazo dai-dai ƙofar fita daga falon naci an dafo kafaɗata ta baya,na juyo a firgice na zage iya ƙarfina zan ƙwala ihu naji an toshe mini baki na fara cikiniyar ƙwacewa.
"Matsoraciya kawai tsoro kamar farar kura"ya faɗa yana janye hannunsa daga kan bakina.
Na ɗan jefa masa harara ya tsareni da ido yace"Dakika fito ɗin ina zakije hmm watau anason abu ana kaiwa kasuwa".
Na ware idanuna akansa inajin haushin kaina dana fito lokaci guda kuwa kunya ta mamaye ni,narasa yaushe Habib ya zama haka.
"Muje mu zauna sai muyi maganar"ya faɗa yanayin gaba nabi bayansa izuwa cikin falon muka zauna akan kujerun dake fuskantar juna,haske farin wata d kuma walƙiyar da akayi wanda ke nuni da ruwan sama kan iya ɓarkewa a kowani lokaci yake hasko cikin falon,hakan ya bani damar kallon fuskarsa.
"Shine duk kukayi zamanku anan kuka bari ni ɗaya ko?".nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsun hannuna nace"Nazata Yasira zata kwana acan ɗinne shiyasa".
"To tashi mu tafi"nayi saurin cewa"mu tafi ina".
"Ɗakin mijinki mana".
"Baka kunyar Ummi ko wani gobe ya ganni ina fitowa daga part ɗinka,uwa uba ma Yasira".
Ya aiko min da wani irin kallo dana kasa gane manufarsa kafin yace"Shiyasa ai nazo da kaina dan nasan ke bazaki iya zuwa ba tashi mu tafi kawai malama".duk na daburce nafara waige-waigen ina duban hanya kar wani ya fito.
Naji ya rungumo ni yanacewa"Nima wasa nake miki kawai nazone naganki rabin raina domin nayi bacci mai daɗi,ku shirya cikin satin nan zamuje Nijar in sha Allah".
"Baka sha maganinka ba bari na ɗauko maka,sai na taso maka Yasira itama ku gana".na faɗa ina rabashi da jikina har nakai ƙofa naji ya kuma riƙo hannuna najuyo ya marairaice fuska yace"Inasonki matata sonki yaabi dukkan sassan jikina Allah ya muku albarka".Sosai naji daɗin kalamansa nace"Amin rajlun amin"sannan nawuce ɗauko masa maganin inata juyayin canzarwa Habib lokaci guda dan ko mace bata fishi kunya ba rashin kunyarsa sai mun shiga ɗaki mun rufe ƙofa.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________
Page 4⃣6⃣
Maganinsa na ɗauko sannan na fara tashin Yasira,duk yanda nake bubbuga pillown da ƙiran sunan ta kasa tashi tayi,dan bacci yaci ƙarfinta sosai haka na fito na sanar dashi sannan na bashi maganinsa yasha muka yiwa juna sai da safe.
Ranar har kusan sha ɗayan dare muna chart dashi,sosai na sake ina maida masa da kalaman soyayyar dake mini,haka kuwa na kwana raina fes da soyayyar JIGONA.
Washe gari da wuri muka tashi muka haɗa breakfast kasancewar Daddy zaiyi tafiya,muka gama muka jeresu a dinnig.
Munacin abincin Habib ke sanar da Daddy tafiyar dazamuyi zuwa ƙasar nijar.
"Lalle ka kyauta dan kuwa daman suna ƙorafin cewa baka kai musu ziyara,kaga kuwa yanzu sai ka ɗeba matanka kuje dasu".
Granny ta ɗaura da nata"Ka gaishe su sosai inkunje don Allah".yace"In sha Allah Hajiyata yau baza abani abincin bane?".
Ta ɗan harare shi kana tace"yau kuma banyi niyya ba ai ga matanka nan suka baka".
Muka sa dariya Sayyid yace"Yau kuma keda mai gidan nakin".
Muka tashi muka raka Daddy compound ya tafi su Granny ma ayau ɗin zasu koma damaturu,muma haka nan yau naji Daddy dazai tafi yana cewa Ummi ta tabbatar mun koma ɗakunan mu.
Tun taran safe su Granny suka tafi muma maka fara namu shirin Ummi ta haɗa min tsumi masu kyau da wasu turarurruka ma'abota kamshi.nayi godiya sannan muka tafi,duk muka watse muka barta daga ita sai Sayyid dan sunyi hutu a makaranta.
Muna isana wuce part ɗin Hajja nasanar da ita komai,tsabar murna har sujudul shukr sai datayi.
Da dare kuwa muna zaune duk a falo Habib ke sanar damu jibi ne tafiyarmu,bakina ya kasa rufuwa dan murna a dangin mahaifiyarsa Goggo Suwaiba mahaifiyar Batul ita kaɗai na sani sai kuma wasu siraru.Yace gobe zamuje gano muyiwa su Baffa sallama.
Washe gari kuwa tun ƙarfe bakwai muna Hanyar Kano sosai muke tsala gudu muka isa kuwa da wuri.
Tun a ƙofa na hango Baffa yana tsaye ya tare ƙofar da hannunsa yana bawa Hajara baki gami da haƙuri.
"Malam kasan Allah yau a gidanmu zan kwana,ko ce mata akayi banda gata ne?"furcin Hajara kenan danajisu a kunnuwana yayin danake fitowa daga cikin motar na maida murfin ƙofar na rufe.
Zuciyata ta buga da wani mungun ƙarfi a sanyaye na iso garesu,sai a sannan Baffa ya lura da zuwanmu ya washe baki"A'a Mamana kune tafe?"sannan ya maida idanunsa ga Hajara"Ke kuma ki wuce ciki inna shigo zamu ƙarishe maganar".ta saki wani tsaki mai dogon zango kama tayi ciki.
Nida Yasira muka tsuguna muka gaishe shi ya amsa sannan Habib ma ya rusuna ya gaida shi sunayin musabaha,idanuna suka garwaya cikin na Habib nana take naji hawaye sun zomin da kuma kunyar yanayin damukazo muka iske Baffa da Hajara suna jayayya har a bakin titi.
Nayi wuf na shige cikin gidan Yasira ta rufa min baya,Inna muka tarar tana zaune a tsakar gidan tanacin ɗumamen tuwo,tamiƙe ta tarbemu da fara'arta.idanuna suka sauƙa akan Hajara data garƙame ƙofar ɗakinta tana tsaye da gana must go ɗin kayanta tana ta faman huci da kaɗa ƙudu.
Na sauƙe ajiyan zuciya dai-dai nan Baffa da Habib suka shigo muka tashi muba basu tabarman suka zauna yayin da muka ɗauko kujerun zaman tsakar gida irin na katako muka zaune,nan aka shiga sabon gaisuwa.
Habib ya sanar dasu dalilin zuwar mu,Inna tayi tamana fatan sauƙa lafiya Baffa kam na lura duk hankalinsa ba'a jikinsa yakeba yanaga Hajara da izuwa yanzu take sakin ƙwafa.
Habib ya fita saboda ƙiran zuhr da aka farayi yana fita yara suka fara shigowa da kayan abincin daya siyowa su Inna,aka fakesu a tsakar gidan Inna ta shiga sa masa albarka.
Sannan muma muka tashi domin yin sallan,Yasira ta ɗauki buta ta shiga bayi hakan ya bani damar faɗin abindake raina ga Inna"Inna nikam meyake faruwa ne acikin gidan nan?".
Ta gyara ɗaurin zaninta tace"kedai bari Hibbatu yo mezai faru kuwa banda abunda wannan baƙar makirar nan Hajara keson kitsawa a gidan nan,tun asuba ta hanamu bacci wai sai ya saketa dayake bata ganin mutuncin kowa shima kuma ban isa in faɗa masa yaji ba in sha Allah duk mungun nufinki akanki zai juye".
"Idan kin isa da ɗan naki a yau ba sai gobe ba kisa shi ya sauwaƙe min,domin nima ina son naga jinina a duniya na gaji da zama da juya"
Martanin Hajara kenan dasuka sanya Inna ƙara harzuƙa ta miƙe "Daɗin abun ma dai kafin ke ya auri wata matar kuma har ta haihu Allah ne yayi ikonsa ɗan baizo da rai ba,idan ba ƙaddara ba mai zaisa Adamu zama dake ƙarƙashi inuwar aure wallahi kinacin sa'ar mahaifiyarkine Laminde daba wannan batun yanzu akeyi ba".
Nan suka fara maidawa junan su magana da nasan haka ne zaifaru dan ban fara tarar Inna da maganar ba daman nasanta da gajen haƙuri.
Hayaniyarsu yasa Yasira fitowa daga banɗaki muka fara basu baki,sannan muka ja Inna muka shigar ɗaki.
"Inna dan girman Allah ki daina biye mata,ai ko ba komai gaba kike da ita haka nan ma zurfin tinanin da shekarunki ya ɗara nata".
Yasira ta amsa da"Haka ne Inna sai ana kai zuciya nisa".na ɗaura da faɗin"bari naje na haɗa miki ruwan wanka sai kiyi sallan".
Har na kawo nan Inna bata tanka mana ba illa fucin datakeyi kamar saniya zatakai bugu,ga kuma wani uban zuffan datake haɗawa.
Na fice na haɗa mata ruwan wanka sannan tafi izuwa banɗakin,fitanta daga ɗakin yabani damar sakin kukan dake nuƙurƙusan raina danaji zuciyata na mini soya sosai yayin danaji maganganun da Hajara ta yaɓa min lokacin danake ɗibarwa Inna ruwan wanka suna dawowa kunnuwana
"Bi'izinillahi ta'ala haka zaki ƙare raguwar rayuwarki cikin ƙunci da baƙin-ciki.mijin dakike taƙama dashi ɗinma sai ya juya miki baya sai kin ƙwanmace kiɗi da karatu".
Maganganunta sun taɓa mini rai sosai sannan sunsa na zubda hawaye idaniya,tabbas na daɗe da sanin Hajara bata daga cikin jerin masu ƙaunar ta a duniyar nan amma banyi zaton ƙiyayyar takai har ta fito min da ita a fili haka ba.
Yasira ta fada kafaɗata tana bani baki duk da batasan dalilin kukan nawan ba.
Jin fitowar Inna daga banɗaki yasani share fuskana,nafito na ɗauki buta nayi alwala na dawo nayi sallah.
Naji duk na ƙagu mu tafi dan zaman gidan ya ishe ni,bamu sama zama da Inna ba amma a tsaitsaye na sanar da ita jinin dake zuba min nasama sauƙin shi,tace Yaya Fawas ya sanar da ita tashin Hankalin danazo na samesu aciki shi yasa ta sha'afa da batun tamin murna sosai.
Ta jikin labule na hango inuwar Hajara ta nama laɓe tana sauraron abunda muke zantawa,maganar danake sanar da Inna yasa Hajara kusan faɗuwa a ƙas.
Har sai datayi bol da kwanukan silbobin dake ƙofar ɗakin,batare data saniba tsabar kaɗuwa.
Inna ma data lura da hakan ta ɗaga murna tana faɗin"Allah mun gode maka da kawowa marainiya sauƙi daga ƙunci dake ciki,ƴan baƙin ciki kuma sai a mutu".
"Allah ya kyauta"na faɗa cikin raina.
Munayi Asr kuwa muka fito zamu tafi bamuga Hajara a inda muka barta ba ,Inna ta rakomu ƙofar gida muka tafi.
Koda muka hau titi Habib ya tambaye ni dalilin sauyawa nace masa gajiyace kawai.
Muna isa namusu sai da safe nawuce part ɗin wanka kawai nayi nayi salla na kwanta raina a cunkushe.
Washe gari Ranar dazamu tafi kuwa tun safe muka gama shirinmu mukayiwa Hajja sallama sannan muka biya wajen Ummi itama muka mata sallama.
*ƘASAR NIJER*cikin jahar maraɗi muka dosa tun sauƙarmu a airport aka turo mana driver ya kwashe mu,tun kafin mukai ga shiga cikin gidan manya hatimin sarauta da kuma zane irin na gidan masauta da aka ƙawata ginin dashi ya fara ɗaukar idona.
Aka buɗe mana makeken gate baƙi wuluƙ muka shiga hadimai ne keta safa da marwa a harabar gidan.
Babbane gidan dan duk yanda na baza idanuna ban gano ƙarshen saba.ginin gidan irin na daɗe da ake yinsu da jar ƙasa gefe guda kuwa wasu bukkukine guda huɗu dake fuskantar juna an kewayesu da korayen flower gwanin ban sha'awa.
Girman gidan ya tabbatar min da family house ne,saboda yawan part-part dake gidan.
Wanda ya ɗauko mu daga airpot ya ɗeba akwatinmu yayi gaba dashi muna biye dashi.
Sai da muka ƙetare faloli manya-manya guda uka sannan a na huɗun muke iske jama'ar gidan.
Wata farar mata da shekarunta zaizo kusan dai-dai dana Inna sai dai hutu da kwanciyar hankalin datake ciki sun hana,shekarunta bayyana a fuskarta,ita ta fara miƙewa.tanada jiki da kuma tsayi a haɗe sannan launin fatarta fari sosai mai irin ja haka.
Ta washe baki ta shiga zubo kirari ga Habib"Lalle maraba da Babban mutum dattijon arziki ubanmu maganin kukanmu,Habibu ɗa ga Abubakar da Zainaba Allah ya jiƙan rai,mai farar aniya yakuwar kan kabari baƙin cikin masu taushi matsu kusa daji ɗuminka".
Ya tako a hankali ya isa gabanta tare da rusunawa ta zame hularsa daga kansa ta dafa kansa.
Muma muka ƙarisa cikin dandamalin falon muka fara ɗibar gaisuwa ga baffanisa da sauran ƴan -uwa.tabbas Habib ɗan dangine dan duk girman falon mutane ne keta wulgawa tako ko'ina.
Wannan dattijuwar matar danaji Yasira ta raɗa min cewa sunan ta Goggo Hanne sannan itace babba a zuriiyartasu,ta kalloni kallo ɗaƴa dana mata nagano izza da kuma ƙasaita da mulkin dake bin jinin jikinta dan ko magana zatayi sai sun bayyana.
"Kece Hibbar ko?"na ɗaga mata kaina sannan ta ɗaura"Tabbas na samu labarin gwagwarmayar da Ubana yasha kafin yasama aurenki,ban hallata bikin ba sakamakon lokacin ina ƙasa mai tsarki ina gudanar da aikin hajji".
Falon yayi tsif ita kaɗai ake saurara"Wannan gidan namu yanada tarihi babba a duk ƙasar nijer dan babu gidan sarautar daya ɗara namu a wancan lokacin,kakanmu nawajen uba shi yayi mulki da yayi murabus aka ɗaura wan mahaifinmu wanda har izuwa yanzu zuriyarmu ce ke mulki.Mu goma iyayen mu suka haifa nice babba sai mai bimin Isma'il sai Salamatu,Hadiza,Suwaila,Hayatuddeeni,Suwaiba,Lawisa,Jamila sai kuma autarmu Zainaba.Allah ya azurta mu da yawa dan duk cikin mu inkika cire Suwaiba da Zainaba sune kawai masu ƴaƴa ɗaɗɗaya amma dukkamu babu mai ƴaƴa ƙasa da goma,Sannan a tsarin gidanmu bama auren bare Zainaba ce kawai ta auri wanda ba ɗan zuriyarmu ba ɗan wata ƙabila can daban sannan ta buɗewa ƴan baya ƙofar yin hakan."ta kai ƙarshen maganar tana ɗan tsuke fuskarta.
Adda Suwaila ta umarci ƴan matan dasu kaimu ɗaki mu huta kafin lokacin cin abinci yayi muka miƙe muna biye dasu a baya,ban sani ba ko ni kaɗai na lura da irin kallon da Adda Suwaiba mahaifiyar Batul kemin koko sauran jama'ar dake falon suma sun lura da hakan?.
Irin kallon nan mai cike da ƙasƙanci dakuma son tabbatar min dacewa ni ba kowa bace,na kawar da kaina muka fice daga falon.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________
Page 4⃣7⃣
Farida ƴar Goggo Hanne da