Showing 27001 words to 30000 words out of 110913 words

Chapter 10 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

da kwanonshi a gidan nan. Ni lokacin bana nan don sana'ar mu ce kai shanu kudu ni da Ummaru, kuma in mun tafi muna jimawa ba mu waiwayi gida ba sai mun sayar da shanun da muka kai tas! A kan hanyar Umaru ta dawowa ya yi hatsari sai gawarsa aka kawo wa mahaifiyarsa, a lokacin ba a jima da ba shi sarkin Fulanin Girei ba.
Har gobe cikin mu babu wanda ya san abin da ya shiga tsakanin matar Umaru da Adda Rahin, bayan rasuwar Umaru ta hada komai nata da na yarinyar nan ta yi asubanci ta bar Girei. Matar Umaru kuma mai suna Kulu ta hada bakidaya shanun Umaru ta sayar ta kulle kudin ta bar garin nan kafin dawowa ta, don haka Rahin da jikanyar ta ba su karbi gadon Umaru ko kwandala ba. Kulu ta san makarkashiyar da ta yi mata ta korata inda har yau ba wanda ya kara ganinta cikinmu, don kawai ta wawashe gado ita kadai.
Bayan na dawo matata Dudu ta gaya min abin da suke zargi, cewa Kulu ta yi wa Adda Rahin barazanar kashe jikanyarta Rahinatu muddin ba ta bar Girei ba. Don dai ta cinye gado ita kadai. Ta sayar da komai na Umaru ta gudu cikin dare ba tare da sanin kowa ba.
Damuwar mu a lokacin ba ta ina Kulu ta tafi da dukiya ba ne ko dukiyar da ta handame sai ta ina Adda da Rahinatu suka fada?
Mun yi neman duniya ba mu same su ba. Abin kamar hadin baki, shi ma Usman bai kara zuwa ba tunda ya tafi Karatu Zaria.
In takaice muku zance, Usman bai waiwayi gida ba sai bayan shekaru biyar da barin Rahin Girei, a lokacin babu wayar tarho, san da ya dawo ya gama karatu har ya samu aiki a Kaduna.
Da ya dawo ya tadda tashin hankalin da muke ciki na mutuwar dan uwansa, da rashin sanin inda mahaifiyar su Rahin da Rahinatu suka fada.
Gari-gari haka muka dinga yawo neman su Rahin, ni da Usmanu, a lokacin babu kafafen yada labarai ban da radio duk wani gari da yake makwabtaka da mu mun je mun bincika ba mu same su ba.
Fadin halin da Usman ya samu kansa a ciki a wancan lokacin ba zai yiwu ba, don gara mutuwar iyaye a kan batansu da ransu. A karshe dole Usman ya koma Kaduna ya ci gaba da aikinsa, amma akai-akai yana zuwa muna kara bincikawa Allah bai sa an dace ba.
A shekaru biyu da suka gabata ne wani dan garin nan ya zo mana da labarin ya ga Rahin a cikin Adamawa a kasuwa, ko kafin ya yi mata magana ta bace masa.
Don haka na gaya wa Usman, wanda a halin yau ya zama babban ma'aikaci a gwamnatin tarayyah, ni kuma an jima da maida sarautar Modibbo Umaru a kaina. Wato dai ni ne sarkin Fulanin Girei tsayin shekarun nan bayan rasuwar Modibbo Ummaru.
Usman ya zo muka durfafi cikin Adamawa cike da bakin cikin ashe duk wahalhalun nan da muke sha wajen neman su Rahin ashe ba nisa ta yi ba, don dai bawa ba ya hada sani da UbangijinSa ne. Kasancewar zuwa lokacin an samu ci gaban zamani mun kai hotunan Rahin kafafen yada labarai na Adamawa, mun saka cigiya musamman a talbijin. Kuma ba a fi sati biyu ana cigiyar ba wani likita daga asibitin jihar Adamawa ya bayyana kansa a matsayin wanda tsohuwa Rahin ta mutu a hannunsa a dalilin cutar ciwon zuciya na farad daya. Ya bada dukkan shaidun da suka tabbatar mana cewa Rahin ce.
Daga nan ne muka yi ta bibiya har muka samo muhallin ta, makwabtanta sun tabbatar mana cewa ta rasun, kuma tana da jika budurwa wadda aka biya wa karatu a kasar waje ta tafi shekara guda kenan da tafiyar tata a lokacin binciken namu. Amma su basu san kowacce kasa ce ba.
Yau Allah cikin ikonsa ga Rahinatu ta dawo gidan su da kafafunta. Zan so ganin murmushin da zai bayyana a fatar bakin Usmanu, don haka tunda kun zo da mota, gobe in Allah ya kai mu za mu yi asubanci zuwa Kaduna, in sada Rahinatu ga Babanta Usmanu".
Raheenah ba ta san sanda ta karasa gaban dattijon ta rike kafafunsa tana kukan farin ciki ba. Yafendo da Nene sai kabbara suke yi suna gode wa Allah tare da yi wa Daada Rahin addu'ar neman rahma da gafarar Ubangiji.
Kafin su kwanta sai da Nene ta kira Ambasada ta gaya masa duk halin da ake ciki, cikin farin ciki ya ce shi ma zai same su a Kadunan don gobe zai baro Abuja, da sun shiga Kaduna ta shaida masa don za su tsaya a can su jira isowarsu.
A daren duk 'ya'yan Sarkin Fulani da ke gidan aure sai da iyayensu mata suka aika musu suka zo suka ga Raheenah duk da cewa dare ya yi. Nene ta yi alkawarin dawo musu da Raheenah in sun sake zuwa karshen shekara, idan kuma ta gama karatunta bakidaya za ta dawo Girei bakidaya ko wajen kanin Baban nata.
Godiya da fatan alkhairi gami da shi albarka su Yafendo sun sha shi daga Sarkin Fulani da iyalin sa, washegari bayan sun yi wanka sun karya kumallo daga tukwanensu Dudu suka kama hanyar Kaduna tare da Sarkin Fulani a gaban mota da babban dan sa Ilyasu.
Tun a hanya ya sanar da Alhaji Usman cewa ga su nan tafe tare da diyar Modibbo Ummaru ta hannun Adda Rahin, wadda aka ce ta tafi karatu ketare. A lokacin Alhaji Usman yana Abuja, amma haka ya ajiye duk ayyukan da ke gaban sa ya taho Kaduna a safiyar don su yi taho mu gama, ya kuma sanar da matar sa cewa ta shirya musu kyakkyawar tarba ta musamman.
Suna shiga Kaduna Nene ta kira Ambasada ta gaya masa, ya ce ai su tuni suna cikin kaduna suna jiran su, Ilyasu ne ya bai wa Nene lambar Alhaji Usman ta tura wa Ambasada don haka Alhajin da kan sa ya kwatanta wa direban Ambasada gidan sa wanda ke unguwar Sarki.

Alhaji Usman Girei na tsaye a kofar tankareren gidan sa yana jiran isowarsu. A gefensa babban dansa ne Musaddiq dan kimanin shekaru goma sha biyar. Suna fitowa daga mota Alhaji Usman na karasowa, burin sa kawai ya dora idanun sa a kan diyar dan uwansa.
Raheenah na fitowa daga mota ta gane shi ne Alhaji Usman kani ga mahaifin da ba ta taba sani ba. Ya buda mata hannuwa ta tafi da sauri ta shige, Nene sai da ta ji hawayen tausayi da farin ciki ya cika idanunta.
Daidai lokacin da motar su Ambasada ta iso, suka jira har direban sa yayi parking ya bude masa mota ya fito, sannan Alhaji Usman yayi musu jagora zuwa babban falon sa, tarba ta girma da karamci sun ganta gun iyalin Alh. Usman, bayan an gaggaisa Sarkin Fulani ya sake maimaita labarin da ya basu a Girei, Ambasada kuma ya dora nasa na yadda aka yi Raheenah ta zo hannunsa a kasar Jamus.
A lokacin maidakin Alhaji Usman ta fita, tana kitchen tana hada-hadar hada abincin alfarmar da ta tanadarwa bakin nasu. Don haka bata ji labarin da Ambasada ya bayar ba. Amma ta san yar Yayan sa ce mai rasuwa data tafi karatu ketare aka kawo masa. Wadda ta dade tana jin labarin batan su a bakin sa tare da mahaiyar sa.
Hatta auren Raheenah da Habibu sai da Daddy ya labarta masa komai da yadda auren ya kare. Abinda ya hana Rahinah yarda da sulhun da komen ne shi har gobe bai sani ba.
Alhaji Usman ya ce ya zama dole su yi tracing Habibu, wannan ai zalunci ne, dauke yaron da ke shan nono daga uwar da ta haife shi ko kotu za a je sai ya kwatowa Raheenah dan ta. In ya koma wajen ubansa to ya balaga ne, yana bayan hukuncin da Rahinah ta yi wa aurenta da Habibu ta karbi 'yancinta, inda gaske yana son ta ya kasa hakurin ya nemi iyayenta ya nemi aurenta cikin mutunci a hannun su mana? Sai wata watsatsiyar mata Laura? Shi kwata-kwata bai ga laifin Raheenah ba. Maza-maza a ba shi lambar Habibu yanzu zai je ya karbo wa Raheenah dan ta.
Amma me?
Lambar Habibu da Daddy ke da ita ta kasar Jamus ce, sai a lokacin ya tuna tunda Habibu ya zo Nigeria bai kira shi a waya da lambar sa ta Najeriya kamar yadda suka yi alkawari ba. Haka ya yi ta gwada ta Jamus din duk da ya san ba shiga za ta yi ba. A karshe ya gaya wa Alhaji Usman tunda ya taho bai kira shi ba, amma yana da yakinin zai kira shi komai daren dadewa, domin yaro ne mai hankali da biyayya, sannan da zuciya daya yake son Rahinah. Ya kwantar da hankalinsa ya sa a ransa cewa, Dan Raheenah yana a kyakkyawan hannu. Domin yaron Uba ne har da rabi.

Daidai lokacin da Hajiya Badiya ta shigo masu aiki biyu a bayan ta dauke da kabakin abinci, suka shirya komai tare da ita a kan tebirin cin abinci, ta zo tana tsokanar Raheenah wai anya ko tana jin 'ZO' da harshen Hausa? Ta gan ta sullubebiya kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba. Yafendo ce ta tare mata da cewa "ko jakar Kano nan ta ganta ta barta wajen jin hausa". Hajiya Badiya ta gabatar mata da kannenta, Musaddiq da Mubaraq da Mu'allim da Zarah. Raheenah ta rungume Zarah sosai kaunar yaran na shigar ta, tana ta yi musu tambayoyi a kan karatun su, sun tattauna muhimman abubuwa a kan Raheena tsakanin Daddy da Alhaji Usman kafin su yi sallama tare da amsar lambobin juna.
Shi da su Nene washegari da asubah suka juya zuwa Bichi a motar da Daddy ya zo, direban su Nene kuma ya juya da mutanen Girei zai maida su. An bar Raheenah sai za su wuce Jamus jibi ita da Safeenah direba zai tsaya ya dauke ta a nan Kaduna su karasa Abuja su hau jirgin Jamus.
****
: SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870

Zaman Raheenah na kwana biyu a gidan Kawun ta tare da matar kanin mahaifinta Aunty Badiya da 'ya'yanta hudu gwanin ban sha'awa, ba ta bambanta Raheenah da Musaddiq ko magana za ta yi sai ta ce, sai Raheenah ta fara kaza sannan Musaddiq zai yi tunda ta girme shi. Jininta ya fi haduwa da na Musaddiq sabida ilminsa, ga Raheenah da son yara masu kwazo. Zarah ma suna shiri don sai ta ke kwatanta girmanta da na Abdallahnta a halin yanzu, ita in ba idonta ne ma ke mata gizo ba sai ta ce, Mu'allim yana mata yanayi da danta Abdallah. Sai dai yadda ta binne uban Abdallah a ranta a yanzu, haka ta ke so shi ma Abdallahn ta daina ko tuno shi duk da ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne.

Lokaci-lokaci sai ta tsaya ta bar abin da ta ke yi tana tunanin Abdallah, ko me yake yi yanzu? Ko ya manta ta? Ko ya daina kiran sunanta? Wannan da wancan.... Amma ko ya ya tunanin Habibu ya kutso cikin kan ta da zuciyar ta sai tayi kokarin yakice shi da dukkan karfin ta.

Ba shakkah ta ji dadin zama da Aunty Badiya da yaranta da Kawun ta, tsayin kwana biyun, ji ta ke kamar kada ta koma Jamus, but she want to be that Otorhinolaryngologist she promised to be. Wannan ne kadai ya sa ta yarda ta koma Jamus tare da Safeenah a washegarin ranar da suka biyo don tafiya da ita, inda suka tashi ta filin jirgin saman Abuja.

Kudi mai yawa Alhaji Usman ya ba ta, ya ce ta rage wa Ambasada nauyi, kuma ya yi alkawarin aika mata kwatankwacin su duk karshen wata.

(Ranar da Rahinah ta tashi Abuja da safe, da yammacin ranar aka dawo da Abdallah daga Zamfara inda ya je ya yiwa Hajiyar Nahuce hutu).
*****



















*KOMAWAR RAHEENAH JAMUS*

Bayan sun koma Frankfurt ita da Safeenah, kowacce tana dakinta babu mai shiga shirgin kowa. Ko da ma can jininsu ba wai ya hadu ba ne, don haka kowa sabgar karatunta ta ke yi ita kadai a dakin ta. Ta kan dai ji wani lokacin Safeenah na waya da saurayin ta Muktar a barandar dakunan nasu. Raheenah Omar ta fuskanci karatunta da wani irin zeal saboda a halin yanzu ba ta da damuwa, tana cikin farin ciki na haduwa da danginta. Sai ta dauki hankalin ta da nutsuwarta kacokam ta mika wa MBBS dinta.

Har zuwa lokacin da su Daddy suka dawo, suka ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin gidan yadda suka saba.

Amma me? Ita diya mace a yayin da ta samu contentment na rayuwa, nutsuwa da kwanciyar hankali, abin da ya saura mata shi ne, DA NAMIJI a gefenta. A matsayin mijin aure ko manemin aure.

Wannan ne kadai gibin Raheenah a rayuwa. Somehow, wani bangare na zuciyarta kewar Habeebu yake yi, tana karyatawa da gangan. Tana bai wa tunanin rashin muhimmanci, tana ganin she can overcome it by force, amma a hankali sai tunanin Habib Nahuce da wata sabuwar kakkarfar soyayyarsa suka zo suka soma cin karfintaba tare da ta ankara ba.

Wannan wani sirri ne tsakanin ta da zuciyar ta, wanda daga ita sai Ubangijin ta suka san da shi. Bata kuma fatan wani cikin gidan ya san da shi.

Raheenah Omar ta gama MBBS a wannan shekarar, da sakamako mai madaukakiyar daraja, ta kammala ne (as the overall best student). A wannan lokacin Alhaji Usman Girei sai da ya taka kafafunsa har Jamus da taimakon cuku-cukun visa da Ambasada ya yi masa ya taya Raheenah murnar karbar kwalinta.

A wannan ranar Raheenah sai da ta yi kuka don farin ciki amma duk da haka; ta rasa dalilin da ya sa farin cikin nata ya zama incomplete, tamkar tana missing someone important, musamman da ya kasance kusan duk abokan karatunta mazajen su ne suka taya su karbar nasu kwalin, wasu kuma fiances dinsu. Ita ce kadai mai Uncle da Daddy a gefe, babu mijin da ya taya ta karbowa ya karba a nashi hannun bayan ta karbo ya bi ta da murmushin kauna.

A hakan ma ta fi kowa godiyar Ubangiji domin ba ta taba tunanin haduwa da wani nata ba har zuwa sanda za ta bar Jamus kwata-kwata. Amma yau ga ta tare da kanin uban ta har Jamus din.

Kafin ta fara specialization dinta sai da ta zo Girei ta yi sati biyu da su Goggo Dudu, sannan ta wuce Kaduna can ma ta yi sati biyu. Ba tare da ta sani ba, a ranar da ta je Kaduna, a jiyan ranar Habibu Nahuce ya zo ya dauki Abdallah daga wajen Aunty Badiya zuwa Zamfara don ya yi hutun kirsimetin sa tare da Hajiyar Nahuce.

Satin ta biyu ta koma Jamus ta fara specialization din ta a otorhinolaryngology.

Daga lokacin da ta fara specialization din kasancewar wahalar sa bata kai ta MBBS ba ta kan samu lokacin kan ta da lokacin tunani, a lokacin abubuwa suka fara rikice mata. Soyayyar (her ex Habibu) ta kada ita wanwar. Ta soma tunani da neman hanyar samun labarin sa. Ba don ta kula shi ba, sai don kawai shes curious ga son ta san me yake ciki shi da gudan ran ta, don haka ta soma sha'awar bibiyar Habibu Nahuce a kafafen sadar da zumunta, amma ko daya ba ya kai. As the busy person that he is, bashi da lokacin wadannan abubuwan (social media platforms). A karshe ta yanke shawarar duba shi a yanar gizo (google) ta san bazata kasa samun wani abu da shafe shi ba komai kankantar sa.

A wani marece ne ana tafka ruwan sama mai karfi a garin Frankfurt, ta rufe tagogi da kofar dakin ta, ta saki fararen curtains din dakin, sannan ta kunna (room-heater), ta dauko kwamfutar bisa cinya (loptop) ta shiga google kawai ta rubuta sunan sa HABIBU MUSTAPHA NAHUCE. Ita kuma googlesai ta kai ta LinkedIn. Kasancewar sa (professional platform). A can bata samu wani cikakken bayanin sa ba sai na profession din sa (as a Hotel Administrator), sai kuma a wani website na hotels din sa. A canne ta ga cikakken sunansa da cikakken bayaninsa a halin yanzu.

"Habibu Mustapha Nahuce (Lucky), Young Nigerian Hotels Owner, the Proprietor of NAHUCE GROUP OF HOTELS, Excutive Director TRANSCORP HILTON, NIGERIA.......

(With so much interest) hadi da mamaki da dokantuwa, wani irin inquisitivity and curiousity, Raheenah ta ci gaba da surfing tana bin bayanan wadanda duk sun kunshi gwagwarmayar rayuwar Habibu ne, ta neman ilmi, ta fadi-tashi a Jamus, da ayyukan Hotels a gida Nigeria, saicurrent hotunansa wadanda suka kusan gusar da numfashinta.

Yana nan a handsome HABEEBUNsa, dan gayun nan wankakke, mai iya daukar wanka, mai iya sanya karin hula, kuma dan kwalisar shi yadda ta san shi a baya cikin birnin Cologne, sai wata 'yar kiba ta hutu da zaman naira a muhallin ta ya sabbaba kawai da ya kara, hadi da wani irin kwarjini da kamala wanda rikon addini ke haifarwa mutumin da ya rike addinin sa da gaskiya, ya kuma san ciwon kan sa (at approaching 40).
Numfashin Raheenah yayi balaguro na tsayin lokaci daga kirjin ta.

Ba ta iya ci gaba da karantawa ba, haka bata iya cigaba da kuma kallon hotunan tallbuildings din NAHUCHE HOTELS dake kasa ba ta kifa fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba.

Numfashin ta na racing...cikin sassarfa, zuciyar ta na wani irin bugu cikin ragaita... So Habibu yana can kasar shi Nigeria yana progressingto such extent harya manta da ita. Ya manta an yi halitar ta. Mai wannan tarin achievements din ina zai tuna da wata halittar Allah mai suna RAHEENAH! Ya gama cimma komai na rayuwa, da duk wani buri da dan adam ke da shi, watakila ma har aure ya yi ya dau Dan ta Abdallah ya baiwa wata, in ba haka ba yaya zai yi da yaron???

Wannan tunani ya dugunzuma zuciyar Rahinah. Kishi da bakin ciki matsananci suka lullube ta. Kawai sai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login