Showing 87001 words to 90000 words out of 110913 words

Chapter 30 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ka aje iyalin. A bar kaza cikin gashin ta, amma 'yar ku duk ilminta na nasara ne kawai, tana bukatar training na UWA, a kan zaman aure saboda goyon Kaka ce..."
Aunty ta ce, "Na sani Habibu, kuma na yarda da kai, as far as I'm concerned now zan yi iyaka kokari na a kawo karshen matsalolin nan duka, idan har ka bar maganar auren da ka rakito".
"Kun makara Aunty, its too late! Don har na samu mata a Bidda mun daidaita da Yayan ta yanzun nan, wanda tare muke da shi a Transcorp Hilton, in na dawo zan je Biddan in ganta ku kai kudin aure. Sunan ta Zeena".
Ya kara da cewa, "Kada fa ki damu, ba zan hada ta gida daya da 'yar ku mai halin mutanen farko ba, ko don kada ta lalata min tarbiyyar ta da rashin sanin darajar aure".
Aunty ta ce, "Yaa Salam! Habibu me yayi zafi? Ina raba ka da matan zamani, wallahi Allah duk wadda za ta aure ka a halin yanzu ba soyayyar Allah ba ce, abin hannun ka ta ke hange, ka fara dawowa gida tukunna ka bamu wata uku, daga nan in komai bai canza ba, na yarda ko uku za ka karo ka yi ta karowa".
Bai san sanda ya ce.
''Wata ukun zan kara nan gaba babu mace? Ai sai dai in mata sun kare a duniya ne. In ba za ki hado min lefe ba Maman Musaddiq ina da masu hadowa fa. Wannan da kudi na ma zan hada, in wancan gudunmawa ki ka ba ni don ki san cewa I'm serious".
Da ta ci gaba da turzawa kan sai ya bar maganar karin aure ya dawo gida tukunna, in ya so nan nan da wata uku sannan ya sake tado maganar (hausar ta zuwa lokacin ya ga irin canjin da aka samu sun daidaita da Rahinah), sai ya ce mata,
"Maman Musaddiq, bana jayayya da ke kin sani, amma yau kam, na yi.
Ba zan kara sati biyu babu matar aure ta hakika a gida na ba. Ita 'yar ku tana Abuja, ita Zina tana Lagos ba shi ke nan ba? Kowacce ta zauna da irin halin ta da irin tarbiyyar ta a inda ta ke. I can handle them both".
Aunty Badiya sai ta kashe wayar ta, ganin Rahinah na hawaye. Bata san bakaken maganganun da zai cigaba da antayowa ba in ta cigaba da sauraron sa. Sabida Rahinah na jin komai.
Duk abin da suke fadi a kunnen ta ne, don Aunty a fili ta saka wayar don dai Rahinah ta ji ta kara sanin matakin da za ta dauka.
Washegari suka juya zuwa Kaduna. Ta ce nan da kwana uku za ta turo Musaddiq ya dawo ya kawo sakonnin nata, za ta gaya mata (Procedures) din ta waya. Kada kuma ta yi masa maganar auren da ya kafe a kai, ta rabu da shi.
Ita kanta Aunty ta lura Rahinah ta yi sanyi, ta kuma yi laushi, ko magana ba ta iya yi sosai. Alamu ne na TA HUCE DAGA FUSHIN TA.

A daren ranar da kyar ta iya yin barci. Washegari ba ta kai Abdallah makaranta da kanta ba, ta sa direban sa ya kai shi, tunda ya nuna ba ya son fitar tata kai Abdallah makaranta. Ita kuma daga yau duk abinda Habibu bai so ta daina shi duk son ta da abun kuwa.
*****

PACE-SETTERS COLLEGE, WUYE, ABUJA
T
sananin kulawa irin ta malaman wannan makaranta ya sa suka gane canzawar yaro Abdallah Nahuche. In ana karatu ba ya fahimtar komai yanzu, sannan in an fita break sai ya daina fita sai dai ya kwanta a kan tebir ya yi shiru.
Performance din sa na contineous assessment very poor. Haka walwalar sa cikin yara 'yan uwan sa ta karanta. Abincin da ya zo da shi haka yake komawa da shi ko ya zubar, don kada Rahinah ta gani ta yi masa fadan maiyasa bai ci ba.

Mrs. Easther Dekini wato classmistress din su ita ce ta lura da wadannan sauye-sauyen nasa, Mrs. Dekini sai ta hau jan yaron a jiki da wayo da tambaya tana son jin abin da ke damun sa. Rannan ta kawo katuwar ball ta ba shi, ta ce ya tashi ya shiga cikin yara 'yan uwan sa su yi wasa, sai ya bi ta da ido bai ce komai ba.
Mrs Dekini ta zauna kusa da shi a kan desk din sa, ta ce, "My dear Abdoulayi what's bothering you? Ka gaya min na yi maka alkawarin ba zan gaya wa kowa ba".
Yaron sai ya kama kuka. Ya yi kukan sa mai isar sa har yaba uku lada. Ta yi ta lallashin sa har ta samu ya yi shiru. Ta bude masa abincin sa, amma sai ya ce mata a'ah. Sai Daddy da Mummy sun daina fada zai dinga cin abinci.
Ba ya jin dadi kullum suna fada a kan sa.
A matsayin ta na malamar makaranta kuma mai ilmin psychology nan ta ga symptoms na kamuwa da depression a tare da shi.
Da aka kada kararrawar tashi ya mike ya dauki jakar sa zai fita, kawai sai ya yanke jiki ya fadi, wata irin kumfa na fita daga bakin sa.
Yara 'yan uwansa suka hau ihu suna fadin, "Abdallah ya fadi". Wanda hakan ya janyo hankalin malamai a kan sa.
Lokacin direban sa bai iso ba, don haka a motar makarantar aka wuce da shi asibiti, sannan aka kira lambar Habibu aka gaya masa yaron sa yana National Hospital.
Da direban sa ya je daukan sa ne a ka gaya masa an tafi da shi asibiti ba lafiya. Ya tambayi wane asibiti ne, aka gaya masa. Da gudu ya dawo gida ya sanar da Sahura don ta sanar da Rahinah.
"Abdallahn da ya fita lafiya kalau?"
In ji Rahinah, cikin dimauta da gigita, irin wadda ba ta taba yi a rayuwar ta ba.
"Wallahi kuwa dai sun ce faduwa ya yi haka kawai".
National Hospital ba bakon ta ba ne, don haka kai tsaye (emergency paeditric unit) ta nufa gudu-gudu sauri-sauri har tan cin karo da mutane. Likitoci uku ta samu a kan sa, sun rufu a kan sa. Domin saita bugun zuciyar sa da ke yi rapidly. Wajen awanni biyu suna kan yaron kafin a samu kan sa, a kuma maida shi aminity.
Awanni biyun da suka kasance tamkar shekaru biyu a idanun Dr. Rahinah Omar, domin ta gama sakankancewa dan ta Abdallah ba zai tashi ba.
Sun samu sun ba shi dukkan taimakon da ya dace sun masa allurar barci a karshe, yana ta barcin sa sadidan, ana masa karin ruwa kansa bisa cinyoyin Rahinah sai sharar hawaye ta ke yi babu kakkautawa, wasu na korar wasu.
Da sanyin safiya Habibu ya sauka a Abuja domin boarding flight ya biyo daga Lagos. Kuma ko gidan sa bai biya ba daga filin jirgi sai National Hospital afujajan da shi, domin zai iya cewa wannan ne karo na farko da aka ce Abdallah ya kwanta a asibiti a kan lalurar da bai san mece ce ba.
Yana yin ciwo sama sama amma bai taba kaiwa ga kwanciya ba. In ka ce tashin hankali ga Habibu, to daya kenan domin kuwa lokacin da aka kira shi a kan maganar, meeting yake yi da ma'aikatan sa duka na Nahuche Hotel Lagos amma sai cewa ya yi,

"Excuse me...!".
Daga haka bai kara cewa komai ba. Ya tashi ya fita da sauri, sai Rasak ya bi bayan sa, ba su tsaya ko'ina ba sai filin jirgi.
Cikin rashin sa'a jirgin Abuja bai jima da tashi ba a lokacin, sai kuma wanda zai tashi sha biyun dare, amma haka ya zauna a lounge din bai koma gida ba, don gani yake in ya koma za a kira shi kawai a ce babu Abdallah.

: *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870

NA HUCE*



PAID BOOK


Jiran lokacin tashin boarding flight din da ya zame wa Habib Nahuche tamkar jiran ranar busa kaho, finally, jirgin ya zo ya kuma dauko su zuwa Abujan, sun bata lokaci sosai don sai shidda na safe suka samu baro filin jirgin zuwa cikin gari, daga nan zuwa National Hospital.
Rahinah ba ta son tuno abin da likitan da ya jagoranci duba Abdallah ya fada mata, Abdallahnta is too young da samun wannan lalura, don haka yanzu ma da suke zaune su duka a gaban sa, ita da Habibun, ya kuma maimaita wa Habib Nahuche abin da Rahinah ta rigaye shi ji, Habibu bai san sanda ya juya ya kankame Rahinah ba.
"Depression and Anxiety Disorder, sannan zuciyar sa ta fara tabuwa.
Daga bayanin da Mrs Dekini ta makarantarsu ta bayar sanda aka kawo shi, mun tattara mun gano musabbabin matsalar sa.
Ya dade yana ganin iyayen sa cikin halin da ba ya so. Me ya sa ku ke yin abin da zai daga masa hankali a gaban sa?
He's too young da daukar matsalolin ku. Kwakwalwar sa karama ce, you all have to pay for that". In ji likitan cikin bacin rai da matsanancin fushi.
Rahinah ba ta san sanda ta daddage ta ture Habibu da ya kankame ta ba, dukkan su jikin su rawa ya hau yi. A fusace ta ce.
"Duk ba kai ka jawo ba? Sau nawa zan gaya maka ka daina hantara ta a gaban sa, ka daina daga min murya a gaban idon sa?"
"Really? Ni na jawo ko ke ki ka jawo? Do you have the guts na fadar hakan? Shekara goma bai san ki ba sam sai yanzu, ina ya wani damu da ke har haka? Ciwo ne kawai daga Allah".
"In ma ba ku kuka jawo ba you all contributed immensely to it". In ji likita Mansur. Yana buga tebirin gaban sa.
Cikin kuka Rahinah ta ce,
"Tun farko ai kai ka fara poisoning mind din sa, da abin da shekarun sa, tunanin sa ba su isa ya gane, ko zuciyar sa ta dauka ba.
Ni kokari na kullum shi ne ya saki jiki da ni kawai, ya dauke ni mahaifiya ban taba zaunar da shi na gaya masa laifuffukan ka ba, amma kai hum!! Allah kadai ya san iya abin da ka gaya masa, ban taba gaya masa cewa ka yi min wata rashin kyautawa ko guda daya ba".
A fuskar sa akwai nadama tsantsa, duk da haka bai yi admitting gabadaya ba. Hararar ta ya yi ya ce.
"Amma ai da kunnen sa yana ji kina min Allah ya isa in na debi abincin ki. Kuma ya gaya miki ba ya so".
Dramar ta su sai ta koma baiwa likita Mansur dariya, wadannan wadanne irin iyaye ne? Gasu duka educated and matured, amma suna behaving kamar yara.
Haka suka yi ta mai da wa juna martani ba kakkautawa, likita Mansur na kallon ikon Allah. Suka yi suka gaji kamar zasu baiwa hammata iska, kuma a karshe suka bar ofishin sa zuwa dakin da yaron ke kwance a Aminity. Rahinah na hawaye.
Bayan ya gaya musu a yanzu dai Abdallah yayi kankanta da shan antipsychotics, counselling yake bukata daga gare su iyayen nasa da sauran clinical treatments a nan asibiti, wanda zai kwantar masa da hankali ya koma cikin hankalin sa.








WA KE DA LAIFIN?

Habibu da Rahinah sun tambayi kan su wannan tambaya har babu iyaka. A lokacin da suka tasa Abdallah a gaba suna kallo. Ya tashi daga baccin sai kallon ceiling yake, yana mamakin a ina yake haka? Shi da yake cikin ajin su? Kwana daya kacal duk ya rame.
A tare kuma a sukwane suka isa gaban gadon sa har suna hada baki wajen tambaya.
"Abdallah ka tashi?"
Ta zauna tana matsar kwalla rike da hannun sa, yayin da Habibu ya zauna daidai kafafun sa ya dauki???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? kafafun ya aza bisa cinyoyin sa yana matsa masa su sannu a hankali.
"Sannu Abdallah na, Daddy is here, ba zan kara tafiya in barka ba Abdallah, duk inda za ni da kai da Mummy zan tafi.
Mummy ai za ki bi ni Lagos ko?"
Da sauri Rahinah ta gyada kai idanun ta a kan sa tana kakalo murmushin dole.
"Sosai ma Dad, kafar ka-kafar mu ni da Abdallah, ai mun daina fada tuntuni ko Daddy? Abinda yasa ma ban bi ka PortHearcourt ba sabida makarantar Abdallah ne".
Ta karasa fada tana gallawa Habib harara ganin Abdallah ya lumshe idanun sa yana sauraron su.
Habibu ya ce "ni ai na manta yaushe rabon mu yi fada, kin ga yau har zobe na sayo miki, yana mota in mun koma gida zan ba ki, ko kin fi so in saka miki da kai na?".
Likita Mansur na ci gaba da auna yaron yana jin su yana ta dariya a cikin sa. Iyaye da yawa ba su san cewa zaman lafiyar su ko akasin sa na affecting yaran su psychologically and morally ba. Daga Habibu har Rahinah babu wanda ya taba kawo wa ran sa wai Abdallah yana lura da abin da suke yi, yana kuma ajiye abin a ran sa.
Nan suka wuni, kowanne da irin kulawar da yake yi wa Abdallah, a lallai sai sun nuna masa jiya ba yau ba, lafiya suke zaune. Amma duk sanda suka hada ido sai Habibu ya balla mata harara. Itama ta rama.
Mr. Atiku ne ya kawo musu takeaway daga (Dominos) bayan azahar, suka ci tare a kan gadon Abdallah suna ba shi a baki suna masa hira, sai ga Nene da Sahura sun turo kofar sun yi sallama sun shigo, Sahura rike da basket din abinci.
Rahinah kunya kamar ta nitse a wurin. Domin sun bararraje akan gadon ita da Habib sun sanya dan a tsakiyar su kamar zasu maida shi ciki. Ta yi maza ta diro daga gadon tana yi wa Nene barka da zuwa.
Da sauri Nene ta iso jikin gadon ta kama hannun Abdallah ta ce,
"Sannu Abdullahi, me ke damun ka? Dazun nan Sahura tai min waya wai duk kuna asibiti an kwantar da Abdallah".
Rahinah da Habibu aka rasa mai bada amsa domin duk sun karaya, sai Habibu ne ya yi ta maza ya ce da Nene Balki, "Sun ce Anxiety ke damun sa".
Nene ta yi salati, ta ce, "Depression and Anxiety ba ciwon manya bane, ina Abdallah ina damuwar da za ta sa shi zama cikin Anxiety? To ikon Allah ya fi ga haka, ina fatan an dauki duk matakin da ya dace?"
"Sun yi iya kokarin su, amma sun ce, counselling ya fi bukata a kan kwayar magani sabidda karancin shekarun sa, sai Therapy da zai karba na sati biyu".
Zuwan Nene ya sa dole ya fita ya bar musu dakin, masallacin asibitin ya tafi don yin sallah. Nene Balki bakin ta bai yi shiru ba, sai kakabi ta ke kan me ya hada Abdallah da anxiety? Daga baya ta kira Aunty Badiya ta gaya mata.
Badiya bata yi mamaki ba ta ce, "Allah ya ba shi lafya, amma ai su suka jawo masa Nene, Habibu da Rahinah, sun ki yarda Annabi ya faku. Kullum kananan yara su ke maida kan su. In suka sabauta dan ai shi ke nan sun huta".
Ta soma kwallah saboda ba karamin so ta ke yi wa Abdallah ba.
Uncle Usman yana garin don haka da daddare ya zo duba Abdallah. Nan suka hadu da Ambasada a parking lot suka jera zuwa ciki, suna tafe suna hira wadda duk ta Habibu da Rahinah ce, da dan su Abdullahi. Maganar aikin Rahinah ya roki Ambasada ma ya saka baki Habibu ya bar ta ta koma. Ambasada ya ce,
"A'ah Usman, ka barshi ya yi cikakken iko da iyalin sa, in ya amince don kan sa, fine, in bai amince ba ta hakura babu rashin ci babu rashin sha, we are not to be interfering tunda dai mun yi mai wuyar mai kuma muhimmancin".
Sun duba Abdallah sun jajanta kafin su bar asibitin su duka. Direba ya maida Sahura gida, dakin daga Rahinah sai Abdallah.

"Mummy zan sha Kelloggs". Ya fada kan sa na bisa cinyar ta.
Ta shafa kan sa ta ce, "To Abdallah bari Daddy ya zo sai ya sayo ko?".
"Ki masa waya mana! Yanzu nake so!".
Jiki na rawa ta zaro waya ta hau zakulo lambar sa, ashe ba ta yi saving ba, kawai sai ta shiga inbox din ta inda ta ga sauran sakonnin sa rututu da ya turo mata yana PortHearcourt, ba ta ko kai ga budewa ba, balle ta goge. Kawai sai ta yi sha'awar yau ta bude duka sakonnin Habib ta karanta da nutsuwa kafin ta kai ga kiran sa, don ya kawo sakon Abdallah.
Ga abin da Habibu ya rubuto wa Rahinar sa.
1- "Kin yi tasiri mai yawa cikin rayuwata, tasirin da a tarihin soyayya a rayuwar Bahaushe ban ga irin nawa ba RAHINAH.....Kin jijjiga rayuwa ta tsayin shekaru goma da doriya, amma duk da haka ban fidda rai watarana na zuwa da zamu koma daidai ba, har mu zama ma'aurata ababen misali. An ce abinda hakuri bai bayar ba rashin sa bai taba bayarwa, zan ci gaba da hakurin nan na wasu shekaru goman a gaba su zamo (two decades). Watakila sai a shekarun furfurata ne zan ci ribar hakurin nawa?!"

2- "Ni Habibu ina mai ba ki hakuri Rahinah, da guiwowina a kasa.. a bisa duka laifuffukana na baya, wanda na sani da wadanda ban sani ba, irin hakurin da ban san yawan sa ba, ban san adadin sa ba, ban san iyakar sa ba.
Na yi kuskure ina mai rokon a ba ni dama in gyara shi, ko da wannan ce dama ta karshe a gare ni. Na yi alkawarin zan goge tabon AUREN KWANA BAKWAI of the past Decade in only one night..... idan kika bani dama!
Nayi alkawarin zan biya bashin soyayyar shekara goma da muka yi missing in only one night".

A hankali Rahinah ta wani lumshe idanun ta, kafin ta kai ga bude su daga lumshewar da ta yi musu, Habibu ya bude kofar dakin ya shigo da sallamar sa ba tare da ya san me ta ke yi ba.
Sai ta kasa bude idanun har ya iso jikin gadon yana tambayar Abdallah,

"Ya ya dai apple of my eyes?"
Abdallah ya ce. "Mummy na ce ta kira ka ka kawo min kelloggs tun dazu. I guessed she

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login