Showing 18001 words to 21000 words out of 110913 words

Chapter 7 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

bace. Don haka ya kwantar da hankalin sa.

Habib s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ai yayi murmushi, his beautiful serene smiles. Ya ce "ai komai ya zo karshe ranka ya dade, na kammala karatuna zamana a kasar Jamus ya kare. Nazo ne in dauki Abdallah bisa iznin ku, zamu koma gida Zamfara".


Ambasada shiru yayi, hukuncin da yaron ya yanke yayi matukar impressing din sa. Da gaske gara yayi nisa da Rahinah ya kuma dauke dan sa, watakila hakan yasa ta yi gaggawar gano muhimmancin su cikin rayuwar ta.

"Amma ka san mai raba ta da dan nan sai Allah ko? Kuma kana da wadda zata kula da shi kamar yadda mahaifiyar sa zata kula da shi? Idan babu, kai namiji bazaka iya rainon da ba, na gaya maka".

"Mahaifiyata tana raye ranka ya dade, sannan Yayata Badiyya, duk cikin su babu wanda bazai rike min shi kamar koma fiye da yana gaban mahaifiyar sa. Albarkar ku kawai nake bida, da fatan alkhairin ku".

Ambasada couldn't keep his tears wato ya kasa maida hawayen sa. Yayi saurin share su kafin Habibu ya gani. Ya kira Nene ya gaya mata ko me kenan. Itama Nene tafi mijin ta shiga rudun tunanin mai iya raba Rahinah da Abdallah.

Sai ga yaron ya shigo tinkis-tinkis, cikin tafiyar shi mara kwari, ya yi kyau cikin kayan sanyi, yana ganin Babansa ya tafi da gudu ya fada jikin sa. Habib sai ya ga kawai bari yayi amfani da wannan damar, kada dama ta biyu ta sake kubuce masa.

"Zan tafi dashi yanzun nan ranka ya dade, ku gafarce ni"
Nene ta soma kuka, ta saba da yaron ya shiga ranta da zuciyar ta duka. Daga ita har Ambasada aka rasa mai karfin halin hana Habibu wannan danyen aikin, har ya fice falon da yaron a kafadun sa. A lokacin da Rahinah ke dakin ta tayi dai-dai a tsakiyar gadon ta tana ta sharar barci abinta.
""""


Koda ta farka bata ga yaron ba bata damu ba, ta dauka yana wasan sa ne a dakin su Ahlan kamar yadda ya saba. Tayi wanka ta ci abinci ta koshi ta janyo littafanta ta karkade, gobe ne zata koma makaranta daga deferring din ta. Saboda haka tana bukatar dumama kwakwalwar ta, duk da cewa a son karatu irin na Rahina ko da bata zuwa makaranta kuma babu jarrabawa a gaban ta bata fasa bitar littafanta ba lokaci-zuwa lokaci.

Amma ga mamakin ta har tayi sallahr maghriba da Isha Abdallah bai shigo ba, bata kuma ji tashin muryar sa ba. Nene kuma tana sassan Daddy a irin wannan lokacin, watakila kuma ya bita can din ne.

Amma da lokacin kwanciyar su yayi bata ganshi ba dole ta fito tana kwala masa kira. Gaban Nene da ke daki ya bada dam! Tayi zamanta a daki ta ki fitowa, sai ga Rahinah ta shigo.
"Nene ashe kina nan? Abdallah nake ta nema tun rana rabo na da shi". Nene ta daga ido ta dubeta idon ta fal tausayi, ta ce "yaki Rahinah, zo nan mu yi magana".

Rahinah ta soma shiga tashin hankali, ta dafe kirjin ta da hannayen ta da karfi, "ba dai wani abu ne ya same shi ba Nene?""Ba abinda ya same shi Rahinah, he's healthy and vibrant, amma Baban sa ya ce mu gaya miki ya zo ya tafi da shi, idan kin canza ra'ayin ki kan zaman ku tare ku raini yaron tare ki fada masa zai dawo ku koma auren ku!"

Rahinah ta dora hannuwa aka ta zuba ihu, sannan ta sulale a wurin babu yadda take, tamkar wata mai tashin jinnu ta koma tana kuka tana birgima a kasa tana kiran Abdallah ".....wayyo da na, wayyo Abdallah!" Nene sai da ta firgita ta kuma yi nadamar gaya mata ta wannan sigar, ita ta fada ne don Rahina ta ce ta amince zata koma dakin ta su kuma su yi wa Habibu magana ya dawo. Amma a yadda Rahina ta karbi lamarin babu zancen sulhu face Habibu Nahuche yayi mata kidnapping Da.

Data gaji da ihu da birgima hawaye ya hade da majina duk jama'ar gidan na kanta har Yafendo, hatta Safeenah da bata son ta yau ta tausaya mata. Nene na bata hakuri tana gaya mata abu ne mai sauki, ta yarda kawai ta koma dakin ta ta raini dan ta a gaban ta amma ina! Tunanin Rahina yayi fintinkau da tunanin kowa. It goes far beyond mere or casual assumption.....ta riga ta sanyawa zuciyarta tsanar Habibu kuma bata jin akwai abinda zai kankare wannan tsanar ban da ikon Allah.

Hanya ta saba babu ko lullubi data faki idon Nene ta shiga sallah, Yafendo ma ta koma daki ta rabu da ita, bata manta nisan dake tsakanin Cologne da Frankfurt ba tafiyar awanni biyu ce kwarara a mota, amma ji take zata iya zuwa a kafa.....
Tafe take a gefen titi tana kuka kamar mahaukaciya. Daidai lokacin da anka rufe kofar jirgin Lufthansa....wanda zai tashi zuwa kasar mu mai dimbin albarka. Ba da jimawa ba ya soma rugugin sa mai gigitarwa kafin ya dauki hanya dodar, ya daidaita sosai, ya cigaba da keta hazo a sararin samaniya......


Ya tafi tareda duk wani farin cikin RAHINAH OMAR.....Ya kassara ta.... ya raunata jarumtakar ta. A da tana ganin ita jaruma ce zata iya fuskantar komai don ta kwaci 'yancin ta wajen Habibu Nahuche. Ashe wani 'yancin ba ya kwatuwa ta karfi duk yanda anka so, Habibu bai shigo rayuwar ta don ya fita a sanda take so ba. Ya shigo ne don ya dai-daita (shattering) farin cikin ta ya raba ta da sauran hope din da ya saura mata a rayuwa......

"Allah ya isa na.....Allah ya isa tsakanina da kai Habibu! Kuma ko zan mutu ba aure, ko haka zan kare rayuwata single bazan koma gidan ka ba.....mugu, magulmaci, maketaci, maha'inci, the rapist!".

Ita kadai take tafiya tana hada hanya tana sakin zance kamar zautacciya. Habibu ya shammace ta, shammatar da da ace idanun ta biyu ko duk kotun duniya zata taru a kanta bazata raba ta da danta ba. Ai addinin ma da ya bashi wannan damar sai idan dan ya fara girman da zai iya kula da kan sa.

"Jahilin banza jahilin hopi, algungumi munafiki, in ba tsoro ba ka dauke shi gabana mana? Ai faduwar gaba asarar namiji ce.....".

Babu wani mummunan suna da bata kira Habibu da shi ba, babu mugun alkaba'in da bata yi masa fata ba. A karshe ta fashe da kuka ta durkushe a inda take, data ga ta dauki hanyar barin Frankfurt kuma tafiya ta ki ci ta ki cinyewa.

Hankalin ta ya fara dawowa jikin ta ta tabbata bazata iya kai kanta ga inda zata riski Habibu ba kuma bata da kudin motar da za ta biya a kaita, haka babu katin bankin ta a tare da ita.

Wannan ya tabbatar mata har yanzu tana cikin hankalin ta bakin cikin Nahuche bai haukatata ba.

Zata yi amfani da sauran hankalin da ya rage mata wajen gina rayuwar ta, ta ga cewa bata kamu da ciwon damuwa ba, da wajen ganin cewa bai yi amfani da soyayyar da take wa Dan ta ya karasa cin galaba a kan ta ba, ya kara kassara ta, ta hanyar maida ta kurkukkun auren sa, wanda babu komai a ciki sai biyan bukatar ran sa.

A tunanin ta har abada bata son Habibu, kuma har abadan bazata so shi ba. Abin da bata sani ba SO daban, haka bacin rai daban. Bacin rai is *mortal* and LOVE is *inevitable* . Watakila kuma ganin ta da shi na farko abinda ta ji akan sa wani abu ne daban ba so ba, wanda ta dinga fatan in sun zo mutuwa a jirgi...to Allah ya sa ta mutu manne cikin jikin sa.
*****



*NA HUCE..* ..is not for freee.
It's 1000 via 3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Shaidar biya 07030137870
: Habibu Mustapha Nahuche ya sauka a filin jirgin saman Abuja daga Frankfurt ta kasar Jamus da misalin karfe shidda na safiyar Jumaah, yana rungume da dan sa Abdallah a kafadun sa na dama, wanda ke ta barci sadidan cikin gajiya tun suna cikin jirgi.
Kai in ka ga irin rikon tsantsenin da yayi ma dan na sa, gami da tsantsar kulawar da ya ke baiwa kankanin yaron, tsammani za ka yi cikin sa zai maida shi don tsananin So da kauna irin ta mahaifi. Mahaifin ma irin Habibu Nahuche wanda samun Uban da ke son dan sa kamar sa sai an tona. Har ila yau, tsatstsauran rikon da ya yi wa yaron, yana da nasaba da kasantuwar sa cikin fargaba da tsoron ko Raheenah za ta biyo bayan su afujajan kafin su kai ga sauka a kasar su ta haihuwa, Najeriya.
Duk da ya san hakan ba mai yiyuwa bane ba tare da shiri ba. Amma hanakalin sa bai kwanta ba har sai da ya gan shi a filin jirgin saman birnin tarayyah. Saboda yana da tabbacin abu daya: A yadda Raheenah ke son Dan ta, da yadda ta damu da kasancewa tare da shi ko barci bai taba raba su ba, da kuma yadda ya san ta wajen kafiya da naci akan abun data ke so, da bakin cikin shammatar da ya yi mata, ya tabbata za ta iya takowa ko da da rarrafe ne ko da akan gajimare ne tun daga Frankfurt, ta biyo bayan su ta cikin hazo don ta kwace dan ta Abdallah, shi ya sa bai je dauko Abdallah daga gidan Ambasada bama sai da ya kayyade ya kuma kintaci lokacin tashin jirgin su.

A yayin da jirgin ya karci kasa ya bar babban birnin Frankfurt din Jamus, sai ya ji tamkar ya nannade komai na Raheenah Omar daga zuciyar sa, tamkar yadda ake nade tabarma, ya baro shi a can. Ya cire ta kenan HAR ABADA daga rayuwar sa, ya hakura da ita, ko da ita ce autar mata a duniya, kamar yadda babu shi babu kara yin aure a duniya.

Raheenah Omar, ta kassara shi, ta raunata shi, ta ji masa ciwo mai muni a zuciya, bashi da sauran wata soyayya da zai iya baiwa wata diya mace, ta kashe duk wani burin sa a kan yaya mata (ko dama can bai da buri akan su, ita kadai Allah ya sallada zuciyar sa kan ta, ya jarrabce shi akan ta da mafi girman jarrabawa). Juya masa baya da ta yi da sulhun da ya nufa na alkhairi a gare su ya dauke duk wani farin ciki da walwalar sa, ta zagwanyar da farin cikin achievements din da ya dawo da su daga kasar Germany. Wato kwalayen sa guda biyu, masu daraja ta farko.

A kan ta ya san so, a kan ta ya fara so, haka a kan ta ya kare so, kamar yadda daga kan ta ya rufe SO. Ta tafi da dukkan (charming and amiable) Habibu Nahuche bata bar shi da ko guda ba cikin dabiun sa da halayen sa na baya.
Amma a matsayin sa na musulmi kuma haihuwar musulunci, ya san komai muqaddari ne daga Allah watakila Allah ya rubuta iya rayuwar auren da zai yi da Rahinah kenan ta kwanaki bakwai, watakila a rubutun kaddarar su; babu sauran zama a tsakanin su. Hakan ba zai sa ya kasa rayuwa a kasar haihuwar shi ba. Hakan ba zai hana shi godiyar Allah da ya bashi tsatso daga gare ta ba. Zai yi gammo ya dauki rayuwa a duk yadda ta zo masa, ba tare da Rahinah Omar a cikin ta ba.

Abin da zai sa a gaba yanzu shi ne: hanyoyin da zai bi ya maida kobo ya koma dari don tserewa bakin ciki da takaicin duniya, don samawa Abdallah kyakkyawan future, da kuma hanyar da zai bi wajen rainon gudan ran sa (ABDALLAH), zai yi duk yadda zai yi wajen ganin ya bashi rayuwar da ta dace da kowanne Da mai gatan UBA har ma da UWA (tunda Hajiya da Badiya na raye) da kuma ilmi mai inganci.
Ko a lahira ba ya fatan Allah ya sake hada shi ko a hanya da uwar Abdallah.. Infact, abinda ya lura a tare da Raheenah Omar; babu zuciyar imani ko kankani a cikin tsakiyar kirjin ta, babu compassion, babu love, babu affection, ita da sassakakken dutse basu da maraba. Taurin kai ko irin na mutanen farko, she has no love in her talk more of offering it to someone. To Idan so cuta ne. Hausawa suka ce hakuri ma magani ne!.
Zai hadiyi hakurin nan komin dacin sa, komin baurin sa, komin girman sa, zai kuma hada da addu'a da rokon Allah dare da rana kan ya fidda Rahinah da komai nata daga zuciyar sa da rayuwar sa bakidaya.

Daga Abuja shatar karamar mota ya dauka kai tsaye har garin su Zamfara, tun a wancan lokacin jihar Zamfara babu filin jirgi. Ya tsaya ya yi canjin kudin sa a Abuja daga Euros zuwa Naira, ya saya wa Abdallah abincin da zai rika ci a cikin mota har su isa Zamfara.

A lokacin Abdallah ya tashi daga barci sai faman kalle kalle yake na ganin sa a bakon wuri da bakin fuskoki, amma ko tari bai yi da sunan kuka ba, tunda dama ya saba da Baban sa sosai.
******



UNGUWAR KOFAR JANGE ZAMFARA STATE (GIDAN MARIGAYI ALH. MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE)


Yau unguwar kofar Jange cike take makil da matasa, ana ta hada-hadar siyasa, unguwar ta cakude da hargowar samari da 'yan jagaliyar siyasa masu yawo da fastocin 'yan takara suna musu kamfen. Don haka da kyar direban da ya dauko su ya samu hanya suka kutsa suka isa har kofar gidan da ake kira 'GIDAN NAHUCE'.

Duk inda suka gifta cikin unguwar tasu sai Habibu ya bi wurin da kallo (with nostalgia) da tsananin begen gida, yana mai tuno wani abu na dabdalar kuruciya da ya yi a wurin, shekaru bakwai kenan da barin sa gida idan har lissafin da yake yi daidai ne.
Yau ga shi ya dawo gida lafiya, amma ba shi kadai ba kamar yadda ya tafi, ya dawo ne tare da wani replica din sa (photocopy of Habib Nahuce). Wanda kaddara ta tanadar masa, ta kuma ba shi ba tare da ya tsara ba.

Yana godiya da wannan kaddara tasa da hannu bibbiyu, domin kyautar Da sukutum! Rahma ce daga Ubangijin Talikai. Wadda ba kowa Allah yak e baiwa ba.

Hajiyar Nahuce (kamar yadda kowa a dangi dama jamaar unguwar ke kiran ta) tana alwala da buta a gindin famfo lokacin da Habib ya yi sallama. Muryar sa ta dira a cikin kunnuwan ta kamar cikin mafarki.

Sai ta dakata daga wanke kafafun ta da ta ke yi, ta yi tsam! Da ran ta, tana son gasgata abin da ta ji. Kafin ta dago manyan idanun ta wadanda da gani ka san babu tambaya ita ce ta haifi Habibu Mustapha Nahuce. Alamun girma da ya soma kamata bai boye zahirin kamannin su ba na Rumawan Nahuche.
Bude baki ta yi cikin mamaki, da tuajjibi, don ko shekaranjiya sun yi waya dashi Habibun, amma bai ce mata yana tafe ba.
"Wa nake gani kamar Habibuna? Habibullahi?"
Duk yadda Da ya kai ga canjawa, cikin halin jin dadi ne ko akasinsa, to fa Uwa ba ta kasa gane abinta. Don haka komawar Habibu kyakkyawan Bajamushe kuma gogaggen bakin bature bai hana Uwarsa Hajiya Kaltume gane shi ba, daga kallo na farko da ta yi masa.

Har gabanta ya karaso ya sunkuya, cikin gajiya, sannan ba tare da ya ce komai ba ya mika mata Abdallah da ke hannunsa makale a kafadun sa. Amma sai Abdallah ya ki zuwa, ya makale sosai a jikin Baban nasa.

Jikin Hajiyar Nahuche ya hau rawa da makyarkyata.

"Ni Kaltume Nahuce! Habibullahi ina ka samo yaro mai kama da kai haka???"

Ba jikin ta kadai ba, hatta muryar ta Hajiya karkarwa take yi.
Magana ya shiga yi wa Abdullah da harshen German"Abdallah Sie istmeine Mutter, geh zuihr (she's my mother go to her)". Yaron ya make kafada cikin rashin yarda, tare da sake makalewa cike da tsoro da kyuya a jikin Abban sa.

Yara suka soma shigo da jakunkunan Habibu manya-manyan trollies. Haj. Kaltume gabadaya mamaki da tsoro ya hana ta kokarin karbar yaron da yake ta faman son ta karba.
Sai ta fara hawaye daga tsaye. Sakamakon abinda zuciyar ta ta hasaso ta kissimo mata.

"Sai ka fara gaya min ina ka samo shi tukunna zan karbe shi, Habibu Allah ya sa ba shegensa ka yi ba a can kasar masu jan kunne". Idanunta na zub da hawaye suna nuna tsananin kidima da fargabar da ta ke ciki.
Da sauri Habib ya hau girgiza mata kai. Shima nasa idnun suka kawo kwallah.

"Wannan ba rainon da ki ka yi min ba ne Hajiyata, ban taba yin zina ba, ban taba kusantar ta ba, tun ban san ma'anar ta ba kike nusar da ni illar ta, kuma har in mutu ba zan yi ba insha Allahu.
Ina baki hakuri Hajiyarmu, domin hakika na miki laifi, (na yi aure a Jamus ba da saninki ba)".
Dogon Salati Hajiyar Nahuce ta saki,
"Aure kamar ya ya?"
Habibu bai bata amsa ba, sai ya kara mika mata Abdallah, wannan karon ba musu ta sa hannayen ta biyu ta karba, tunda dai ta samu tabbacin ba shegen sa akai ba. Sannan kalmar aure ta gitta. Komai zai biyo baya a ganinta zai kasance da sauki.

Daki suka shiga, Habib ya shigo da jakunkunan sa, kafin ta yi komai flask ta jawo wanda dama ba ta rabo da kunun tsamiya a cikin sa, ta zuba a kofi ta saka dan suger ta motsa ta soma kokarin baiwa Abdallah.

Kasancewar Yafendo tana ba shi ya san kunu sosai, ya karba yana sha, ta dora shi a cinyoyinta tana rirriga shi, sannan ta maida hankalinta kacokam a kan Habibun, wani irin mabayyanin bacin rai kwance-kwance baro-baro a kan dattijuwar fuskarta.
"Yanzu Habibullahi wuyan ka har ya yi kaurin da za ka yi aure kan gaban kanka babu sanin kowa naka?
In Shafa'atu ce ba ka so ai ba sai ka yi haka zan san ba ka son ta ba, wane irin aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login