Showing 15001 words to 18000 words out of 110913 words

Chapter 6 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

barage.
Ta zauna daidai kafar Nene Bilki ita kuma tana daga saman gadon ta, tace "Rahinah meyasa bazaki koma gidan mijin ki ba? Yaron nan ya bani tausayi sosai, da gani yana bukatar ki cikin rayuwar sa. Can you be open to me? Inaso in san meye matsalar ku? A matsayina na uwa zan iya bada shawara".
Rahinah ta sunkuyar da kai, tana tuno irin rashin tausayi da rashin soyayyar da Habib ya gwada mata, kullum tana ji a littafai cewa aure abu ne na soyayya, miji tarairayar matarsa yake yana bi da ita ta hanyar da bazata cutu a shimfida ba, amma Habib Nahuche a wannan fannin sai dai a kira shi NOVICE. Don haka bata ga amfanin zama dashi ba gara tayi rayuwarta single.
Amma ta yaya zata iya gayawa Nene haka bata ga rashin kunyarta ba? Ita a ina tasan yadda ake rayuwar aure tunda ba taba yi tayi ba! She's just comparing and imagining. Don haka ta ga gara ta rike sirrin auren ta a zuciyarta, shi ciki ba anyi shi don cin tuwo ne kadai ba. Ta soma tunanin abinda ya kamata ta gayawa Nene, don ita duk wata shawara in dai akan ta komawa Habib ne to bata bukatar ta.
"I don't love him Nene!"
Ta fada tana hawaye. "Sabida bai aure ni cikin mutunci da daraja ba, ya sameni a arha da yawa. Cigaba da zama dashi zai iya janyomin psychological depression".
"Allah ya sawwake" inji Nene Bilki, amma daga nan zuwa ki haihu ki nutsu ki fahimci zuciyar ki. Maiyiwuwa wani bacin rai ya sanya miki wanda ya lullube soyayyar. Bazan takura sai naji ba don tsakanin mace da mijinta sai Allah da ya halicce su. Amma shi AURE is not all about love my dear.....so many cirmustances na sanya mu zaman aure. Ni kinga so nake Saffenah ta samu mijin amma Allah bai bata ba, shikuwa Habibu har cikin kwayan idanun sa na hango SO mai yawa, wanda nake da yaqinin da zaki hakura ku koma zai isheku rabawa ku duka, ya yalwaci zuciyar kowannen ku.
Yanzu mu bar maganar kome, mu yi ta karatun ki.
Kinga dai position din jikin ki na da dana yanzu ba daya bane, ba zaki jure wannan zirga-zirgar tsakanin Frankfurt da Cologne ba. Don haka na kawo shawara me zai hana ki nemi iznin accessing lectures dinki online? In yaso lokacin jarabawa sai kije ki rubuta, doctor yace kina bukatar hutu sosai. In yaso in kika haihu sai ki cigaba yadda kike yi".
Rahina bata so ya zamo cewa kowacce shawara da Nene ta kawo bata dauki ko daya ba, banda haka da ta gaya mata......gara ta cigaba da zirga-zirga yadda cikin zai jijjigu ya bare. Cikin da bata maraba da shi ko kadan cikin rayuwar ta.
"To shikenan Nene, insha Allah zan rubuta application na neman iznin hakan, sai a karbo takardar asibitin" Nene tace "hakan dai ya fi".
"Sai maganar abinci, duk abinda kika je shi kike so, shi zuciyar ki ta kwanta da shi, kada kiyi kauron baki ki gayamin, nikuma insha Allahu zan dafa miki muddin ina gida, in ma bana nan ga Yafendo, kada ki dinga zama ke kadai idan ba karatu kike ba". "Nagode, nagode Nene, Allah yayi muku sakayya da alkhairi, yadda kuka dubi maraici na Allah ya dubi haular ku a bayan ku".
****
: *SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)* 07030137870



A nata bangaren, Rahinah Omar, kwana tayi tunanin abinda ya faru a yau, tana mai tariyo komai dalla-dalla. Idan zuciyar jin tausayi ta kutso, sai zuciyar neman kwatar 'yanci ta hambare ta. Mutumin da bai ji tausayinta ba, ita akan me zata ji tausayin sa? Yana son ta koma ne don bukatun kansa amma bai taba tunanin ya tambayeta asalin ta ko na iyayen ta ba. Wanda ke kara tabbatar da cewa ba damuwar sa bace personal life din ta, abinda yake yimawa kawai shine a gaban sa.

Ita wannan soyayya ta Habibu ta kasa ganeta, domin ta hada biyu da uku bata bata ma'ana ba. Tana burin auren mijin da ke matukar son ta, wanda zai rungumi maraicin ta kada yayi amfani da shi ya cutar da ita, wanda zai so ta da dukkan zuciyar sa. Amma Habibu fa? Ta tabbata ba don cikin nan ba da daga ranar da ya sake ta bazai kara waiwayota ba tunda duk abinda yake so daga gareta ya riga ya same shi.

Tsaki tayi ta juya a hankali don taji dadin kwanciyar ta, sai taji gefen wuyan ta na kamshin Carolina Herrera (men) har zuwa lokacin. Abinda ya tuna mata da incidence din. Is what happened Haraam? Bata sani ba, in haramun ne tana neman gafarar Allah, domin kuwa bata da laifi, laifin ta shine kasa yi masa gardama wajen binsa tamkar rakumi da akala. "Ya salamu sallim". Ta fada a fili. Amma wani sako na zuciyar ta na gaya mata it's not haram din, tunda har yanzu cikin iddah take. Kuma abinda addini ke so a wannan tsakanin shine su yi sulhu. Sulhun da bata jin har abada zata yarda da shi.

Washegari Nene ta rakata anti-natal da suke zuwa duk sati, likita ta dubata sosai ta kuma ce baby is breach sai an gyara masa kwanciya. Haka ta daure aka gyara sannan ta karasa duba ta, tace tanaso tayi mata alfarmar zuwa dakin haihuwa tare da mijin ta, sabida suna so mata su dinga haihuwa akan idanun mazajen su, domin neman karin kauna da soyayya, jin kai da tausayi a garesu. Gashi bata taba ganin ta ta zo tare da shi ba.

Rahina dai bata ce komai ba, sai Nene ce ta ce baya kasar ne, amma in ya dawo kafin ta haihu da shi za'a shigo labour room.
Rahinah ta daga 'yan idanun ta taba kallon Nene kamar tace da ita akan me za ki mata karya! Mun rabu, short and simple. Sai ta tuna abinda Ambasada ya taba gaya musu cewa saki ba karamin abu bane a kasar jamus, and it should be abiding by German law. Don haka rufe zancen da Nene tayi kawai shine daidai.

Watanni biyu a gaba, ta shiga watan haihuwa, ta kuma gama shekarar farko ta karatun ta. Wato tsayin semester biyu. A haka take zuwa zana jarrabawa da tsohon ciki har ta kammala da kyakkyawan sakamako. Ambasada ya baiwa Nene kudi yace ta saya mata duk abinda zata bukata na haihuwa ba ruwansa da abinda Habibu zai bayar.

A daren ranar ne kuma sai ga tarin akwatuna shaqe da sitturun jarirai unisex daga Habibu Nahuche. Hatta pampas da feeding bottle sai da ya sayawa dan sa, amma ita ko tsinke bai saka da sunan ta ba. Wannan ya sosa mata rai ba don tana son abin hannun sa ba, a'a yadda ya nuna yafi son abinda zata haifa yanzu akan ta shine abinda ya sosa zuciyar ta.

"To a kan me?"

Zuciyar ta tambaya.

"A kan dalilin da nima ban sani ba!" Ta amsawa kanta a fili.
****


EDD dinta saura kwana biyar rannan da daddare suna zaune a dakin Yafendo suna cin tuwo taji damshi-damshi daga kasan jikin ta. Bata kawo komai ba sabida sabida bata ji ciwon komai ba. An ce mata kuma ciwo ake ji mai tsanani.

Amma ba'a dauki wani dogon lokaci ba ta soma 'yan mutsu-mutsun da ya ja hankalin Yafendo kanta.

"Yar nan lafiya kike yanka gumi haka?" Tayi yake tace "bakomai fa Yafendo, zafi kawai nake ji" Yafendo ta gyada kai ba don ta harda ba suka cigaba da hira. Safeenah ta shigo ta gaida Yakumbo, sannan ta dubi Rahinah tace "Nene ta ce kina da bako a falon Daddy........" amma kafin ta kai karshen maganar ta sai gani suka yi tana shure-shure. Yafendo tace "Aha! Ni na san abun ne ya zo, kika yi mirsisi ke ga jaruma. Ke Safeentu kira Nenen ku ki gaya mata haihuwa ta zo a kawomin reza". Safeenah ta zaro ido sannan ta fita a guje, kada taje ayi haihuwar a gabanta.

Nene ta fado dakin da gudunta, tace "Yafendo wace irin Reza? Ki rufa min asiri in mutu maza su kai ni, ba'a kasar mu muke ba inda ake haihuwar gida. Maza kwarara jikin ki Rahinah mu gangara asibiti, ga Habib nan yana nan ya zo sai ya kaimu tunda direba bai dawo ba har yanzu."

Tsananin halin da take ciki, shi ya hanata yin musun tafiya asibiti tare da Habibu kuma a cikin motarsa. Daga ita sai Nene a baya tana shafa mata kanta da bayan ta tana yi mata addu'a yayin da shi yake tuki cikin wani mawuyacin hali. Ji yake da zai iya da ya karba mata nakudar, kanar yadda ya zamo silar wahalar ta daga zuwa karatu.

Sun samu ganin Dr. Saliha Widad wato likitar data ke gani itace on duty, nan da nan ta karbeta akan gadon tura marasa lafiya daga hannun Habibu da ya sunkotota gabadaya daga cikin mota zuwa cikin reception. Dr. Saliha ta duba ta tabbatar haihuwa ce gadan-gadan sai ta fito tana kiran sa. Ta tambayi Nene shine mijin Rahinah? Nene ta gyada kai ba tareda ta ce komai ba, yayin da likitar tace "kazo ka tsaya tare da ita, ka ga yadda dan ka/'yar ka zai iso duniya".

Habibu ya hada kai da bango yana ce mata "a'ah..." tayi murmushi tace "ashe raggo ne baban baby, Rahinah ta fika juriya. C'mmon ka biyo ni nace". Ya juya yana kallon Nene sai ta gyada mai kai, don bata so a tsaya ana tone-tone. Ai har yanzu tana cikin zummar auren sa.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, haka ya daga kafa ya bi bayan Saliha Widad.
****


"Dada!"

Kawai take kira hadi da sunan Allah,ta yi gumi kashirban, kanta na bisa cinyoyin Habibu gashin kanta ya bazu jikin sa. Ya rike hannayen ta cikin nasa, ita take nakudar amma ya fi ta hada gumi, jikin sa har kyarma yake. Dr. Saliha na fadi tayi nishi baby ya kusan isowa. Da ta daddage ta saki nishin kuwa sai gashi ya fado tare da mabiyar sa. Ya kuma canyara kuka a hannun Dr. Saliha wadda bakin ta ya kasa rufo, shekarar ta kusan goma tana karbar haihuwa amma bata taba ganin haihuwar katon baby black beauty irin na Rahinah ba. Saidai bai dauko komai nata ba har duhun fatar sa na mahaifin sa ne.

Aka gyarata, aka gyara wajen haihuwar, aka dau baby ana gogewa da man zaitoon aka shirya shi tsaf cikin kayan sanyi, aka nannadeshi a shawul sannan aka kawo mata shi saitin kanta. Sai a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta ta kuma ji kamar a jikin mutum take kwance. Tana so ta kalli fuskar babyn amma tana son ganin wanda ya baje mata jiki ta kanannade akai ta haihu haka. A hankali ta daga kanta, sai idanun ta cikin na Habibu, wanda hakan ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba. Kafin ta soma yunkurin tashi ta kuma fashe da kuka.

"Amma Dr. Widad kin cuce ni......" ta fada cikin kuka sosai, kamar Dr. Na jin harshen nata, tayi Allah ya isa da fillanci, tayi da hausa, tayi da German, tayi davduk yaren data iya. Duk akan Dr. Widad data shigo mata da Habibu dakin haihuwa. Nene tana ta bata baki kan ta yi hakuri. Shikuwa ya harde hannuwa a kirji yana kallon ta da wani irin murmushin SO. In da a ce zai iya, zai iya ciro zuciyar dake kirjin sa ya bata a halin yanzu don kawai ya nuna mata dimbin godiyar sa da soyayyar sa gareta. Bisa bashi farin cikin da wani a duniya bai taba bashi ba. Bisa maida shi UBA, bisa bashi precious gem din da kudi ko mulki basu isa su bawa dan adam ba.

Dr. Ta mika mata Babyn bayan ta gama kukan bakin ciki ta share hawayen ta, da sauri ta karbe shi tana kallo. Ba shiri ta daga ido ta dubi Habibu. Yaro kamar Ubansa yayi khaki ya tofar. Ya lumshe mata lumsassun idanun sa ya kuma daga mata girar sa daya, "eh dani yake kama ba da ke ba, kamar ya san ba kya son uban sa". Ta gatsina baki ta cigaba da kallon babyn tana tazbihi a zuciyar ta. Wata irin kauna ta da da mahaifi na keta ruhin ta da zuciyar ta. Her only relative, her only blood! Ta yaya bazata so shi sama da komai a duniya ba?

Bata yi aune ba ta ji Habib ya kashe su da hoto da camerar wayar sa.

Hararar sa tayi, duk wani abu da zai bakan ta mata ya san shi, yanzun ma Nene na bada baya ya matso gabanta, "wai sabida kin haihu gabana kike wannan kukan? Yo wane dare ne jemage bai gani ba? Bani Da na nan in ji dumin sa, kin wani kama shi kin kankame kamar ke kadai kika yi nakudarsa". Ya mika hannu, ta yi maza ta janye dan ta.

"Ba zaka dauke shi ba!"

Ya saki baki yana kallon ta da mamaki, Nene ta shigo jin sautun kukan ta, tace "lafiya? Ki bashi yaron mana ya yi masa khutbah?""Nene bazan bashi ba, da na ne nikadai, ba ruwan shi da mu ba ruwan mu da shi" Nene tace "Rahinah kin san abinda kike fada kuwa? Mahaifin sa ne fa? Yau na ji karfin hali wai barawo da sallama. Ki bashi yaron nan kafin raina ya baci akan hakan". Rahinah ta saka kuka sannan ta mika masa yaron. Ya karbeshi da wata irin kulawa tamkar ya maida shi cikin sa. Yayi masa khutbah da sunan da ya zaba masa wato sunan mahaifin Manzo SAW. Ya tauna dabino (ajwa) ya sanya masa a baki, yaron ya hau motsa dan bakin sa gwanin sha'awa, Habib bai san lokacin da wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa ba. Ya rungume yaron a kirjin sa. A haka Ambasada ya shigo ya same su. Safinah ta biyo bayan sa dauke da kwandon abinci. Ya yi wa Habib da Rahinah "congratulations" sannan ya karbi yaron yayi masa addu'a.

Washegari aka sallame su. Suka koma gida. Tun daga ranar Habib yake zarya, sayo banza sayo hopi, duk don ya farantawa Rahinah. Amma ina! Zuciyarta ta riga ta kekashe akan Habibu, babu wani repenting da zai yi ya burge ta.

Babban tashin haankalin sa shine Rahinah ta gama iddah, gashi yayi alkawarin bazai maida ita ba da amincewa da yardarta ba, shima Ambasada bazai taba amincewa ba yayi forcing din ta akan abinda ta nuna ta gama bashi baya.

Tsayin watanni uku tana shayar da Abdallah kasancewar suna cikin hutun summer. Ta saba da yaron sosai, bata barci sai yana kan kirjin ta, har fargabar komawa makaranta take, don ta san dole zai koma haunnun mai raino. Ita kam ba wanda take jin zata iya baiwa dan ta ya rike mata yadda take ji da abun ta. Ko Habibu bata bari ya dauke shi sai in Ambasada yana gidan yayi mata jan ido. Gabadaya Habibu Nahuche ya gama susucewa, ya fita hayyacin sa don zuwa yanzu ya tabbatar da ya rasa Rahinah.

Lokacin da suka koma hutu Nene tace zata samar mata mai raino, amma Rahinah ta fito fili tace da Nene zata yi deferring karatun ta zuwa shekara ta gaba don ta samu damar kulawa da Abdallah. Da bashi cikakken lokacin ta a lokacin da yafi bukatar hakan.

Nene da Ambasada na jinjina soyayyar Rahinah ga dan ta, amma a zuciyar su suna tausaya mata. Don sun san irin wannan kaunar sai ka samu a karshe iyayen da 'ya'yan basa rayuwa tare. Kaunar tata tayi yawa kuma silence din Habibu na nufin wani abu. Yafi watanni uku bai kara takowa inda suke ba tun wani wulakanci da Rahinah tayi masa, inda tace idan ba ita ce autar mata ba, kuma ba daga kanta an daina haifar mata ba, sannan shi ba maye bane to ya fita hanyar ta ya je ya nemi wani gantalallen auren amma ba nata ba, tun daga ranar bai kara takowa ba, amma sakon shigar kudi basa yankewa a tsakanin su.

A wannan watan da ake ciki ya kammala rubutun proposal din sa, ya karbi shaidar kammala masters din sa, aka yi musu convocation na graduating. A ranar da ya karbi kwalin sa ya hada komai nasa don barin kasar Jamus. In bai yi kuskure ba yau ne Abdallah ya cika shekara daya da haihuwa kuma yana gudun sa ko'ina. Don daga baya ya kan je ganin sa amma iyakar sa falon saukar bakin Ambasada, a kawo masa yaron suyi soyayyar su ta uba da da, ya bashi sayayyar da ya yo masa, ya tafi ya bar shi yana kukan sai ya bi shi. Sun yi wani irin sabo wanda in zaka ga sanda zasu rabu sai zuciyar ka ta motsa, ka kuma tambayi kan ka shin ita Rahina wace irin zuciya gareta? Anya ma tana da tsokar zuciya a cikin kirjin ta?

A wani zuwa da yayi ganin Abdallah, ba tareda sanin ta ba ya fice da shi a mota, tun safe har yamma, a ranar Rahinah har dan karamin hauka ta yi, Nene na kwantar mata da hankali tana gaya mata bazai ki dawo mata da dan ta ba tunda nono yake sha. Yafendo kam haushin Rahinah ta koma ji sabida rashin kawaicin ta akan yaron, tace ita bata taba ganin mara kunyar bafullatana irin Rahinah ba, rashin kunyar tata shahararriya ce kuma a kan dan fari, inji Yafendo. Idan ta kaita bango kuma ta ce "kinibabbiya, sanda tasa Uban sa a daki yayi mata cikin sa ai bata ce masa rowar sa zata yi masa ba idan sun haife shi, in da gaske take son yaron ta koma gidan ubansa mana?

Dukkansu basu san inda Habib ya kai Abdallah ya kuma dawo dashi ba.

Rahinah kamar ta shide da Abdallah ya dawo don murna.
****


Yayi sallama a falon Ambasada Shehu, shi kuma ya amsa cikin sakin fuska da mutuntawa kamar yadda suka saba a kowacce haduwar su. Har kasa ya tsugunna ya gaishe shi. Shikuma ya soma yi masa fada akan irin ramar da yake yi, da kyar idan yana cin abinci yadda ya kamata. Ya ce "shi mace bata isa tasa shi a wannan halin ba, don dukkansu daga karkataccen hakarkari aka halicce su. Yana da tabbacin Rahinah zata huce watarana kuma da kanta zata nemeshi ta nemi dawowa dakin ta. Haihuwa a tsakani ba wasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login