Showing 90001 words to 93000 words out of 110913 words

Chapter 31 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

don't have your phone number, (na fahimci bata da lambar wayar ka), kai ma ba ka da lambar wayar ta?"
Da sauri ta bude ido ya sauka cikin nasa, duk suka kalli juna a tsorace. Habibu ya ce, "Inquisitive Abdallah I have your mother's phone number, amma a nan (ya nuna saitin zuciyar sa) in ba ka yarda a yanzu in karanto maka ka ji".
"Daddy na san ba ka karya, Mummy ke fa? Kina da number din Daddy na?"
Rahinah ta rasa abin da za ta ce, kafin ta tuna Abdallah is now a sick person, a mental patient wanda abin da yake bukata kawai shi ne a yi masa abin da zuciyar sa ke so, wanda ba komai ba ne sai shiryawar su.
"Abdallah, I've your Daddy's phone number, yanzu ma ya turo min message da ita, kana so ka gani?"
"A'a, ki dai karanto min in ji".
Da sauri ta dubi Habibu da idanun neman agaji, shi kuma ya kau da kai ya yana 'yar dariya, ya san yau Abdallah ya saka ta a kwana.
"Abdallah zai fi kyau shi da ya turo sakon,ya karanta maka ko?".
Habibu ya ce me ye a cikin sakon banda I really-truely LOVE YOU? And I promised a changed person?"
Ya fada yana kallon cikin idon ta, kwayar idanun sa sun kada zuwa love colour bakidaya, wanda hakan yasa Rahinah jin kunya mai yawa, ba shiri ta hau rufe fuska da tafukan ta kamar wasu saurayi da budurwa, domin Habibu ya ki dauke rinannun idanun sa a kan ta, wanda hakan yasa Abdallah tuntsirewa da dariya yana fadin.
"Mummy ki bude idon ki, we love you!"
Likita Mansur ya turo kofar dakin ya shigo yana clapping hannayen sa. Don tun daga waje yake jiyo dariyar Abdallah.
"Abdallah and parents, what a good scene? Ina fata sun daina fada Abdallah?"
Abdallah ya yi wani iri da fuska ya ce, "Doctor sun daina ka sallame mu mu koma gidan mu, kuma ka roke ta ta karanta min text din da ta ce Daddy ya turo mata daga PH".
Dariya likitan ya yi yana shafa kan yaron. Sosai ya ji yana son sa sabida wayon sa. Hes really smart.
Ya ce, "Abdallah this is their secret, ka ji? (Wannan sirrin su ne). Ba ruwan ka da abin da Daddy yake rubuta wa Mummy a waya, what matters most... (abin da ya ke muhimmi) shi ne su daina fada saboda ba ka so, su zauna lafiya har abada for you to stay healthy".
Ya gyada kai cikin fahimta, likita ya ce, "That's my boy. Amma ba zan sallame ka yanzu ba Abdallah sai nan da sati uku, in na tabbatar (heart beat) din ka ya koma normal".
Bayan fitar likitan, Habibu ya dubi Rahinah ya ce,
"Abdullah abin da na tura wa Mummy ko ni ban san me na tura mata ba. I just texted her to check on you sanda ina PortHearcourt".
"Ina fatan ta ba ka amsa?"
"Sosai ma, na ba shi amsa tun a lokacin".
Habibu ya dago lumsassun danun sa ya yi mata wani irin kallo, da ya sa bakidaya ta nemi nutsuwar ta ta rasa ta rikirkice, sabida ita ba gwanar karya bace da ta yi ake gane ta. La shakka da a tsaye ta ke ba a zaune ba, ba abin da zai hana ta faduwa kasa sabida yadda Habib yake hukuntata da sexy idanun sa.
"Mai karya dai, dan wuta!".
Rahinah ta juya kai gefe tana 'yar dariya a kan kalaman sa, ba tare da ta shirya yin hakan ba. Dariyar da ta shagalar da Habibu a cikin kallon ta da duk ya bi ya maida Rahinah unease, ta soma tunanin abin da zai tada ita daga gadon.
Gashi kan Abdallah na cinyoyin ta, shi kuma yana zaune a daidai kafafun sa. Abdallah ya ce,
"Zan sha ruwa".
Tun bai rufe bakinsa ba uwar da uban suka mika hannu domin dauko masa a kan (bed-side drawer), hannun ta ya riga na Habibu sauka a kan gorar ruwan Faron, kasancewar ta fi shi kusa da lokar, sai hannunsa ya sauka a kan nata.
Another unbearable chemistry like electrical shocking ya bakunce ta, wanda ya sa ta saurin dagowa ta dubi maigidan ta Habib Nahuche, sai aka yi sa'a idon ta ya sauka cikin nasa.
Habib sai ya samu kansa da cure yatsun ta da ke kan robar Faro a cikin nasa hannun, wanda hakan ya sa Rahinah saurin runtse idanun ta. Tana karbar wasu sababbin pleasant feelings a zuciyar ta da ta kasa gane ko na mene ne, ko daga ina suke yunkuro mata.
Habibu ya yi azamar dauke hannun sa daga kan nata sakamakon cewa abinda ya bakunce ta shima kwatankwacinsa ya ji, sannan ya dauki ruwan ya bude wa Abdallah.
Kunya ta ji sosai kan irin reaction din da ta nuna. Kawai daga Habibu ya rike hannun ta. Dare ya fara yi sosai, dakin ya yi shiru domin Abdallah ya yi barci. Su kuma kamar masu ciwon baki sai zukata da ke adungure a cikin kirjin kowannen su.
Rahinah na so ta ce ya tafi gida, tana so ta gyara gadon ta kwanta, ta rasa da bakin da za ta gaya masa hakan. Ya tattara hankalin sa kacokam ya dora a kan wayar sa, ga dukkan alamu chatting yake yi, kawai sai zuciyar ta ta gaya mata da mace ne, bazawarar da yake nema in ba haka ba da wa zai ke chatting karfe goma sha biyun dare? Kawai ta ji tsuka (tsaki) ya kubuce mata. Wani matsanancin kishi ya zo ya lullube ta.
Habibu ya ji tsakin, amma bai zaci nasa bane, sai ya dago shanyayyyun idanun sa ya dube ta da idanuwan bidar bayani,
"Shin tsakin nan nawa ne ko na wani ne daban?"
Juyar da kai ta yi gefe, ciki-ciki ta ce, "Don Allah ina son filin gadon, zan kwanta kusa da Da na. It's almost past twelve yanzun".
Kin dauke ido ya yi a kan ta, wanda hakan ya sa ta ji duk ta takura. Ya ce,
"Ni kuma yau till down zan yi a zaune ina kallon kyakkyawar fuskar bafulatanar mata ta Rahinah Omar. She's indeed a heroine. Domin a rayuwa ta ban taba ganin mace mai aji, mai kullata, rashin afuwa, rashin yafiya da kafaffiyar zuciyar ta ba.
I wanted to ask Rahinah since, shin zuciyar ta ta dutse ce? Ko kuwa kurmar zuciya gare ta? Shin Rahinah ke a wurin ki lokaci ba ya maganin kullata, a tunani na time heals everything! It's almost a decade and above, amma har gobe Rahinah na nan a yadda na san ta.
Ni Habibu Mustapha Nahuche, dan adam ne kamar kowa, mai tarin nakasu (flaws), kuma mai zuciya da gangar jiki irin na kowanne lafiyayyen dan adam.
In haka ne ta ya ya ba zan kasance cikin masu aikata kuskure ba? In ankara, in so gyarawa, amma a hana ni damar gyarawar?
I'm not saying all these to own your body, I'm saying it because I want you to know that I'm human, not a saint, or a Prophet (ba ina fadar duka wadannan don in mallaki jikin ki da zuciyar ki bane, ina fada ne don ina son ki san cewa nima mutum ne kamar kowa, dan adam ajizi, ba waliyyi ba ba kuma Annabi ba, wadanda ko su ba su tsira da aikata kuskure ko sau daya ne a rayuwar su ba).
Allah shi kadai yake PERFECT a komai Rahinah. I'm saying SORRY for all that happened, a decade ago, from the bottom of my fragile heart.
Sorry for all the grievances and inconveniences that I caused to you Dr. Rahinah, na yi miki alkawarin zama na soyayya da farin ciki mai dorewa har zuwa karshen rayuwar mu. I promised to be far-away from your body...... tunda wannan shine babban abinda ya janyomin bakin jini a wajen ki".
Da sauri Rahinah ta shiga girgiza kai, ammma ta kasa cewa komai, domin kalaman dake fita daga bakin sa a yau bata taba zaton su ba. Anya Habibun ta ne? Her ex Habibu ne? ko wani mai tsananin kama da shi ne??

Bata fita daga wannan mamakin ba, Habib Nahuche, ya sake gigitata da sabon mamaki. Ta hanyar kamo hannayen ta ya rike su tsam cikin nasa.
"Rahinah KIN HUCE?"
Tunda ya fara maganar zuciyar ta ke luguiguita tana kakkaryewa tana kara HUCEWA, domin ta yarda da dukkan kalaman da ke fita daga bakin sa, haka suke har kasan zuciyar sa.
"Ni na ce maka ina fushi ne? To Habibu NA HUCE".
Ya yi mata kyar da ido.
"In ba fushi ki ke ba, me ya hana ki biyo bayan mu? Ban taba tunanin zan isa Nigeria lafiya ba tare da kin tara min mutane a kaina ba da sunan na sace miki Da, bayan nan ki ka dawo ki ka kama ayyukan gaban ki ko sau daya ba ki taba tunanin ki neme mu ba.
In ni ba ki neme ni ba don na yi miki laifi Rahinah, which I'm sure daga baya kin huce kin yi kewata yadda na rayu cikin kewar ki, abinda kike nunawa a zahiri ba haka ba ne a zuciyar ki ba, ai kya nemi dan ki ko? Ki binciki rayuwar sa ko lafiyar sa? Ki ga shin ya ya muke rayuwa? Amma ko sau daya! Baki yi hakan ba.
In gaya miki gaskiya wannan shine babban abinda yayi min ciwo bayan rabuwar mu har fiye da takuramin sakin da kika yi. Kullum a tunani na da tsinkaye na shine zaki dawo da kan ki ki nemi mu koma saboda dan mu, a yayin da kika yi achieving goals din ki. Sai kika nuna min kashi ma ya fi mu daraja ko bayan actualizing goals din".

Ba ta san sanda ta yi dariya ba, ta ce, "Ko? Bari in gaya maka abin da ba ka sani ba...
Duk wani step further da ka taka a rayuwar ka bayan dawowar ka Nigeria ina bibiye da shi.
I'm the first to send an appreciation message to BBC HAUSA a shirin nan na DOMIN MATASA....
I'm the first to send an appreciation message zuwa ga jaridar NEW NIGERIA a kan shirin 'A ROLE MODEL NIGERIAS HOTELS OWNER....
Ni ce ta farkon aika sakon jin dadin shirin "The Legend of the Sahara... HABIBU NAHUCHE na gidan Radiyon Jamus a shekarun da suka gabata...".

Sakin baki ya yi galala! Yana kallon ta domin ta gama mamakantar da shi. Ta shammace shi da abin da bai taba sani ba.
"Abin da kawai ban sani ba a kan ka cikin shekaru goman shi ne, kasancewar ka kanin Aunty Badiya, wadda nake tare da ita sama da shekaru shidda, tun zuwan mu daga Jamus na farko lokaci da na hadu da dangi na.
Had I know ita ke rike da Junior kai ma ka san da tuni wani labarin ake ba wannan ba".
Tasowa ya yi daga inda yake zaune, ya zo ya durkusa a gaban ta daga gaban gadon, ya dora tafin hannun sa saman tafin kafar ta.
"That is what I don't know either. Had I know da tuni ni ma wani labarin ake ba wannan ba".
'Yar dariya ta subuce mata jin yana yi mata tausa a kafafun a hankali har da tafiyar tsutsa . Ta ce,
"Da wane labarin ake to zuwa yanzun?"
Yatsun sa biyar ya daga ya wara mata a kan fuskar ta.
"Da yanzu su biyar ne ba shi kadai ba".
Ta gane abin da yake nufi, wanda hakan ya sa ta murmushi (serene smile) amma sai ta nuna bata gane din ba.
"Su su wa kenan?"
Ya ce, "Abdallah da kannen sa mana".

Hira mai ban mamaki da ratsa zuciya ta ci gaba da gudana (heart to heart) wato daga zuciya zuwa zuciya tsakanin Habibu Nahuche da mai dakin sa Rahinar sa. Hira ce irin wadda ba su taba yi a tsayin rayuwar su ba. Ta ba shi labarin duk halin da ta shiga bayan tahowar su. A karshe ta ce.
"...And evetually I moved on, kafin na gane rayuwar diya mace bata taba cika cikakka idan babu SOYAYYAR MIJI, sai dai hakan ba ya nufin faduwar diya mace warwas, in dai za ta iya kare mutuncin kan ta ta ribaci lokutan rayuwar ta da neman ilmi da neman lahira.
Sabanin sauran mata da ke bata lokutan su wajen kuka da halin maza na sun musu, sun musu kaza da kaza, har hakan ya taba kwakwalwar su ya hana su cigaba. Ni Rahinah I'm apparently a strong woman, wadda ta dauki goal attainment (self-actualization) da matukar muhimmancin da ya danne soyayya.
Shi ya sa na zauna lafiya kalau, in na ce lafiya kalau, ina nufin fa lafiya kalau...".
Irin kallon da Habibu ke mata ya sa ta saurin toshe bakin ta tana dariya. Domin kallo ne na karya kike yi, in fact, you are not well at all.
Ya ce, "Wallahi ba lafiya kalau ki ke ba, sabida ita soyayya barin rayuwa ce, kuma halittar Allah tsakanin Adamu da Hauwa'u.

ABRAHAM MASLOW (1970) (psychologist) wanda ya samar da %?oheory of Self-Actalization. Ya sanya ta cikin jerin rukunin bukatun rayuwar dan adam guda bakwai, wadanda ba zai iya rayuwa babu su ba (HIERARCHY OF NEEDS THEORY OF MOTIVATION).
MASLOW ya ce;

"As long as the more urgent and pressing need is satisfied, another urgent need will emerge and become operative, and a currently satisfied need will become unimportant and underestimated and no longer controls or dominates behaviour...".
-(Abraham Maslow, 1970).

Dariya ta yi cikin matsanancin nishadi, kace ka tashi da 'Hotel Administrator' ka koma malamin %?visychology".
"Ko daya, ni ba ni da alaka da psychology amma na san wannan, na kuma kawo miki misali da theory din ne don ki san cewa, bayan self-actualization din ki ya gamu, dole ki dawo daga baya ki nemi soyayyar miji da ta 'ya'ya (Love and Belonginess Need). Wannan a rubuce yake, sai dai kuma idan Rahinah waliyya ce ba mu sani ba".
"Yanzu ka bar maganar Maslow a gefe, na yarda da kai with no temptation, amma don Allah me ya sa ka aure ni a yadda ka aure ni a Jamus?"
Ya rausayar da kai ya yarfar da hannu ya ce, "Only men in mid - twentieth can relate. I have no option a wancan lokacin, in ba so ki ke in kare da raping din ki ba kuma in kare (behind bars) ban da babbar azabar Allah da za ta jiraye ni ranar gobe kiyama".
Ta kai kyawawan yatsun ta ta rufe fuskar ta, "Habeeeebu you are too much".
"Har na kai ki? My sweet sixteen my Bafulatana Rahinah Omar Girei. Duk da na sha wahala, ina kuma kan shan ta har yau ina alfahari da wannan gantalallen auren.
Ga kyautar Allah wadda bani da tamkar ta (Abdallah).
And by so doing, i then came to realized the worth of a WOMAN, inda na gane abubuwa da dama a kan mata, na gane ba duka mata suka taru suka amsa suna daya ba na cewa su duka raunana ne a kan soyayyah, akwai masu kare %??jelf esteem%??? din su koda soyayyar zata yi ajalin su, wadanda basu dauki soyayya da namiji shine rayuwar su ba, a typical example of my Bafulatana Dr. Raheenah Omar Girei. I salute!!!.
(Ya fada yana yi mata gaisuwar sojoji). Kan ta yayi gingirin-gin. A fili ta ce (cikin shauki).
Baban Abdullahi kana fasa mun kai!
Ba maganar fasa kai bace maganar gaskiya ce. Wanda hakan ya kara sawa na girmama ki, na kara daga darajar ki a zuciyar Nahuche.
Amma don Allah ina rokon alfarmar daga yau dinnan in tashi daga HABIBU in koma HABEEBEE.
Rahinah sai dariya ta ke. Cikin matsanancin nishadin da bata taba tsintar kanta ba. In wani ne ya gaya mata watarana irin wannan na zuwa, da Habibu Nahuche zai tsaya a gaban ta ya bude baki yayi mata magana mai tsayi har haka za ta karyata. Sabida karancin maganar sa. Habibu ya mike daga durkuson da yayi a gaban ta ya koma jikin gadon ya jingina, tare da harde hannayen sa a kirjin sa.
%??mo yanzu dai kin gane ko Maam? Ke da Dan ki ku gyara min waje in kwanta, yanzu zaki ji an kira asubahi bamu runtsa ba, barci nake ji sosai".
"Ai gadon ya mana kadan mu uku Habeebi. Ba ka ganin ba shi da fadi?"
"A haka za mu yi maneji, rayuwa sai da maneji da abunda ka samu. A baya ina na samu wannan alfarmar?.
A hakan suka kwanta. Rahinah a barin dama, Habibu a barin hagu, Abdallah a tsakiyar su, %?nuch is life my dear wife, yadda ta zo wa bawa a haka ya kamata ya karbe ta". Ya fada yana gyara wa Abdallah kwanciya, suka sanya shi a tsakiya suka rungume, suna fuskantar juna suna kuma kashe juna da ravishing smile.
"This is pure contentment of my life". Habibu Mustapha Nahuche, ya fada a ran sa yana sarke yatsun kafar sa cikin na Rahinah, wani irin jin dadi na tsirga masa. Rahinah ta rungume Junior da hannu daya, hannun ta daya cikin na Habibu, idanun ta cikin nasa suna yi wa juna kallo na kauna da soyayya.
Da zasu iya, hakika da, sun rike wannan moment din daga motsawa kada gari ya waye, wani abu ya zo, ya gifta a tsakanin su.
Sai ya mika hannu ya latsa makunnin fitila shudiya ta maye gurbin mai haske (dim light), ta cikin dan hasken shudiyar fitilar suke hango kyallin hawayen da ke kwance yana tsatstsafowa cikin idanun kowannen su.
Hawayen so da farin ciki, wanda kwanciyar hankali kadai ya yi sanadin sa cikin idanun Habibu da Rahinah.

Tun tana tsammanin Habibu zai yi kalar wani motsi bayan wannan (ya nemi taba ta ko kissing din ta) har ta ji saukar numfashin sa a hankali mai nuna ya yi barci.

Da ace wani ne ya gaya mata za ta kwana gado daya da Habibu watarana ba za ta taba yarda ba. Da dai wani ne ya gaya mata Habibu zai iya kwana gado daya da ita bai nemi komai daga gare ta ba, ba za ta taba yarda ba.
Da asubah shi ya fara tashi sakamakon kiraye-kirayen sallah a masallacin asibitin. Junior ya motsa ya ji an matse shi a gadon sa, sai ya bude ido a hankali ya gan shi tsakiyar iyayen sa biyu. Wani abu da bai taba faruwa ba tun dawowar Rahinah cikin rayuwar su.
Sai ya sa hannu daidai ya rungume kowannen su, ya ci gaba da barcin sa a haka.

Habibu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login