Showing 21001 words to 24000 words out of 110913 words

Chapter 8 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ni 'ya su sai ka ce wasan yara? Ina uwar dan da za ka dauko wannan dan tatsitsin yaron tun daga wata uwa duniya kai kadai?"

Habibu Nahuche, bai taba barin weakness din sa ya bayyana a gaban kowa ba, amma wannan UWA ce MAHAIFIYA ce, kafadar da kowanne dan Adam ke iya sauke damuwar sa babu haufin komai. Don haka sanda ya fara hawaye bai san sun zubo ba, dacin tuno kiyayyar Rahinah gare shi, sai da ya ji saukarsu a kan kundukukinsa, da damshinsu a kan fuskarsa.

"Na yi duk iya kokari na a kan ta so ni, ta zauna da ni mu raini dan nan da Allah ya bamu tare abu ya faskara. Ban san meye aibu na har haka ba da Rahinah ta ki ni. A karshe mun rabu, rabuwa ta har abada, ni kuma na dauke Dan ba da saninta ba, amma marikanta sun san na dauke shi".

Ya kwashe gaskiyar komai, har sanadin auren ba-zatan ya gaya mata, sai dai wani sirrin ai bai faduwa, balle sirrin aure. Ya tsaya ya kafe a kan Raheenah ba ta sonsa kawai, sabida ya aure ta baa hannun iyayen ta ba, yace aurensu kaddara ne kawai da rabo rantsatstse daga Allah.

Haj. Kaltume ta rasa abin da za ta ce, amma sai ta ji ya fi mata a kan a ce Habibu zina ya yi ya kawo mata yaron nan. Ta rungume Abdallah sosai a kirjinta, wanda zuwa lokacin ya samu barci yana sauke ajiyar zuciya.

A daren ranar ta kira Badiyya wadda ke aure a garin Kaduna, ta ce duk abin da ta ke ta bari gobe ta zo Zamfara maganar ta fi karfin waya.
Sannan ta sa almajiri ya share wa Habibu dakinsa, ya wanke masa toilet dinsa, sannan ya shigar masa da dukkan kayansa.
Girki na musamman ta yi musu, tuwon shinkafa da miyar taushe da naman saniya zuku-zuku a ciki, ta yarfa man shanu sannan ta hadawa Habibu kunun zaki kasancewar yana son shi sosai mutumin sa ne, amma na gasara ziryan ba na farau-farau ba.

Da dare ya yi Abdallah ya rikice kan bai kwana tare da Hajiya, sai Momin sa, don haka tare suka tafi dakin sa dake zaure yana ta rarrashin sa, sai da ya yi barci ya dauko shi ya maido wa Hajiyar shi.
Hajiya Kaltume tana sallahr dare kamar yadda yake a aladar ta, jefe-jefi tana juyawa tana kallon kyakkyawan yaron dake barci cikin nutsuwa a gefen ta mai tsananin kama da Habibu, tamkar Habibun a lokacin da yana kamar sa, kaunar yaron na dada shiga ran ta, a cikin kowacce sujjadah data yi tana yi masa addua Allah ya raya shi rayuwa mai tsayi da albarka.

Cikin wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar Habib da Raheenah. Dukkan su babu wanda ya runtsa. Ya fidda layinsa na kasar Jamus ya karairaya shi, ya taune shi ya zubar, ya saka MTN NG da ya saya a filin jirgin saman Abuja. Yana fatan yadda ya karairaya shi haka ya zubar, zuciyar sa ta karairaya Raheenah Omar ta zubar, da duk abinda ya shafe ta.

Amma ko da ya so yin barci, sai barci ya ce dauke ni inda ka ajiye ni. Shin ko yaya rayuwa za ta ci gaba musu shi da Abdallah? Shi maraicin matar da yake so daya da daya a duniya? Abdallah maraicin uwar da ya budi ido da ita?
Wata Tambaya ce mai wuyar amsawa farat daya, da ya kasa amsawa kan sa, ya ce bai son ta ma ya san wannan yaudarar kai ne. Raheenah Omar, ta shigo rayuwar sa da wani irin karfi, ta yi tasiri mai yawa a cikin ta cikin auren da bai gaza kwanaki bakwai ba. Tasirin da kafin ya yi nasarar cire ta kwata-kwata, shi ma ya san zai sha wuya, kuma abu ne da ba zai tabbata a lokaci guda ba.
But gradually, by trying to follow the path of reality; yana fatan canzuwar kaddararsu, yana fatan Raheena ta bar zuciyarsa ta sha iska haka, ta bar kwakwalwarsa ta sarara, ta bar gangar jikinsa da ruhin sa su huta. Ta bar sababbin abubuwa da suka fi ta muhimmanci su shigo.

Ba shi ya iya runtsawa ba sai da ya dawo masallacin Kofar Jange sallar asubahi, sannan ne barcin gajiyar da ya tara ta zaman jirgi da shirye shiryen dawowa da ya jima yana yi ta karkashin kasa suka taru suka danne shi bakidaya.
******



Kukan Abdallah ne ya tashe shi wajejen takwas na safe, ya karade gidan da kuka yana kiran ABBANSA da MOMIN SA... cikin harshen Jamusanci. Zuciyarsa ta yi wani irin karyewa, anya cikin hukuncin da ya yanke babu zalunci a ciki ga yaron da ma uwar kan ta?
Yanzu haka yaron zai tashi bai san mahaifiyarsa ba alhalin tana raye a kololuwar duniya?

Da tsananin mutuwar jiki ya fito tsakar gidan hannayensa zube cikin aljihu. Ya zubawa yaron ido daga bakin kofar shigowa cikin gidan. Idanun sa sun kada Abdallah na ganin sa ya taho da mugun gudu ya rungume shi, sannan ya soma gaya masa cikin harshen da yafi iyawa ya maida shi gun Mummyn sa, tashi Mummy din ba wannan ba, yana nufin Hajiyar sa.
Hajiya Kaltume ta fito daga daki tana ta mita.

"Dan nema rigimamme, sakaltacce, ni bana son shagwaba ko kadan, da alama gidan ku can sun gama sangarta ka, in ba haka ba ta ya ya gotai-gotai da kai za ka saki kashi daga tsaye? A ba ka foo ka ki hawa?"

Murmushi Habib ya yi, shima ya san da gaske gidan Ambassada sun sakalta Abdallah, ya karaso inda ta ke yana dauke da Abdallahn.

"Ke da maigidan naki za mu gan ku a rana, Maman shi pampers ta ke saka mishi ba ta dora shi a wani foo".

Hajiyar Nahuce ta ce, "Au? Tunda irin 'ya'yan Badiya ne, to ba zan iya ba, ta zo ta dauki abin ta (Badiyar), su ma haka ta sangarta su da kin hawa foo, yaro dan shekara biyar sai ya saki kashi cikin auduga, mu ba haka iyayen mu suka raine mu ba, to ni ba zan iya wankin kashi a cikin pampers ba da girman yaro da komai".

Karshe Habibu ya je ya siyo pampers gari guda ya kawo mata, yana rokon ta kan ta lallaba Abdallah, a hankali zai koyi hawa foo din. Shi zai dinga yi masa tsarkin ya fidda pampers din. Hajiya sai ta ji su duka sun bata tausayi.

Sai wajen la'asar Aunty Badiyya ta iso daga Kaduna, Aunty Badiya ba ta kama da Habeebu sam, bazaka ce ma cikin su daya ba, don ita mahaifin su sak ta dauko, fara ce ita Barumiyar Nahuce, sabanin Habeeb da yake wankan tarwada.
Aunty Badiya 'yar boko ce sosai, domin kuwa (PHD holder) ce. A wannan lokacin ita ce mataimakiyar Provost ta (Kad-Poly), yayin da mijin ta babban ma'aikaci ne a Abuja, sabida aikinta ta ke zaune a Kaduna sai karshen mako yake zuwar musu.
Yaran Aunty Badiya hudu ne duk maza ta karshen ce kawai mace, Zarah, wadda ba ta fi sa'ar Abdallah ba.

Zuwan Badiya gida da ganin kanin ta da ta yi da Da, da labarin da ta tsinkaya daga bakin mahaifiyar su ya bata mata rai ba kadan ba.

Ta yi fadan kamar ta yi ya ya! A karshe ta ce, "Allah ya kara da ba ta son naka, Allah ya kara karawa, yanzu ai sai ka hakura ka zo ka auri mai son ka (tana nufin yar uwar sa Shafa'atu)".
Ita babban bacin ran ta yadda ya boye musu maganar auren nasa a Jamus, kamar wani wanda bashi da kowa, amma Hajiya Kaltume da ta ga fadan Badiya ya yi yawa, duk hakurin da Habibu ke ta bata ta ki sauraron sa, sai ta ce.

"Maman Zarah, hakuri za ki yi mana, laifi kam ya riga ya yi sai dai tunda ya bada hakuri kuma ya ce ya yi ne don ya ceci kansa daga aikata zina a can, ai ina ga wannan ya isa hujjah, ni tuni na dauki kaddara.

Yaro Allah ya raya mana shi, Ya sa Mahaddacin Alqur'ani ne".
Badiya ta ce "Hakuri na daya ne Habibu ya auri Shafa'atu, ban ce ta rike masa yaro ba, ni zan hada da na waje na in rike, amma auren sa da Shafa'atu ya zama tilas".

Habib da yake neman a yafe masa, ba abinda ba zai yi ba a lokacin. Ya ce da Yayar sa Badiyya "ki bari na gama NYSC sannan a yi maganar auren, ni yanzu da ba ni da abin yi, da me zan yi auren?"

Badiyya ta ce, "A can Jamus da me ka yi auren? Cewa nake karatu kake a inda baka da kowa ma? Balle anan da mu zamu rike maka matar. Ka yi auren ka dandani dadin sa da rashin dadin sa ne zaa kyale ka ka ci gaba da zama a haka?
In dai Shafa'atu ce ba bakuwar zafi ba ce, za ta iya zama a gidan nan tare da Hajiyar mu, sai a gyara muku sassan Baba".
Mikewa ya yi daga gurin yana kakkabe rigar sa, har da kunkuni kamar kuturu yana fadin.

"Ke za ki dinga ciyar min da matar? An ce miki a Jamus ko kai dalibi ne kana rasa aikin yi da zai rike iyali? Nan kuwa fa? Ai ki ji da kan ki kawai Yaya Badiya, ki kyale ni in nemi kobo. In gwaninta za ki min, kawai ki kular min da Abdallah".

Yaron da ya riga ya shige zuciyar Dr. Badiyatu Nahuce farat daya, har fiye da son da takewa Habibu, ta kara rike shi sosai a jikin ta tana hararar Habibu, a lokaci guda tana mamakin irin karfin jinin sa. Yaro kamar Habibu yayi kakhi ya tofar, bai da maraba da shi a lokacin da yana kamar shi. Addu'a ta ke cikin ran ta Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran kula da Abdallah, kamar, ko ma fiye da yana gaban mahaifiyar shi.

A washegari ta juya da Abdallah gidan ta a Kaduna.
******





NA HUCE.... Is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara
Firstbank
Shaidar biya 07030137870
*SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) 07030137870*


PAID BOOK



Ba jimawa da dawowar sa ya yi registration na tafiya hidimar kasa. Aka tura shi Kwara State, ya tafi ya bar Abdallah hannun Yayar sa Aunty Badiya.

Haka yaro Abdallah ya rayu karkashin kulawar Kakar sa Hajiyar Nahuce da Yar mahaifin sa Dr. Badiyatu Mustapha Nahuce, suna zuwa Kaduna ta sanya shi a Kindergarten na (Kad-Poly) tare da diyar ta Zahrah, kullum sai ta sauke su sannan ta wuce aiki.

Sha biyun rana ta sa masinjanta ya dauko su, a can ofis din ta za su yi ta wasan su a gaban ta har ta gama abin da za ta yi su koma gida.

In aka yi hutu kuma ta kawo shi Zamfara ya yi hutu a hannun Hajiya Kaltume, sabida wayon yaron da kokarin sa a karatu da hikimar sa da saurin shiga rai a wajen malamai (double promotion) aka yi ta yi masa ya koma Nursery 3 daga Nursery 1. Sanan duk karshen zango shi yake zuwa na daya a aji, kuma sai ya dawo da prizes gida. Dr. Badiya (is highly proud of her son Abdallah) tana fada a koda yaushe. Yana tuna mata da kuruciyar Abban sa shima haka yake da yana kamar sa. Duk inda yayi karatu sai yayi tambari.

Zuwa wannan lokacin Abdallah ya manta da Raheenah, ya dauki Badiya a matsayin mahaifiyar sa. Hajiya Kaltume da yake kira "Granny kuma ya san Kakar sa ce wadda ta haifi mahaifin sa. Yana kara girma yana fahimtar alaqar sa da kowa.
Tsakanin shi da 'ya'yan Aunty Badiya ba za ka taba iya bambance wanne ne nata wanne ne na kanin ta Habib ba. Yayyen nasu Musaddiq, Mubaraq da Mu'allim suna kula da shi sosai shi da Zarah, don kuwa Uncle Habib (yadda suke kiran Habibu) ba su ajiye shi nan kusa ba, suna matukar son shi, sabida yadda yake nuna musu kauna shima duk lokacin da ya zo ganin Abdallah daga Kwara. Kaunar jini ce ta cakude da kauna ta musamman wadda suke yi wa Uncle Habibu, ta shafi dan sa Abdallah. Ko kuda in suna da iko ba zai sauka akan Abdallah ba.

A haka ya kammala NYSC, sai Aunty Badiya ta karbi takardun sa ta baiwa Baban Musaddiq ya tafi da su Abuja don nema masa aikin yi.

Kasancewar Baban Musaddiq babban ma'aikaci ne a Federal Ministry of Commerce and Industry wadanda Federal Govt. ke damawa da su a lokacin. Ga shi ya san manyan ma'aikata a can Abuja domin ya dade yana aiki, sai bai sha wahalar samar wa Habibu aiki ba tunda abu ne na wa ka sani, gashi da (qualifications) na Cologne University, ya samu aiki mai gwabi a babban Hotel din NICON NOGA, a lokacin shi ne hotel din da babu na biyun sa a Nigeria. Kuma fannin da Habibun ya karanta kenan wato (Hotel Administration).

Habib ya dade a Nicon - Noga, matsayi iri-iri a ya rike a cikin ta, daga karamin matsayi zuwa sama, promotion kan promotion akai-akai. Wani irin mutum ne shi mai nasibi akan duk abinda ya sa gaba. Ba don haka ba manyan mukaman da yake samu akai-akai a NICON cikin 'yan shekaru kalilan da bai isa ya same su a yan shekarun ba. Don akwai wadanda suka fi shi jimawa amma basu kawo matakin shi ba, abin kuma har da kwarewa da baiwa ta daban (exceptional talent) da Allah ya bashi.

A lokacin ne aka bude babban hotel din Najeriya watau TRANSCORP HILTON inda Habib da wasu daga cikin manyan ma'aikatan (Nicon - Noga) suka samu karin matsayin komawa (Transcorp - Hilton), inda Habeeb ya rike mukamin mataimakin manager, ba kananan kudi ke shigo masa ba domin kuwa a Nigeria gabadaya babu hotel din da ya kama kafar (Transcorp - Hilton) a birnin tarayyah.

Yawanci turawa, larabawa da sauran jajayen kunnuwa ke sauka a can idan suka zo Nigeria kan harkokin su, sai ko kusoshin kasar mu, da manyan 'yan kasuwanni, da ke yin conferences acan.
******



NAHUCHE HOTELS, ZAMFARA

Idea din mallakar hotel nasa na kansa ta dade da ginuwa a ransa. A hankali yake saving, har ya tada tubalin ginin karamin gidan saukar baki 'guest inn' a kasar shi ta haihuwa wato ZAMFARA.
Da nan ya fara kamar da wasa, sai gashi Allah ya sa masa albarka da ilhama a ciki, ya fadada guest inn din ya maida shi babban hotel mai zaman kan sa a jihar ta Zamfara cikin Gusau.
Sabida yadda ba ya tsauwalawa ne da kuma kyawun hotel din gami da nagartar ma'aikatan sa ya sa ya yi attracting customers da masu kudin Zamfara nan da nan, inda ya fara da yi masa branch a birnin Tarayya, daga nan sai Lagos, inda can ne ya zamo (headquater) na (NAHUCHE GROUP OF HOTELS).

A cikin shekaru goma da dawowar sa daga kasar Jamus ya mallaki hotels manya-manya a duka manyan jihohin Najeriya. Ba ya wata sana'a sai wannan wadda ya karanta yake kuma da experience a kai, wato (Hotel Administration), ya san duk wata hanya ta bunkasa hotels (gidan saukar baki) a zamanance daga (Cologne) inda ya yi digirgiri da masta.

Daga nan ne kuma 'yammata suka ce salamu alaykum, ta hanyar budewa Habibu wutar so da kokon bara, kamar za su cinye shi danyen sa, ga kuruciya ga rufin asiri ta ko'ina ya samu, amma babu iyali.

Ga kyau na Zamfarawan usli tushen garin Nahuche. Ko marmarin aure ba ya yi, ba abinda baa cewa a kan sa a dalilin rashin aure, lokacin da sunan sa ya fara karade kafafan yada labarai a matsayin (Young Nigerian Hotels Owner) wasu ma sun ce neman maza ya hana shi aure.

Irin wadanan miyagun maganganu da aka soma yi a kan Habibu Nahuche suna dawowa kunnen Yayar sa Badiya, kasancewar ta mai taammali da mutane daban-daban, ta sha titsiye shi ta ce, sai ya gaya mata ko ba shi da lafiyar da zai iya aure ne?

A irin wadannan lokutan, Habib Nahuche, dariya yake yi sosai, ya cewa Badiya,

"Ba ni da lafiyar ki ka gan ni da Da na mai tsananin kama da ni?"

Sai Badiya ta ce cikin kankantar da murya,

"To Habibu ko dai da gaske kana deviating ne saboda bakin cikin Maman Abdallah ta ki ka?"

A wannan karon ma murmushi ya yi wanda Badiya ta kasa fassarawa, yayi kasa da kai, sannan nan da nan murmushin ya bace daga kan kyakkyawar fuskar shi, sabida wannan ba shine karo na farko da yaji hakan ba (ana masa mummunan zargi), ya ce cikin Bazamfariyar Hausar shi mai dadin sauraro;

"Wannan kuma ai tsakkanin bawa... da Ubbangijin sa ne".
*****




Zuwa yanzu kam Shafa'atu 'ya'yan ta biyar kenan, tana auren ta a Talata-Mafara.

Da farko ta gwada jiran sa kamar yadda Badiya ta kwadaitar da ita har ya gama NYSC ya samu aiki, amma tunda ya sa kafa a (Nicon - Noga) ba ta kara jin komai a kan sa ba. Bata kara jin duriyar Habibu ba. Zumunci ma ya yi rauni tsakanin iyayen su a dalilin hakan don iyayenta sun dauki laifin komai sun aza a kan Hajiyarsa, a ganinsu da ta takura masa da tuni ya auri Shafa'atu.

Ita kuwa Hajiya Kaltume kullum Allah ta ke kai wa kukanta a kan auren dan ta Habibu, shi kuma ta bar wa zabi. Baa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login