Showing 30001 words to 33000 words out of 110913 words

Chapter 11 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ji hawaye na saukar mata duk da ba na regret bane, na tunanin ya dau dan da ta sha wahalar dakon cikin sa wata tara da nakudar sa ya baiwa wata ne. Watan da ta ke da tabbacin ba zata rike mata Da sabida Allah ba sai don wannan dukiyar HOTELS da aka tara.
Ba ta san lokacin da ta sake kunna kwamfutar ba ta koma kan browser din ta ta rubuta 'HABIBU NAHUCE'S WIFE', amma kuma no result matched her search, ta yi sau ba adadi ba ta ga wata mace associated with him as a spouse ba, sai Daractoci da manajoji na hotels din shi, wadanda duk kabilu ne.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ce ta kufcewa Raheenah, amma sai wata zuciyar ta ce,

"Kada ki yi saurin sauke numfashi Rahinah, watakila yana daga cikin mazan da ba sa exposing matan su a internet, ko da gani ma wadannan bayanan duka ba shi ya dora su ba, website ne na hotel din sa ya dora, ya kuma kunshi dukkan bayanan da suka shafe shi.

Da sauri ta soma binciken babban location na shedkwatar Nahuche Hotels, da kuma ainahin jihar da garin NAHUCHE yake, ba jimawa adireshin ya bayyana;


'ZAMFARA STATE, NIGERIA'.

Ta koma da baya ta jingina da allon gadon ta tana wani irin lumshe idon ta.

So Habibu dan Zamfara ne kenan all these while ba ta taba sani ba. Yau har karamar hukumar da garin Nahuce ke ciki sai da Rahinah ta binciko (aiki ya samu manyan mata) Ranar dai baki dayan ta ta zama ta DAN NAHUCHE jikan NAHUCHE ce a wajen Raheenah.....

Gabadaya ta birkice a searching din komai da ya dangace shi, sai da ta binciko komai concerning Young Nigerian Hotels Owner Habibu Mustapha Nahuche. Ba kuma da nufin za ta taba neman sa ba; she is only infatuated and truely in LOVE... ba tare da ita kanta ta san soyayyar gaskiya ke dawainiya da ita a daidai wannan lokacin ba.

Dankwalin kan ta yayi nasa wuri gashin kanta na fulanin usli duk ta hargitsa shi kamar yadda ta hargitsa zuciyar ta da tunanin ta.

Duhu na neman shigowa, har zuwa lokacin Raheenah na bisa kwamfuta ba tare da ta tuna da abincin rana ba. Wanda ta ce ma Nene in ta gama abinda take yi zata zo ta dauka.

Jin shiru har karfe shidda na yamma Rahinah bata fito ba sai Nene ta shigo mata da shi tana tambayar ko lafiya ba ta fito cin abinci ba gashi har an gama na dare? Idanun Nene Balki suka kai kan allon kwamfuta (screen) inda ta hango fuskar Habibun su ta cika screen din, da alama zooming hoton ta yi. Tana kara kallon kyakkyawar fuskar sa da kyau. Da sauri ta kife fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba. Nene ta yi kamar ba ta gani ba, amma ta kusa sakin salati don mamaki, ta ajiye mata abincin da ta biyo ta da shi, ta ce.

"Ki daure ki ci abinci ki koshi, sai ki fi jin dadin tada tsumin tsohuwar soyayyah".

Raheenah ta yi maza ta rufe ido ruf! Tare da dora hannayen ta biyu a kai kamar ta ce, "wayyo Allah kasar ta tsage ta shige". Nene ta gani, ta gan ta da hoton Habibu cikin kwamfutar ta! Yau ina za ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sa kanta da wannan dingimemen abun kunya???
Nene ba ta tsaya sauraron borin kunyarta ba ta juya ta fice daga dakin. Ba ta kuma tsaya ko'ina ba sai falon Ambasada, ta labarta masa abin da ta gani a kwamfutar Raheenah yau. Mamaki kamar ya kashe ta.

Ambasada Shehu Bichi murmushi ya yi, ya ce,

"Shin ke Nene da can kin dauka wai ba ta sonshi ne? Ai ki bar bacin rai a lokacin da yake cin zuciyar diya mace. Sannan shi bacin rai (is mortal but love is inevitable). Amma kuma duk da hakan zuciyarta mai rauni ce a kan ta Da namiji. Bari ta gama karatun ki sha kallo, da kan ta za ta nemo shi duk inda yake.

A lokacin ne yake gaya mata shi ya san inda Habibu yake, (Habibu is now a successful business tycoon) a garin Zamfara, amma har gobe bai yi aure ba, me ye dalili? Wanda ke nufin uwar dan sa yake jira TA HUCE DAGA FUSHIN TA.

Ya kara da cewa, abin da ki ka ga tana yi yanzun, alamu ne na ta fara HUCEWA, sai mu ba su lokaci su duka, mu kuma bi su da kyakkyawar addu'a.

Amma a yadda na fahimta Habibu na da zuciya, soyayyah ba ta rufe masa ido ya kasa sarrafa kan sa.

Idan kin ga ya yarda ya maida Raheenah to fa sai dai idan ita da kanta ta neme shi, ta ba shi tabbacin amincewar ta a kan komawar ta dakin ta. Ya riga yayi zuciya da Raheenah. Yayin da ita kuma Rahinatu in kin lura akwai ta da ki-fadi (mawuyaci ne hakan ta kasance daga bangarenta)".

Nene ta dinga jinjina kai. Ta rasa abinda zata ce.

*****




*COLOGNE, ALUMNI*

A yau ne jamiar Cologne ta kasar Jamus, jamia mai dadadden tarihi, ke bikin kammala karatun su Raheenah daga jami'ar wato (convocation ceremony). Duk inda ka duba dalibai ne daga kasashe daban-daban na duniya, tun daga Amurka, Birtaniya, Asia, Africa and Latin-America. Suna saye da bakar rigar kammalawa (convocation gown) da hular ilmi, farare sun cakude da bakake ba ka iya tantance nationality din kowannen su.

Dr. Raheenah Omar, ta fita da matsayin overall best student a department din ta (Otorhinolaryngology) ta karbi wannan kambu daga shugaban jami'ar Cologne. Ta karbi membership daga (AFHNS) wato (African Head and Neck Society) da kuma (ORLSON) wato (Otorhinolaryngocological Society of Nigeria).
Kamar yadda ta yi wa kasar ta alkawari, wannan ne lokacin dawowar ta gida bakidaya domin ta taimaka wa kasar ta ta amfana daga ilmin da ta tsaya mata ta yi.

Yau gidan Ambasada Shehu Bichi komawa ya yi kamar gidan mutuwa don koke-koke, sakamakon cewa gobe ne Raheenah za ta bi Uncle din ta zuwa gida Nigeria. Wanda ya kara zuwa Jamus a karo na biyu don tafiya da ita. Ahlan kuka har da majina, Yafendo kuwa habar zani ta sa tana ta fyace hanci kamar an aiko musu da manzon mutuwa, Nene ce kadai mai lallashin kowa tana tuna musu suma kwanan nan za su koma Nigeria, sabida tenure din Ambasada Shehu ta kusan karewa.
Rabuwar Raheenah Omar da iyalin Ambasada wata irin rabuwa ce veryemotional. Wadda mai raguwar zuciya ba zai iya tsayawa a wajen ba. Abu daya ya kwantar musu da hankali, shi ne, su ma ahalin gidan na gab da dawowa Abuja bakidaya.
Suna sauka a Kaduna, Alhaji Usman ya sa direban sa ya wuce da ita Girei, kafin ta huta ta zo ta wuce NYSC, lokacin har an fara daukan batch A, don haka Uncle (yadda ta ke kiran sa) ya shigar da sunan Raheenah cikin masu tafiya hidimar kasa na wannan shekarar.

Ba ta fi sati biyu da dawowa Kaduna ba ta wuce NYSC a Ibadan inda suka yi posting dinta zuwa asibitin koyarwa na Ibadan.
Duk inda Raheenah ta shiga farin jinin ta da kyawun ta ke sayo mata soyayyar jama'a. Ga ta nan kamar ka taba jini ya yi tsartuwa (jazir sumul da ita) bafullatanar usli, wadda ta samu gogewa cikin zuzzurfan ilmin zamani. Ta wanke ta yi sumul ba za ka taba tunanin bafulatana ba ce, ta fi kama da larabawan Oman, Qatar haka, ko kuwa na Maghrib.

A Ibadan Teaching Hospital ne wani babban likita dan uwanta ya like mata wai shi Dr. Aryan dan jihar Minna ne, aiki ne ya kai shi Ibadan kuma karkashin team dinsa ta ke aiki. Rahinah ta yi duk iya kokarin ta don ta nunawa Aryan ba auren sa za ta iya ba, amma ya ki ganewa, mutum ne mai nacin gaske kuma girman mukamin aiki da ke tsakanin su ya sa ba ta isa ta wulakanta shi ba don ba ya shiga hurumin aikin ta sam-sam ya san lokacin da yake damunta da nacin kira da zarya a inda duk ya san zai ganta kasancewar sa ya manyanta don ya jima yana aiki a nan, matarsa ta mutu da jimawa ba shi da Da ko daya.

Don haka da Allah ya kawo lokacin kammala NYSC din ta, ji ta yi tamkar an raba ta da kaya, ta dawo gidan su a Kaduna a ranar matsayin cikakkiyar Otorhinolaryngologist mai lasisin aiki tare da Hukumar Lafiya ta kasa, ba da jimawa ba aka tura ta National Hospital Abuja matsayin ENT Surgeon. Dr. Rahinah Omar ta fara gudanar da ayyukanta na likitancin kunne, wuya da makogaro cikin dumbin nasara.

Ita ce likitar kunne ta farko a Africa da ta gudanar da dashen dodon-kunne (cochlear Implant) a Nigeria gabadaya. Kuma kafafen yada labarai suka yada nasararta a wannan surgery na kunne mai hadarin gaske, wanda ya zamo na farkon yi a kasar Najeriya. Kuma wanda ta sanyawa din ya ji magana sosai. Don haka manyan asibitoci masu zaman kansu na birnin tarayyah da wajen ta suka ankara da ita, ta yi attracting asibitocin kunne masu yawa suna masu gayyatar ta aikin part-time job tare da su. Amma duk ciki sai ta zabi babban asibitin NIZAMIYE ta hada da aikinta na gwamnati a National Hospital Abuja.

An bai wa Raheenah gidan likitoci a cikin National Hospital. Uncle ya ce bai son ta je ta zauna ita kadai ba muharrami don haka Aunty Badiya ta samo mata mai aiki a nan kaduna suka tare tare, wai ita Sahura. bazawara ce da ba ta fi shekaru arba'in ba.
Daga lokacin da Raheenah ta gane dangin ta zuwa yanzu ta zo Kaduna ya kai sau shida, amma cikin wani hukunci na Ubangiji ba ta taba haduwa da Abdallah ba, duk lokacin da ta zo yana Zamfara ko wajen mahaifin sa a Lagos inda harkokin sa suka fi karfi yanzu. Sai dai cikin hirarrakin su da Aunty Badiya da su Musaddiq ta fuskanci akwai dan kaninta da ta ke riko tare da Zarah, Baban sa bai cika barin sa ya zauna a Kaduna ba cikin hutu wanda ita lokacin take zuwa sai lokacin makaranta. Haka a bakin su Musaddiq tana yawan jin sunan Junior sunan da duk jamaar gidan suke kiran Abdallah, kasancewar shi ne karami a cikin su.

Tun komawar su Abuja ita da Baba Sahura Raheenah ta zama ba ta da lokacin kan ta, sabida documentation na kama aiki. Tana jin dadin zama da Sahura don kullum kafin ta dawo ta gyare musu dan madaidaicin gidan su tsaf! Ta kunna turaren wuta, ta kuma dafa musu abinci. In Raheenah ba ta ra'ayi daga waje ta ke taho da abin da za ta ci. Uncle ya mallaka mata karamar mota KiaPicanto don ta samu saukin zirga-zirgar ayyukan ta.

Wannan ya taimaka ainun wajen kwashewa Raheenah hankali a wannan dan tsakanin. Ba ta da lokacin da za ta zauna ta yi tunani. Ko bibiyar lamuran dan mutanen Nahuce. Aiki ta ke tukuru da kwarewa da patriotism domin saka wa gwamnatin Najeriya da ta tsaya mata, ta tallafi ilmin ta da (scholarship).
Ranar da ta fara daukan albashin ta na farko ko naira ba ta ci a ciki ba ta kasafta wa iyayen ta, bayan ta ware wa Ambasada kaso mafi tsoka, sannan Yafendo da Nene. Tana mai dakacen ina ma Daada tana raye?

Wannan ihsani da girma da Raheenah ta bai wa iyayen dakinta ya kara mata martaba a idanun su, ba don ba su da shi ba, sai don ganewa da suka yi ita din mutum ce mara manta alkhairi. Bayyanar iyayen ta bai sa su ta daina kallon su da matsayin iyaye ba.

Asibitin Nizamiye wani babban asibiti ne mai zaman kansa a birnin tarayyah. Suna matukar ji da Dr. Rahinah Omar wadda ke aiki part-time da su a matsayin ENT Surgeon (otorlaryngologist).

Nizamiye Hospital na nan a (Life-Camp). They have the latest technology for the treatment of most common ENT cases irin su Rhinitis, Sinusitis, Myringoplesty, Tympanoplasty, Mastoidectomy, Septoplasty da sauransu. The World Class Private Hospital wanda Turkawa suka kafa a birnin Tarayyah.
Don haka Raheenah ba karamar sa'a ta taka ba a rayuwarta da ta samu kujera a Nizamiye. Kudi sosai ya soma shiga account din yar mutanen Girei.
****


NA HUCE is not for free. It's 1000 via
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Shaidar biya 07030137870

: Wata ranar Litinin, Dr. Raheenah ta dawo aiki a gajiye likis, tana yin parking a apartment din ta Baba Sahura na fitowa za ta zub da shara. Da sauri ta aje kwandon sharar ta iso ta karbi jakar uwargijiyar ta tare da (lab coat) da ke hannun ta tare da yi mata barka da zuwa, Rahinah ta bata mukullin booth din motar ta ce ta fidda cefanen da ta yo musu ta sanya a freezer.

Wayar Raheenah ta yi kara a lokacin da ta ke fidda leshin jikin ta za ta shiga wanka. Dakatawa ta yi ta dauki wayar inda ta ga Aunty Badiya ke kiran ta.

"Maman Musaddiq ya ku ke?"

Ta ce, "Muna lafiya cikin alkhairi Raheenah, Uncle ne ya ce in tambaye ki yaushe za ki samu shigowa Kd? Akwai muhimmiyar magana da ya ke so ku yi".

Raheenah ta ce, "Aunty a wannan watan duka ba zan samu lokacin shigowa ba, due to my tight schedules, amma insha Allahu weekend din karshen wata zan shigo".

Aunty Badiya ta ce, "Ni kuma zan je gida Zamfara lokacin, zan dauko dan kani na Junior daga wajen Hajiyar mu, Baban sa zai dawo daga Belarus ina so kamin ya wuce Lagos ya gan shi, amma kwana daya zan yi. So, insha Allah za mu hadu kafin ki koma, a kula da aiki, a kula da mutunci. Allah ya kara wa rayuwar ku da nema albarka".

Sati biyu bayan nan Ambasada Shehu da iyalinsa da mahaifiyarsa Yafendo suka sauka a kasar Nigeria. Sun jima a Bichi cikin 'yan uwa da danginsu kafin su yi relocating a gidan da Ambasada ya saya a Abuja tun kafin barowar shi Jamus. Gidan yana nan a unguwar Maitama.

Raheenah na dakin tiyata, fitowar ta kenan ta samu kira daga bakuwar lamba. Sai da ta zauna bisa kujerar ofishin ta ta warware nadin mayafin da ke kanta, sannan ta bi bayan kiran.
Muryar wa za ta ji? NENE! Sannan lambar ta kasar Nigeria ce.
Wata zabura da Raheenah ta yi daga kujerar ta tana kiran sunan "Nene!" Sai da ta bai wa Nene Balki dariya, ta ce,

"Finally, ga mu a Abuja, kuka ya kare ko?"

Hawayen farin ciki suka zubowa Raheenah, da ma kewarsu da kadaici sun addabe ta musamman da ta fara samun saukin ayyukan da ke gaban ta. Sannan ba ta da kowa a Abuja bayan Uncle Usman, shi kuma ba haduwa suke ba sai idan ta samu lokaci ta je ofis din sa ko shi ya zo nata.

Don haka dawowar iyalin Ambasada Shehu Abuja ba karamin kwanciyar hankali ya kara wa Dr. Raheehah ba. A ranar a gidan Nene suka kwana dakin Yafendo ita da Sahura ana ta hirar yaushe gamo.

Daga wannan lokacin ne kuma rayuwar Raheenatu ta dauki sabon direction. Rayuwa ce ta 'yanci ta ke ciki wadda kowanne mai ilmin boko ita yake yi wa buri, ga aiki, ga gida ga albashi ga motar kan ta, ga kuma rayuwar Abuja. Don haka abu daya ya rage mata shi ne mahadin rayuwar diya mace, wato mijin aure. Mazan da har gobe ta kasa daga ido ta yi musu kallon maza, sai muna-maza, domin kowa ya zo gare ta da kalmar so ji ta ke tamkar ya daba mata mashi a kahon zuci, bai kai ba, bai isa ba. Wanda ta ke binnewa da gangan a karkashin ran ta, shi kadai ne namiji a idanunta a zahiri da badini, dan Hajiyar Nahuce (Habibu).

Ta zama infatuated a kan Habibu kwarai, ta ci gaba da follow up a kan duk wani takunsa na rayuwa, da halin da yake ciki. Duk wasu nasarorin sa na rayuwa a kan kunnen ta, Amma ta yanke shawarar never to look for him ever! A wurin ta kaddara ta riga ta gama playing game din ta, tsakanin ta da Habibu Nahuche. Amma ta rasa dalilin da ya sa har gobe ta kasa daina bibiyar halin da yake ciki.

Shin da gaske ne kaddarar ta gama playing game din ta a tsakanin su???

Ta tambayi kan ta a ranar da ta ji (live programme) din sa da British Broadcasting Corporation wato gidan rediyon BBC Hausa. Ta kashe rediyon ta koma jikin taga ta tsaya standstill tana kallon harabar gidan ta wanda shuke-shuken korran ciyayi suka yi wa kawanya. Abdallah ko yanzu in ya gan ta zai iya shaida ta? Ko ya taba gaya masa yana da uwa a duniya? Ko kuwa bacin ran ta ya sa bai taba gaya masa ba? Habibu kadai ya san duka amsoshin wadannan tambayoyin.
******



Yau juma'a ba ta da aiki sosai a ofis don haka ta yanke shawarar tattara komai nata ta wuce Maitama wajen su Nene ta kare ranar yau tare da su. Ta kira Sahura a waya ta ce, kada ta dafa abinci da ita ta wuce wajen su Yafendo sai dare za ta dawo.
Rahina na tuki cikin nutsuwa kamar yadda ta saba, lokacin da direban sa Yohan dan kabilar Igala ya shararo motar su a guje kirar 'Discussion Contineous' saura kadan ya goga mata. Da sauri ta dauke kan motar ta tana mai Allah wadai da halin wasu direbobin, shi ko Yohan Ubangidan sa ke azalzalarsa a kan ya yi sauri, saura mintuna goma sha biyar meeting din zai halarta a Transcorp Hilton.

Amma me? Motar da ta kauce musu is a glimpse of her Fulani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login