Showing 78001 words to 81000 words out of 110913 words

Chapter 27 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

yana takawa da sassarfa zuwa saman benen, yana amsawa Abdallah.
"Yo wa ya sani ne ko tana nan din? Ko kuma ta tsallake magana ta ta zame ta tafi Nizamiye din nata?"
Yana rufe baki idanun sa suka sauka cikin nata, wadanda ta ke kokarin lumshewa don kauda bacin ran da ke kwance kasan jijiyoyin su, da Habibun ya gama dasa mata yanzun nan ta waya.
Yaron ya tsaya kawai yana kallon ta da kallo na rashin sabo, ita ma tana kallon sa with so much adoration cikin fararen kwayan idanun ta. Ta tuno shi yana karami, yadda baya iya barci sai ya ji shi cikin jikin ta, ta tuno dabdalar sa gidan Ambasada ya shiga nan ya fita can tare da su Ahlan. Ta tuno rana ta karshe da ta rabu da shi daga kwanciya barcin laasar sai ta ji kwalla ta taram mata. Habibu ya cuce ta da yawa Allah ne kadai zai musu alkalanci amma don cuta ya gama cutar ta. Abdallah bai zurfafa kallon da yake mata ba ya kauda kai, ya bi bayan Baban sa wanda ya bude dakin sa ya shige ba tare da ya ce mata komai ba. Haka bai kara yi mata kallon arziki ba.
Abdallah yana gab da shigewa shima, ta bude baki a hankali ta ce da shi cikin shaukin da bazai misaltu ba;
"Abdallah!!!".
Sai ya dakata kadan, shi bai dawo ba shi bai juyo ba haka shi bai shige dakin ba.
Murmushi Rahinah ta yi wanda bai gama karade fuskar ta ba ta ce da shi.
"Im saying Welcome Abdallah".
(Ina yi maka barka da zuwa).
Yana so ya amsa, because he dont know why he likes her, amma kuma sai ya tuno abubuwan da Habibu ya gaya masa a kan ta daren jiya a Lagos.
"Wallahi ba ta son mu, tunda ta iya barin mu shekaru goma muna watangaririya cikin maraicin ta, ba ta taba neman mu ba.
Ba ta zo don ta zauna da mu har abada ba Abdallah, sai don ta kwace ka daga hannu na ta kara gaba.
Imagine Abdallah har kotu ta kai ni don a kwace ka daga hannuna a bata...".
Sai kawai ya yi mata wani irin kallo da ya fi kama da na rashin yarda da jin haushi zallah, ya sa kai zuwa dakin Baban sa ba tare da ya ce da ita ko uffan ba.
In ta ce ran ta bai sosu ba, da biris din da Abdallah ya yi da ita, hakika ta yi karya. Amma sai ta ce a ran ta "Da dai ba Habibu ne ya haife ka ba, shi ne za'a yi tsammanin halin ku ba zai zo daya ba".

Duk da gwiwar ta ta yi sanyi da irin karbar da dan ta Abdallah ya yi mata, for the first time na zuwan ta gare shi a matsayin mahaifiyar sa a tsayin rayuwar sa ta yanzu, kuma tana da tabbacin yaron ya san da hakan, don ta san zuwa yanzu ba zai kasa gaya masa gaskiyar wacece ita a gare shi ba, hakan bai hana ta tunanin me za ta ba shi ya ci ba. Daga yau zata fara rayuwar motherhood, zata dasa tubalin irin rayuwar da kowacce uwa take yi da yayan ta.
Kitchen ta shiga ta soma tunanin me za ta dafa masa, ba ta san komai a kan likes and dislikes din sa ba wannan ma cuta ce mai zaman kanta da Habibu ya yi mata.
Musaddiq ya fado mata a rai, da sauri ta latso shi a waya.
Bayan sun gaisa da tambayar mutanen gida, ta ce,
"Musaddiq ni me ye favourite food din Junior ne?"
Musaddiq ya yi dariya, ya ce, "Wannan ai shazumamu ne, kawai ki ba shi cornflakes din Kelloggs ya ji madara da suga zau, shikenan kin gama masa komai.
Wasu lokutan kuma Mummy (Aunty Badiya) tana yi masa danwake ta sa shi a gaba ta ce sai ya fara ci zai sha Kelloggs".
Ta yi wa Musaddiq godiya, ta ce a ran ta, "To ni kuma daga yau abincin da zai gina masa jiki ya kara masa girma zan koya masa ci (carbohydrate). Ni ba zan biye masa ba, gashi nan da jiki lange - lange kamar na Uban sa".
Girki sosai Rahinah ta zage tana yi har da sanya apron. Farin cikin ganin sa ya sa ta maida tension din da Habibu ya hada mata a kan maganar aikin ta a ba komai ba. Za ta ba shi mamaki kuma. Wannan karon da gaske ta gama da BOKO; motherhood din ta ke so. Shine kuma ya saura mata yanzu. In ma da gatse ya fada don yana ganin bazata iya ba to ya yi sara a kan gaba.
Ta kammala girkin ta mai rai da motsi tana kwashewa a sundukin abinci na zani (warmers), cous-cous ne ta yi wa wata irin dahuwa da %??ieggies%??? da %??ipices%??? masu sanya kiran yunwa, ga hanta ta wadace shi. Duk kitchen din da ma area din benen nasu ya dauki kamshin girkin Rahinah.

Habibu ya shigo karamin kitchen din wanda anan upstairs din nasu yake, bayan yayi wanka yana sanya maballan wuyan rigar shi TommyHilfiger fara sol. Bakin wandon Jeans ne mai kauri a jikin sa. Kitchen ne na zamani mai aji da mukami da ya ji komai na na'urorin zamani amma karami ne. Ya shigo ne da niyyar daukar ruwan FARO mara sanyi domin ya hada wa Junior Kelloggs. Ko kusa bai kawo a ran sa Rahinah zata yi musu girki ba. Kai shi ba ya jin ma Rahinah ta iya shiga kicin banda rike allura. Ta wutsiyar ido ya hango lafiyayyen abincin da ta ke kwashewa a food warmers wanda kamshin sa kadai azaba ne ga mai jin yunwa kamar sa. Rabon sa da abinci tun na daren jiya a Ikko.
Ya dauki ruwan da ya zo dauka har zai wuce ya yi wani tunani, in ya bar abincin nan bai ci ba bata da asara, ita gaba ma ta kai ta, kuma ya tabbata ba da shi ta dafa ba, bari kawai ya yi wa kan sa gata in ba haka ba da yunwa zai kwana, ya juyo gabadaya ya yi facing dinta hannun sa daya cikin aljihun wandon shi, daya rike da gorar ruwan Faro, ya ce cikin tsokana.
"Sabbeni mu ina namu?"
Hararar sa ta yi son ran ta, ba tare da ta tanka ba, tamkar idanun ta zasu fado kasa, wata zuciyar ta ce ta rabu da shi shiru ma amsa ce, wata ta ce dan yaba masa mara dadi wadda zai kwana tana nukurkusar sa.
"Na yi kama da kukun gidan ka ne? Aikin banza!".
Takowa ya yi zuwa gaban ta a hankali, ya tsaya dab da ita, har numfashin sa na dukan fuskar ta, ya kankance ido ya hade giran sama da na kasa tare da yin kasa da murya yadda ita kadai za ta ji shi ya ce.
Waye mai aikin banzan?%???
Ta murguda baki ta ce duk wanda ya tsargu.....
Kafin ta rufe baki ya kai hannu zai dauke warmer din gabadaya, ta yi maza ta danne hannun sa da iyakacin karfin ta ta rike foodflask din tamau.

"Idan ka ci min abinci Habibu Allah ya isa!"
Karaf! A kunnen Junior da ke shigowa kicin din, don shirun Baban sa ya yi yawa daga zuwa dauko ruwa a firji, shine ya taso ya biyo bayan sa, jin abinda Rahinah ta fada, sai ya dan dakata cikin jin tsoro, ya rakube a jikin kofa jin yadda ta yi maganar cikin tsiwa kuma da daga sauti sannan ga uban sa ta dannewa hannu kamar zata karya shi. Da sauri ya juya ya koma daki kirjin sa na bugawa lokacin da ya ji Baban sa na fadin.
"ina rokon ki Rahinah. Ki cigaba da yi min Allah ya isa, because it%??j turning to BLESSINGS upon BLESSINGS.
Allah ya isan ki ba ta tsiro, da tana tsiro da ban kawo yau ba, don Allah ki cigaba da yarfa min ita, shekaru goma ki kai kina jefo min ita tun daga Jamus zuwa Zamfara don na dauke miki Da, kin ga wani abu ya same ni ban da progresses da tarin achievments?
Ke kuwa yau ga ki kin kare a gidan auren da ki ke gudu. Qualifications sun zama na banza! Tunda na hana aikin. Na fada, na hana!
Da ma kin yi zaman aure na shekaru goman da ya fi miki alkhairi, da yanzu kin tara 'ya'ya biyar wadanda za su ji kan ki a tsufanki, at the very long last auren da ba kya so da shi ki ka tsira".
Ta yi maza ta dauke hannun ta daga kan nasa, sakamakon wani irin shock da ya bakunce su su duka. Lokacin da Habibu ya matse nata hannun shima da dayan hannun sa. Har yanzu tana ignoring kallon cikin idanun sa da ya ke binta da su ba tare da ya sani ba, ta ce,
"Idan kai ka dauki nauyin karatun nawa sai ka hana ni aikin in gani. Yaro kuma ya zo kenan hannun mahaifiyar sa, da shi da aikin al'umma duk zan iya hadawa in kula da abina. Babu ruwan ka.
Me ye naka a ciki? Auren da aka maida da wannan ka'idar ta hana ni aiki aka mayar da shi? Ko ko salon muguntar ka da zaluncin ka da ba ya taba karewa a kai na?"
Habibu ya kara matsawa zuwa gaban ta sosai, kirjin sa da nata na bugawa wani irin fat-fat, ya kai hannu ya dago habar ta. Ta yi maza ta runtse ido gam! Tare da doke hannun nasa daga habar ta. Da azama ya matsa ya sumbaci eye-lashes din ta, sannan ya sauko a hankali kan karan hancin ta ya dora lips din sa a kai shima ya bashi kyakkwar sumba. Rahinah ta yi maza ta ja da baya tana hararar sa, domin hakika ya shammace ta, ya kawo sumbar a lokacin da bata zata ba, bata tsammana ba. Shi ko ido lumshe yake kallon ta tamkar ya hadiye ta ya huta da azabar soyayyar da ke kwance kasan kirjin sa, ya ce cikin sassanyar murya wadda ta samu rauni sanadin sumbar da ya yi. Kamar kuma baya so Abdallah ya jiyo su.
"Aiki a Nizamiye na hana, na soke shi bakidaya daga yau. Idan kuma kina ganin ban isa ba, ko wasa nake, ko na yi kadan in yi umarni ki bi, to ki sake sa kafa a Nizamiye ki ga abin da zai faru%???.
Ya dauki flask din abincin gabadaya da plate da cokula biyu ya kama hanyar ficewa. Kasa ko motsi ta yi har ya fice daga kicin din. Bai ga Abdallah a dakin sa ba, don haka ya sauka zuwa downstairs inda main falon gidan yake.
A can ya tadda shi ya yi zugum da remote din talabijin a hannu, amma hankalin sa ba ya kan cartoon din da ya kunna, ya yi nisa a tunani. Da sauri ya karasa gare shi, ya ce,
"Abdallah, what's up?"
Firgigit yaron ya juyo ya dube shi, shi bai taba jin wani ya yi wa Baban sa Allah ya isa ba, ko ya daga masa murya, everyone treats his father with utmost respect including Hajiyar Nahuche da ita ta haife shi, in tana so yayi mata abu lallashin sa take yi with love and respect, sabida son da take masa, ma'aikatan sa kuwa kamar su yi masa sujjada sabida ladabi, don haka sosai abin da Rahinah ta yi wa Daddyn sa ya tsaya masa a rai.
Habibu bai kula da halin da yaron ke ciki ba ya hau zuba masa abincin yana cewa, "Daure ka ci Abdallah, sai mu sha kelloggs din ko?".
Girgiza kai ya yi da sauri. Kamar mai kyamar abincin.
"Ni ma ba zan ci ba!".
"Saboda me Abdallah?"
Sai ya kasa gaya masa sabida ya ji ta yi masa Allah ya isa ne a kan abincin, kuma ta yi masa tsawa. Baban zai ce ya yi labe, bayan kullum yana hana shi sauraron zancen da ba nasa ba, kuma zai masa fada sosai.
Don haka ya yi shiru, Habibu ya debo abincin a cokali zuwa bakin sa. Dole ya bude baki yana ci. Ga mamakin Habibu yau Junior ya ci abinci yau sosai, cin har ya wuce daidai cikin sa. Ko shi da ya yi loma daya da cous-cous din Dr. Rahinah, sai da ya ji hatta fatar kunnen sa yana wani irin motsawa. Sai ya gyara zama ya shiga ci sosai da wani irin shauki, ko kuwa santin hannun da ya sarrafa girkin ne? Ba zai iya cewa ba.
Ko da ta koma daki kasa tabuka komai ta yi, sai safah da marwa da ta hau yi, yar sumbatar ta da Habibu yayi lightly duk ya birkitata ya kashe mata kuzari, ta fahimci Habibu zai iya barin komai a rayuwar sa amma banda kusantar jikin ta ko da accidently, wanda shi ma bai san lokacin da hakan ke faruwa da shi ba.
Hakan ya faru sau biyu kenan daga zuwan ta gidan nan zuwa yau. To ashe da ma ya iya kiss din ne har haka a baya yayi mata kwauron sa, ko ko yanzu ne ya je ya koya tunda ya gane ire-iren abinda take so kenan? A sanin ta dai a hawan kawara kawai Habibu Nahuche ya iya yi wa matar sa yadda zata cutu. Sannan ya bi ta da bakar magana. Bai iya wannan sanyaya murya da lallashin ba irin wanda ya yi yanzu har abin ya tsirga a zuciyar mutum, ya wuce ya bar shi da tunanin abun. Tsaki tayi a fili.
Haushin tunanin da ta ke yi din ne kuma ya zo ya kume ta, me ta zama ne haka? Me ya ke kokarin samun ta? Kada dai fa Habibu ya karya lagon ta cikin dan lokaci kalilan irin wannan ta tashi a tutar babu daga kan perception din ta. Yes, ta dade da gane shes romantic by nature, tana romance daga mijin auren ta, tana son romantic husband ba irin Habibu ba, tana son lallashi da tarairaya. Kuma akan haka ne ta tsani Habibu Nahuche, gashi tun baa je koina ba ta ga yana kokarin canzawa daga yadda ta san shi zuwa yadda ta ke son shi.
Neman tsari ta shiga yi da shi a zuciyar ta, domin dama can ta sani, baa kidnapping Da kawai Habibu ya kware ba; har da sace zuciyar diya macen duk da ta yi kuskuren hawa kan hanyar sa.
Ta mike ta bi bayan su zuwa kasa don dai ta tabbatar Junior ya ci abincin da don shi ta girka ba don Uban sa ba.
A ran ta ta yanke shawarar hakura da aikin Nizamiye din, don ta tabbatar masa da ba bokon ne a gabanta ba yanzu, kuma ba shi kadai ya ke son Abdallah ba, don ta gane kamar yana kokarin ya nuna wa yaron hakan, kamar ma ya zuge shi a kan bata son shi, amma aikin gwamnati ba za ta daina shi ba ko da hakan zai kai ga ta gurfanar da shi a gaban Baba Ambasada, tunda a maida auren su da aka yi ai babu wannan yarjejeniyar ta son zuciyar sa.
Uwa uba ta ci amfanin scholarship na gwamnatin kasar Najeriya wanda take fatan ta biya kasar ta wannan bashin ta hanyar cin moriyar ta. Tunda aikin ta halastacce ne a addinin muslunci.
Ba ta daddara ba da shareta din da Abdallah yayi dazu, ta fito falon ta isa kusa da shi ta zauna. Da sauri ya matsa gefe kamar ta tsikare shi, yana ta faman sunkuyar da kai ga barin kallon ta, cikin mamaki Rahinah ta ce,
"Abdallah gudu na ka ke yi?"
Ya yi mata shiru, ya sunkuyar da kai kasa, ta ce, "To tashi ka je ka yi sallah maza".
Ya yi kamar bai ji ta ba, don haka abin ya soma taba ran ta, ta tabbatar ba haka Habibu ya bar shi a kan ta ba kamar yadda ya ci mata alwashi. Tana iya ganin tsanar ta muraran cikin idanun yaron.
Haka ta rabu da shi zuciyar ta na kuna ta koma daki, Habibu bai taba bakanta mata ba a tsayin dambarwar su irin yau, don me zai sako innocent yaro cikin rikicin su? Allah kadai ya san abinda ya gaya masa a kan ta. Ba haka yaron ya yi mata a gidan Aunty Badiyya ba. Amma babu komai baa san maci tuwo ba sai miya ta kare. Ita da shi zata ga wa yafi son Abdallahn.

Ba ta daddara ba da daddare ta sake yi wa Abdallah girki. Wannan karon tuwon semo ne ta yi masa da miyar agushi, ta shirya abincin a kan tray ta nufi dakin Abdallah.
Yana sauya kayan jikin sa zuwa na barci, lokacin da ta shigo da sallama. Abdallah a can cikin cikin sa ya amsa mata sallamar, don ya san muhimmancin amsa sallama a addini, ko ta waye balle ta iyaye, sannan duk ya bi ya bata rai, Rahinah ta langabar da kai rike da farantin da ta shiryo abincin da ruwa da lemo,
"Abdallah its time for dinner". Wato Abdallah lokacin cin abincin dare yayi. Ya yi wani kicin-kicin da fuska, tare da turo baki gaba irin na yayan gata, ya ce,
"Na gode. Amma ba na ci".
Bata bata ran ta ba duk da kamar ya gwale ta ne (in a polite manner), kuma ta ji babu dadi, murmushi tayi ta ce.
"Ko da na ba ka a baki da hannu na?"
Ta zauna a gefen sa ta bude plate din ta debo tuwon ta shafo miya da yatsun ta ta nufi bakin sa.
Kin karba ya yi, ya kauda kai, sai da ta ce, "Please Abdallah!". Tare da yin narai-narai da idanun ta.
Sai ya ji ya kasa tankwabar da wannan kyakkyawar kulawar tata, at least da girman sa dai ba wanda ya taba cewa zai bashi abinci a baki, har wata kunya ya ji, ya karbi plate din abincin daga hannun ta, ya ce a hankali kamar cikin rada.
"Ki bari zan ci da kaina! Kada Daddy ya zo ya ga kina bani abinci a baki".

"That's my boy!"

In ji Raheenah.

Tana zaune har ya kammala ci, sai ta tattara kwanukan ta ce. "Ka zo mu tafi daki na mu kwanta ko Abdallah? Kada mu makara sallar asubahi". (Duk a kokarin ta na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login