Showing 72001 words to 75000 words out of 110913 words

Chapter 25 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ta kwance, ta kasa kukan da amare suke yi sakamakon rashin nutsuwar da rashin ganin Abdallah har lokacin ya haifar mata.
Abdallahn da ta dawo domin sa, ta yi matukar kokari ta yi fulatanci (alkunya) bata tambayi kowa yaron ba har aka yi biki aka kare daga jama'ar Girei har zuwa na Zamfara zuwa Nahuche bata tambayi kowa ina Abdallah ba, ta dauka da ta zo gidan da shi zata fara tozali, ga %??ia%??jan Aunty Badiya babu wanda bata gani ba, kada dai ace tun dauke shin da yayi akan idon ta bai dawo da yaron daga inda ya kai shi ba? To ina ya kai shi?
Ita ba abun ta dauki waya ta kira Badiya ta tambaya ba, fillancin da ta daure ta yi a baya ya tashi a banza.
Daman dai bata yi tsammanin ganin Habibu ba. Shima kuma koda ya dawo gidan daga gidan Ambasada karfe goma sha dayan dare inda acan ya ci abincin dare bai yi tunanin neman ta ba. To yace mata me? Shekara goma da doriyar watanni masu yawa yayi babu ita cikin rayuwar sa, don haka, a ganin sa, dawowar ta yanzu ba abinda zai kare shi da shi, ba abinda zai sa ba abinda zai hana, ita da babu duk daya.
Data ga barci yaki zuwa alwala tayi, tayi sallolin shafa%??j da wuturi da bata yi ba, ta zauna bisa darduma tana lazimi, anan barcin gajiya ya sace ta.

Da asubah sautin kira'ar Minshawy da ya karade gidan cikin suratul Dalaq shi ya tashe ta, ta rasa daga ina karatun yake fitowa. Sai ta tashi ta fada toilet tayi wanka da brush ta dauro alwalah sannan ta fito.
Data fito tsayawa tayi tana kallon yanayin tsarin komai na dakin, kyan ginin gidan kadai ya isa, tana mamakin irin dukiyar da ya tara cikin dan lokaci kankani da dawowar sa. Hatta marbles din gidan sa bata taba ganin shi a ko%??jna ba. Tsaki ta ta yi a fili ta ce.
%??mllah ya sa halal yake ci%???.
Bayan ta idar da sallolin ta na farillah da na nafila da kayan da ta zo da su tun jiya ajikin ta ta koma gado ta nade cikin duvet, kayan duk sun bi sun dame ta amma ta kasa cire su ta huta don ba ta so ma ta saki jikin ta in ta tuna a gidan Habibu take, tana sauraron karatun da yake ta tashi a gidan, yanzu kuma Suratul Tagabun ake karantawa. Sai ta lumshe ido tana bin kira%??jr a hankali da fatan barci ya zo ya dauke ta, ko ya mantar da ita a ina take, ko ya maida reality din ya koma mafarki, burin ta a lokacin bai wuce a ce tare da Abdallah take kwance ba tana biya masa wannan karatun, tana yi masa tambabyoyi akan rayuwar sa da bata sani ba, amma barcin kamar ya san neman sa Dr. Rahinah ke yi ruwa a jalloh sai yayi kememe ya yi kemadagas yaki zuwa. Idanun ta dai suna rufe bata bude su ba, tana cigaba da bin karatun cikin Suratul Tagabun.
Ya dawo masallaci ne zai shiga dakin barcin sa ya ji tashin sassanyar muryar ta, tana bin karatun da ya kunna kafin ya fita.
Dakin da aka sauki Rahinah wato bedroom din ta opposite din nasa ne, a kusa da natan na Abdallah ne wanda yasa aka shirya shi da duk wani abun da yaro mai shekarun sa zai bukata, an narkar da dukiya ba kadan ba a dakin Abdallah, katifar sa kadai water mattress ce.
Tsayawa yayi kasake! A kofar dakin sa yana sauraron ta. Bata son abinda zai tuna mata a gidan Habibu take, a gadon auren sa take kwance, don haka karatun ya tafi da bacin ran ta ya wanke wannan damuwar, ya sanya mata nutsuwa da confidence din jin cewa zata iya sake zama da Habib Nahuche, da So ko babu So, Albarkacin Abdallah, dawowar ta gidan sa baya nufin karshen rayuwar ta.
Karatun ta ya mishi dadi ba dan kadan ba domin ya maida gidan lively. Duk da gari bai gama wayewa ba, sai ya tuna jiya bai bata komai ta ci ba, a matsayin ta na bakuwa a gidan sa wadda bata kai ga sanin ko%??jna na gidan ba, sannan bai duba ta ya ga yadda ta zo ba ko da bazata kula shi ba.
Tun jiya ya sallami kukun sa na gidan, ba zai jure wata mu%??jmala ko yaya ta shiga tsakanin Rahinah da wani namiji ba bayan su Musaddiq shaqiqan ta, bai san yana da kishi na fitar hankali ba sai ranar da Rahinah ta ambaci ta zabi wani Irshad a kan sa. A daren ranar ya san ba bakaken maganganun Rahinah ne suka hana shi runtsawa ba face wannan subul da bakan da ta yi a gaban sa. Har da cewa ta gwammace shi (Irshad) duk da kasancewar sa womanizer a kan sa.
Yanzu kam yana tantama a kan cigaba da aikin ta, ina amfanin tarin dukiyar da ya mallaka idan matar sa bata zauna a gida ta kula da Abdallah da kannen sa ba? Duk da ya san ita wannan Rahinah daban ta ke da sauran mata a kan boko zata iya barin komai, son Dan kawai ta sani, amma baya jin ta san yadda ake kula da yara da tarbiyyar su.
Yunwar da yake ji shima ta sa ya bar tunanin komai da sauraron karatun Rahinah ya nufi kitchen. Ya bude freezer, an zuba komai na amfani kamar yadda yayi wa Atiku umarni, one regrettable thing shine ya sallami Kukun gidan, don kada ya kalle masa mata, shi kuma ko suyar kwai bai iya ba.
Sai kawai ya jona kettle din dafa ruwan zafi ya dafa shayi ya hada shi sosai da peakmilk da lipton ya zuba a kofuna guda biyu, ya dora su akan karamin faranti, ya dauko sabon cake a firji ya aza bisa, da pizza wadda ya san Atiku ne ya ajiye masa su don baya rabo da cin su koyaushe. Kai tsaye ya koma sama, so yayi ya zauna ya ci a kicin din amma wata zuciyar ta ce a%??jh, akwai hakkin ciyarwa yanzu a wuyan ka.
Don haka ya nufi dakin Rahinah kan sa tsaye, an ce faduwar gaba asarar namiji ce, kamar yadda yayi tsammani dakin a bude yake, sakaya kofar kawai aka yi. Don duk mukullan gidan suna hannun sa jiyan da dare Nene ta damka masa bayan sun koma.
Sallamar da yayi ciki ciki yayi ta kamar an tilasta shi, don ya sa a ran sa ba Rahinah yayi wa sallama ba, a%??jh, mala%??jkun da ke tare da ita ne. Bata ji sallamar da yayi ba haka bata ga shigowar sa ba domin ta dora filo akan ta ta rufe fuskar ta tana cigaba da bin karatun ta cikin taushin murya, sanye yake da kayan barci pajamas samfurin %?diloomingDale%??j%???. Jin kamshin turaren sa yasa ta janye filon daga fuskar ta a hankali.
Yana nan a handsome HABEEBUNsa! Dan gayun nan wankakke, rashin wadatar haske ne ya hana mata ganin yanayin kyakkyawar fuskar sa wadda ko cikin duhu kyakkyawa ce.
%??morry for the interruption Ma%??jm%??? (ya nemi afuwar katse mata karatun ta). %??m brought tea for you%??? (na kawo miki shayi ne) ya sake fada. Tare da dora mata farantin akan bedside din ta. Wanda yake dab da inda kan ta yake.
Kamshin tsadadden lipton din ne ya tuna mata rabon ta da abinci, amma ko wannan shi ya saura shayi a duniya da garin Abuja bakidaya bazata sha shi ba.
%??mauki tsiyar ka ka fita min a daki, bana son ganin mummunar azzalumar fuskar ka%??? maimakon kalaman ta su bashi haushi kamar yadda ya san ta fada ne don ta bakanta masa, su yi irin wacce suka saba, sai ya hada hannuwa cikin salama yace,
%?"nhe ugly wicked man comes in peace. Maida wukar Ma%??jm. Albarkar haihuwa kike ci har gobe kuma ita za ki cigaba da ci har karshen rayuwar mu%???.
Da fadin hakan ya juya akan takun sa zai bar dakin, yana kokarin fita ya ce,
"Welcome to your humble abode!%???.
Sai ji yayi kamar daga sama ta ce
%??mabib!%???
Bai juyo ba amma ya dakata, hannun sa akan marikin kofa, sai ji yayi taratsatsa! Ta hada kofin shayin da shayin da bango, %?"no hell with your tea, wannan ya zama lokaci na karshe da zaka kuma shigo min daki, kuma ka gaggauta kawo min Da na%???.
A wannan lokacin duk yadda ya so ya hakurkurtar da zuciyar sa ya kasa, juyowa yayi ya dubeta a gicciye da sexyeyes din shi, wadanda a kullum su ke gilma mata tamkar shifcin gizo.
%??ma dauka kin fi kowa sanin hanyar kotu, ko kin ji nace da ke ki janye karar ki? Ba%??j gaya miki na amsa sammaci na zo ba? Don in tsaya da ke a kotu a kan kwatar Da?%???
Ya karasa fucewa daga dakin. Tare da cewa "kina bukatar komawa islamiyya ki kara koyo tarbiyyah, Kura da fatar Akuya kawai%???.
Kafin ya kai ga bude kofar ta yi maza ta sha gabansa.
%??mayi kadan kace min jahila, tunda duk jahilcin nawa a haka ka like mini, ka hana rayuwa ta sakat tun haduwa ta da kai, bayan na samu mun rabu meyasa ka ki yin auren ka da wadda ke son ka, har sai da ka janyo aka sake lika min kai?
Wallahi ka sayar da maza, mara zuciya kawai wanda bai yarda bakin da ya furta rashin so har abada ba zai taba dawowa yayi furucin so ba. Na tsane ka Habibu Nahuche, na fada na kara bana son ka, Dan da na Haifa da kai kaddara ce ta yi min sanadin sa amma ba so ba.
Don haka ka sa a ran ka don shi na dawo, kuma zaman sa nake yi. Ka dauko min Da na duk inda ka kai shi ko in koma kai karar ka wurin Allah%???.

*SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870*


NA HUCE

PAID BOOK




Tana shiga yana shiga, kafin ta juyo ya maida kofar ya rufe har da key. Ta daga idanun ta cike da masifa da hawaye ta dube shi.
"Me ka zo yi min daki? Ko kana bina bashi ne? Ko ka zo raping din ne irin wanda ka saba tun kana cikin kuruciyar ka?"
Kawai sai ya hau undressing kan sa ba tare da ya ba ta amsa ba. Rahinah ta yi maza ta rufe idon ta ga kunya da ta kama ta kamar ta ce kasar wajen ta tsage ta shige. ...Ya Subhanallah Habibu menene haka?
A lokacin har ya gama undressing din, yace.
"Ban so zan maimaita laifi na ba, amma bazaki daina kira na rapist ba ko na bari ko ban bari ba, sabida ke abu ba ya taba wucewa a wajen ki, na ga alama ke kam da dutse ba ku da maraba, ko kuwa in ce baki da lafiyar da yan adam ke da ita, ga shi tsufa na kwankwasa min kofa ban tara masu yi min addu'a da yawa ba.
Dan kwaya daya tal da Allah ya bani so ki ke ki kwace min shi ta karfi da yaji, da kissa da kinaya da nunkufurci irin wadanda kika kware a kai, don haka ina son yin ajiya a nan yau dinnan ko da tsiya ko da arziki%???.
(Ya nuna cikin ta). Yana kara takowa slowly zuwa gaban ta kamar mai tausayin kasa, lumsassun idanun sa da suka canza launi na gaya mata zahirin bukatuwar sa zuwa gare ta, abinda yake fadi haka ya ke har zuciyar shi kuma yau mai kwatar ta hannun Habibu sai Allah, ya kara da cewa,
In ma ya kasance ta hanyar rape din ne again ina ganin babu laifi don ke kika ja, tunda hakan kika zaba mana mu rayu, mu kuma cigaba da rayuwa, kuma ai na ga yayan rape din sun fi son iyayen su maza a kan ki, kamar sun san hobbasar uban su shi kadai ce ta samar da su ba tare da taimakon uwar su ba.....
In haka ne ni kuwa akan me zan ki haifuwar yayan rape tunda zasu so ni su kauna ce ni fiye da uwar da ta haife su?
Dr. Rahinah Omar Allah ya gani na yi hakuri iya hakuri a kan ki, irin wanda ba kowane namiji ne kama na mai shekaru na zai iya ba. Shekaru goma kenan baki bar zuciyata da gangar jiki na sun huta ba, kin dawo cikin rayuwa ta again kina azabtar da ni da muguntar ki, bayan ban roke ki ki dawo ba tunda na fi kowa sanin wacece ke, tunda dai ni din mutum ne dan adam mai jini a jika kamar kowa ba daga sassake aka halicce ni ba dole yau in nemawa kai na mafita. Don haka yau daga ni sai Allah sai ke a dakin nan zaa goge raini da duk wani guntun munafunci da ke tsakani na da ke Rahinah ......
Ta wara dukkan idanun ta da gabadayan girman su tana kallon sa cikin sabon tsoron da kwayar idon ta ce kawai ta bayyana shi banda action din ta. Wato a idon ta tsoro ne karara, a zahiri kuma ego din ta da pride din ta na nuna akasin hakan. Habibu ya karanto hakan, ya hango tsananin tsoron abinda ya tunkaro ta shi din tsakiyar (almond shaped eyes) din ta, kwatankwacin na shekarun kuruciyar ta.
Sai Habibu ya sassauta murya ya koma lallashi da ban baki. Irin wadanda shi kan sa bai san iya iya su ba ko a ina ya koyo su ba, ya yarda circumstances na rayuwa yana koyawa dan adam komai. Murya can kasa ya soma bayani cikin lallashi.
Tafiya zan yi zuwa Portharcourt wadda za ta debe ni har sati hudu, kin ga kuwa ai akwai babbar matsala alhalin na san yanzu ina da mata wadda ke zaman bukatu na. Azumin kamar... kamar ya daina aiki a jikina a kwanakin nan Rahinah, wallahi ba na iya barci, a duk dare nikadai na san ya na ke wayar gari cikin soyayyar ki. Alhalin na san wannan karon ban tursasa ki ga aure na ba yardar kan ki da ta iyayen ki ce ta kawo ki cikin sa?
Don haka ga zabi; ko dai mu tafi tare mu yi honeymoon wanda bamu taba yi ba sai rikici da balai wanda ni na fara gajiya da su, rayuwa mai maana nake bukata yanzu, in yaso Abdallah a kai shi gidan Ambasada har mu dawo; ko kuma please yau daya kar ki yi kokawa da ni. Give me this night, I don't want it to be hurting..... only loving and romantic!".

Da fadin hakan ya yi maza ya hada ta da jikin sa ya rungume ta tsam-tsam, wata irin kyakkyawar runguma tamkar zai tsaga kirjin sa ya sanya ta ciki ko ya samu sa'idah daga azabar da yake dandana na kauna da soyayyar ta, Rahinah Omar, na iya jin yadda sautin bugun zuciyar Habibu ke dokawa, tana harbawa da karfin gaske a nata kirjin da nauyin soyayyar dake addabar sa cikin ta.
At the same time da Habibu Nahuche ya soma kissing din ta a zafafe, kamar kuma a yunwace, koko ta ce a urunce (hungrily) sannan in perfect style. Sumbatar ta kawai yake yadda ran sa ya ke so (tun daga sama har kasa.....)!
Ko ta yi kokarin gocewa ko nokewa a zuwan pretending a wannan karon, a wannan dan tsukin, a wadannan yan dakikan gangar jikin ta bata bada goyon bayan hakan ba%???, domin ta kasa yin hakan ko yatsar ta ta kasa motsawa da nufin kwatar kai, sakamakon ruhin ta da ya yi accepting komai (with a warm welcome) gangar jikin ta kuma ta amsa kyakkyawan kiran mijin nata Habibu, wanda abinda ta jima tana buri tana fata tana kuma mafarki kenan daga gare shi wato (soyayyah).
The way and manner da Habibu yake sumbatar nata in style bai taba yin irin hakan ba, it's so soothing. Hatta babbar yatsar kafar ta ta tabbata yau Habibu bai bari ba, sai da ya kama ya tsotse in a soothing romantic manner, yana gaya mata wasu irin kalamai cikin kunnuwan ta da suka zam sirri ne a tsakanin su su biyu, wadanda duk na ban hakuri ne da neman hadin kai, wadanda suka gigita Rahinah Omar, suka kuma hautsina kwanyar ta, suka gusar da hayyacin ta na wucin gadi.
Wani tunani ne ya zo wa Rahinah a wannan lokacin, wato Habibu ya dauka ya ci banza raba ta da aikin ta da ya yi? Aikin da ta kwashe shekara goma tana karantawa don ta tsaya da kafafun ta. Ta zama abar hutun sa kawai daga yau tunda ta dage sai ta zauna da dan sa ko? An ce babu kyau kawo wani issue ga maigida a irin wannan lokacin, amma ita kam, ba ta da hanyar ramawa sai ta nan din. In yaso daga baya zata yi istigfari. Har kuma in da ahali ta nemi gafarar sa. Amma yau dinnan bata shirya karbar sa a matsayin miji ba, bata gama amincewa da canzawar sa ba, sannan ban hakurin sa bai gamsar da ita ba tunda yayi ne a lokacin da yake cikin halin bukatuwa.
"Shin ka manta cewa zaman Da na na zo ba zaman ka nake ba? Ai zaman kula da Da nake yi babu wannan responsibility din cikin ajandar mu".
Idanun Habibu ko buduwa ba sa iya yi a wannan lokacin. Cikin rikicewa da gigicewa ya soma ya daga ido ya dube ta ya soma begging.......
"Ki yi wa Allah ki yi hakuri ki yi min rai Dr. Rahinah, likitar zuciya ta... likitar kunnen duk duniya, na kara fadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login