Showing 42001 words to 45000 words out of 110913 words

Chapter 15 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ba, ita da Dan ta! Wannan karfin hali zata ce ko fin karfi da me zata kwatan ta shi (Hausawa suka ce gwano ba ya jin warin jikin sa).
Dr. Rahinah Omar ta yi ajizanci mai girma da ta manta baya, kalaman ta na shekaru goma a baya har kullum dada komawa danye kumakorre sharr suke sake yi a zuciyar Habibu Nahuche. Tsayin shekarun nan da suka gabata da canzawar zamani da yanayin rayuwa hadi da tarin nasarorin da ya samu a rayuwar sa, basu sa ya manta da zafi, daci da dafin da kowannen su ya zuba kamar digar dalma a zuciyar sa ba.
Rahinah na nan tsaye kamar an dasa ta a wurin. Daga karshe ta ga cewa in ta yi kuka a dalilin wulakancin dan mutanen Nahuche ta fadi babu nauyi, tana da tabbacin ya yi ne don ya bakanta mata, idan ta bari ran ta ya sosu irin haka Habibu ya ci nasara kenan? Don haka ta daddage ta hadiye wani mayataccen kukan bakin-ciki da ya yunkuro mata. Ta yarfe wasu zafafan hawaye da suka tsatstsafo mata.
Juyawar nan da za ta yi da nufin komawa cikin gida, sai ganin kafatanin jama'ar gidan ta yi tsaye a bayan ta. Sun zuba mata ido suna kallon duk abin da ke faruwa.
Rahinah ta rasa inda za ta sa kanta don kunya, bakin ciki da takaicin wulakancin da Habibu ya yi mata a bainar jama'a. Ga hawaye shabe-shabe a idanun ta. Ita ba shi ta biyo ba, dan ta ta biyo. Linzamin da ke zarge wuyan Uwa akan dan ta, shi ya zargo ta ya fiddo ta daga daki ta biyo bayan Abdallah ba tare da ta san lokacin da ta yi hakan ba.Yanzu kuma za ta ci gaba da bibiyar abin ta da karfin gaske, daga nan har kotun koli sai an ji su ita da Habibu Nahuche, sai ya ba ta abin ta in dai akwai shari'ah a duniya.

"Lafiya Rahinah? Kin san su ne?"

Daddy da Aunty har suna hada baki wurin tambaya. Sai ka rantse da Allah basu san komai ba. Ba kuma su suka hada komai ba. Maimakon ta ba su amsa sai ta girgiza kai ta russunar da jikakkun idanun ta, wadanda nan da nan sun kada sun yi jajir kamar gauta, abin ki da farar mace ita kanta tayi jazur musamman dogon karan hancin ta, ta sa kai ta wuce su zuwa ciki da dan banzan sauri, har tana hadawa da gudu-gudu da mugun cin tuntube.
Kai tsaya bata tsaya a falon ba. Dakin ta ta nufa ta soma kwashe komatsan ta data barbaza a kan durowar gefen gado tana dannawa a hand bag din ta, sannan ta janyo trolley din kayan ta ta fito rataye da mayafin ta bisa kafadun ta, idanun ta bakidaya sun kankance sun juye sun canza launi. Har wani hayaki-hayaki da yaji-yaji suke yi mata. Tsabar tukuki da bakin-cikin dake cin ran ta.
A bakin kofa suka ci karo da Aunty, ta saki baki tana kallon Rahinah.
"Ina za ki je haka Rahinah a daren nan?"
Ba ta san lokacin da hawayen da take ta tattali suka balle mata ba, ta yi maza ta sadda kai don kada ta ba su damar zubowa a gaban Anty, raunin ta ya fito baro-baro wato (weakness) duk da yadda ta ke kokawa da shi, ta ce,
"Aunty za mu koma ne, ina nufin Abuja".
Aunty Badiya ta yi murmushi wanda ya tsirga har cikin ran ta, ta ce, "Anya Rahinah? A wannan Najeriyar da muke ciki ne za ki kama hanyar Abuja after 8pm (bayan karfe takwas na dare)? Ido na ganin ido ma yaya aka kare da insecurity? Ki sake tunani dai. In dai don Baban Junior ne, ya tafi, kuma bana jin zai dawo gidan nan nan kusa......".
A firgice Rahinah ta kalle ta. Aunty ta sake yin murmushi wanda har hakoran ta sai da suka fito, ta kama trolley din ta maida mata dakin tare da kamo hannun ta suka koma ciki.
A gefen gado suka zauna hannun Rahina na cikin na Aunty Badiya. Ta rike Rahinah tsam-tsam kamar ta maida ita cikin ta don so da kulawa. Tana jin wata sabuwar kaunar Rahinahn na ratsawa a ran ta. Wadda ta zarta ta alaqar diyar miji dake tsakanin su a baya wadda mijin ta Uncle Usman Girei ya hada, a yau dangantakar ta kara matsayi mai girma dalilin kasancewar ta mahaifiya ga dan ta Junior. Dan ta Abdallah, da kanin ta kwalli daya a duniya ya haifa, kanin da bata da kamar sa a duniya, uban dan da take so har fiye da nata %??ja%??jan data haifa a cikin ta.

Rahinah, gaya min gaskiya, kin san Baban Junior ne a wani wurin?"

Da sauri Rahinah ta cira kai ta dubi Aunty, sannan tayi saurin sadda kan ta kasa, ba tare da ta ce komai ba. Amma komai ya gama bayyana kansa cikin idanun ta. Idanun sun ce "sani ba dan kankani ba!"
Aunty ta ci gaba da nacin tambayar ta.
"In ba ki san shi ba ta yaya daga ganin sa za ki ce za ki tafi Abuja afujajan? Me ye ki ka bi su wajen mota daga ganin mutum da Dan sa in baki san su ba? Kuka fa muka ga kina ta yi har da sheshsheka Rahinah?"
Nan ma Rahinah shiru ta yi kamar da dutse Aunty Badiya ke magana. Aunty ta jinjina kai cikin mamaki, ga dukkan alamu Habibu ya gamu da wadda ta fi shi iya zurfin ciki. Wadda ta fi shi taurin kai da wuyar sha'ani. Tambayar duniya Aunty Badiya ta yi amma Rahinah gumm! Ba ta ce komai ba. A karshe ma sai ta kifa kai akan cinyoyin ta ta fashe da kuka.

"Ya sake tafiya da Abdallah for the second time (a karo na biyu) wannan karon ban san ina zai kai shi ba kuma..., I have no idea a kan abinda zai yi yau, don ya kara raba ni da shi....
Aunty Habibu bashi da adalci ko kankani, bashi da tausayi bashi da imani a zuciyar sa in dai a kai na ne, ban san meyasa ba, ban san dalili ba, kan sa kadai ya sani da selfish interests din sa....
Na tabbata yanzu zai yi duk abinda zai iya wajen kara nesanta ni da ABDALLAH, har fiye da wanda ya yi na shekarun baya tun da yau na gan shi a inda bai zata zan zo ba. He%??j good at kidnapping a son from his mother (ya kware wajen sacewa Uwa dan ta) da kuma raba zuciyar Uwa da ta dan ta. Wannan shine babban abinda HABIBU NAHUCHE ya fi kowa kwarewa a kai Aunty; ZALUNCI!"

Magana%???. zarar bunu ta fito daga zuciyar Rahinah don bana ce daga bakin ta ba, irin maganar nan ta mutum da zuciyar sa.....domin fatar bakin ce kawai ke motsi, amma zuciyar ta ce ke magana.
Amma hakan bai raunata ta ba kamar wulakancin da Habibu ya yi mata a idanun jama%??jr gidan, ta hanyar pretending kamar bai san ta ba, yayi mata kallon banza, ya kuma dauke dan sa yasa a mota suka yi tafiyar su, bayan ya bule ta da iskar motar sa.

Aunty ta rungumo ta a jikin ta cikin kauna, tana lallashin ta ta hanyar jijjiga kafadunta kamar tana rarrashin karamin yaro. Zuciyar ta bakidaya ta karye. Lallai abinda suke zato cewa karami ne tsakanin Rahinah da Habibu to ba karamin ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bane asexpected (yadda suka zata). Wadannan sunaye da Rahinah ta kira Habibu da su sun bata mamaki matuka, domin a iya sanin ta a duniya babu mai akasin su irin Habibu, bata taba ganin ko jin wani ya suffanta shi da su ba (zalunci). Karewa ma, ita bata taba ganin mutum mai kirki, mai saukinkai, mai tausayi da adalci a duniya irin kanin ta Habibu ba!
Dankwalin Rahinah ya zame ta baya, wanda hakan ya sa sassalkan bakin gashin kan ta na fulanin usli ya kwanto lambam a gadon bayan ta ya rufe fuskar ta bakidaya. Aunty ta dauka tana daura mata bayan ta tufke mata jelar dogon gashin kan nata wuri guda. A lokacin Uncle Usman ma ya shigo dakin, tun daga waje ya ke kakabi yana fadin,
"Me na ji ana cewa ne? Wai Rahinah zata tafi Abuja yanzu? To me yayi zafi?
Ki kama hanyar Abujan a daren nan ki ga yadda za mu yi ni da ke Rahinah. Shin Mai sunan Dada, a ina ki ka san HABIBU ne ma???"
A muryar Uncle babu wasa ko kadan yau, babu lallashi irin wanda ya saba yi mata, tambaya ce kawai yayi bisa umarni da ke tsananin bukatar amsa. Bai taba yi mata magana in a serious tone irin na wannan karon ba. Don haka kukan da Rahina ke yi ya katse kan sa da kan sa, ta soma shiga taitayin ta yayin da wata irin fargaba da tsoro suka rufto mata a lokaci guda.Me zata ce da su tunda itama har yanzu bata gama tabbatar da irin alaqar da ke tsakanin su da shi ba?
Uncle Usman ya zazzaro ido yayi kan Rahinah kamar zai buge ta yana fadin,
"Za ki gaya min inda kika san shi ko in kira shi da kaina shi ya fada min? Na ce a ina kika san shi?"
Da sauri ta dago ido ta dubi Baban nata, ta yarda yau ya kauda duk wani wasa da farantawar diyancin da ke tsakanin su, amsar ta kawai yake bukatar ji ko yakai hannun sa jikin ta.

Murya na rawa Rahinah ta ce.

"I... I know him from Germany..." (Na san shi a Jamus). Sai kuma ta kifa kan ta a kafadun Aunty wadda da ke kusa da ita. Ta soma wani irin girza kuka da ta tuno ranar da ya raba ta da diyaucin ta by force, abinda a turance ake kira (marital rape) da kuma ranar da ya dauke mata Abdallah ya janyo mata (maternal deprivation) tsakanin ta da dan ta. These are the worst parts of him da ba za ta yafe ba!Ta kuma kasa mantawa har gobe, har abada kuma bazata manta ba, baza ta yafe ba. Uncle ya ce,
"Sai kuma aka yi yaya a Germany din?"
Cikin kuka Rahinah ta ce, "sunan sa HABIBU NAHUCHE... my ex-husband. Ya aure ni ne ba da cikakkiyar amincewa da yarda ta ba. Ba kuma hannun iyaye na ba. Ya aure ni a wulakance a hannun wata uwar daki na a Jamus mai suna Aunty Laura. Auren ya kare a kwanaki kalilan. Har muka samu rabon wannan yaron, sai ya sace min shi ya taho da shi daga yaye shi%???. %???.
(Tuno ranar da ya dauke mata Abdallah, ya kara rura kukan ta). Da yadda ta bi titi a Frankfurt kamar mahaukaciya zautacciya. Sai da ta yi mai isar ta tana yi tana fyace hanci, tayi jajir don kuka musamman hancin ta komawa yayi kamar jini ya kwanta. Daga Aunty har Daddy babu wanda ya sha numfashin ta, sai dai kuma kukan da ta ke yi yana ratsa su yana sanyayar da jikin Aunty, sai da ta yi kukan da ya samarwa zuciyar ta rangwame da salama.
A yau Dr. Rahinah ta yarda da gaske kuka Rahma ne ga zuciyar dan adam wani lokacin. Kuka ne na tasowar tsohon miki da aka samu ya jima da yin healing. Sai da ta samu rangwame daga nauyin da zuciyar ta ta yi sannan ta cigaba da gaya musu cikin murya mai ban tausayi.
%??mabibu ya yi min laifuffuka masu yawa Uncle, wadanda bazan iya fada ba, don ban san tsakanin ku da shi ba, zai cigaba da zama sirri ne tsakani na da shi har abada, kuma bazan iya yafe masa su ba har abada, in na ce zan gaya muku tun haduwa ta da shi da irin laifuffukan da ya yi mun, girman sa zai zube a idon ku, kuma zuciya ta bata da jarumtaka da juriyar tuna abinda ya yi mun, bazata dauka ba. Na riga na baiwa abin baya.
Shi ya sa na ki yarda in koma wa auren sa (no matter how much he repented). Duk da Daddy Ambasada, Nene har ma da Yafendo sun so hakan sosai (komen auren mu).
Yanzu kuma ina so in karbe yaro na ko ta halin kaka. Ka taimaka min Uncle....., don Allah ka taimake ni in karbi yaron nan!". Ta ci gaba da kuka mai ratsa zuciyar duk mai sauraron ta.

Wani irin hararar ta Uncle Usman ya hau yi, ya ce, "Yaron da ba ki taba waiwaya ba tsayin shekaru goma ko? Yau ne kika san yana raye? Saboda kin gan shi kin tuna shi? Me ya ci ya rayu shi da dan sa baki sani ba? Yaya ya yi da kashin sa da fitsarin sa duk baki sani ba! Sai yau don kin gan shi healthy and vibrant karkashin kyakkyawar kulawar jajirtaccen Uban sa mai son sa da gaskiya?
Wace irin Uwa ce ke da zaki kasa waiwayar dan ki shekaru goma alhalin kin san yana raye a duniya?
In baki waiwayi uban ba da hujjar ya yi miki laifi shi Abdallah laifin me ya yi miki?
Har kina da bakin cewa zaki dauki dan ki yanzu? Sabida kin gama da boko ko kin zama abinda kike son zama? Cewa nake uwa tagari tana iya sadaukar da komai, don ta rayu da dan ta?
Yanzu ne kika san yana raye? Na dauka kin san da su a duniyar Subhana amma tun bayan dawowar ki baki kara yi mana zancen su ba mu iyayen ki, ko da da subutar baki ne, ko ki je a je a gano shi in ke baza ki je ba, sabida neman duniya ne a gaban ki babu neman aljannah? Ke Rahinatu, ki fita ido na in rufe, zan fyato ki in kika nemi bata min rai.
Ke wacece da ba za%??j yi miki laifi ki yi afuwa ba? Kowanne irin laifi ne ba ya wucewa ke a wurin ki? Ina amfanin kullatar dan uwan ka musulmi irin wannan kullacin na shekara goma wanda aure ne ya taba hada ku ba shashanci ba har da albarkar yaro?
In ji dai Habibu ko me ya yi miki ba shirka yayi ba? Ko Allah (S.W.T) ba hakuri Ya ke da mu dukkan mu bani Adam ba?
Da Allah ba ya hakuri da mu, tare da yi mana afuwa bisa tarin laifuffukan mu, da tuni ya kifar da mu kamar yadda ya kifar da al%??jmmar Annabawan da suka gabace mu sabida yawan laifuffukan mu da sabawar da muke maSa tare da rashin godiyar mu gare shi.
Kullum cikin saba masa muke da karkacewa umarnin Sa, amma afuwa Yake mana kullum da zarar mun roka.
Ke wace ce da ba za ki yi afuwa ga wanda ya saba miki ba, ya kuma dawo ya nemi gafarar ki? Ko kema Allah ya dube ki sanadin hakan ya yafe miki zunuban ki?"

Rahinah kuka ta ke tana girgiza kai, ta ce,
"Uncle Uncle ba za ka gane ba...... shi nasa daban ne, he%??j selfish by nature, kuma azzulumi ne na kin karawa".
"Kwarai da gaske. Ba abin da zan gane cikin wannan dambarwar taku mai sunan Daada, face ke da shi duka masu zurfin ciki da taurin kai ne na rashin dalili, rashin afuwa da wahalar da kai siddan da kuma kafiya. In ba haka ba ki fada mana mu ji menene laifin? Mu gani in girman sa ya yi yadda kike kambama shi. Sannan kuma ku yarda ko kada ku yarda har gobe son juna ne yake wahalar da ku ya kuma hana ku yin aure a inda kuke, tunda bazaku ce kun rasa masoya ba.
Amma a wannan karon muddin mu muka haife ku, ba ku kuka haife mu ba, to kuwa za mu saka muku waigi cikin wannan rashin hankalin da kuke yi. Ke ba aure shi ba aure kun gwammace ku mutu gwauraye sabida son juna. To mu zuba mu da ku. Kafar wando guda zamu saka ni da ku bakidaya".
Da fadin hakan ya juya ya fita cikin fushi. Aunty ma bin bayan sa ta yi zuwa falon sa, ta zauna daga gefen sa tana diallingnumber din Habibu, jikin ta duk yayi sanyi. Iya kintacen ta da hasashen ta da tsinkayen ta, ta kasa gano hakikanin laifin da Habibullahin Hajiya ya yi wa Rahinah haka.

*****
A
lokacin suna cikin wani daki na musamman (VIP room) na NAHUCHE HOTEL na garin Kaduna shi da Abdallah, daga shi sai farar singlet da dogon wandon da bai kai ga canzawa ba, ya sirkawa yaron ruwan dumi a kwamin wanka (bathtub), ya ce ya yi wanka don ya ji dadin yin barci, don gobe asubanci za su yi zuwa jihar Lagos.
Kiran Aunty Badiya ya shigo cikin Thuraya din sa, da farko kamar ba zai amsa ba, don ya san tatsuniyar gizo bata wuce koki, haka ya kyale wayar ajiye daga gefen sinkdin toilet tana ta burari yana kallon ta ta gefen ido yana cigaba da sirka ruwan wankan Abdallah cikin rashin damuwa, wani abu da bai taba yi wa Badiya ba, ko dakin meeting ya ke baya kin daga kiran ta don ya san in har ta kira shi to sako ne mai muhimmanci take son ta isar, sai Abdallah ya juya ya dube shi yace.
%??maddy, Mummy ce fa ke kira%??? kasancewar ringtone din da ya sanyawa Badiya daban yake, kuma Abdallah ya san shi, ala dole ya yanke shawarar amsawa, ko don kyawawan idanun Abdallah (Almond shaped eyes) masu kama da na uwar sa dake karakaina a kan sa kamar yana son karantar canje-canjen da yake ta gani na (facial expression) a tare da Baban nasa tun barowar su gidan Aunty Badiya,
%?na yi wankan Abdallah kafin na amsa wayar, ina zuwa, zan zo na cuda maka baya%???. %??mar ni ma kawai Daddy ba sai ka zo ba, na iya da kai na ai yanzu%???. In ji Abdallah.
Ya fito gefen gadon dakin ya zauna, ya amsa kiran Yayar tasa cikin madaukakiyar nutsuwa. Muryar sa kuwa Anty bazata iya fassara yanayin ta ba.
"Kuna ina ne Habibullahi?%???
"At the hotel%???". Ya ba ta amsa a matukar gajarce, kuma a takaice. Kamar mai fama da ciwon makogaro. Irin baya bukatar wasu tambayoyin daga wannan.
"Wane hotel din? Daga nan sai ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login