Showing 45001 words to 48000 words out of 110913 words

Chapter 16 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

kuma?" Aunty ta sake tambaya, wannan karon murya cike da lallashi (mai nuna concern) fiye da ta baya.
"ba sai kin ji kowanne hotel bane don da Assubah muka barin shi. Zuwa duk inda Allah yak-kai mu". Habibu Mustapha Nahuche, ya amsa wa Yayar sa Badiya da Bazamfariyar accent din sa. Za ka iya jin helplessnessda hopelessdin da ke kwance cikin muryar sa.
Ajiyar zuciya Aunty ta yi, ta ce a raunane,
"Will you do me the favour of coming back now (za ka yi min alfarmar dawowa gida na yanzu)?"
Da sauri ya girgiza kai, kamar tana ganin sa.
"Ni da gidan ki har abada Maman Musaddiq!". Daga haka ya kashe wayar sa.

Aunty da Uncle suka dubi juna, dama wayar a bude ta saka ta, Uncle na jin komai. Uncle Usman ya yi murmushi haka itama Badiya, ya ce, "Tabdi! Yau nake ganin abin da ya fi karfin ji da gani na. Su kuma irin tasu nau%??jn salon soyayyar kenan? Ana so ana kai wa kasuwa karfi da yaji? Amma babu komai, mu basu lokaci mu gani, na tabbatar miki zasu nemi juna da kan su, ko da tsiya ko da arziki, tabbas daya zai nemi daya%???.

Uncle Usman kamar mai gani har hanji. Cikin daren Rahinah kasa barci ta yi, ta kasa sukuni akan gadon ta, daga karshe ma sauka ta yi daga gadon kamar mai aljannu sabon kamu sai safah da marwah take a dakin ta, tana tunanin ta ina zata fara? Ko ta halin kaka zata kwaci Abdallah a cikin watan nan ba sai an ja dogon lokaci ba. Ta yarda ta amince daga lokacin da ta sake dora ido akan Abdallah (her maternal love for him increased) wato KAUNAR UWA ta motsa fiye da kintatawa bazata kuma iya rayuwa babu shi ba.
Abu na farko, tana son lambar wayar Habibu Nahuche, a yau ba sai gobe ba, don aiwatar da kudirin ta na farko, wanda zuciyar hankali da kyakkyawan tunani ke halartowa. Idan ya ki, sannan sai ta aiwatar da kudiri na biyu, wanda shi ya kamata kawai ta dauka don huce takaicin abinda ya yi mata yau, da nuna masa da da yanzu fa ba daya bane. Wata fuskar.. yanzu ta fi gaban mari.
Amma zuciyar hankali da nutsuwa da Allah ya halicce ta da ita, har ma da bangaren adalci na zuciyar ta, sun ki amincewa da hakan; sun ce ta bashi dama ko sau daya ne ta ji amsar da zai bata%???. Once and for all.
Duk da zuciyar girman kan ta da jiji da kai irin na diya mace mai aji daidai da nata, har ma da ego din ta na tankwabe shi. Abin nufi anan; zuciyar hankali na fadin ta fara sauke kai, ta ajiye kullacin ta da shi a gefe, ta roke shi (alfarma), ta hanyar bin sa ta lalama da neman alfarmar karbar yaron ta cikin mutunci (in such a way that) babu cin mutunci ko tozarta juna da zai biyo bayako don albarkacin Aunty Badiya data tabbatar jinin sa ce yanzu, bayan wannan babu wani abu daban a tsakanin su da zai kuma wakana balle ya samu damar yi mata kallon banza.
Daga nan sai kowa ya kara gaba (in ta karbi Abdallah), ya cigaba da gudanar da rayuwar sa yadda yake yin ta. In dai yaron ta yana hannun ta falillahil hamdu, bata da sauran matsala kuma a rayuwa.
Amma a ina zata samu lambar Habib Nahuche ba tare da Anty Badiya ta sani ba?
Kawai sai Musaddiq ya fado mata a rai. Dama dan gidan ta ne. Da sauri ta dauki wayar ta ta kira shi, karfe goma sha biyun dare ta gota lokacin, shi har ya fara barci tace ya kawo mata aron wayar sa, zuwa safe zata bashi.
"Aunty Rahinah kin san bama shigowa cikin gida after 12 am?%???
Musaddiq ya fada cikin mamaki. Numfashin Rahinah na sassarfa, kamar yana shirin daukewa daga kirjin ta sabida azalzalar da zuciyar ta ke yi da cewa "a yi ta ta kare ita da Habibu Nahuche, a yau ba sai gobe ba, kowa ya san matsayin sa, tunda hakkin haihuwa kowa da nasa, ba nasa ne shikadai ba, ta ce
"Musaddiq ka ajiye min a bakin kofar shigowa falo ka tafi, zan fita in dauka da kai na%??? da sauri Musaddiq ya amsa.

"Rightaway Aunty Rahinah!%???

Duk da cikin zuciyar sa yana mamakin me Antin sa Rahinah zata yi da wayar sa, ba dai zata ce credit din kira ne bata da shi ba shine zata yi amfani da wayar tasa, a hakan dai ya bi umarnin ta domin ta wuce tayi masa umarni ya tsaya questioning din ta.
Cikin nutsuwar da take tattarowa da kuma baiwa kanta karfin guiwa ta saka suna 'HABEEB%??? a cikin wayar Musaddiq, ta kira.
Nan take kuwa sunan "UNCLE HABEEB! Ya bayyana kan sa. Sai ta yi maza ta kashe, ta kuma kwafe lafiyayyun lambobin na gidan wayar mtn a tata lafiyayyar wayar. Kai da ganin su ka san lambobi ne na musamman (special numbers) da ba kowa mtn ke baiwa ba.


NA HUCE is not for free
It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank
Shaidar biya 07030137870

SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870



*HABIBU NAHUCHE*


Ya bai wa kan sa hutu ne domin ya gama fahimtar a hargitse yake, ci gaba da ayyukan sa a wannan halin da ya ke ciki ba abin da zai haifar sai tarin nakasu da koma baya cikin harkokin kasuwancin sa. Domin hatta lissafi kowa da ke tare da shi ya san ya daina yin sa daidai.
Ya dauka komai nata ya tafi, tafiyar da babu dawowa, ya dauka ya riga ya binne ta a zuciyar sa ba don ta mutu ba, sai don ta gama taka rawar ta a rayuwar sa, ya dauka komai nata ya zama bygone? Tunda bai hana shi progressing ba. Amma ashe likimo ta yi wa zuciyar sa mai kama da kwanton Bauna!
Daga lokacin da idanun sa suka shiga cikin those innocent fulani eyes din na Rahinah Omar, komai ya dawo masa sabo fil. Wai kunama ta harbi gyambo.

In ma ya ce har da kari ba zai yi karya ba. Yanzu ya gan ta ne a matsayin cikakkiyar mace (matured young lady in her late twenties fiye da yadda ta ke a baya. Yanzu ne ta ke amsa sunan mace sosai, ta ke amsa sunan (Dr. Rahinah Omar Girei Otorhinolaryngologist) ba 'yar yarinya budurwa mai tsananin kyau da ya sani a Jamus, mai amsa sunan Rahinah Omar ba.
Wannan kyan na yanzu hade yake da sanin ciwon kai, matured mind, contentment of life.

A halin yanzu ka ganta tsammani za ka yi balarabiyar kasar Oman ce sabida yadda fatar jikinta ke glittering.

Dr. Irshad bai iya boye hakan a ran sa, a duk lokacin da ya ga Rahinah ko wani aiki ya kawo ta ofishin sa sai ya fada kasa-kasa cewa, %?riooking Ravishing'.

A duk sanda ya fadi hakan ita kuma za ta yi kicin-kicin da fuska, don duk namijin da ya yabe ta haushi yake ba ta.

Habibu Nahuche has never praised her beauty, watakila bai ma san ya ake gaya wa mace abin da zai dadada mata rai ba. Yet shi kadai yake burge ta, shi kadai ta ke so ta ji ya yabi wani abu nata. Unfortunately bai taba ba, sunan ta %?nuguwa-azzaluma%??? a bakin sa.

Watakila wadannan muggan kalaman nasa da suka haukata ta a kwanakin nan, su za su cigaba da birkitata suna farautar farin cikin ta da nutsuwar ta har zuwa ranar da ta daina numfashi.
*******


Duk da bai san wace irin alaka ce tsakanin ta da su Uncle Usman ba, ya fahimci alaka ce ta kusa ba ta nesa ba.
Maimakon ya samu hutu kamar yadda yake bukata cikin %?ljahuche Hotel%??? na garin Ikko, tun bayan da ya sada Abdallah da %?dioarding School%??? don ma kada Rahinah ta samu access din sake ganin sa, sai kadaicin ya bankado wa zuciyar sa tsohon kundi da tsohon miki na rayuwar KWANAKI BAKWAI a birnin Cologne din JAMUS.

Rayuwar da har yau bai kara maimaitawa ba, bai kara samun kwatankwacin ta a gardi ba, bai kara attemptingdin ta da kowacce %??ja mace ba tsayin shekaru goma, wato rayuwar auratayyah! For she left no space in him. Ta mamaye ko%??jna na zuciyar sa.

Ya rike kan sa ta duk hanyar da addini yayi umarni, ta hanyar maida kan sa busy kullum, da neman kudi da azumin tadawwu%??j don kada ya tuna ta. Don kada ya nemi mata. Ya sani ba irin mummunan zargin da duniya bata yi masa akan rashin aure.
Idan ya ce yana sufferinginternally a cikin wannan dan tsakanin, ya yi kadan ya bayyana irin halin da ya samu kan sa. Ganin ta ya tuna masa cewa shima NAMIJI ne mai lafiyar bukatar aure, don a baya ya dauka ya dade da komawa mace. Sabida kowacce macen kallon mata-maza yake mata sai ko yau da ya ga RahinahOmar ganin idanun sa, ya kuma ji muryar ta jin kunnen sa%???

******



*ASHE RAHINAH BAKI SAN GATSE BA?*

Mr. Atiku wato PA din sa na Abuja ne ya kira shi, da bai same shi ba, sai ya kira PA din Lagos. Rasak. Cikin tashin hankali yake gaya masa ya hada shi da Oga, itisurgent. Shi kuma yace masa Oga fa ba ya amsa waya currently, yana hutu a Hotel, ajiyar zuciya PA din Abuja ya yi, yace.

"Sai ka gaya masa hutu bai gan shi ba, an turo masa da SAMMACI daga Federal High Court, Abuja, kuma zance har ya bullawa media.

He has to be in Abuja today or tomorrow a kashe zancen nan kafin 'Daily Trust%??? su shigar da jaridar da zasu fitar jibi zuwa yanar gizon su, ko su fara sayar da ita a kan takarda.
Ban san wa ya kai musu zancen ba kuma ban san wa ya yi karar sa ba. Amma hakika a kan yaron sa ne, Abdallah. Har suna questioninglegitimacy din sa dalilin hakan. Ana neman sa nan da kwana uku a kotu!%???.

Jeremy da ke kula da abincin sa shi ya shigo masa da jaridar yau da ya sayo tare da lunch din sa. PA dinsa ne ya ce ya kai masa jaridar tare da abincin rana, tunda sun yi-sun yi da shi akan ya daga waya don su gaya masa yayi wani abu kafin %?`jaily Trust%??? su saki labarin, amma ko damar ganin sa bai basu ba balle ya san abinda ke faruwa.

Headline na jaridar Sabuwar Najeriya (NEW NIGERIA) dauke ya ke da kanun labaru kamar haka%???..

"NAHUCHE%?rj EX-WIFE DRAGS HIM TO COURT, ACCUSES HIM OF INJUSTICE ON THEIR CHILD%?rj CUSTODY%???.DR. RAHINAH OMAR OF NIZAMIYE APPEALS THE COURT FOR JUSTICE...

Yayin da Headline na 'Daily Trust%??? ya ce.

"IS ABDALLAH NAHUCHE A LEGITIMATE CHILD???%???

A cikin kanun labaran kuma an yi bayanin zuwan sa Germany karatu, tare da dawowa da yayi tare da karamin yaron, ba tareda kowa nasa ya shaida auren sa ba.

%??mo one knows how, and where Habibu Nahuche got his beautiful son Abdallah in GERMANY%???..not even his Mother%???.%???.

Ba da niyyar cin abinci ya fito falon ba, ya fito ne domin ya dauki wayar sa da ya bari akan diningtable din. Babban abinda ya fizgi hankalin sa kan jaridar da ke ajiye shine hoton Abdallah a fuskar jarida, sai na shi dana Rahinah, a kagauce ya bi headlines din. Wadanda suka sa wani irin gumi tsatstsafo masa.

%??mta kenan bata san gatse ba?! Ashe Rahinah bata da hankali da hangen nesa har yanzu tana nan yadda take da kafiya da taurin kan ta? Nauyin shekaru ba su kara mata komai ba daga sanin da ya yi mata a baya, basu canza ta ba haka basu ishe ta yin hankali ba?

Har yanzu tana nan a sha yanzu magani yanzun ta! (not giving things a second thought)%???.
Ya tambayi kan sa cikin tasowar wani matsanancin bacin rai, da bai taba ji a rayuwar sa ba, ba don yana shayin kotu zata kwace masa Abdallah ta bata ba, sai tunanin wannan tereren da ta ja musu, da Dan sa da ya ji ana kokarin sheganta masa!%???
A take ya yi waya yayi booking jirgi mai zuwa Abuja, da zummar zai je yau ya fuskanci Dr. Rahinah Omar da duk abinda take taqama da shi a duniya, sai ta gwammace bata yi karar nan ba%???ai ta gwammace bata san shi ba, sai ta gwammace wata alaqa bata taba hada su ba. Yau za ta san ko waye "REAL Habibu Nahuche%??? domin zai fiddo mata truecolour din sa.
Abdallah kuma sai dai ta daukaka kara zuwa SupremeCourt, (Federal High Court) ta yi tsararo ta kwatar mata shi, kai duk duniya bai ga kotun data isa kwatar Abdallah ba a kasar nan da wajen ta daga hannun sa%?9?? ??

(Babban bacin ran Habibu Nahuche ba karar sa da Rahinah tayi gaban Alkali bane, kamar shegan ta masa Abdallah da ta janyo ake kokarin yi a kafafen yada labarai babu gaira babu dalili, sai don neman magana da neman suna irin na %??jan jarida).
******












*ABUJA*

Kafin ka ce meye wannan labarin ya bazu kamar wutar daji a media, musamman cikin birnin tarayyah, kowace jarida tun daga ta cikin gida wato LEADERSHIP har Daily Tribune da Sahara Reporters ta maida shi headline din ta na wannnan satin. FACEBOOK, TWITTER, WHATSAPP groups kuwa sun maida shi %??jopic of discussion%??? hotunan Habibu da Rahinah da kyakkyawan dan su Abdullahi ya baibaye wayoyin al%??jmmah. Kowa yana fadin albarkacin bakin sa mai dadi da marar dadi.
Duk wanda ya kwana da sanin Habibu Nahuche (Lucky), Hotelier, ya ji labarin tsohuwar matar sa ta maka shi a kotu kan ya bata dan ta, dan da ba%??j da tabbacin na halaal ne don a kasar Germany suka haife shi ba da sanin kowa nasu ba.

Washegari Aunty da Uncle suka bi bayan su zuwa wajen Hajiya, Aunty ta tabbatar wa Uncle babu inda Habibu zai je da Abdallah sai Zamfara, don ba zai iya yawon jihohin Najeriya da yake yi da yaron ba, don ba ya so jama'a suna tanka wa a kan tsananin kamannin da ke tsakanin sa da yaron.

A cewar sa don kada baki ya kama shi. Yana guje masa kambun baka. Don haka Aunty ba ta raba dayan biyun tabbas Zamfara suka nufa.

Ilai kuwa Hajiya Kaltume sai ganin Aunty da maigidanta ta yi sun yi sallama suna shigowa.

Suka zazzauna suna gaggaisawa da Hajiya cikin tsananin girmamawa. Hajiya ta ce,
"Ni laifin me kuka yi wa Baban Abdallah ne?%???
Dariya Aunty da Daddy suka yi a tare, Aunty ta ce,
"Babu laifin fa da muka yi masa. Laifin mu daya kasancewar mu iyayen mahaifiyar Abdallah".

Hajiya ta dan zamo jikin ta daga cikin kujerar ta, ta tattara hankalin ta kan babbar diyar ta, cikin rashin fahimta ta ce.
"Wace mahaifiyar Abdallahn?"
Aunty ba ta bata lokaci ba, ta ce, "Dr. Rahinah, mahaifiyar sa wadda ta haife shi, matar Habibu a Jamus, wadda ta guje shi.
Diya ta ke ta halali ga Baban su Musaddiq shi da mahaifin ta mai rasuwa ciki daya suka fito".

Hajiyar Nahuche ba ta san sanda ta ce, "Allahu Akbar!" ba, "Allah da iko Yake, to ya aka yi da can ba mu sani ba?"

Aunty ta ce, "Muna tare da Rahinah tsayin shekaru masu yawa, tana karatun likita a Jamus, sai dai ta zo ta kwana biyu ta koma. Yanzu ne ta dawo gida gabadaya ta fara aiki a Abuja. Circumstances ne ya sa muka gane cewa ita ce, ba don wani cikin su (ita ko Habibu) ya gaya mana ba.
Hajiya gudun juna suke yi, bayan kuma a fili yake dayan su bai iya sake aure ba da dan uwan sa ba.
Laifin da muka yi masa har ya kwace Abdallah shi ne, mun yi plan din da ya ga Rahinar sa a gidan mu. Ba don haka ba sun zabi har su tsufa ba su kara neman juna, while dukkannin su sun san inda junan su ke rayuwa. Alaqar da ke tsakanin mu ce basu sani ba.
Hajiya, Habibu da Rahinah suna bukatar interference na iyaye da masu iko da su, domin su taimaka wajen gyara rayuwar su, su kuma ci gaba da rainon dan da Allah ya ba su a tsakiyar su".
Hajiya ta nisa cikin al'ajabi,
"Ke nan 'yar family din Sarkin Fulanin Girei Habibu ya aura?"
Daddy ya ba ta wannan tabbacin, sannan ya kara da cewa, "Uban ta shi ya sha nono ya saki na kama. Abin da dukkanin mu ba mu sani ba, kuma muke son sani shi ne, laifin da Rahinah ta yi wa Habibu, da laifin da Habibu ya yi wa Rahina suka gwammace su rayu a tagayyare cikin soyayyar juna shekara goma ba tare da juna ba".
Hajiya ta ce, "Sha'ani na miji da mata ai babu yiwuwar sai an san abin da ya hada su. Hanyar gyara kawai za a nema a sulhunta su. Oh ni Kaltume Ya Allah ka nuna min wannan ranar... da Habibullahi zai sake aure a rayuwar sa ta duniya, duniya kuma ta shaida".
Sai kawai ta soma matsar kwallah. Kwallan da ba ta komi ba ce face ta farin ciki, a dalilin sunsuno cewa lokacin auren Habibu ya zo. In dai da gaske 'yar su Aunty ita ce mahaifiyar Abdallah, ita shaida ce kan cewa babu wadda Habibu yake jira sai ita, ko da za ya soma furfura ba aure.
Uncle Usman ya ce, "Ai sulhu ba zai yiwu ba tare da an san rootcause na matsalar ma'aurata ba. Ta hanyar sanin mene ne hakikanin matsalar su ne za a san hanyar magance ta da hana ta sake faruwa a gaba.
Don haka Hajiya komai yana hannun ki yanzu. Ke kadai za ki iya tankwara Habibu ya nemi sulhu da matar sa.
Hajiya ta girgiza kai ta ce, "Wani irin lallashi ne ban yi masa ba a kan aure? Wane irin nasiha ne ban yi masa ba? Wace irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login