Showing 63001 words to 66000 words out of 110913 words

Chapter 22 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

Sarkin Fulani, manyan %??ia%??jan sa su Ilyasu, Dagacin garin Girei, makwabta da dattijai abokanan arzikin Sarkin Fulani, abokan mahaifin Rahinah na kuruciya da abokan Uncle Usman na garin Girei da duk wani mai fada a ji a garin Girei, jama%??jr gari %??ian gayyar sodi ma ba%??j bar su a baya ba.

Iyayen Habibu (Baffannin sa) suka mika sadakin su mai daraja wanda ya fito ne daga aljihun su da aljihun Hajiyar sa da suka yi karo-karo suka hada ba tareda sun bi ta kan sa ba, kasancewar kowannen su a kage yake kan yayi auren kawai koma da wacece, to balle da aka ce uwar dan sa Abdallah.

Don haka kowannen su cikin farin-ciki yake yin komai, ba bata lokaci aka daura auren HABIBU MUSTAPHA NAHUCHE da DR. RAHINAH OMAR GIREI. Wani aure da ya bar tarihi cike da farin cikin kowanne bangare. Ana yi ana raha da annashuwa. Limamin masallacin Juma%??j na garin Girei ya bi auren da addu%??j%?gj na musanman, tare da rokawa ma%??juratan zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada a tsakanin su.

Washegri Asabar kowa ya kama hanyar komawa garin da ya fito, tarewa sai Habibu ya zo da kansa inji Sarkin Fulani. Ya ce Usman ya kawo masa Rahinah nan gidan sa, daga nan Girei za%??j dauke ta zuwa gidan mijin ta bayan sun yi biki irin na al%??jdar garin Girei. Usman ya gaya masa tana gidan Ambasada yanzu haka, amma Nene Balki da Yafendo zasu dauko ta su kawo ta, in ya so, su rankaya daga nan Girei zuwa duk inda Habibu ya zaba mata ta zauna.

Kwanaki biyu kenan da daurin auren, ba tare da Habibu ko Rahinah wani ya kara neman dan uwan sa ba ko a waya, amma suna sane da cewa an daura din. Ita tana dakin ta na gidan su Nene a kwance kawai, ba abinda ke tada ta sai sallah.
Ta kashe wayoyin ta bakidaya tana wani irin jinyar zuciyar ta, da jinyar matacciyar gangar jikin ta kamar wadda ke fama da cutar paralysis, sabida yadda ta bi ta rafke akan gado, kokwakkwaran motsi bata yi, sallahr ma bata sanin lokaci yayi har sai Nene ta leko ta shaida mata cewa an yi kiran sallah.

Tun daga ranar da aka kara daura musu aure uffan bata kara cewa ba, domin kalaman Habibu na ranar da ya zo, sun yi wa zuciyar ta lahani da barna mai yawa.

Idan ta yi tunanin wai yanzu ya kara zama mijin ta na sunnah, sai duk wani kyakkyawan tunani ya subuce mata. Ta rasa wanda za ta kama.

Bata da tsumi ba ta da dabara a halin yanzu, sai na irin zaman da za ta fuskanta nan ba da jimawa ba a gidan Nahuche, a karo na biyu!

Ita dai ta san trial din ta da Habibu bai kare ba, akwai sauran manyan kalubale da ya tanadar mata, wadanda suka fi na baya. Domin ya rama abinda ya ke ganin ta yi masa. Abinda za ta rike a matsayin makamin ta yanzu shine kadai (maintaining self-esteem) din ta, na cewa ta fi gaban duk wani wargin sa a halin yanzu, za ta nuna masa cewa wata fuskar yanzu ta fi gaban mari. In Rahinah ya sani, wannan Rahinatu ce, warki daidai kugun kowanne da namiji.

Daga ita har shi sun kasa kulla komai sai tunani, wanda ya kasa basu mafita ga tarin damuwoyin su da tarin kalubalen da suke hangowa sake zama da juna, tunda dai har yanzu basu kai ga cimma matsaya kwakkwara wadda za ta yi maganin matsalolin su da rashin fahimtar da ke tsakanin su ba.

A nasa bangaren, Habib Nahuche, ya kudurce a ran sa ko kadan ba zai dauki rabin abinda ya dauka a baya daga Rahinah da sunan rashin SO ba, tunda dai yanzun ita ta amsawa kanta ba wani ya tursasata ba, don haka babu hannun sa a ciki. Nan kusa ma bai shirya mata tarewa ba ko inda zata zauna, don kamar yadda yace din ne da gaske bashi da bukatar ta cikin rayuwar sa ta yanzu.

Da dai Uncle da Ambasada sun sani da sun bar bygone a muhallin ta, don basu gama sanin ko wacece %??iar su Rahinah ba har gobe, shiyasa suke tsammanin da zuciya daya ta amsa, shi kam ya dade da sanin cewa ya riga ya bata baya. Ya manta da ya taba auren ta, ya dade da karbar rayuwa a yadda ya same ta, kuma yana jin dadin ta a hakan. Da Rahinah, da babu ita, ba zai kasa rayuwa ba, insha Allahu.

Me jiya ta yi bare yau? Abin nufi me rashin ta na shekaru goma ya kara musu ko ya hana musu shi da Abdallahn?

Da wannan jinyar zuciyar kowannen su ke jibge akan gadon sa, ya dakatar da kowanne ayyuka na cigaban rayuwar sa da dailyactivities din sa.

Amma ga iyayen su da masoyan su abin ba haka yake ba, aunty Badiya, a ranar don farin cikin an daura wa Habibu aure da Rahinah, sai da ta kai goshin ta kasa ta yi sujjadar shukr, ta kuma dafa abinci mai rai da motsi ta rabawa mabukata sadaqah.

Hajiya Kaltume kuwa, ko da bata maraba da Rahinah, farin cikin yau Habibullahi yayi aure da azumi ta tashi a bakin ta.

Itama ta sa an dafa abincin sadaqa an raba a Kofar Jange har gidajen makwabtan ta, ko dama duk Juma%??jh tana bada sadaqar naman saniya, da ake kayarwa a rabawa mabuqata na Kofar Jange, ranar da Uncle Usman ya tabbatar mata sun dauro auren suna kan hanyar dawowa Shanu uku ta sa aka kayar don yin sadaqah.

Nene Balki da Yafendo kuwa suna can suna yi wa Rahinah kyakkyawan shiri irin na iyayen kwarai masu shirin kai %??iar fari daki, Nene tayi ordern kayan gyaran mata %??ian gaske tafiyayyu tun daga Nijar. Ta kuma yi Magana da Yagana %??iar Maiduguri mai yi mata gyaran jiki kan ta zo a washegari ta fara gyara Rahinah.

Sahura mai aikin Rahinah tana Kaduna, da Anty Badiya ta yi mata waya ta ce su fara shirin tarewa har rawa sai da ta taka. Don haka duk wani masoyin su cikin farin ciki yake, ya kuma ci wa auren nan alwashi da buri sabanin ma%??juratan, wadanda ke ganin tamkar Alkiyamar su ta matso.

Kowanne gani yake an katse masa rayuwa an kuma hada shi da alaqaqai, tunda kar ce ta san kar, kowanne da irin alwashin da yake ci wa zuciyar sa a kan dan uwan sa.

Shi dai Habibu alwashi ya ci ba zai bari Rahinah ta shiga tsakanin sa da dan sa ba, tunda tare ta gan su, ta sake kutsowa cikin rayuwar su don ta kara tarwatsa ta.

Ita kuwa Rahinah abu daya ne yake sassauta zuciyar ta in ta tuna yanzu zata samu kusanci da Abdallah. Za ta maida hankalin ta ne kacokam kan cike wawakeken gibin da Habibu ya samar a tsakanin su wanda ta san ba zai yiwu a lokaci guda ba, sai ta yi da gaske wajen kwatowa kan ta soyayyar dan ta, ta cike ratar da Habibu ya janyo a tsakanin su.

Wannan shi ne kadai abin da zai zaunar da ita a gidan Habibu Nahuche amma ba Habibu ba; soyayyar dan ta Abdullahi!

Uwa uba farin cikin iyayen ta da kwanciyar hankalin su wato Ambasada da Uncle Usman. Ita kan ta Aunty Badiya Rahinah tana darajja ta, bata jin Habibu ya isa ya farraqa tsakanin su.

Domin Badiya ta kaunace ta kauna ta hakika tun kafin ta san alaqar da ke tsakanin su. A lokacin da ta ke neman dangin da za su rungume ta. Don haka ko wanene Habibu ga Badiya alaqar su mai kyau tana nan bazata taba canzawa ba saboda shi.
******


*Na huce* is not free.
It's 1000 via 3094856450
Sumayyah Kabara Firstbank

Shaidar biya
07030137870

PAID BOOK




Tunda ta soma maganganun nata har da kuka ba kalaman nata Habibu Nahuche ke saurare ba, a%??jh, yanayin motsawar dan bakin ta ne cikin tsiwa jazir da shi (pink lips), lookingkissable, shi yake ta kallo, yana tuna wani lokaci can da ya shude a Jamus, a cikin motar sa a lokacin da take da cikin Abdallah da ya sato ta daga Library, abinda ya faru cikin motar wanda har abada bazai gushe daga zuciyar sa ba.
Wannan tunanin ya tada tsohon kwantaccen tsumi, domin ya tuna masa kowacece Rahinah a kan gadon auren sa. Dadin dadawa kewar shekara goma! Ba wasa bace ga muminin da ya rike kan sa. Su suka hadu suka tado masa wata gigitacciyar sha%??jwa wadda soyayyar da yake yi wa Rahinah ta jagorance ta, suka mantar da shi cewa fada su ke yi, sabani ne mai girma a tsakanin su.
All of a sudden idanun sa suka lumshe a cikin kallon ta, hannayen sa kuma suka kai kan su gare ta suka zagaye ta. Rahinah sai jin ta tayi bakidaya kwance lamau a jikin Habib. Wani al%??jmari tamkar haduwar chemistry din gravity ya bakunce su su duka, shock ne na bazata na wata irin sha'awa ya bakunce shi a take.
Wata irin tsuma jikin sa da zuciyar sa suka shiga yi lokacin da ya soma kissing Rahinah, wani irin lafiyayyen kiss, wanda ya gigita Rahinah Omar, ya kuma fidda ta a hayyacin ta nan da nan, (as it happened abruptly) ba tareda ta shirya ko ta yi tsammani ba. Kuma ba tare da ta kawowa ranta hakan zai kara gudana a tsakanin su nan kusa ba.
Ta dade da sanin rana irin wannan na zuwa, tunda auren ne dai suka kara yi, sannan a wannan fannin ba shi da hakuri, amma bata zace ta nan kusa ba, yanayin yanda yake sumbatar ta ya mantar da ita komai da ke tsakanin su. Hatta sunan ta na yanka a wannan lokacin bazata iya tunawa ba.
Ko me Habib Nahuche ya tuna? Sai ya nemi kuzarin jikin sa ya rasa. Yayi maza ya tsayar da sumbar da yake mata tare da janye jikin sa daga gare ta, ya shiga cusa yatsun sa cikin sumar kan sa cikin nadamar abinda ya aikata.
Ya yarda akan Rahinah Omar ba shi yake sarrafa gangar jikin sa ba, yana runtse ido yake fadin,
%??m%??j sorry, it wasn%??j intentional%??? (kiyi hakuri ban yi da niyya ba).
He doesn%??j want to be that abusive husband again, sabon Habibu yayi alkawarin komawa. Wanda ba zai kara forcing matar sa akan shimfidar sa ba. Ya yarda wannan shine deadlymistake din sa a duniya a idon Rahinah wanda ya shiga tsakanin sa da Rahinah Omar. Rahinar da ya tabbatar ba zai iya cikakkar rayuwa ba tare da itaba. Kuskure ne wanda ko Rahinah bazata kara son sa a gaba ba a dalilin sa, yana fatan ya gyara shi, yana kokarin ya goge shi daga zuciyar ta yadda ya kamata. Yayi repenting in har za ta bashi dama.
A kan ta bashi da zabin yadda yake so su rayu yanzu, zaman nasu zai kasance ne yadda ta zaba musu.
Rahinah durkushewa ta yi akan kafafunta tana kuka na bakin cikin abinda Habibu yayi mata. Sanda ya bar dakin bata sani ba, ta dai ji lokacin da ya rufo mata kofar silently.

Daga shi har Rahinah haka kowa ya kwana ya kuma wuni a dakin sa sukuku, ba wanda ya fito, ba wanda ya kara shiga dakin dan uwan sa, haka ba wanda ya ci abinci, kowa tasa ta ishe shi. (Jinyar zuciya da ruhi).
A satin duka ba wanda ya zo musu, sai wayar %??ian uwa da abokan aikin ta da take ta karba, suna masu tayata murnar aure da suka samu labari ta kafafen yada labarai da jaridu. Jaridar Sabuwar Najeriya cewa ta yi %??mrom Court Issue to Love Reunion (Habibu Nahuche and Ex-Wife).Sai hoton su itada Habibu wanda ta rasa a ina aka same shi. Duk Safeenah ta turo mata ta waya ta gani.
A ran ta tace %?nu dai %??ian jarida akwai tada zaune tsaye, ko wa ya ce musu tun da can soyayya ce tsakanin ta da Habib Nahuche balle yanzu? Me jiya ta yi bare yau?%???
Da daddaren ranar da suka cika sati da tarewa ta kira Aunty Badiya.
Tana jin muryar Badiya na amsawa ta sa kuka, kuka sosai mai cin rai, hankalin Badiya ya tashi, ta shiga tambaya %?nafiya Rahinah? Me ya faru? Habibu ne ko?%???
Cikin kuka ta ce %??munty tunda na zo gidan ban ga Abdallah ba, Anty bazan iya zaman gidan babu shi ba, kin dai san komai, saboda shi na yarda na dawo%???.
Aunty Badiya ta nisa, cikin lallashi ta ce ki yi hakuri Rahinah, ki rabu da shi ki nuna baki damu ba, ya dauke shi ne don ki damu, wallahi ko ni ban san inda ya kai shi ba, amma na tabbata yana lafiya kuma yana kula da shi har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Da za ki kwantar da hankalin ki ku zauna lafiya Habibu ya fi ruwan sha saukin sha%???.
Haka Aunty ta yi ta lallashin ta, a karshe ganin Rahinah ta ki daina kukan ta ce za ta sa Hajiyar su ta shiga maganar, ya dauko shi daga duk inda ya kai shi ya kawo mata shi.

Wayar mahaifiyar sa Hajiya Kaltume ta same shi a washegari, yana kwance a daki ya kasa ko zuwa kofar daki, don kada yayi kacibus da Rahinah cikin gidan. Ya yarda in har zai ke ganin Rahinah to kuwa burin sa na son zama SABON HABIBU ba zai taba cika ba, ba zai iya sarrafa kan sa ba dole ya kai kansa gare ta in one way or the other.
Baya so ya kara lalata komai, zai daure, zai cije by becoming achangedperson, har zuwa ranar da Rahinah zata nemi wannnan don kan ta. Amma anya hakan mai yuwuwa ne daga Rahinah Omar? Ko dai mafarki yake yi? Rahinah ce watarana zata nemi wannan daga gare shi? Ashe kuwa ranar za'ayi ruwa har da kankara. Abin yi guda daya ne, shine ya kaurace mata ya nisance ta har sai ta nemeshi don kan ta.
Sai kawai ya tashi ya hau tattara abubuwan bukatar sa, da nufin booking din jirgi a yau ya koma Lagos. Sai kuma ga wayar Hajiya ta shigo.
%??mabibullahi ina fatan kuna lafiya", Hajiya ta tambaya da muryar uwa, %?nafiya muke cikin alkhairi Hajiya ta%??? Hajiya Kaltume tace %?"no bisa umarni na ba neman jin ba%??jsi ko naka ra%??jyin ba, ko wata tashin tashina, ka je ka dauko Abdallah daga inda duk ka boyeshi, ka kawowa uwar sa.
Habibullahi ina jiye maka kada hakkin su ya kama ka, tana da hakki babba a kan sa, har fiye da kai. Shekaru goma ka raba ta da danta bata san komai a kan sa ba balle halayen sa da irin tarbiyyar sa, ta dawo gidan ta don ta samu kusanci da dan ta amma ka dauke shi wannan ya zama mugunta.
Bana so Allah ya kama ka da hakkin wani ko wane iri balle hakkin iyalin ka%???.
Murya can kasa Habibu ya amsa da %??mnsha Allahu Hajiya ta zan dawo mata da shi, makarantar kwana na kai shi a Lagos%???.
Hajiya ta ce %??mbdallah yayi kankanta da makarantar kwana, kuma ya gaya maka ba ya so, kusanci da uwa yake bukata ba makarantar kwana ba, da saka idanun ta akan tarbiyyar sa a wadannan shekarun na rayuwar sa, kai dai kawai ka ce ka so yin mugunta ne shi yasa ka dauke shi amma in banda haka ko zaka kai shi makarantar kwana ai ka bari ya isa shiga babbar sakandire".
"Insha Allahu Hajiyata zan cika umarnin ki"
"madallah, ko kai fa, Allah ya karawa rayuwa, iyali da nema albarka".
Sai da ya kammala shirin sa na tafiya tsaf, yayi booking jirgi online, ya yi matukar kyau cikin wani tsadadden yadi filtex mai hasken sararin samaniya, ya fito a handsome Habeebun sa, dan Nahuche jikan Nahuche, shalelen Hajiya da Aunty Badiya, sanan ya rufo kofar dakin sa zuwa dakin Rahinah don yi mata sallama irin wacce addini ya rataya a wuyan sa.
Sallahr walha ya iske tana yi, bai zauna mata a daki ba, daga tsaye ya tsaya yana karewa komai na dakin kallo yana mamakin yadda iyayen ta suka shirya mata shi gwanin ban sha'awa, har ta idar da sallahr. Jikin ta ne da numfashin ta suka bata yana cikin dakin a tsaye sabida yadda atmosphere na dakin bakidaya ya canza da sassanyar kamshin Carolina Herrera wanda shi ke fallasa shi a koyaushe, hannayen sa biyu zube cikin aljihu ya taka sannu a hankali zuwa gaban ta, da ya tabbatar ta yi sallama.
"Shin Rahinah me ag-gamin ki da Da na ne? Ni ban taba jin inda akke son Da haka amma ba'a son uban sa ba, Dan da kinka jawo anka kussa sheganta min a media sabida rashin hankalin ki da rashin tunani, yanzu kuma kin kai kara ta wajjen Uwata kan dole sai nak kawo miki shi, me zaki masa Me zaki bashi wanda Allah bai masa ba bai kuma bashi ba tsayin shekarun da yayi ba tare da keba?
Rahinah sai ta rasa amsar da za tabashi, ita kanta ta yi nadamar shigar da kara kotu daga lokacin da ake tantamar halarcin dan su, da ta san abinda hakan zai haifar kenan da ko kusa bata fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login