Showing 33001 words to 36000 words out of 110913 words

Chapter 12 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

face. That magical beauty of her's, wanda cikin kowanne hali ba zai kasa shaidawa ba. Cikin hali na mafarki ko ido biyu ba zai taba mancewa da kamannin Raheenah Omar ba. Waiwaye wani abu ne da ba ya yi sam, amma yau ya yi waiwaye har ba adadi kamar wuyan sa ya karye amma motar ta bace masa. Abu daya ya gane, motar fara ce sol! Kirar kia picanto, kuma yana da tabbaci a kan-kan sa (self-assurance) na ko da ba ta bace masa ba, ba zai bi bayan ta ba. To ya bi ta yace mata me? Ko ya yi mata me?

Ta bar shi da tabo a zuciya, it's a deep wound that can never be healed, watakila har sai ranar da Raheenah Omar ta nemi KOME zuwa auren su da kan ta da bakin ta.

Wanda kuma yake da tabbacin abu ne mai matukar wuya a kafiya da taurin kai irin nata da ya dade da fahimta.
Wannan na nufin ta dawo Nigeria...

Wannan na nufin she's progressing without him, shi da dan sa ta ba su baya, ta manta da su kwata-kwata.

A duk lokacin da ya tuna Raheenah, fada yake da zuciyar sa ta ci gaba da yin tauri, kada ta karaya, kada weakness din ta ya bayyana. Amma yau fa? Raheenah ya gani ba hotonta ba, her humble self bayan wucewar shekaru goma, which is hard for him to control himself domin kuwa ko meeting din da yake gaggawar zuwa har aka yi aka gama bai tsinci komai a ciki ba.

Ta iso gidan Nene wajejen karfe sha daya na rana. Da Ahlan ta soma cin karo suna wasan kwallon kwando da abokan sa a harabar gidan. Ya baro abokan nasa ya zo ya bude mata kofa yana fadin, "Yayata tafi ta kowa, Yayata likitar da babu kamar ta'.
Dariya ta yi suka rankaya zuwa ciki.

Nene na kicin tana girki lokacin da suka shigo. Ta kama mata suka karasa komai, suna aikin Nene ta ke gaya mata Yafendo ba ta jin dadi tun jiya.
"An je asibiti?" Ta tambaya cikin damuwa.
Ba yadda Daddy bai yi ba dazu su tafi asibiti ta ki, wai in mutuwa ce a bar ta ta mutu a cikin dakin ta. Ba ta son zakule-zakule, Raheenah sai ta bar komai ta nufi dakin Yafendo.
A kwance ta same ta tana lazimi ta tsaya daga bakin kofa ta ce, "Yafendo me ya same ki?"
Yafendo ta sauke idanun ta da suka kada sabida zafin zazzabi, ta ce,
"Ya ki 'yar albarka, da ma yanzu zan ce wa Ahlan ya danno min ke a waya, ki zo ki ba ni magani, bana son zuwa asibiti a yi ta jagwalgwala ni".
Ai kuwa sosai Rahinah ta bincike ta, ta kuma ba ta treatment din da ya kamata, domin ta fahimci zazzabin typhoid ke son kamata, har allura ta yi mata wadda ta aika Ahlan ya sayo.
Zuwa la'asar Yafendo ta ji dadin jikin ta sosai, sai suka koma hira, Yafendo ta ce,

"A yi magana cibi ya zama kari, amma bari Baban naki ya shigo".
Raheenah ba ta gane me Yafendo ke nufi ba sai da Daddy ya dawo, ya kuma shigo don ya duba jikin Yafendon, nan ya ga Raheenah ya fadada fara'ar fuskar sa, yana fadin, "Lale-maraba, da manyan otorlaryngologists".

Yafendo ta ce, "Ai gara da ka zo, da ma yanzu zan ce ta latso min kai. Shigo ka zauna, magana za mu yi ta gaskiya ni da ku".
Ambasada ya samu wuri gefen Yafendo ya zauna, ita kuma sai ta fara magana cikin tsananin damuwa.

"Yanzu saboda Allah haka za ku zuba wa Rahinatu ido ta kare rayuwar ta babu aure? Talatin ta ke nema fa rabin sittin ba ashirin ba. Ni ban ce lallai sai ta koma wa Baban Abdullahi ba, tunda wannan shi ta ga zai fishshe ta, amma ta fidda miji ta yi aure ko wane ne tunda ta ki komen mai kaunar ta da gaskiya.
Amma wallahi ku yi a hankali daga ku har ita, kada bokon ku ya kai ku wutar jahannama".

Shi kam Ambasada murmushi kawai yake yi domin a yau din nan ya gano wani muhimmin al'amari, wato Yayar Habibu Nahuche Uncle din Rahinah Alhaji Usman Girei ke aure. Ya gane hakan ne daga hirar da suka yi da Uncle Usman yau a ofishin sa, inda yake gaya masa ai NAHUCHE HOTELS na kanin maidakin sa ne Badiya, lokacin da aka nuno sabon ginin NAHUCHE HOTEL da ya yi launching a jihar Rivers (PortHercourt) a talbijin din da ke cikin ofishin a gaban su lokacin da suke hirar. Shi kuma Ambasada bai gaya wa Uncle komai a kan sanin da ya yi masa yana dalibi ba, ko girman alakar da ke akwai a tsakanin su yanzu. Shi Uncle Usman din da Habibun (wato surakuta). Ya bar wa Allah ikon Sa ya ci gaba da yin hukuncin Sa a kan Rahinah da Habibu Nahuche, don ya gane ba karshen kaddarar su kenan ba, tunda har wannan babbar alaka ta sake bayyana kan ta a tsakanin su.

Da wannan Ambasada Shehu ya samu ya rarrashi tsohuwar sa Yafendo cewa, shi da Uncle Usman za su zauna da Raheenah don jin hakikanin halin da ta ke ciki, kuma za su yi duk mai yiwuwa su ga cewa ba ta kara shekara daya a nan gaba babu aure ba.

"Ah toh ya rage naku kuma, ni dai aikina tunatarwa da tsoratarwa a inda na ga an yi ba daidai ba. Ya rage naku ku yi ta biye wa boko kuna bautar sa ba Allah ba. Ni rayuwata ta yi kyau, na kare ta cikin bautar aure har ya koma ga mahaliccin sa, shi ya sa nake mata kwadayi ita ma ta mutu karkashin igiyoyin aure, don ni rayuwata ta kare, rakawa muke yi, dole kuma mu yi muku tunatarwa a lokacin da ku ka nemi kauce hanya".
Jiki a sanyaye Dr. Rahinah ta koma gidanta sabida irin maganganun da Yafendo ke yi sun karya mata zuciya, sai fada ta ke ita rayuwarta ta kare. Alal hakika ganinta ta ke kamar Daadarta.

Kamar yadda ta yi alkawari, a ranar asabar din karshen wata ta shirya suka kama hanyar Kaduna ita da Sahura don amsa kiran Uncle Usman.

Wajejen azahar suka shiga Kaduna, ba ta samu Anty ba sun wuce Zamfara ita da Zarah da Musaddiq sai Mu'allim da Mubaraq da mai aikin Aunty sai kuma Uncle da kansa kawai a gidan.

Dakin na gidan wanda anan ta saba sauka in ta zo a can ta sauka, amma yau jin duk jikin ta ta ke wani irin dizzy kamar zazzabi na son shigar ta.

Uncle bai kira ta ba sai da ya dawo sallar isha'i.

Ta nutsu a gaban shi tana sauraron abin da zai ce mata, wanda muhimmancin sa ya wuce su tattauna shi a ofis sai ya kira ta har Kaduna.

"Rahinatu yau na kira ki ne a matsayin mahaifin da ya damu da 'yar sa, ina so in san hakikanin shin me ya hana ki aure? Ko kusa kada ki ce min miji ne Allah bai kawo ba, don kuwa ko ta bangarena mutane hudu ne ke son ki ba su dama.

Haka Chief-Medical Director na Nizamiye Dr. Irshad mutumin nan shi ma ya yi tattaki gare ni har ofishi na a kan maganar ki.
Ga wannan Aryan na Minna shi ma har gobe ba wai ya hakura ba ne, lokaci-lokaci yana kira na a kan batun ki.

Ya gaya min kin sanya layin shi ma a divert call sabida ba ki da lokacin sauraron shi. Shi ne nake so in san matsalarki ta hakika, wadda ta sa ki ke gudun masu kaunar ki, ko kuma ki gaya min gaskiya, har gobe Uban dan ki ki ke kwadayin komawa ko me?"
Da sauri Raheenah ta cira kai ta dubi Baffan ta, me ya sa zai yi mata wannan hukuncin? To amma in ta kalubalanci Uncle za ta kalubalanci zahirin abin da ke karkashin zuciyar ta ne? Maza ba sa burge ta ko kadan, sai dan mutanen Nahuche... The one that took away her pride na diya mace. Ya san sirrinta ta san nasa, reality din shi ne ba za ta iya kara hada jiki da wani Da namiji bayan shi ba. Ba za ta iya kara hada rayuwar ta da kowa ba shi ba. Amma kuma ba za ta taba neman sa ba balle ya yi tunanin kome ta ke nema, ko tana so ya dawo mata da dan ta, har ya yi amfani da damar hakan ya gina wata sabuwar mu'amala a tsakanin su.

Yaro Abdallah Allah ya raya shi, ta tabbata duk inda yake yana cikin koshin lafiya, yana samun ilmi mai nagarta kamar na Bajamushen mahaifin sa, watarana da kafafun sa zai neme ta in har ita ta haife shi.

Uncle sai a lokacin ya ankara da cewa, Rahinah kuka ta ke yi tana share hawaye da gefen gyalen ta, kukan da in za a kashe ta ba za ta ce na hakikanin mene ne ba. Ta fi alakanta shi da cewa, kuka ne na tausayin kai, tausayin yadda Habibu ya yi shattering (daidaita) zuciyar ta da rayuwar ta bakidaya, ya hana ta jin dadin achievements din ta na rayuwa ko kadan. Tun rabuwar ta da Habibu Nahuche abu daya za ta ce ya sanya ta farin ciki (zuwan ta Girei) bayan wannan babu abin da ya kara faranta mata zuciya sai kunci maras dalili, har kuwa da kwalinta na Overall Best Otorlaryngologist.

A hankali ta ke kuka, sautin na ratsa zuciya da kwanyar Uncle Usman. Bai san sanda ya ce, "Ki yi hakuri Rahinatu, I don't meant to hurt your feelings.But I must perform my role as a father in tabbatar da cewa a wannan stage din kin shiga gidan aure.

Na ji ba Baban Abdullahi ki ke jira ba, amma akwai abin da ke damun ki a karkashin zuciyar ki wanda nake so in sani yanzu?"
Rahinah ta shiga girgiza kai tana fadin, "Babu komai Uncle, I'm just finding life boring...".

"...Without him ko?" Uncle ya karasa mata yana murmushi.

Za ta iya cewa ta firgita da wannan furucin na Uncle din ta. Me ya sa duk wani makusancin ta yake alakanta damuwar ta da Habibu Nahuche? Me suke gani suke fadar haka? Ita kawai har gobe ba ta ga wanda ya yi mata ba ne, amma ba shi ta ke jira ba.

"Alright Rahinatu, je ki kwanta. Amma na ba ki kwana daya, wato zuwa gobe da daddare, tunda jibi da safe za ku koma, ki zo ki gaya min mijin da ki ka zaba cikin maneman ki, ko in bai wa duk wanda Allah ya tsaga da rabon sa auren ki. Idan ba ki gaya min mijin da ki ka zaba a gobe ba ya tabbata Baban Abdullahi ki ke jira. Wanda na tabbata duk inda yake zuwa yanzu shi ya manta da ke tunda har aka kai DECADE bai neme ki ba.

Bayan ya san inda ki ke, wanda ke nufin bai da sauran bukatar ki a rayuwar shi ke kadai ki ke dakon wahala".
Raheenah kuka ta ke yi ta ce, a hankali.
"Uncle I'm not waiting for him..."

"To in ba shi ki ke jira ba wane ne? Na gaya miki kwana daya na baki ki zo min da abin da ki ka yanke ko in bai wa (Chief Medical Director of Nizamiye) damar fitowa".


A hectic night for Raheenah, ta kasa barci a tsayin daren bakidayan sa, zaben miji a kwana daya ai ba mai yiwuwa ba ne, da ace ta san abin da kiran Uncle na yau ya kunsa kenan da ba ta zo Kaduna ba, da ta yi ta bada uzuri da aiki har sai ya gaji ya manta. Ya aura mata Dr. Irshad ta kai shi ina? Wannan mayen matan idon sa kullum a kan matasan likitoci mata masu tashen kwarewa a ayyukan su, bin mata kamar bunsuru. Ita farin mutum ma ba ya burge ta sam, this gentle handsome black man ya dusashe hasken fatar kowanne namiji a idanun ta.
"Yaa Salamu Sallim!"

Raheenah ta furta a fili, ko dai Habibu na da alaka da cin kurwa ne (Maita)? Ta yadda ya cinye kurwar ta bakidaya bai barta da ko guda daya na extra-space a zuciyar ta da za ta iya sanya wani a muhallinsa ba. Idan har mayen ne da gaske, hakika ta yarda ya gama lashe kurwar ta.

A washegari da safe Aunty Badiya ta kira ta, ta ba ta hakurin rashin samunta a gida ta ce, amma tana bisa hanyar dawowa daga Zamfara ta je kai Junior ne.

"Ni wannan Junior wane ne ne? Babu ranar Allah da za ta fito ta fadi ban ji an ambaci sunan sa a gidan nan ba". Rahinah ta tambayi Aunty Badiya cikin raha.

Murmushi ta yi, ta ce, "Kada ki damu, yau za ki ga Junior Abdallah, dan kanina ne, gwauro mai gudun aure irin ki, da za ku taimaki juna ku auri juna da kun taimaki kan ku, mu ma kun taimaka mana".

Nan da nan Rahinah ta yi fuska, kamar Anty na ganin ta, amma sunan yaron da Aunty Badiya ta ambata ya tsaya mata a rai, yana son tono da tsohuwar soyayyar nata Abdallah din, da ta bi ta sa block ta bibbinne a zuciyar ta.
*******



Sumayyah Abdulkadir

: Kafin Aunty Badiya ta iso Raheenah ta yanke shawarar barin Kaduna don dai ta guje wa haduwar su yau da daddare da Uncle. Bata da amsar da zata bashi.

Ta soma shirya karyar da ya kamata ta yi masa, amma da yake karyar ba dabi'ar ta ba ce, duk wadda ta kama sai ta kubce, ga shi ba ta shirya fuskantar sa a yau ba don ba ta da amsa ga umarnin sa.

Na farko ba za ta iya auren Dr. Irshad ba don halayen sa kwata-kwata ba su yi mata ba. Ba ta son namiji mai son mata, sannan ga shi foreigner ba kasa daya ba, ba kabila daya ba. Ko dan kasa ne ita kam farin mutum ba da ita ba, sannan ita ba Habibu ta ke jira ba, to me ta tanada da za ta gaya wa Uncle?

Ta iso kofar dakin mai aikin Anty ta tadda Sahura suna hira ita da Labo mai aikin Aunty Badiya.

"Sahura taso tafiya za mu yi".

Sahura ta ce, "Tafiya ran ki ya dade? Yanzu Labo ta ce Aunty na hanya fa sun kusa shigowa Kaduna. Na dauka kin ce sai gobe za mu koma har ina shirin shiga Malali (gidansu) in dawo?"
"To na fasa kwanan, tafiya za mu yi, in kuma in barki kya taho a motar kasuwa ne to?"

Da sauri Sahura ta mike tana janyo hijabinta tana fadin, "A'ah uwargijiya ta, ba zan barki ki kama hanya ke kadai ba".

Uncle ya fita bai nan tun safe, ta ji hakan a bakin Mu'allim, don haka ta jefa jakarta a bayan mota ta shiga ta tayar, Sahura ma ta shiga ta yi reverse ta durfafi get, maigadi ya bude musu za su fice sai ga Mubaraq na shigowa.

Ta dan dakata ta sauke glass ya ce, "Aunty unguwa za ku je ne? Mummy sun kusa isowa har da Uncle din mu da Junior, ya dawo daga Belarus kuma anan gidan zai fara sauka ya ga Junior".

Murmushi ta yi, ta ce, "Mubaraq ana kirana da gaggawa a asibiti, so I must go now, na yi wa Daddy text, ka gaya wa Aunty zan kira ta in na isa Abuja. A gaida min Junior da Uncle din mu, wani lokaci za mu hadu ai insha Allah".

Da haka suka yi sallama da Mubaraq ta ja motar da gudu suka hau kwalta. Da ta tabbatar ta yi nisa da Unguwar Sarki, ta hau titin fita garin Kaduna fintinkau, har wata ajiyar zuciyar samun kubuta ta saki.

Daidai lokacin da direban Habibu Mustapha Nahuche, ya karya kan motar su kirar Camero, onedoor, mai dauke da tambarin (NahucheHotels4) mai lambar jihar Lagos wadda a ciki ya dauko Habibu daga filin jirgin saman Kaduna ya shiga gidan Aunty Badiya, da yake suna waya shi da aunty da kamar mintuna biyar da isowar su yana cikin motar yana waya bai kai ga fitowa ba itama ta iso tare da nata direban, wanda ya daukota daga Gusau, Junior a gefen ta, Zarah a gidan gaban motar.

Yana kokarin parking Mu'allim na isko su da gudun gaske sabida jin dadin ganin Uncle Habibu, kusan watanni ukku kenan basu gan shi ba, shi ya bude bangaren (owners side) don Habibun ya fito, tun kafin direban sa ya gama parking, ya kuma karasa ya bude wa mahaifiyar sa tata motar. Yana yi musu oyoyo dukkan su.

Aunty Badiya ta fito tana mika, cikin tsabar gajiya tana, "Wash Allah!". Sabida gajiyar zaman mota tun daga Zamfara har Kaduna.

Mu'allim ya ce, "Welcome Uncle, welcome Junior". Tare da rungumo kyakkyawan dan uwan nasa Abdallah wanke hannu ka taba dan Habibu Nahuche. Wanda ke sanye cikin tsadaddun shirt da wando masu duhun kala samfurin (Dolce&Gabbana).
Junior ya na fitowa ya ce, "Yaya Mu'allim ina kwallona da na ba ka ajiya?"

Hararar sa Daddyn sa ya yi, ya ce, "Kwallo? Kwallo daga zuwan mu za ka fara ko Abdallah?"

"Afuwan Daddy, ka sani in ban yi kwallo ba bana jin dadi, ni so nake ma in na gama jarabawa ka kai ni Manchester in zama dan Manchester United".

Dariya Aunty ta yi, ta ce, "Karewar buga kwallo kenan, wallahi Baban Junior in ba mu yi da gaske ba Junior dan kwallo zai zama".

"Allah ya sauwaqe!".

In ji Habibu cikin takaici, a ran sa kuwa cewa ya yi, "Ranar da Alhuda-hudar uwar shi ta gan shi ya kare da zama dan kwallo da me zan mata tutiya da shi na cewa da na yi, zan fi ta iya kula da shi?

Suna takawa zuwa cikin gidan Mu'allim ke cewa,

"Aunty Rahinah ta tafi, ta ce in ta isa Abuja za ta yi miki waya, an kira ta on emergency a wajen aiki".
Kwakwalwar Habibu ta tsaya cak! Da aiki, kamar yadda ya dakata da tafiyar da yake yi. Sakamakon ambaton sunan Raheenah da Mu'allim ya yi, but he didn't take it further, and he did not show any reaction. Rahinah nawa ce a duniya kuma ba tun yau ba yake jin zancen ita wannan Aunty Raheenar a bakin su. Ya fahimci wata 'yar uwar su ce makusanciya ta bangaren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login