Showing 93001 words to 96000 words out of 110913 words

Chapter 32 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

da dabara ya zame daga rikon da Junior ya yi masa a hankali ya sauka zuwa toilet wanda ke makale a cikin aminity room din.
Motsin sa ne ya tada Rahinah ita ma, ya fito daure da alwallah. Lokacin ta tashi ita ma ta kunna fitilar dakin. Suka dubi juna sai ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya.
"Dauro alwallah mu yi jam'i kawai, sai in wuce gida in yi wanka".
Ta bi umarnin sa, shi ya ja su jam'in suka yi raka'atainil fajr, sannan suka bada faralin asubahi. Suka kara da sallahr nafilah.
Suka yi addu'o'i masu yawa a kan su da zuri'ar su, iyayen su da suka rasu da wadanda ke raye har ma da masoyan su, sannan Habibu ya mike don tafiya gida yin wanka, har ya kai bakin kofa ta ce.
"Ka dauko min wani bedsheet din in canza wannan, da man shafawa ta a kan mudubi na".
"An gama Habeebty, me ku ke son karyawa da shi?"
"Kada ka damu da wannan, Nene da Sahura duka za su kawo".
"Kwalliya kuma fa? Wace iri za'a yi min? Kalli idanun ki, duk sun jeme".
Yar dariya ta yi ta ce, "kai kuwa dan kwalli daya kwal ya tsoka daya a miya aka ce min kwakwalwar sa ta tabu fa! Ai in da akwai abinda yafi jemewa da ramewa duk zan yi su. Allah shine shaida. This the terrible moment of my life bayan na sace shi da kayi%???.
Habibu ya gyada kai ya ce umh. I can relate, sai son dan kawai aka sani, baa san ta ya zaa nuna masa soyayyar ba.
Mu bar wannan zancen. Ka zabo duk kayan da ka ke so in saka a wardrobe dina, ka dauko min turare Yves Saint Laurent a kan mudubi na".
Ya ce, "Da kuma mascara da wet-lips ko? Bakin duk ya bushe"
Dariya ta yi ta ce,
"Anything that will beautify me Habibi".
Sai kuma ta rufe ido ta ce, "kai ma yau ka sako kananan kaya, don in gan ka dan saurayin ka yadda ka ke a Jamus, dan saurayin nan nawa na cikin jirgin 'Boeing' da na rungume cikin rashin sani, wanda ya sanya wa Rahinah Omar, rigar kubuta daga hadarin jirgi".
Dariyar da Habibu ya yi sai da ta fiddo fararen hakoran sa, ya kada kai ya sumbuci Junior da ke barci. Rahinah ta saki baki da kunci tana jiran tata sumbar har da lumshe idanu, sai ta ji shiru, wayam.
Kafin ta ankara ta ji shi ya kai bakin kofa yana fadin,
"Sai na dawo!".

Wai kuma sai ta ji duk babu dadi, Habibu na nufin ya daina kai hannun shi jikin ta kenan ko me? Tun zuwan sa ban da a ofishin likita da ya kankame ta saboda razana, ko sau daya bai kai hannu shi jikin ta ba.
Da gaske yake kenan da ya ce ta jika komai nata ta shanye, he is going for a second wife ko me?
Wani abu da a halin yanzu ta san ko sama da kasa za su hade ba za ta taba yarda ba, (kara auren Habibu) don yanzu ne ta san tana son mijin ta uban dan ta! Tana kuma hakikanin kishin sa.

: HAJ. KALTUME HAJIYAR NAHUCHE

B
a da sanin Habibu ba, Aunty Badiya ta kira Hajiyar Nahuche ta zayyana mata halin da Habibu da Rahinah suka sanya Abdallah. Lokacin sun yi sati guda a asibitin saura sati a sallame su.
"Ki duba ki ga Hajiya, wautar su ta janyo wa karamin yaro lafiyayye irin Abdallah mental instability. A da ina blaming Rahinah ne ita kadai, amma wallahi yanzu na gane Habibu ya fi ta laifi, don shi yake biye mata a matsayin sa na namiji, mai hankali kuma babba sama da ita.
Karfe daya ba ya amo. Don haka zan maida yaron hannu na da zarar an sallame shi daga asibiti in ya so su je su haukata kansu su kadai.
Na yi nadamar sa wa ki ba su yaron, ban san shirmen da suke aikatawa cikin gidan su kenan ba sai da na je na gani da ido na".
Hajiya Kaltume ba ta iya ta ce komai ba, bayan, "Allah ya kyauta. Allah ya ba shi lafiya".
Amma can kasan ranta abun ya dame ta sosai, domin tana tsananin son Abdallah. Abdallah dan lelen Hajiya ne.
Wunin ranar zungur da abun ta wuni yana damun ta a rai, tana ta sake-sake, ba ta yi niyyar zuwa gidan Habibu nan kusa ba, sabida rike girma da dattijantaka irin nata, amma ta yanke shawarar gobe dole ta je ta gano lafiyar Abdallah.
Ga Hajiya Kaltume ba ta iya sa abu a rai ba, in ta sa abu a ran ta ya yi ta damun ta kenan, wannan damuwar ce ta tada hawan jinin ta ba tare da ta sani ba. Wuni ta yi kwance a daki.

Ta shiga bayan gida da asubahi ta daura alwala duk da yadda ta ke jin jiki, ta dawo kenan za ta shiga daki sai kawai ta zame ta fadi bisa kofar dakin ta. Faduwar da sai gadon asibiti aka nufa da ita gari na dan yin haske da taimakon masu aikin ta.

Habibu da Rahinah, wadanda a ranar ma sun yi kwanan zaune ne cikin rayuwa ta %??jeart to heart talk%???, wadda ita suke kwana yi duk dare a gadon asibitin Abdallah, wadda a yanzu ta samar da mashahurin kusanci da aminci ga zukatan su. Hatta sallahr asubahi kullum tare suke yin jamin ta a dakin asibitin, sai gari ya waye ne Habibu ya ke zuwa gida ya yi wanka ya dawo.

To yau ma kamar kullum, dawowar sa daga wanka kenan ya shirya cikin babbar shadda getzner mai hasken sararin samaniya, suka tsinkayi wannan mummunan labari na faduwar Hajiya da kwantar da ita a babban asibitin Zamfara da sanyin safiyar ranar a bakin mai aikin Hajiyar wato Larai, wadda ta dau wayar Hajiya ta kira Habib din, bayan ya dawo asibitin daga wanka da ya je ya yi.
Rahinah dai ta ji Habib yana salati, sai kuma ya mike ya hau neman takalman sa da mukullan motar sa bayan ya sanya hular sa a gicciye, ya dau makullin mota, Abdallah na barci lokacin bai tashi ba.
"Lafiya Habibi?" (Sabon sunan da ya farlantawa Rahinah kiran sa madadin Habibu). Ta tambaya cike da damuwa cikin sanyin murya.
Habibu na takawa zuwa kofa ya ce "Hajiya ce wai babu lafiya, zan wuce yanzu, ki kula da Abdallah please, zan tsaya Kaduna in dauki Maman Musaddik mu wuce Zamfara".
Cikin damuwa sosai ta yi wa Hajiya addu'a, sannan ta yi masa addu'ar sauka lafiya.
Har ya kai bakin kofa zai fita, ta ce, "Habibi".
Sai ya dakata, sannan ya juyo yana duban ta da manyan kyawawan idanun sa.
Ta taka a hankali zuwa gaban sa, ta sanya hannu a wuyan rigar sa tana sanya masa maballan da rudewa tasa bai balle su ba, a hankali Habibu ya dan rufe idon sa jin sanyin hannun Rahinah a wuyan sa, sannan ta makala masa links din hannun rigar shi da shima yake a bude. Ta yi kamar za ta sumbace shi, ko me ta tuna? Sai ta ji kunya, ta fasa. Ta yi maza ta ja da baya.
Murmushi Habib ya yi, sannan ya sa kai ya fita daga dakin, ba tare da ya yi mata abinda take so din ba, ya fice yana fadin.
"Sai na kira Ummu Abdallah, ki zauna da waya a kusa da ke don in ke jin lafiyar ku".

Bayan fitar Habibun, Rahinah kasa komawa ta zauna ta yi har sai da ta ga fitar sa, ta ci gaba da safah da marwah a dakin, tana kallon dan su Abdallah da ke barcin sa peacefully. Idan ta tuna kwakwalwar Abdallah yanzu ba daidai ta ke ba, duk sai ta ji ta daina jin dadin komai na duniya.
A wani gefen tana jajanta rashin lafiyar Kakar sa don ma ba ta san musabbabin sa ba. Bata san cewa a kan Abdallah bane Hajiya ta fadi. Hajiya Kaltume bata aje kaunar Abdallah anan kusa ba sabida shakuwar da ke tsakanin su wadda ta samo asali tun yana yaro. Ta yi addu'ar ko me yake damun Hajiyar Allah ya ba ta da sauki.
Da Abdallah ya tashi ta yi masa brush ta yi masa wanka, sannan ta sa shi ya yi sallah. Sai ga sallamar Sahura ta kawo musu karin kumallo. Ba jimawa Nene da Ahlan ma suka zo, sai dakin ya yi albarka, nan ta ke gaya musu maganar rashin lafiyar Hajiyar Nahuche.
Nene da Sahura duk suka yi wa Hajiya addu'a, nan suka taya Rahinah wuni a asibitin kasancewar karshen mako ne.
******







ZAMFARA GALMA UWAR RUFI, KO BAKU SON MUTUM BAKU HWADI!

S
un isa garin su na haihuwa wato Zamfara shi da Badiya dukkan su ba cikin nutsuwa ba. Aunty Badiya ta yi nadamar gaya wa Hajiya rashin lafiyar Abdallah, ta manta shaf da halin ta na sanya abu a rai fiye da kima. Habibu ma ta sha fada a wurin shi kamar shine wan ita kanwar. Da ta gaya masa tana tsammanin abinda ya tada ciwon Hajiya kenan.
Sun samu an ba ta gado a Aminity 'yan aikinta suna ta kula da ita. Amma ganin halin da Hajiya ke ciki ya rikita Habibu, tsufa ne ya hadu da dadadden ciwo da damuwa, sai ya ce da Badiya zai dauke Hajiya ne kawai zuwa Jamus cikin satin nan don ta samu kulawa yadda ya kamata. Ya fi yarda da hospitalization din su fiye da na ko'ina.
Tun a lokacin ya soma tuntubar likitocin ta akan shawarar da ya yanke, duk sun ce ya bar ta zasu iya shawo kan matsalolin ta amma ina! Habibu gani ya ke basu iya komi ba, ba ya hada lamarin Hajiya da komai, a take ya kuma soma shirin tafiyar tasu ta yanar gizo, washegari suka tafi da Hajiya daga Zamfara don shigar da neman visa.
A hanya suke shawarar wadanda ya kamata su tafi da Hajiyar asibiti cewa bai kamata su tafi dukkan su ba, dole daya ya tsaya sabida Abdallah da ba'a sallama ba. Habibu ya ce shi zai zauna tare da Abdallah har a sallame shi, in ya so sai ya biyo bayan su daga baya, Badiya kuma ta ce zai fi kyau su tafi har da Rahinah tunda likita ce, kuma a can ta yi karatun ta ta iya harshen German, she will have more rapport da likitocin can tunda ita Badiyan ba ta iya Jamusanci ba, sannan again Rahinah can play the role of a support doctor ga Hajiya, za ta taimaka dai ta kowanne bangare.
(Badiya ta kawo wannan shawarar ne don tana son dinke 'yar barakar da ke tsakanin Hajiya da Rahinah). Don ta samar da 'yar shakuwa da fahimatar juna tsakanin su ko yaya ne.
Ba bata lokaci ya amince da shawarar Yayar tasa, don haka suka bar Abdallah tare da Nene, suka dauki Rahinah a asibiti suka wuce %?djerman Consulate%??? har da ita wanda ke a garin Lagos don neman %?fjospital Visa%???.
Masu abu da abun su, babu bata lokaci cikin sati aka yi musu komai da taimakon Ambassada Shehu, likita ya ki sallamar Abdallah ya ce sai ya gama karbar treatment.
Sahura ce ta hada wa Rahinah kayan da ta ware don tafiya da su Germany. Ta sanya a ran ta in ta samu dama kuma Hajiya ta samu lafiya za ta nemi Aunty Laura a Germany don kawai ta gaishe ta, ko babu komai ita ce silar duk abubuwan da suka faru dasu a Jamus, tsakanin ta da Habibu Nahuche har zuwa inda yau ke motsi.
Tunda ita tayi uwa ta yi makarbiya ta kulla auren su. Auren mai tsohon tarihi da dabaibayin zukata iri-iri. Har aka samu Dan da silar zuwan sa duniya ne ya yi connecting komai.... ta wani bangaren, ba ta san dalili ba; a yau sai ta samu kan ta tana mai gode wa Aunty Laura, tunda ita ta yi silar dukkan kaddarorin su; masu dadi da marassa dadi.
Laura ta cancanci abinda yafi godiya yau daga gare ta in akwai, tunda ta mallaka mata Baban Abdallah (Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche).

******
JAMUS
S
ai da ya gama musu komai a filin jirgin saman Murtala Mohamed dake Lagos ya kuma ga tashin su, sannan suka koma gida shi da P.A din sa Atiku, yana tafe yana waiwayen jirgin da ya daga da Yayar sa, Mahaifiyar sa da Matar sa; mata ukun da bai da ya su a duk fadin duniya, wadanda su ne farin cikin sa, kuma komai na sa.
Habib Nahuche, sai ya ji tamkar shi kadai ya rage yanzu a fadin duniya in ka dauke dan sa Abdallah da ke gadon asibiti. Nene Balki na asibiti wajen sa ita da Sahura, sai dare zai koma musu.

Dr. Rahinah Omar a Jamus a karo na biyu. Wannan karon ba a daliba ba a matsayin mai jinya. Ita ta rinka jagorantar su a komai har suka sauka a masaukin su. Asibitin da aka yi wa Hajiya booking yana 'Bonn City' wato St. Josef Hospital, Bonn. Rahinah ce tsaye a kan komai har aka ba su daki, cikin kwanaki uku da zuwan su Hajiya ta ga duk likitocin da ya kamata ta gani. Babu irin binciken da basu yi mata ba (complete check up) na duka ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????abinda ya danganci lafiyar ta.
Kuma a binciken su sun gano sugar (diabet) ma a jikin ta, sannan ciwon kafar Hajiya na da alaka da hawan jinin ta, treatment na kwararru kawai ake ba ta iri-iri.
Tun zuwan su asibiti Rahinah ta ajiye komai ta ke hidima da Hajiya, ita ke kula da komai nata, wanka take mata da tawul kullum, kula da cin abincin ta irin na masu hawan jini wanda asibitin ne ke ba ta da kan sa, kula da shan maganin ta a kan lokaci da communicating da likitoci, Habibu sai dai kawai Badiya ta yi masa waya ta ba shi labarin abin da ake ciki da irin kokarin da Rahinah ke yi. Tace ita zaman kashe zani take yi kawai. Rahinah ce ke jinyar.
Ita kanta Hajiya da ta ke a kwance ta san Rahinah a tsaye ta ke tsayin daka a kan lafiyar ta, ta baro nata yaron wanda shi ma kulawa yake bukata amma kacokam hankalin ta yana kan Hajiya. Duk abinda ya shafi lafiyar Hajiyar da ita likitocin ke tattaunawa.
Wannan kokari na zuciya daya da kulawa kamar ita Hajiya ta haifa ba Habibu ba, ya wanke Rahinah a zuciyar Hajiya Kaltume, ta kuma fahimci abubuwa masu yawa a tare da Rahinah da a baya ta kasa fahimta, wato dai ta gane Rahinah mace ce mai saukin kai da dadin mu'amala akasin yadda ta ke kallon ta kuma dai tana son Habibullahin ta, ta sani in har da a ce ba ta son Habib din, ba za ta yi wannan tsayuwar dakan a kan ta ba.
Balle kuma tana jin su cikin dare suna waya, wata irin waya da du kwakwar ka ba zaka gane me suke fada ba, a zaton Rahinah Hajiyar na barci ne, lokacin da Habib ke mata (midnight call), amma duk da kuskus din na su ta kan fahimci wasu daga kalaman Rahinan ga mijin nata Habibu a waya, duk na ban hakuri ne da tausasawa a kan kewar su da watakila yake cewa Rahinar yana yi, da kuma tambayar yaushe za ta dawo da Abdallah ke ta yi masa.
A kwana goma da zuwan su Jamus Hajiya ta fara samun sauki sosai, tana zama sosai a yi hira da ita, ana i-gobe za su cika sati biyu a Jamus Badiyya ta ce, Habibu ya yi mata booking za ta koma gida, sabida yara da kuma aikin ta, don excuse din sati biyu ta dauka dama.
Ta ce "ka ga zaman nawa bai da wani amfani tunda Dr. Rahinah ke yin komai, ni 'yar taya su hira ce kawai. Asibitin kuma sun ce sai Hajiya ta yi sati uku za su sallame ta".
Don haka Habib ya yi ma Badiya shiri ta dawo Kaduna.
Badiya ta taho a washegari, shi kuma Habib ya yi booking din tahowa domin an sallami Abdallah daga gadon asibiti, Nene ta tafi da shi gidan ta wato gidan Ambassada.
Ko a daren ranar sun yi waya har tsakar dare ita da shi, amma bai gaya mata cewa yana (on transit) ba ne ma lokacin a kasar Neitherlands, ya dai gaya mata an sallami Abdallah yana gun Nene Balki.
Ta ko'ina yanzu Raheenah ta wanke kan ta a dan tsukin a wajen Hajiya Kaltume, ta saki ran ta da Rahinah, ta cire wa kan ta shakku a kan surukar tata, ta yarda ita ce daidai da rayuwar Habibullahin ta, wadda ya ke so saboda Allah, take kuma auren sa ba don wani abu da ya mallaka ba, in ka ji su suna hira da rigima a kan shan magani itada Hajiyar Nahuche kamar Yaya da kanwar ta.
A yanzu kam Hajiyar ta amince za ta iya baiwa Rahinah amanar da a baya ta ke ganin ba za ta bata ba, wato zamowar ta abokiyar sirrin da za su kashe su rufe a kan komai na Habibu tare, ba zancen surukuta ko shakku a tsakani.
Ta maida Rahinah 'yar cikin ta, ba maraba da Habib da Badiyya.
******
BAKON BAZATA
"
Daure ki sha Hajiya, daga yau zan roke su su rage yawan kwayoyin nan, tunda dai ba kya son hadiyar su, kullum sai mun fafata har waje ana jiyo mu akan shan maganin nan".
"Ke ko Rahinah shan maganin bature ai sai dole, dolen ma sai dole, amma ina ya ga dadi? Nafi gane in yi jikon sassake tunda alhmadllh babu cutar da bamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login