Showing 6001 words to 9000 words out of 110913 words

Chapter 3 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ya takura musu don dai basu da yadda zasu yi da ita ne.

Tunda suka shigo motar take kuka, kuka tukuru tamkar zata fidda rayuwarta. Wannan wace irin rayuwa ce? Daga ganin mutum bata san komai a kan shi ba, don kawai musulmi ne kuma ya zo daga kasarta sai a aura mata? Kawai don an ga bata da gata? Ita bata ce lallai sai ta zauna da Dr. Laura ba ta so ta koma hostel kawai tunda ko ta koma Najeriya babu Dada wajen wa zata je?

Tunda ta taso bata san kowa nata ba sai Dada, daga dangin uwa har na uba, ta rayu karkashin kulawar tsohuwa Dada a shekarun rayuwarta bakidaya. Yau ga rayuwar da rashin gatan Dada ya jefa ta a ciki; auren mutumin da bata sani ba, bata san asalin sa ba, bata san halayen sa ba, bata san manufar sa a kanta ba. Just haduwar kan hanya wadda bazata iya bada shaidar komai a kan sa ba, wannan taimako nasa ya zame mata masifa, duk yadda aka yi yana da target dinsa a kanta, amma in ba haka ba ta yaya daga ganin ta bai san asalin ta ba zai zabe ta ta zama matar auren sa?

Ko da take goyon kaka, tana da hankalin ta. Bazata taba barin shi ya gurbata mata rayuwa ba.

Ta soma yi mishi kallon mutumin kirki tun daga haduwar su ta farko, amma ashe ba haka bane yana da mission dinsa da yake son cikawa a kanta.

Zata bashi mamaki, zata nuna mishi ka bar raina allura....karfe ce, komai kankantar ta.

Wannan take hakkin dan adam ne, a aure shi babu cikakkiyar yarda da amincewar sa.

Tana da damar da zata kai su ga hukuma daga su har anty Laura, amma bazata yi hakan ba, sabida ko yaya dukkan su sun taimaketa a Jamus. Kuma Dr. Sayed yayi iya kokarin sa wajen convincing din ta.

Amma ta gama kudurta mafita, mafitar da zata nemawa kanta ta kwatarwa kanta 'yanci.....

"Bazata taba bari ya samu access din keta mata haddi ba, in ma kwadayin hakan ne yasa shi auren ta da gaggawa haka. Har sai ya gaji ya bata 'yancin ta na dalibtaka wanda shine abinda ya kawo ta Jamus ba auren sa ba".
*****

*Na Huce!* IS NOT FOR FREE. IT'S 1000 VIA ;

3094856450
SUMAYYAH KABARA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA 07030137870
: SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870


*NA HUCE* (DAGA FUSHI NA....)

PAID BOOK


Kugin karshe da motar tayi, a kofar flat din Habibu ne, wanda ke shiyyar Klettenberg. Shi ya bude mata kofa da kan sa ya kuma rungumota barin jikin sa. Ji tayi kamar ya dala mata wuta, amma haka ta daure ta cije ta shiga gidan tana hawaye.

Dr. Sayed ya biyo bayansu har falon gidan, ya zauna yayi musu nasiha sosai, yace su taru su rufawa juna asiri su zauna lafiya, duk wata matsala da suke da ita su sameshi, shi uba ne a garesu, kuma Raheenah ta kwantar da hankalin ta Habib mai son ta ne, bai aureta da wata manufa ba sai bisa son cika sunnar Ma'aiki SAW.

Da wannan yayi musu doguwar addua'a sannan ya tafi, bayan Habib ya taka masa ya rufe gidan ya dawo.

A inda ya barta anan ya sameta, amma ta yaye lullubin fuskarta tana yi masa wani irin kallo, kallo irin na kamar ka ga makiyin ka, koko abunda zai cutar da kai. Da gaske zuciyar ta da dan kankanin tunanin ta basu bashi kowanne matsayi ba, face na mai mugun nufi a kanta.

Ya zauna dab da ita, har tana iya jin kamshin turarensa Carolina Herrera (Men). Da sauri ta matsa ta ja baya, sannan ta nuna shi da dan yatsa ta soma magana cikin hawaye.

"Allah ya fi ka! Duk abinda kake nufi da ni Allah ya fi ka".

Cikin madaukakin mamaki yake kallon ta, baki sake, ya ce
"Rahinah are you alright?"
"A'a a haukace nake, kawai daga ganin mace akan hanya baka san ko wcece ba sai kasa power ka aureta? Sabida ka fahimci bani da gata ko? Shiyasa ban cancanci ka nemi soyayyata ba, ka nemi dangi na ka aure ni cikin mutunci, ka taimaka min inyi abinda ya kawo ni sai kawai kayi min kutse a rayuwa ka raba ni da burika na?

Ni na ce maka na zo Jamus don in yi aure ne?"

Habib yayi mata wani irin kallo, domin ji yayi ya muzanta a gaban ta, yarinya tamkar mai gani har hanji! Da gaske yasa kaimi ya aureta ne don biyan bukatar ruhin sa da gangar jikin sa, bai taba fadawa a wani abu wai soyayya ba, kallon ta yake da jin ta as waste of time, burin sa da lokutansa na tunanin maida kobo ya koma dari ne, yana da manyan burika da suka zarce soyayya. In fact, bai dauki mace a bakin komai ba banda abar hutawar gangar jikin mijin auren ta.

Amma ita wannan inda bata bullo masa ta haka ba, da bata nuna ta san ba son ta yake ba, bayan target dinsa na auren ta yanada burin tallafar rayuwar ta da maraicin ta, tare da cigaba da zama da ita har karshen rayuwar sa.

Amma tunda ta nan ta bullo, ya san ta yadda zai yi maganin ta.
Daga sanda ya mike ya durfafe ta, da sanda ta soma ja da baya cikin tsoro, cikin abinda bai gaza sakan bane idanuwan su suka hadu, ta hango wani boyayyen al'amari cikin brown kwayan idanun sa, al'amarin da har gobe ta kasa mantawa, shekaru bakwai kenan; Babu soyayya a cikin a cikin kwayar idon Habibu ko kankani face lustfuldesire wanda ya kara darsa mata tsanar sa. Ta kuma kara yarda da cewa manufarsa kenan ta auren ta.
Da farko yayi kokarin lallashin ta, amma sai ya gane zai bata lokacin sa ne kawai, ga rashin kunya da tsiwa kala-kala na fita nau'i-nau'i daga bakin ta, sai ya ce.
"Raheenah bari in yi maganin ki.....".

Duk wani kokari na kwatar kai da neman ceto Raheenah Omar ta yi, kafin ta gane all her effort was futile (kokarin ta na banza ne), tamkar Habib Nahuche ya jima yana jiran wannan ranar, ya gama shirya mata. Abubuwanda suka wakana a tsayin daren bakidayan sa ba masu dadin fada bane. Saboda al'amarin baida maraba da 'rape' banda igiyar aure data suturta shi.
Kuma wannan ne abinda ya gina matsanancin tsoro da kiyayyar sa a zuciyar ta. She hates him with passion from their first night. Ta alkawartawa ranta koda jan ciki sai ta bar Jamus, gara ta dawo Adamawa ko bara ce ta yi ta ci da kanta, da dai ta zauna da wannan mugun mutumin mai halin dabbobi.

Tamkar ya san tunanin ta, washegari da zai fita makaranta saida ya kulle ta ta waje.
*****



Ba shi ya dawo ba sai yamma lis, tunda ya san ya bar mata komai da zata bukata. Amma ga mamakin sa a inda ya fita ya barta anan ya dawo ya sameta, a kwance akan marbles kamar kayan wanki, baya tunanin ko sallah ta tashi ta yi, balle akai ga wanka.
"And your name is bride?"
Ya tambayeta cikin zolaya.
Hararar data ke masa tamkar idanunta zasu fado, wadanda suka kada suka yi jajazur kamar an gumbuda musu barkono. Da za'a bata dama zata iya kashe shi ta hanyar rataya, sabida tsanar data yi masa.

Ya tsugunna a gabanta ya ajiye mata ledar abincin McDonalds da lemun power horse mai sanyi, yana wani makalallen murmushi na tura haushi yace "ki ci ki sha, ko kya wartsake kinji amarya ta! We're going for the second phase.,.... what is the marriage meant for? I don't believe in what is called love. Ban sani ba ko in kika haifa min 'ya'ya..... ""ta Allah ba taka ba..kada Allah ya nuna min wannan ranar""ko?" Ya tambaya yana kara hade filin dake tsakanin su...... kuma wannan karon ma kokarin ta da bijirewar ta, bai kwace ta da komai ba.

"You goddam lunatic! I hate you.....kuma insha Allahu sai Allah ya saka mini, ta hanyar da baka taba zato ba. Abinda kayimin sai an wa 'yar ka, in baka haifa ba kanwar ka, in baka da ita UWARKA!"

Bai san sanda ya daga hannu ya zabga mata mari ba, marin da Raheenah ta tabbatar taga wuta a cikin sa. Kafin ya kama hannun ya rike cikin nadama! Wai shine da dukan mace.....macen ma mai amsa sunan matar sa. Amma abu na karshe da bazai iya dauka ba shine raini, don abinda take gani a matsayin babban laifi daga gare shi shi ko kusa bai kalle shi hakan ba. A tunanin sa ana aure ne for sex only, kamar yadda ake cin abinci kullum. Baya jin a duniya zai so wata mace bayan mahaifiyar sa. Kuma baya comparing din ta da sauran mata. Talkless of Rahinah ta ambace ta ta zaga.

"Duk rainin ki ya tsaya a tsakanin ni da ke, kada ki sake ki hada da uwata".

Ya fada yana sake rugumota jikin sa ba tareda tausayi ba ya sake maimaita laifinsa, har da cewa "ai sadaki na biya, ki jawomin ayar da tayi umarni da soyayya, aure Ubangiji yayi umarni mu yi ba soyayya ba".

This man is unbelievable ga tunanin Raheenah bata san a rukunin mutanen da zata sanya shi ba, gashi dan boko mai matakin master, amma jakancin sa akan diya mace ko gardin kauye bazai yi ba. She hates him again and again for his wickedness.
Tunanin ta gabadaya ya koma kan how to escape from this abusive marriage.

Amma har kwanaki suka nausa zuwa biyar, bata samu wannan damar ba.

Yayin da Habib ya dukufa ga morar sadakin sa, don bai taba tunanin abinda yake yi din ba daidai bane, ko zata iya tafiya ta barshi tunda bata da kowa.

(Akwai maza da yawa irin Habibu Nahuche, wadanda baza'a ce rashin ilmi ya hana su son matan su ba, ko kasancewa masu nuna soyayya da tarairaya koda fake ce. Suna aure ne for their own pleasure. Ita mace kuwa 'yar son lallashi ce da soyayya kuma har abada in baka iya tafiyar da ita ba, hankalin ta bazai taba nutsuwa da kai ba. Ita Rahinatu ma kallon Habibu take as rapist don bata yarda miji zai iya yiwa matar sa izayar da yake yi mata ba).

A duka kwanakin nan bata ci bata sha, sai taji hanjin cikin ta na neman tsinkewa ne take shan ruwan bunu ko ta sha madarar kwali, wanka kuwa da sabulu rabon ta dashi har ta manta, iyakaci ta yi wankan sallah, watakila in yaji tana tsami, a yadda yake dan gayun nan mai son wanka da kamshi zai daina rabar ta.

Amma gogan nata ko a jikin sa, wani sabon abu ma ya tsiro da shi; fesa mata turaren sa 'Carolina Herrera' a duk sanda zai kusance ta, tana kuka tana tsine masa, amman kaman tana kara zuga shi.

Tsahon kwanaki shida ya tabbatar shi kansa ya samu lafiya daga masifar dake damun shi akan Raheenah, zamu iya cewa kanwa ce ta kar tsami kwannafi ya kwanta. Ya soma jin tausayin ta, kuma ya rage takura mata.
*****




*RANAR KWANA BAKWAI*

Ranar da auren su ya cika kwana bakwai ne komai ya faru, haduwar da rabuwar masu kama da blink of an eye (kiftawar ido). Gabadaya haduwar sa da saninsa da Raheenah Omar, zuwa auren su da zaman auren watanni uku ne cif har kwanaki bakwai na aure data yi a gidan sa.

A safiyar ranar tun asubah ta faki idon sa ta dauke masa mukullai, neman duniya yayi musu bai gan su ba, kuma baya so ta gane abinda yake nema kenan, don haka yaja bakin sa yayi shiru, kada ta gane bai rufeta ba tayi tunanin guduwa, shi kuma daga ranar ya fara nadama, ya kuma alkawartawa ransa bazai kara kusantar ta ba sai bisa amincewar ta.

Sannan zai yi kokari ya koma yadda duk take son sa, wato namiji dan soyayya, mara gaggawa, loving, caring, romantic. Mai bin komai a sannu. Sex will be his last priority a rayuwar auren su. In ta kama zai je makaranta ya shiga aji ya zauna a koya masa yadda zai koyi zama da mata ne zai yi hakan, sakamakon wani irin pleasant feeling (so na hakika) tamkar maganadisu mai jan zuciya da ruhi da ya ji yana shigarsa a hankali akan RAHINAH OMAR daga daren jiya zuwa wayewar garin yau.

Wayewar garin data cika kwanaki bakwai da auren su.
Bata taba yarda sun kwana gado daya ba, in suka gama damben su yayi galaba akanta anan kasan marbles da ya barta bata canza matsugunni, sai in ya fita ne taji yunwa zata kasheta take yunkurawa ta isa ga firji ta sha madara ta koma ta kwanta. Haka zata wuni kuka idan ta tuno karatun ta, da abokan karatun ta da Dadar ta. Yau ta dauke masa mukullai ne da niyyar zata gudu, kuma zata bar Jamus gabadaya.

Bai nuna mata bai ga mukulli ba, tana daga kwance inda take ya sunkuya ya ajiye mata kofin tea. Sai tiriri yake. Ta runtse ido hawaye na bulbula domin ko fuskarsa bata son gani. Kamshin turarensa duk ya mamaye ta. "Kiyi hakuri sweetie, i promised to become a changed person, if you give me another chance (nayi alkawarin canzawa, in har zaki bani dama). Yanzu dai na makara, inna dawo zamu tattauna sosai".

"Allah yasa kafin ka dawo ka tadda gawata!"

Ta fada cikin rishin kuka. Tana mai addu'ar Allah ya dauki ranta ta huta kafin Habibu ya dawo.

Murmushi Habib yayi, sannan ya sunkuya ya sumbaci bakin ta lightly. Wani abu da bai taba wanzuwa tsakanin su ba (sumba). Ta tattaro miyau ta tofa masa a fuska. Maimakon ta ga ransa ya baci ko ya falleta da mari kamar yadda ya saba, sai taga yasa dan yatsa ya lakato miyan ya kai bakin sa ya lashe.

Ya kuma kasheta da murmushi yace "i know that i offend you, and it's intentional as you expect, but i promised to become new HABEEB (masoyi) har sai kin koreni sabida soyayya.
Ki bani thirty minutes yanzu zan dawo we will discuss everything, in nace EVERYTHING ina nufin har ASALI NA da naki".

Maimakon maganganun sa su farantawa Raheena, sai ma suka kara shafa masa shuni a idanun ta. Ba abinda zai ce ta yarda yana kaunar ta. Ya baro gini tun ran zane....zuciyar ta ta riga ta mace a tsanar sa.

Abinda kuma zai farfado da matacciyar zuciyar nan ba kankani bane. Ya riga ya raunata zuciyar ya yi mata illah. Tsanar data yi masa ba 'yar kadan bace. Kuma zata nuna masa ita ba yar tsana bace duk rashin gatanta ta san 'yancin kanta.

Haka ya fita yana waiwayen ta, ita kam ko ido bata sake dagawa ta dube shi ba. Mintina goma sha biyar ta bayar bayan fitar sa, ta mike tasa jallabiyya, tasa jilbab, sannan ta tattara duk wasu muhimman takardun ta da passport dinta ta fice cikin zafin nama.
*****

"Divorce ( *Scheidung* ) a kasar Germany: ba karamin abu bane. Domin tunda ke ke son sakin, sai kin dauki lawyer. Sannan zaki biya kusa '???3,000 kudin kotu dana daukar lawyer. Ki rubuta application for divorce (divorce petition) in kin tabbatar kina da gamsassun hujjoji. Sannan ne za'a shiga family court a gudanar da sakin under German-law. Tunda dukkkannin ku kuna kasar Jamus. The divorce will run in accordance with German law regardless of your nationality (sakin zai kasance ne karkashin kundin tsarin shari'ar Jamus batare da la'akari da kasancewar ku ba 'yan kasa ba).

However, also in this case, sai kin jira end of the one-year-separation before starting the divorce procedure".

Ambasadan kasar Najeriya a kasar Jamus yayi mata bayani cikin nutsuwa. Da gani yarinyar is desperate, sakin kawai take so ba tareda ta san aikin dake gaban ta ba, "tun farko me ya kai ki amincewa da auren sa in kin san ba kya son sa?" Ya tambaya calmly, Rahina ta sanya gefen jilbaab dinta ta goge gumi da hawaye, "ranka ya dade basu bani damata ba, uwardakina ta kasar nan ita tayi min fin karfi, hujjarta kakata tace kowa aka samu a aurar dani gareshi. Ni kuma ba na son sa, ban san shi ba, ban san komai a kan shi ba".

Ambasasada Shehu yace "zaki iya gaya min hujjojin ki na rashin son zaman aure? Idan har akwai ci da sha da suttura?"

Rahinah ta rasa inda zata sa kanta, da kunya ta fadi hujjojin ta, balle a gaban alkali. Me take so daga gareshi banda SOYAYYAH??? Asalin sa, da sanin dalilin sa na auren ta?"

Kuma a yau ya ce, tayi hakuri in ya dawo zasu tattauna komai and he promised to become a changed person irin yadda duk take son sa. What else take so daga gareshi bayan wannan? Ya riga ya dasa kiyayyarsa a zuciyarta ne ta yadda babu wani repenting da zai yi ya wanke dattin laifukan da yayi mata.

Ambasada ya ga shirun ta yayi yawa, yace "bazan iya tsaya miki ba, har sai na san hujjojin ki masu karfi ne, sabida Jamus ba Najeriya bace, karshe a kare da cin ki tara. A yanzu haka ma in zai sake ki sai kin biya shi kudi masu yawa, do you have any source of income bayan alawus din ki na cin abinci?"

Rahinah ta kara rudewa, tace "ka taimakeni yadda Allah ya taimake ka, banida komai da zan biya shi, bani da kowa da zai kwatar min 'yanci. Shin rashin so bai zama hujjah ba? Bana son sa ne, kuma bazan taba son sa ba".

Ambasada Shehu yayi murmushi, ya gama gane wauta da tarin kuruciya a tare da ita, banda haka auren, ai shine rufin asirin ta. Kowanne iri ne kuwa. Don haka yace.

"'Ya ta, zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login