Showing 54001 words to 57000 words out of 110913 words

Chapter 19 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ma'aikaciya ce da za a iya nema a kowanne lokaci, amma ta kulle kanta ta kulle wayoyi. Ta manta tana zuwa aiki kullum. Halin da ta ke ciki ya danne komai. Ita kadai ta ke suffering a zuciya da ruhi, ba tare da Habibu Nahuce ya san tana yi ba.

A lokacin shi da Abdallah suna gidan sa dake Ikoyi. Har ya fara registration din makarantar Abdallah.

Daga wannan ranar, daga wannan lokacin daga Habibu har Rahinah babu wanda ya kara nutsuwa, babu wanda ya kara samun sukunin zuciyar sa, (they are internally suffering with concurrent love, hatred, and emotional torture). Habibu ya shiga tafka shirme a wajen aiki bisa rashin sani, haka a takardu muhimmai sai ya yi ta kuskure ana ankarar da shi.
Wannan ne yasa PA din sa na Lagos, Rasak, wanda bayerabe ne ya karbi komai daga hannun sa ya dauki hutu na tsayin sati uku.
Maimakon ya zauna a gidan sa na Ikoyi bayan ya kai yaron makaranta sai ya tafi NAHUCHE HOTEL, LAGOS, ya kama (Excutive VIP room). Ita kuma daga baya Dr. Irshad ya ba tahutudon ta gaya masa bazata iya aiki ba awannan dan tsakanin tunda ta san rayukan mutane ne hannun ta a NIZAMIYE kasancewar shi da kan sa yafahimci ba daidai ta ke ba a satin nan. Ta gaya masa tana neman wanda zai shige mata gaba on a legal issue zata maka wani kotu!
Dr. Irshad ya dauka wasa take yi sai ranar da ta kira shi a waya ta roki alfarmar ya zo ya dauke ta a 'Federal High Court%??? baza ta iya tuki ba, tana fama da ciwon kan barin kai guda (migraine).
Dr. Irshad ya dauko ta daga kotu zuwa asibiti ba tare da ya san abinda ta je ta yi ba, a hanyar su ta dawowa Rahinah tace ta bashi dama idan har yanzu yana son auren ta ya turo wajen iyayen ta.
Dr. Irshad dai ya san Dr. Rahina ba daidai take ba a satin gabadaya, wannan amsawar da ta yi masa ma ta farat daya bai gane mata ba, tana magana idon ta a rufe kamar mai ciwon baki, butkoma dai menene matsalar ta he will not miss this golden chance (wannan kyakkyawar damar data bashi wadda ya dade yana jira), yace insha Allah cikin satin nan zai turo magabatan sa daga Yemen.

Ita kadai cikin gida kamar sabon kamu, gabadaya ta birkice. Gashi dai ta ce da Irshad ya turo, amma duk da haka ta kasa nutsuwa, Habibu Nahuche ya kusa haukatata da mere kalaman bakin sa, wadanda basu fi kalma biyu ba.
%??muguwa-kawai-azzaluma!%???, sune kalaman da ke haunting din ta.
Gashi ta baro Sahura a Kaduna. Da ta ga za ta mutu ita kadai a cikin gida don ko abinci ba ta iya girkawa sai dai ta sha madara, da dan abin da yake cikin firjin gefen gadon ta, sai ta tattara inata-inata ta nufi gidan su Nene.
Don ma kada kadaici ya sake tambayar ta wane ne Habibu Nahuche? Ko ya tuna mata kalaman bakin sa. Sai ta ki sauka a dakin ta na gidan kamar yadda ta saba, ta sauka a dakin Yafendo. Ta tabbata duk runtsi tsohuwa Yafendo ba za ta barta da damuwa da kadaici ba.
Ai kuwa Yafendo ta shiga hidima da kawar ta likita Rahin (yadda ta ke kiran ta) ta tashi musamman ta yi mata burabuskon shinkafa da miyar taushe tana cewa,
"Mutumiyar Rama, ko a jika rama ne?"
Ta yi dan murmushi ta ce, "Komai ma na samu zan ci Yafendo, kwana na hudu kenan ban ci dafaffen abinci ba".
Yafendo ta kama haba, ta ce.
"Kwana hudu? To a dalilin me? Haba, ni fa na ga duk kin yi wani zuru-zuru, firgai-firgai da ke".
Ba ta bai wa Yafendo amsa ba ta mike tana rage nauyin kayan jikin ta. Laffaya koriya sharr da ta ji adon pinkflowers. Amma da zata iya da ta gayawa Yafendo cewa; A dalilin HABEEBUN su, a dalilin dan mutanen NAHUCHE, ba zuru-zuru firgai-firgai ba har dan karamin hauka ta tabbata ta san ya same ta a tsayin satin nan bakidayan sa, tunda kuwa an dakatar da ita daga ayyukan ta na fidar kunne, hanci da makogaro wanda tafi kowa kwarewa a kai a garin Abuja don shugaban ta ya gane ta fara zautuwa.

*******
*SUMAYYAH ABDULKADIR* 07030137870



*NA HUCE*



*ZAMFARA*

Dr. Badiya ta isa Zamfara yamma lis, domin su hadu ita da Hajiya da sauran %??ian uwa su shirya yadda tarewar Rahinah za ta kasance. Ta sha kiran Habibu a waya tun daga ranar da aka daura aure, ba don ta yi masa albishir din komai ba sai don ta ji lafiyar sa. Duk da ta san fushi ya ke da su daga ita har Daddyn Musaddiq tunda su ne silar komai, silar sake kulla masa Rahinah Omar a matsayin matar sa, amma duk sanda ta kira sai ta samu duka wayoyin sa a kashe suke.

A karshe ta kira PA din sa na Lagos wato Mr. Rasak, shi yake gaya mata Ogan sa ya dauki hutu baya ganin kowa kuma baya amsa wayoyi, tace ya kai masa wayar, ya ce daga gida Zamfara ne. Amma sai ya ce mata %??m%??j sorry Ma, bani da hurumin yin hakan, bai bani damar zuwa inda yake ba, in ba shi da kan sa ya neme ni ba.

Amma ki kwantar da hankalin ki lafiyar sa kalau, don Cook din sa ya tabbatar min yana dan cin abincin da yake kai masa".
Aunty Badiya ta yi a jiyar zuciya, a zuciyar ta ta yi alkawarin sai ta ji abinda ya hada wannnan gabar tsakanin Habibu da uwar dan sa Rahinah daga bakin ita Rahinah, don ta tabbata Habibu ba zai taba gaya mata ba.

Abinda Badiya bata sani ba shine har gara Habibu wani lokacin akan Rahinah wajen taurin kai da zurfin ciki irin na Fulani.

Badiya ta lura yau annurin da ke tare da Hajiyar su ma daban yake, alamu ne masu kyau na ta fara sakin ran ta a kan auren. Bayan sun gaisa ta ce "me yasa bata zo mata da Zarah ba ta debe mata kewar Abdallah, tunda Juniour din uban sa ya dauke shi? Don ya gwada musu shi ke da iko da dan sa?%??? Badiya ta bata hakuri tace %??marah na da (common entrance exams) shi ya sa basu taho tare ba%???.

Hajiya ta ce %?ne kika tsara game da tarewar %??iar taki? Ta wani fannin kanwar taki? Kuma yaushe zaku je ku dauko ta?%???

Badiya ta langabar da kai cikin damuwa ta ce %??majiya ina naga Habibun balle mu tsara tarewa? Ko waya ya daina amsawa tun daga ranar da aka daura aure%???.

Hajiya ta jinjina kai ta ce %?nhin wai ni menene hakikanin matsalar su ne? Sama da shekara goma kullum magana daya yake yi a kan ta %?na ta son shi%??? ku kuma kun dage sai ita, tunda %??iar ku ce. Amma ai gara ka auri wanda ke son ka, a kan ka auri wanda kake so, ba ya son ka%???.

Badiya ta ce %?ni ki bar maganar rashin so a tsakanin su Hajiya, tsabar iya shege ne kawai. Sabida son junan su suka kasa aure kowa ya shaida wannan. Manema ba irin wadanda Allah bai baiwa Rahina ba, har da %??ian asalin kasasshen larabawa, shikuma Habibu wadanne irin mata ne ba%??j kawo masa ba? Ko bai gani a duniya ba?

Don haka ni bana regretting maida auren nan da su Daddy suka yi kuma har abada ba zan yi nadamar hakan ba. Sannan Daddy ya gaya min da amincewar ta suka maida auren, ba tursasa ta suka yi ba.
Sanda suka hada kan su a can wata uwa duniya suka yi aure har suka haifi da ai bamu sani ba, basu yi shawara da mu ba, to haka yanzu ma, sanda zasu daidaita kan su, su yi wa kan su maganin matsalar da suke da ita baza mu sani ba Hajiya. Ko labari ba zamu ji ba. Tunda dukkan su ba yara bane.
Abinda yake hakkin mu shine mu tabbatar Habibu ya zama cikakken mutum ta hanyar cika sunnar Manzo SAW, haka itama Rahinah, abinda ya ragewa Baban ta kenan, ya sada ta da dakin aure don cika amanar dan uwan sa marigayi.
Don haka ta fannin mu mun sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu. A dai wadannan shekarun na Habibu da ya dace ace yana da %??ia %??ia hudu ko biyar.
Don haka Hajiya ki daina fargaba kan duk wani nunkufurci da zai nuna, ina mai tabbatar miki a zuciyar sa farin ciki ne zallah, jin zafi ne kawai akan abinda ta yi masa wanda su kadai suka san shi, kuma a hankali bacin rai mai gushewa ne. Amma soyayya ba mai gushewa bace, da sannu zan binciki ko ma wace irin matsala ce a tsakanin su don a magance ta%???.
Hajiya Kaltume ta ji dadin bayanan babbar %??iar ta Badiya, hankalin ta ya kara kwantawa. Domin hakika a baya ta shiga rudani akan auren, sabida yadda Rahina ta fita fit! Daga ranta, yanzu kuwa Anty ta dan kankaro mata mutunci tunda ta ce da ita tana son Habibullahi itama, bacin rai ne ya sa ta kai shi kotu, sannan ba shi kadai yake koshin wahala ba, itama kuma ta dandana rashin auren na shekara goma a kan sa ba don ba ta da manema ba.
%??mo yanzu ta yaya kike ganin tariyar zata kasance tunda kin ce ko waya ba ya dagawa? Nima bai kira ni ba. Bana so iyayen ta su gane baya murna da komen auren%???.
Hajiya ta fada cikin damuwa, Badiya ta ce %?"nattaki zamu yi har Lagos din mu same shi, ni da ke da Baban Musaddiq, sai dai kawai ya gan mu a gidan shi, in ya so ayi wacce za%??j yi ya fadi duk inda yake son ta tare. In gidan shi na Abuja ne? In kuma Lagos din za%??j bi shi da matar shi to duk ya fada, ba zai mai da mu kananan mutane a idon surukai na ba.
Habibu yayi kadan ya dinga juya mu, wanda yayyi a baya ma ya isa. Hajiya sanyin ki yayi yawa a kan Habibu shi yassa yakke yin yadda yagga dama%???. Murmushi Hajiya Kaltume ta yi ta ce,
%?"no Badiya in ban tausasa masa ba wa zai tausasa masa shi ba mata a gida ba? Mu bi komai ta nutsuwa. Kuma a hankali, abinda lallashi bai bayar ba tursasawa ba zata bayar ba.
Ni babu Ikkon da zan iya zuwa, kafafun nan bazasu jure hawa jirgi ba don kwanannan ba dadin su nake ji ba, ku dai je ke da mijin ki amma don Allah ku lallabashi ku lallashe shi%???.
Dariya Aunty Badiya ta yi, "Habibullahi autan Hajiya!" Hajiya tace "na ji din".
A haka suka tsayar da maganar, cewa a gobe, kwanaki hudu da daurin auren, Uncle da Aunty zasu bi jirgi zuwa Lagos domin su tadda Habibu a gidan sa.

******



Rahinah na kwance rigingine a dakin ta bisa gado, cikin dakin ta na gidan Ambasada Shehu, ita ba barci ba ita ba ido biyu ba, Allah kadai ya san abinda ta ke sakawa tana warwarewa a zuciyar nan tata. Wadda ke cunkushe taf da al%??jmura daban daban duk a kan komen ta gidan Uban dan ta Habibu Nahuche.
Nene ta yi sallama a dakin, biye da ita wata bakar babarbariyar mace ce, ta yunkura kadan ta tashi zaune tana amsa musu da kyar, kallo daya Nene ta yi mata ta gane tun safe bata yi wanka ba. Ta ce %?nnya Rahinah? Wannnan wace irin amarya ce? To tashi maza in hada miki ruwan dumi ki yi wanka, ga Yagana ta zo zata fara miki gyaran jiki yanzun nan%???.
Kamar mai fama da ciwon baki ta motsa ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kin ta kadan tana tambayar Nene %?(nane irin gyaran jiki Nene?%???
%? nrin wanda ake yi wa amare %??ian gata mana! Wadanda ake so mijin ya so su, ya gigice a kan su, balle mazan duniya irin Habib Nahuche wadanda ba irin matan da basa gani suna zarya a hotel%???.
Murmushi ta yi mai ciwo, ta ji ta kara tsanar auren bakidaya, har gara mata sanda yake dalibi akan yanzu da ya zama mai budadden ido, tace,
%??mene ki yi hakuri ki sallami Haj. Yagana domin bana bukata, bazan yi ba%???.
Nene ta ce, %?(nannan ne kuma baki isa ba, in kika yi min musu in kira Yafendo yanzu ta wanke min ke tas. Wawuya kawai ana nuna mata abinda ya dace tana shirme%???.
Ala dole ta mike cikin dacin rai ta zuro fararen kafafun ta kasa, sumul sumul da su tamkar bata taka kasa. Suka nufi toilet tare da Nene.
Nene Balki ta hada mata ruwa mai zafi a kwami ta yi wanka da kyau sannan ta fito, hatta cikin ruwan wankan ta saida Yagana ta zuba turarukan humra wadanda take tafe dasu.
Lokacin da Rahinah ta fito daga wanka sai mai gyaran jikin ta hau aikin ta a kan ta, ta yi mata Dilke da Halawah ai kuwa ta ci kwakwa kasancewar ta mai yawan sumar jiki, a zuciyar Yagana mamakin kyawun jiki da kyawun fata irin na Rahinah take yi tana tazbihi ga Sarkin halitta. "Rahinah matar manya ce, Allah SWA ya kyautata halittar ta. Tana ta tsokanar ta da cewa
%??mmma Anti Rahinah angon ki ya more!%???.
Bata san bakanta mata ta ke da wadannan kalaman ba. Wai angon ta! Don haka ta zabga mata harara kasa-kasa.
A daren ranar Ambasada ya kira Rahinah falon sa, ga Nene a zaune, yayi mata nasiha mai ratsa jiki da bargo irin wadda ta dace kowanne uban kwarai ya yiwa diyar sa da zai kai gidan miji, don ko Safeenah iyaka abinda ya gaya mata kenan da zai kaita gidan nata mijin shekaru biyar a baya (da jimawa an yi wa Safeenah aure a Jos, ta auri wani Navy Officer Suhail Sajoh a can amma bata haihu ba har yanzu). Sannan ya kawo mukullin sabuwar mota irin tata ta baya ya bata, yace ta barwa Musaddiq tata.
Rahinah sai da ta yi hawaye, a zamanin nan samun mutanen kirki irin Ambasada da iyalan sa masu halin maida dan kowa na su zai yi wuya. Mutane yanzu kowa dan sa ya sani bale wanda baku hada alaqar jini da shi ba sai ta mutunci. A karshen nasihun sa Ambasada ya ce.
%??mna fatan matsalolin ku da kuka kunshe cikin cikin ku, ku kawo karshen su yanzu da kyakkyawar fahimtar juna. Allah yayi muku albarka, ya albarkaci dan ku da sauran kannen sa masu zuwa a gaba%???.
Ta rasa ina zata sa kanta yau, don yanzu ta gama saddaqarwa ta tabbata matar Habibu Nahuche a karo na biyu.
Washegari suka kama hanyar Adamawa duk gidan, har da Safeenah wadda ta zo tun jiya daga Bukuru, tafiya ce su ke yi mai dadi yau, domin hatta ruwn da zasu sha a hanya da abincin da zasu ci sun tanade shi tun daga gida sun zuba a kuloli sun tafi dasu domin tafiyar wuni guda ce curr. Raha kawai suke suna tsokanar Rahinah wadda bata iya tankawa kowa.
Safeenah ta ce %?nai ni babbar kawar amarya, amara kirjin biki%??? bayan a baya sam bata shiga harkar Rahinah har zuwa sanda aka yi mata aure, amma yau kam ta ware sai tsokanar ta take yi don ta fahimci bata son komen.
Sai bayan isha suka isa Girei, a dakin Uwargida Dudu su Yafendo suka sauka, Rahinah da Safeenah suna dakin Surbajo amaryar Sarkin Fulani.
Duk %??ia%??jan Sarkin Fulani da da ke gidan aure a washegari suka zo gidan tun da safe suka taya iyayen su dora tukwane. Sarkin Fulani yasa aka kada shanu har biyu don a yi hidimar abincin biki dasu. Ya kuma gayawa Usman ya gayawa matar sa cewa duk hidimar aure da ake yi na al%??jda a garin Girei bai yarda ba sai an yi wa Rahinah, don haka yana umartar sa da ya gayawa angon da iyayen sa.
Uncle Usman ya gayawa Badiya sakon Sarkin Fulani, ya kara da cewa ya ce ba zai basu Rahinah su tafi da ita ba sai sun sauke duka wannan nauyin na al%??jdar su.
Na farko tunda an daura aure gabanin kawo wadannan kayayyaki na al%??jda to sun zama bashi dole ango da iyayen sa su kawo.
Kayan aure wato %??iefe%??? shi ne na farko, sannan zasu kawo %??iuddaje%??? ga dangin amarya, wato turamen Atampha guda dari, sai akwatin Uwa da na Uba duka za%??j hada a kawo mana su tare da kayan aure.
Mu kuma zamu yi wa dangin ango %??iaute%??? kwatankwacin yawan kayan auren d suka kawo mana (Paute shine kaiwa dangin miji kwanukan samiru, kuloli, gado da katifa da kayan abinci kamar %??iara%??? a harshen Hausa amma ya banbanta dana Hausawa) domin su rarraba a tsakanin su. Ana yin paute ne iya yawan kayan aure da dangin ango suka kawo.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login