Showing 81001 words to 84000 words out of 110913 words

Chapter 28 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

son ya sake da ita).
Ya dage kafada cikin rashin yarda. "Ni ba zan kwana a dakin ki ba, sabida ban san ki ba, ina jiran Daddy na ya dawo ne, a dakin sa zan kwana, tare muke kwana in yana gari".
" And I'm also your Mum Abdallah".
"Na sani!".
In ji yaron cikin kosawa,
"Amma don Allah ki daina shigowa daki na, don Allah".
Raheenah ta ji jikin ta ya fara yin la'asar ganin yaron ko hada ido da ita ba ya son yi, Allah kadai ya san irin hudubar da ya yi masa a kan ta.
Sai ta mike zuwa dakin ta da sauri ba tare da ta iya daukan kwanukan da ya ci abincin ba, jin takun Habibu yana hawowa benen. Ya ga sanda ta shige daki da sauri, ita kuwa ko waiwayowa ba ta yi ba sakamakon kwallah da ta cika idanun ta.
Ta dade ba ta samu barci ba yau, tana tunanin ta wace hanya za ta bi ta dawo da zuciyar dan ta gare ta? Gaskiya ba karamar cuta Habibu yai mata ba. Ya gama nesan ta ta da dan ta Abdallah.
A dakin sa Habibu ya same shi ya yi tagumi da kwanukan abinci a gefe. Ya ce Abdallah ya ne? Wa ya baka abinci?
Ita ce ta kawo ya amsa a gajarce, kuma Habibu ya gane wa ya ke nufi, amma sai ya ce ita wa? Abdallah ya yi shiru bai ce komai ba.
Well Abdallah shes your Mum, and her food is nice, just eat, don ba ita ta kawo abincin ba ai ni na kawo, ita girkawa kawai ta yi, gyara zama mu cinye shi tas! Allah ne ya ce ta dafa ta bamu.

Da safe ba ta gaza ba, ta sake shirya masa karin kumallo. Tana kokarin saukowa daga bene zuwa dining dake kasan bene don ta aje masa abincin, tunda dai don shi kadai ta ke girkin ta, ta ji muryar sa yana gaya wa Baban sa shi ba zai kara cin abincin ta ba, duk da cewa da dadi, ya tashi su tafi Eatry ko restaurant su samu abin da za su ci, tunda ta masa Allah ya isa a kan food (he will never love her).
Yana maganar (with a bitter tone) a kan harshen sa, shi kan sa Habibu ya yi mamakin maganganun yaron, daga yadda Abdallah yake maganar zaka fahimci abun ya tsaya masa a rai ya kasa wucewa, irin yaran nan ne da baa taba musu iyaye su kyale kuma yana da sanya abu a ran sa.
Maganar da ta sa Rahinah komawa sama da gudu, shi kuma Habibu ya yi sakale yana kallon yaron, kafin ya ce,
"Junior kada ka kara labewa idan muna magana, ba Allah ya isa ta ce ba, ba ka ji daidai ba ne. Tashi mu tafi restaurant din".
Yana kokarin gayawa Habibu ba labewa ya yi ba shigar sa kicin din kenan ya ji tana fade Habibu ya yi masa tsawa..Cmmon, lets go i said. Dole yayi shiru yana kakkarwa. Ya saka takalmin sa ya bi bayan Baban nasa.
Kwanansu uku kenan a haka, kullum sai ta musu girki sau uku a rana, ba ta damuwa don Junior ya ki ci, yaro sai zucciya kamar tsohon kuturu, tana samun wani irin pleasure ne a ranta idan tana hidimta masa. Ko kaya ya cire ba ta saka su a kwandon kayan wanki ita ke wanke masa su da kanta a injin wanki. Ta kuma shanya a toilet din sa.
Ya ki yarda ya kwana a dakin ta ko sau daya sai a nasa dakin. Duk lallashin data ke masa kuwa. Don haka da ta idar da sallar isha ta ke kulle kofar dakin ta ta bar mukullin a jiki.
Abin da ba ta sani ba shi ne, ko da ta bar kofar a bude in dai Habibu ne ya dade da sallama ta ta wannan fuskar. Sex is now his last priority. Azumin tadawwu'in da yake yi duk Litinin da Alhamis har yanzu bai fasa ba. Musamman yanzu da yake tare da Rahinah Omar kullum, cikin gida daya, abubuwa ke neman canza masa a matsayin sa na namiji mai lafiya wanda ya san yana da iyali na halali, duk irin dauriyar sa wata rana baya iya barci, kusan kullum yanzun ya farlantawa kansa azumin nafilah baya shifting din ma. Duk ya kara ramewa dama ga jikin ba wani jiki ba. Sai ya kara nesanta kan sa da it aba ya bin ko hanyar dakin ta, ko motsin ta ya ji ta fito to kuwa zai kara zama a daki har sai ya ji ta koma dakin ta ta rufe.
Sannan ba sa haduwa ma sam in ba a dakin Abdallah ba da safe. Yana da sabgogi masu yawa da yake gudanarwa a cikin Abuja da kuma Hotel din 'Transcorp Hilton' da suke dauke masa hankali daga Rahinah, ba ya zaman gidan ko kadan. Ko ba shi da abin yi a waje da dai ya zauna yana jin motsin ta yana kissime-kissimen da ba samu zai yi ba ya gwammace ya tafi gidan Ambasada ya karasa daren sa wajen su Yafendo. Ya ci abincin dare gun Nene tare da Abba Jakada.
Sanda zai koma zai tarar ta yi barci sai ya shige dakin sa bayan ya duba Abdallah wanda shi daman da wuri yak e barci.
Satin su uku kenan da dawowar Abdallah Abuja har yau babu wani improvement tsakanin dan da uwar sa. Tana iya kokarin ta wajen jan sa a jiki da cusa masa akidu masu kyau, madadin na gata da ya tashi cikin su.
Habibu bai gaya mata yau zai kai yaron makaranta ba. Ta makara ba ta fito da wuri ba, sai jin tashin motar su ta yi suna ficewa daga gidan. Da sauri ta daga labulen dakin ta sai ta hango su direba ya fita da su, Abdallah da kayan makaranta a jikin sa.

Ya kamata a ce shi da ita sun zauna sun yi magana kafin yaron ya fara zuwa makaranta, amma sai ya ce wa kan sa ta yi kadan ya tsaya shawara da ita, don zai kai Abdallah makaranta.
Da can da yaron ya yi primary tana ina? Ba tana can tana gina kan ta ba? Don haka yanzu ma da ta ke cikin gidan in dai a kan al'amarin Abdallah ne ba ta da wani amfani a wurin sa.
*******
"Pace-Setters Collage" ya kai shi ya nema masa gurbi, aji daya na karamar sakandire, makaranta ce ta 'ya'yan masu ido da kwalli da ke wajejen Wuye, Life-Camp da Gwarimpha a Abuja.
Can Habibu ya kai Abdallah, ya kuma ware direban da zai dinga kai shi yana dauko shi kasancewar shi ba mazauni ba, ko yana gari ba zai jure kai shi da dauko shi ba.
A tsarin ayyukan hotels din sa bai iya sati guda cikakka a gari daya, don haka yanzu ma shirin wucewa Porthearcourt yake yi, kan ba yadda zai yi ne zai bar Abdallah daga shi sai Rahinah a gidan nan, wadda ya san neman duk hanyar da za ta samar mata kusanci da Abdallah ta ke yi.
Tafiyar sa Portharcourt kuma a wannan dan tsakanin, daidai ta ke da ya bata filin da zata samu damar kanainaye masa yaro. Don kuwa shi yake kara zuga Abdallah kullum da cewa yayi a hankali da ita. Ba zama ta zo yi ba, in ya bari ya saba da ita ta zo ta kara gudar su shi zai sha wahala shi ba ruwan sa.
Don haka da dacin rai yau ya shigo dakin ta, domin tilas zai yi tafiyar, an samu matsala tsakanin hotel din sa na PH da gwamnatin jihar ta Cross-Rivers suna so zasu saye filin wajen don amfanin gwamnati, don haka dole ya je ya daidaita komai in sayar musu zai yi ya sayar in ya so a sake gina wani a wani filin daban.
Ya shiga dakin ne da niyyar gaya mata abinda zai bata mata rai, wanda har ya dawo zai hana ta shiga harkar Abdallah, ana-i-gobe zai tafi PH.
Bai gan ta a dakin ba, har ya juya zai sauka kasa kuma sai ya jiyo maganar ta a dakin Abdallah. Don haka can ya bi su%???
Yana gab da shiga dakin ya ji tana dungure kan yaron tana cewa,
"Mai bakin hali da kuturwar zuciya kawai irin na Uban sa".
Yaron ya yi kicin-kicin da fuska, ya wani irin manne idon sa cikin takaici da bakin cikin kalaman ta, ya ce,
"Baban nawa ne mai bakin hali, mai kuturwar zuciya? Baba na!"
Rahinah ta ce, "Exactly! Like father like son, ba ka baro shi a komai ba t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????un daga kamanni har halayya, ban da haka sau nawa zan gaya maka Abdallah ba'a yi wa uwa haka, ko ka ki ko ka so dai ni din nan dai, ni na haife ka, sai in gani in zaku iya sake ni, Allah ya ce a bi UWA sau uku, kafin ya ce A bi UBA, kuma ban gaya maka baa kwanciya da uniform ba? Da an dawo ake cirewa amma kullum sai na maimaita?"
Sai Abdallah ya ce cikin kunkuni, "To ke Antyn gidan nan me ye damuwan ki da ni ne? Na roke ki ki daina shigowa daki na kin ki. Na fada miki I'm not your son, I'm Daddy's son!".
Sai jin sautin tafi suka yi daga bayan su, raf-raf-raf irin 'sound claps' dinnan. Habibu ya shigo dakin yana taku dai-dai cikin kasaita yana cewa,
"Ka haifu Abdallah! Ai ka san wasu mutanen ba su da zuciya kare ya cinye, in ba haka ba ban ga dalilin da za ta dinga shiga sabgar ka ba, bayan ta jefar da kai a zanin goyo ta rungumi boko".
Wannan karon a fusace ta ce, "Ka daina yi min haka, ka daina fadin kowacce magana ta zo bakin ka a gaban sa... shi yasa yake kara tsana ta.
Na jefar da shi ko ka sace shi? Ka dinga yi kana tsoron Allah cikin al'amarin ka".
Ta juya ta fice daga dakin hawaye fal idon ta. Ga ta da qi-fadi, ba ta son nuna raunin ta ko kadan a gaban Habibu Nahuce, shi yasa ta fice, kafin hawaye su gangaro mata, yaron sai ya ji dan tausayin ta ya kama shi yau, ganin tana hawaye da girman ta. Habibu kuwa ko a jikin sa, juyawa ya yi ya bi bayan ta zuwa dakin ta.
8/24/22, 10:35 - Bilkisu Adam ???f??_Hq??: U
ncle Usman ne ya yi mata waya yana neman karin bayani a kan barin aikin ta, don abokan aikin ta sun bi ta kan sa a kan ya roke ta ta dawo aiki. They cannot afford to lose such a golden Doctor like her, inda ya sanar da su ba shi da masaniya a kan barin ta aiki, amma zai yi wa mijin ta magana, mai yiwuwa ne shi ya dakatar da ita.
Ko da ya kira Habibu yana tambayar ba'asin maganar, sai ya yi shiru. Wannan ya tabbatar wa Uncle Usman zargin sa na cewa shi ya hana ta din, kuma ba abin da za'a iya yi wa Rahinah barazana da shi ta bar aikin ta na likita a yanzu in ba dan ta ba.
Uncle Usman ya yi wa Habibu fada sosai ya ce,
"Aikin ta bai da alaka da rigimar ku Habibu, ko da ka gan ta da karatun ta ka same ta, kuma ta sanadinsa ne har ka samu damar auren ta, har ku ka haifi Dan da ka ke mata barazana da shi Habibu.
Don haka ka bar ta ta yi aikin ta tunda aiki ne na taimakon al'umma. Bana son zuciya ba ne ko na rashin godiyar Allah".
Habibu ya yi mamakin jin Rahinah ta bi umarnin sa ta bar ayyukan ta duka, shi iya na Nizamiye ya ce, wannan ya kara tabbatar masa Rahinah ta fara canzawa daga kafaffiyar da ya san ta a baya, kuma da gaske ta ke za ta yi wa Abdallah goyon da ya kubuce mata na shekaru goma ba da laifin ta ba, sai ya ji tausayin ta ya kara ya tsirga masa.
Amma ko da ya dawo gidan a washegari daga PH, bai nuna mata hakan ba. Bai nuna mata cewa ta fara karya lagon sa ba. Ya sha tura mata %??iext masseges%??? yana PortHarcourt amma ba ta taba replying ba, ko tana gani ko ba ta gani? Allah masani.
Ko da ma ba masu bukatar reply ba ne, yawanci na ban hakuri ne kawai da alkawari kala-kala, a kan ya yi alkawarin zai canza, zai zama miji abin alfahari a gare ta. Zai koma irin yadda duk take son shi. Zai zame mata Mijin marainiya kuma loving and caring husband.
Bai tsammaci da ma za ta kula shi ba, kamar ya san a duk lokacin da ta gani ba ta bata lokaci ta ke share su daga fuskar wayar ta duk da a lokuta da dama kalaman suna taba ta, suna sassauta fushin da ke zuciyar ta.
Amma still ta kasa sakewa da shi wholeheartedly. Ta kasa yarda duk abinda yake fadi haka yake har zuciyar shi. A ganin ta he needs time wato yana bukatar lokaci.

Ba tare da ta san cewa yau zai dawo ba, tana kicin tana juya lafiyayyar miyar Talo-Talo (Turkey) da ta ke soyawa mai yawa ta saka a firji. Sai jin takun sa ta yi ya nufo kitchen din. Kasancewar shi mijin ta, Habibu Mustapha Nahuche, mutum ne mai takun kan sa (duk inda ta ji takun sa sai ta gane), yana ta hayaniyar cigiyar Abdallah cikin gidan bai san yana can bayan gidan yana fama da dirkeken 'Bike' din sa ba.
Abdallah where are you? Im here now!
Daga bakin kofa ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu yana kallon bayan ta da wata irin siga, yana jin wani irin contentment da wata nutsuwa ta musamman suna baibaye shi. Samun mace kamar Rahinah kadai matsayin matar aure is a BLESSING da bawa domin sai wanda Allah ya zaba ya ga damar ba shi, a ganin sa ko da ba za ta amfana wa mijin ta komai a shimfida ba, kallon kyakkyawar fuskar ta kadai da fararen idanun ta sun isa sanya shi farin ciki kullum.
Ga shi ta yi wani abu da ya tsaya masa a rai, ya kuma lankwasa zuciyar sa yau, wato ayyukan ta da aka ce da gaske ta bari saboda Abdallah.

"Good afternoon Dr.\Mrs NAHUCHE".

Habibu ya fada da lallausar muryar da Rahinah ta kasa amincewa tasa ce. Sabida a kullum yana mata magana ne harshly and loudly da sigar tonon rigima, amma yau ba abin da muryar sa ke dauke da shi sai lislama, ni'imtacciyar soyayya da kulawa tsantsa.

Banza ta yi da shi ta ci gaba da soya miyar ta, sai ya tako a hankali tamkar mai tausayin kasa zuwa inda ta ke. Ba ta yi aune ba ta ji ya rike ludayin, ya kuma kashe cooker din.
"Ki ba ni attention daga tafiya na dawo. Kuma kin san cewa I missed you ko?".
Ta daga ido ta dube shi a fusace ta ce, "Ina ruwana da tafiyar ka? Na aike ka? Ko na ce ina bukatar dawowar ka? Na bi I missed you din da gudu na tattake da takalmi mai tsini a kafa ta!" Ta fadi tana tattaka kafar ta a kasa.
Dariya ya yi. Rahinah ko tsufa ta yi baya jin zata bar ki-fadin ta da tsiwa. Amma kwayar idanun ta sun fallasa cewa ta ji dadin %??m missed you%??? din, ita haka Allah ya halicce ta son soyayyar miji.
"Ba ki ce ba, amma kin iya kai kara ta gun Baban ki ki ce na hana ki aiki, kin manta cewa yanzun ba ikon Baban ki ba ce, iko na ce (ya nuna kirjin sa da dan alin sa) To na hana din, ki yi duk abin da za ki yi, tunda na ce zan biya scholarship din da aka biya miki ga duk wanda ya bukata".

A kufule ta dube shi, sabida kalaman sa sun bata mata rai matuka. Shi da ya ke neman shiri amma ba zai bar gadara da fadin rai ba. Hausawa sun yi gaskiya da suka ce Mai hali ba ya fasa halin sa don shi hali kaman zanen dutse ne.
"Ba ka da arzikin da za ka fanshi ilmi na, domin shi ilmi ba a sayen shi da dukiya, wadannan kudin naka da babu tabbacin ba na haram ba ne sun yi kadan su fanshi karatu na".
Ba zan kara cewa ka sake ni ba, don I'm now matured enough ga bukatar hakan, amma har abada ba za ka samu zuciya ta tare da amincewar gangar jiki na ba....".
Sai juyawa suka yi su duka suka ga Abdallah a bayan su, hankalin sa a tashe da fadan da ya tarar suna yi kamar za su tada kicin din.
Kafin Habibu ya yi masa magana Abdallah ya juya da sauri, da sauri ya sakar mata ludayin ya bi bayan sa, sai kuma ya juyo yana kallon ta a kaskance. Domin kalaman ta sun masa ciwo ba dan kadan ba. (Cewa da tayi ba zai taba samun zuciyar ta da amincewar gangar jikin ta ba).
"Ki jika komai naki ki shanye don Allah Rahinah, I'm going for a second wife, wadda ta fi ki duk abin da ki ke takama da shi. Za ki ga ranar da kudin haram za su yi wa dan halal".
"Ka dade ba ka yi ba! Tunda ka kwashe shekaru goma ba ka yi ba sai yanzu, in ka yi yanzun gaskiya zai fi zama fashionable, sai ana son mutum a ke kishin sa".
Ta karasa cikin karkarwar murya da ita kanta ta ba ta mamaki. Da gaske yake? Ko kuwa barazana ce irin wadda ya saba? In ma da gaske ne bai kamata ta ji faduwar gaban da ta ji a kan maganar sa ba, in har da gaske sai da so ake kishi.
Duk abin da suke fadi a kunnen Junior wanda ke bakin kofa ya kasa tafiya daki yana ta tsuma, zazzabi ne ya zo ya rufe shi sabida a rayuwar sa ba ya son fada, kuma ya tsani hargagi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login