Showing 36001 words to 39000 words out of 110913 words

Chapter 13 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

mahaifin su.

Aunty ta ce cikin takaici, "Amma Rahina ba ta kyauta min ba, sai fa da na ce ta tsaya yau za su hadu da Junior". Takaicin ta daya ta so yau Raheenah da Habibu su hadu, ko Allah zai sa a dace su yi wa juna, don dai ta dade tana shaawar gwada wannan saar tata a ran ta, don a ganin ta Rahinah ba daya take da sauran mata da Habibu yake gudu ba, tafi karfin namiji yayi mata kallo daya.

Habibu ya yi gaba zuwa cikin gida ya bar su yana ta amsa wayoyin da ke shigo masa, bai saurari zancen da suke yi ba.
Bai tafi ba sai da Uncle Usman ya dawo, sun dade suna tattaunawa a falon Uncle a kan harkokin su. Suna cikin maganar sako ya shigowa Uncle daga Rahinah.

Uncle I'm so sorry, an kira ni on emergency ba zan iya jiran dawowar ka ba, yanzu har mun shiga Abuja, Uncle ba ni da amsa ga umarnin ka, I have no one, I have only myself". Rahinatun ka.

Murmushi ya yi, ya san da ma za ta gudun, amma kawai sai wani bakon tunani ya shigo kan sa, a lokacin da ya daga ido ya dubi Habibu da ke cin abinci a dining din falon sa.

-Wace ce uwar dan sa? Me ya sa ko zancen ta bai taba yi ba?

-Habibu ya rayu ne a Jamus, haka diyar sa Raheenah, Habibu na da Da Abdallah, Raheenah na da Da ita ma mai suna Abdallah, amma ko zancen dan ba ta yi.
-Habibu ba ya zancen tsohuwar matar sa, Raheenah ba ta zancen tsohon mijin ta. Ambasada ya ce mijin dan Zamfara ne...! Matar sa Badiya da kanin ta Habibu sun fito daga Zamfara ne...
A fili Uncle Usman ya ce, "Ya Jamilal Munzar! (Wato, Ya Mafi Kyawun Masu Gani) Ka taya ni duba al'amarin nan".

"Habibu!".

Ya kira sunansa da karfi, wanda hakan ya sa Habibu dakatawa da cin abincin sa, ya dago lumsassun idanun sa yana kallon Uncle cikin mamakin karfin tone din da ya kira sunan sa da shi, Uncle ya mike jikin sa har rawa yake, ya isa ga dining din. Ya ja kujera wadda ke fuskantar Habibu ya zauna.

"Ka gaya min sunan Babar Abdallah, da garin da ta fito".
Da wani irin mamaki yake duban mijin Yayar sa, wanda yake tamkar ubangida a gare shi. Duk wasu achievements din sa a rayuwa Usman Girei shi ne sila, don haka yana da matsayin da ya zarta na siriki kawai, yana kallon sa ne a matsayin Yayan sa da suka fito ciki daya kamar matar sa Badiya. Yana da wannan kimar. Ban da haka shi tun barin sa Jamus harshensa bai kara ambaton sunan Rahinah Omar ba... In ya ji mutum dan Adamawa ne ma ba ya tsayawa a inda yake, kada tsautsayi ya sa ya kasance ya san Raheenah Omar ya yi masa zancen ta.
Muryar sa na rawa ya ce,

"Uncle Usman me za ka yi da sunan ta da garin ta? Ina fatan ba neman ta za ka je yi ba? I don't need her in my life anymore...!"

Girgiza masa kai Uncle yayi. "Ba neman ta zan je ba, ba kuma bikon ta zan maka ba, hakkin haihuwa zan ba ta in kai mata dan ta ta gan shi ta san yana raye, kada hakkin su ya kama ka.

Shekaru goma decade guda ka raba Uwa da Dan ta....

Yaa Subhanallah! Sai a yanzu Uncle Usman ya kara tabbatarwa yar sa Rahinar sa ce uwar Abdallah da ya tuna farkon bayyanar Rahinah gare su an gaya masa Habibu ya sato shi ne daga hannun ta yana dan shekara daya.

Kuma tabbas Junior ya zo hannun su ne bai fi shekara dayan ba, ina kwakwalwar su da lissafin su ya tafi tuntuni suka kasa gane hakan daga shi har Badiya?

"Ka gaya min sunanta na ce Habibu, da garin da ta fito".
Ya fada wannan karon cikin karyewar murya da karewar kuzari a jikin sa.

Cikin in'ina da magana daga kasan can makoshi ya ce.

"Rah...Rahinah Omar... Adamawa...!!!"

Uncle Usman ya tsura masa idanu, ya kasa cewa komai. Hawaye suka cicciko a idanun sa, hawayen da bai san na tausayin Habibu ne ko na tausayin Rahinah ba? Shekaru goma suna dakon soyayyar juna da kuma Da a tsakanin su? Habibu bai gane halin da Baban Musaddiq ke ciki ba, kuma bai san dalilin ganin cikowar hawaye a idanun sa ba, sai gani ya yi ya tashi daga wajen, ya dauki wayar sa da hanzari ya yi waje.
Mikewa ya yi don ya kasa ci gaba da cin abincin ya nufi sassan 'yar uwar sa. Tana falo ita da su Junior sun kunna kwallo (ball) suna kallo shi da Mu'allim sai iface-iface suke. Tambayar da Baban Musaddiq ya yi masa ta sa duk ya birkice, idanun sa sun kada, afterten years yau ya ambaci sunan ta.

Kuma ba a fatar baki kawai ya fada ba, ya ne tun daga karkashin zuciyar sa, wanda hakan ke bankado rufaffen gyambon yana kaikayi da son neman agaji. A yadda Aunty Badiya ta gan shi ya shigo falon sai ta ce da karfi.

"Junior, kashe kwallon nan ku tafi dakin ku???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, zan yi magana da Daddy".

Mu'allim ne ya kashe suka fita, Junior na cewa da Abban sa, "Don Allah kada ka je hotel ka kwana, ka zo mu yi sharing daki na". Amma ga mamakin Junior Daddyn nasa bai iya ya ce masa komai ba, which is very unusual Junior ya yi magana ya ki kula shi.

"Zai zo Junior, ka karkade masa shimfida". Inji Aunty.

Da murnar sa ya fita yana cewa, "Thank you Mummy. You know I love you ko? Ke da Daddy?"

Murmushi Aunty Badiya ta yi, ta ce, "I know Abdallah, and Mummy da Daddy loves you more".

Da haka ya fice yana tsalle.

Habibu ya zauna gefen Yayar sa, tamkar wanda ya dauki azumin rashin magana. Aunty Badiya ta ce,

"Tsakani da Allah Habibu me ye reality na rashin auren ka? Habibu ko dai ka zama ba namiji ba ne bayan haihuwar Junior da ka yi?"

Duk halin da yake ciki sai da Dr. Badiya ta ba shi dariya. Ta gefen ido ya kalle ta ya yi murmushi, ya ce, "Auren ne kawai bana ra'ayi, tunda kuma ina azumin litinin da alhamis ina iya rike kaina. Stop all these silly thoughts. Yau ki ce wannan, gobe ki ce wannan.
Badiya ta yarfar da kai gefe, ta ce,

"Tsakani na da Maman Abdallah Allah ya isa! Ita ta ki zama da kai, sannan ta hana ka auren kowa. Wa ma ya sani ko asirin su irin na fulani ta yi maka?"

Mikewa ya yi yana dan murmushi kafin ya ce da Yayar sa Badiya.

"Ai ita ba ta so na ma ko kadan, balle ta yi min asiri. Masu yin asirin ina ce sai suna son zama da mutum suke yin sa? Ba ta taba so na ba, kuma har abada ba za ta so ni ba".

Yana fadin hakan ya doshi kofa ba tare da ya juyo ba, kada Aunty Badiya ta ga kwayar idanun sa, ta hango weakness din da ya bakunce su.

"Gobe ba zan biyo ta nan ba, daga Hotel zan wuce Lagos".
Badiya ta yi masa Allah ya kiyaye hanya, ya wuce ba tare da ya kara waiwayowa ba, ya bar ta da hannu bisa haba.

A harabar gidan ya ga Baban Musaddiq zaune bisa fararen kujeru yana waya, ga yadda ya bada nutsuwar sa kacokam ga wayar za ka fahimci waya ce mai muhimmanci yake yi. Habibu na dosowa ya kashe ta, ba tare da ya gama ko ya yi sallama ba.

"Baban Musaddiq zan wuce masauki, gobe zan wuce Lagos, ba zan shiga Abuja ba sai upper week".

Baban Musaddiq sai kallon sa yake kamar yau ya soma ganin sa yana kissima abubuwa masu yawa a cikin ran sa.

Ashe surukin sa ne... Ashe shi da Badiya har jini sun hada... Ashe shi ya sa yake matukar son ABDALLAH... Abubuwa da yawa yake kissimawa wadanda sai a yanzu suka samu damar dawowa suna warware kan su, yana kara mamakin ta yadda har ya kai tsayin wannan lokacin bai gane din ba.

Hannu kawai ya iya mika wa Habibun, ba tare da ya ce komai ba suka yi musabaha ya wuce zuwa motar sa. Ya shiga ya tayar da kan sa don ya sallami Solomon tun dazu, Baban Musaddiq bai bar wajen ba sai da Habibu ya fita daga get gabadaya.

Wayar da Uncle Usman ya fito waje yana yi, ba da kowa yake yi ba da Ambasada Shehu ne. Har kuka ya yi a cikin wayar, a lokacin da yake gaya masa ashe Habibu shi ne mijin Raheenah ba su taba ganewa ba?

Murmushi Ambasada ya yi, murmushi mai sauti kafin ya ce.
"Finally kai ma ka gano da kan ka kenan, kamar yadda na dade da ganewa. Da ma na ce ba zan gaya maka ba ne sai ranar da ka gano don kan ka...".

Nan aka dauko tsohon tarihi, Ambasada ya warware wa Uncle Usman rikicin auren su a Jamus kaf! Ya kare zancen sa da cewa.

"Har gobe daga ni har Nene Bilki da kawar ta Yafendo, babu wanda ya san hakikanin laifin da Habibu ya yi mata. Bata taba fada ba. Which means tana sirran ta sirrin sa. Amma kuma tana fushi da shi, ban yarda rashin so ne ba, kada ka takura sai ka ji, don tsakanin mace da miji sai Allah.

Yanzu neman hanyar sulhunta su za mu yi, in ba haka ba ina mai tabbatar maka Habibu da Rahinah za su yi furfura a kan su ba tare da sun yi aure ba".

Uncle Usman da Ambasada suka ci gaba da kulla mai yiwuwa a tsakaninsu su biyu ba da sanin Aunty Badiya ba, haka ba da sanin Habib da Rahinah ba, sun aje kwanaki uku masu zuwa za su hadu su je Girei su samu Sarkin Fulani a san ta yadda za a shawo kan al'amarin. Bayan nan, sun yanke tabbas za su hada Habibu da Rahinah a gidan Uncle Usman ba tare da sanin kowannen su ba, don su ga irin reaction din kowannen su.
Don a cewar Ambasada Rahinah ta HUCE daga fushin ta tuntuni, ki-fadin ta ne ba zai bari ta nemi Habibu ba. Shi kuma Uncle ya musanta da cewa har yanzu ba ta huce ba, don ko jiya da ya matsa mata da zancen aure, kuka ta yi masa. Ta kuma gudu. Ba za su gane hakikanin abin da ke zukatan su ba har sai sun hada su sun ga juna unexpectedly.

Abin da dattijan biyu ba su sani ba shi ne, daga Habibu har Rahinah babu wanda bai san garin da dan uwan sa ke rayuwa ba... Babu wanda bai san duk wani taku na dan uwan sa ba. Babu wanda bai san ci gaba da nasarorin dan uwan sa ba. Abin da ba su sani ba shi ne, alakar da ke tsakanin su, wadda Badiya da Uncle Usman suka hada, wato kasancewar Habibu kanin matar Uncle din ta, da kasancewar Rahinah diya ta halali ga ubandakin sa, kuma sirikinsa Baban Musaddiq Alh. Usman Girei.

******


Sarkin Fulani ya gama jin duk abin da ke akwai, ya yi kabbara takbir da tahlili cikin jinjina kudurar Ubangiji. A karshe ga bayanin da ya yi musu, a matsayin sa na babba, wanda dukkan su ya fi su shekaru da tsinkaye.

"Bana bayan shawarar ku, ta a maida musu aure ba da sani da amincewar su ba. Kada ku manta Rahinatu na a matsayin bazawara ne a halin yanzu, addini ya ba ta damar zaben mijin aure. Alhamdulillahi tunda saki daya ne a tsakanin su, abin da za ku yi yanzu shi ne, ku yi kokari su hadu da juna, ta ga dan ta ta san shi ne. Ya gan ta, ta ganshi su san alakar zumuncin da ke tsakanin su.
Daga nan ku bar komai a hannun su, ni na gaya muku za su sulhunta kan su. A wannan lokacin addu'a ce tsakanin ku da su ba tirsasawa ba".

Daga Uncle har Ambasada sun yi na'am da shawarar Sarkin Fulanin Girei.
******

*SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)* 07030137870

*NA HUCE!*
(Paid Book)




Ta fito daga bedroom dinta a shirye tsaf, likita mai aji, rike da 'yan mukullayen motar ta ta tadda Sahura a falo tana kallo, ta ce, "Sahura, yau in na fita sai Allah, don haka kada ki yi girki da ni, ki yi daidai cikin ki, za mu yi dashen dodon kunne har biyu (cochlear implant transplantation) a Nizamiye, don haka sai kin gan ni kawai".

Sahura ta ce, "Allah ya yi jagora, Allah ya bada sa'a uwar daki na, Allah ya bada ladan ceton kunnuwan al'umma".

Dariya ta yi ta wuce ta fita tana karanto addu'ar fita daga gida.

"Ina so ki ba ni hankalin ki".

Baban Musaddiq ya ce da Aunty Badiya.

Ta gyara zaman ta tare da tattara masa kafatanin hankalin ta. Baban Musaddiq tun jiya ta ke ganin shi upset, ga waya akai-akai shi da wadanda ba ta san ko su waye ba, abu kadan ya dau waya ya fice ya gama magana sannan ya dawo, abin da ba halin sa ba, babu wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta a baya.

Yanzun dai Nene Balki ce ta ba wa Ambasada shawarar ya kamata Badiya ta san komai, kuma a gidan ta ya kamata Habib ya ga Rahinah ba a Abuja ba, tunda a can Junior yake. Ba ta ga amfanin kin sanar da Badiya da wuri ba.

Shi kuma Ambasada ya gaya mata cewa, Badiya tana kullace da tsohuwar matar Habibu a kan ita ta hana dan uwan ta aure, da yadda ba ta taba neman ta ga dan da ta haifa ba inji Uncle Usman, Nene ta ce,

"Akwai fahimta da kyakkyawar mu'amala tsakanin Rahinah da matar kawun nata, insha Allah komai zai zo da sauki".

Don haka shawarar Nene Balki Uncle Usman ya bi yanzu. Ya ce,
"Maman Junior I have something special for you, mene ne zai zama tukwici na?"

Murmushi Dr. Badiya ta yi, ta ce, "Duk abin da ka ke so shi zan ba ka Daddy".

Ya ce, "Shin wace ce babar Abdallah ne, kuma a ina ta ke?"
Nan da nan Aunty Badiya ta canza fuska kamar ba ita ke ta fara'a yanzun ba, ta ce, "Daddy da zan ganta Allah kadai zai raba ni da matar nan, na tabbata surkullen su na fulani ta yi wa Habibu ya kasa yin aure.

Ban san ta ba, ko sunanta ban taba tambayar sa ba, sabida ba ni da wata alaka da ita. Yaron da ta haifa ta yasar, babu ko waiwaye ga shi nan Allah ya raya shi.

Ita kuma Allah ya yi mana shari'a da ita a lahira".

Uncle sai ya kama dariya, ya ce, "Wato fulani surkulle gare mu? Kuma 'yan Nahuche ai fulanin ne in miki kirarin garin ku Zamfara GALMA UWAR RUFI, ko ba ku son mutum ba ku hwadi. Ke kam ba ki yi galmar ba kin hwadi ba ki son matar Habibu, ga shi kuma ta zame miki dole, sai ki dau na Annabawa ki soma tunanin hanyar sulhunta su, tunda kuwa ba kowa ba ce 'yar ki ce Dr. Raheenah".

Kusan za a ce Aunty Badiya shidewar wucin gadin razana ta yi, sabida ta san Baban Musaddiq ba ya yin joke shi kai tsaye yake fadar komai. Ta kura masa ido ta kasa daukewa, shi kuwa sai lumshe mata ido yake yana gyada mata kai cikin ba ta tabbacin maganar sa. Da kyar Aunty Badiya ta iya cewa,

"Wace Dr. Rahinar?"

Shi kuma bai bata lokaci ba ya ce, "Ya ta Raheenah".
Ya kwashe labarin komai ya gaya mata, sak! yadda Ambasada ya labarta masa.

"Idan Ubangiji ya lullube al'amari, babu dan Adam din da ya isa ya bankado shi, sai a lokacin da Ya nufa. Don haka ki sauke duk wasu makaman yakin ki a kan Maman Abdallah mu taru mu taimaki yaran nan su koma auren su, don zan iya yi miki rantsuwa kan cewa soyayyar juna ta hana su aure.

"Yanzu me ye abin yi? Da me zan iya taimakawa?"
cewar Badiya cikin mutuwar jiki.
Uncle Usman ya gyara zama. Tiryan-tiryan suka soma tsarawa.

******





"Kin kyauta Rahina, ni da ma na san kafin in dawo za ki gudu, to duk abin da ki ke yi ki bari ki zo karshen satin nan, I'msure ba kya aiki asabar da lahadi, Sarkin Fulani ma ya ce ki biya ku gaisa idan kin zo".

Raheenah ta marairaice murya abin tausayi, ta ce, "Uncle, bana son zancen aure, don Allah Uncle ka kyale ni, idan ka takura zan iya kamuwa da depression, I have a lot to do I can't put myself in any relationship... Zan iya rike kaina Uncle, don Allah kada ka sake yi min zancen aure".

Murmushi Uncle ya yi, ya ce, "Na yi alkawari ba zan sake ba, za ki zo din? Weve planned a get together dinner na kammala karatun Musaddiq".

A hankali ta ce, "Insha Allahu zan zo Uncle, tunda ka yi alkawari".

Murmushi ya yi yana kallon matar sa Badiya.

"Finally, ta amince za ta zo din".

"To Allah ya sa shi ma ya yarda ya zo don ka san shi kamar tsuntsu yake, yanzu haka sai ka ji ya bar Lagos din ma".
Ta fada tana dialling number din Habibu Nahuche.

Har ta yi karar ta ta gama bai dauka ba. Tana kokarin sake kira sakon sa ya shigo.

"In a meeting, call later".

Murmushi ta yi, ta tura masa nata sakon.

"Call me da zarar ka fito".

Yana fitowa din kuwa ya kira ta.

"Ya ya ku ke Aunty, ya Abdallah?"

"Sarki mai Abdallah, ni boarding zan kai shi in huta kallon kwallo. Za ka iya zuwa karshen satin nan? Baban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login