Showing 24001 words to 27000 words out of 110913 words

Chapter 9 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

shaidar dan yau, amma ita kam ta shaidi nata. Sabida yawan ibada da tsaida sallah yana hani dga aikata alfasha wanda kuma kowa ya san dabiun Habibu kenan, ga yawan azumin tadawwui. Ta dade da sanin akwai abinda ya kulle a zuciyar sa tun daga kan Maman Abdallah. Wadda ita tasa ya ki jinin mata. Duk ya hada su yayi musu kudin goro. Har ila yau, Hajiya Kaltume ta gama fahimtar ba ya son Shafa'atu, in ta takura masa ya aure ta zaa bata goma ne daya ba ta gyaru ba. A lalata zumunci kuma auren bazai dore ba. Sannan ta fahimci baya yin wani abu na banza duk da ba tare take da shi ba a yawancin lokuta amma ta fi kowa karantar sa, bata taba jin yana waya da 'yammata ba. Don ba wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta.

Ta fahimci in ta takura masa ya auri Shafa'atuba zai kula da ita ba don kwata-kwata yanzu hankalinsa bai kan mata. A duniya abu uku ya sanya a gaba; (bautar Allah da neman kudi, sai rainon dansa Abdallah, Dan da Raheenah Omar ta haifa masa).

Ita kan ta Dr. Badiya ba karamin gata ta ke samu a wurin Habibu ba, duk da kasancewarta mai albashi mai tsoka nata na kanta itama, to balle kuma mahaifiyarsa da Dansa. Wadanda duk abin da ya samo nasu ne, a cewar sa su yake nemawa. Duk fadi-tashin sa a rayuwa sabida su ne. Sau uku a jere Haj. Kaltume da Badiya na tafiya aikin Hajji duk shekara.

Tuni ya buge gidan su an zuba gini na zamani na gani na fada, kai ka ce gidan wani minista ne ba gidan tsohuwa Kaltume matar marigayi Bilyamin Nahuce ba, duk fadin unguwar Kofar Jange babu gida mai fasali da zubin zamani da ya kai kwatankwacin GIDAN NAHUCE.

Ga maaikata rututu Habibu ya zuba mata. Kullum zaka sameta zaune a tankareren falon ta akan kilishi mai taushi tana lazumi ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?na ibadah, don a cewar ta su kadai suka rage mata yanzu, sai ko ganin auren Habibullahi. Hajiyar Nahuche ta zama wanke goma ka tsoma biyar. Jawur da ita, tsafta da naira sun kama jikin ta. Ga hasken rikon addini. Gidan ta kullum cike da yan cin arziki daga jamaar unguwa dana garin su Nahuche.

Daga baya Hajiya Kaltume ta soma karbar tayin hotunan 'yammata da ake kawo mata daga Nahuche da Bungudu, sannan yayan masu da shi anan Zamfara da iyayensu ke son hada auren 'ya'yansu da Lucky Habibu Nahuce duk haka ake kawowa Hajiyar Nahuche. Eh, wasu kan kira shi 'Lucky' sabida kafin ka samu mutum mai sa'a a kan duk abin da ya sa gaba kamar Habibu Mustapha za a dade.

Komai ya sanyawa hannu na harkokin sa sai ya zama kamar magic sai ka ga ya bunkasa ya shahara ya yi albarka cikin dan lokaci. Wannan kuma albarkar bakin UWA ne da addu'o'inta da ba sa yankewa a gare shi. Kullum Haj. Kaltume a kan dugaduganta take kwana sallah, kuma duk yawancin addu'o'in ta akan Habibu ne.

Nasarar rayuwa, kariya daga sharrin Shaidan, albarka a dukiyar sa, da mata tagari (wadda zata kaunace shi saboda Allah ba don dukiyar sa ba) su ne abubuwan da kullum take roka masa.
Hotunan 'yammata iri-iri 'ya'yan manya a garin Zamfara da garin Bungudu da Nahuce an sha kawo wa Hajiya Kaltume, amma a duk lokacin da ta dumfari Habibu da su ko dubawa ba ya yi zai ce,

"Ki yi hakuri Hajiyata, ni na riga na gama aure a duniya".

In ta takura masa kan sai ya duba kuma sai ya fara mata yan kanan kwallah, da dole zata mayar dasu inda ta dauko cikin mutuwar jiki. In ya so tsokanar ta kuma sai yace.

Hajiya kada ki damu akwai (hurul eeni a aljannah, inshaAllahu).
Bata taba daukar maganar sa a bakin komai ba, face lokaci ne bai yi ba, in lokacin yayi shi da kan sa zai kawo mata matar da yake so, bacin ran uwar Abdallah (Rahinah) ta yi amanna da cewa shi ke walagigi da shi har zuwa lokacin. Ya ke ganin don ita ta ki shi, ba zai samu mai kaunar sa ba. Ko kuwa an ce ita ce autar mata da za'a debewa sauran mata tsammani a kan ta??? A bisa wannan dalilin Hajiyar Nahuche ta ji ta fara tsanar wannan Rahinah duk da bata taba ganin ta ba ko a hoto.
******



*MUTANEN JAMUS (BAYAN BARIN HABIBU FRANKFURT).* Tun daga lokacin da Habibu ya dauke mata Abdallah, rayuwa bata kara komawa yadda ta ke a baya ba ga Raheenah Omar. Sauran kadan ta zama depressed wato ciwon damuwa ya kama ta. Ita kadai sai ka same ta a dakinta tana magana cikin safah da marwah, karatu ta daina fahimtarsa kwata-kwata, zuwa makarantar tana yi ne kawai bisa tursasawar Nene da Ambasada Shehu, amma ta kasa concentrating a kan komai. Komai ya fice mata a ka. Hatta kasar Jamus bakidayan ta.

A jarrabawar karshen zangon da suka yi Ambasada Bichi bai ji dadin sakamakon Raheenah ba ko miskla zarrah; ta fadi courses har biyar. Don haka ya kira ta falonsa don su yi magana ta Uba da Da.

"Rahinatuh. Ina son sanin hakikanin abinda ke damun ki? Akalla in ban miki maganin sa ba a matsayina na Uba zan baki shawara wadda nake ganin ta dace. Wannan wane irin mummunan sakamako ne nake gani haka?"

Raheenah ta share zufar da ta jika goshinta, cikin rauni da karaya ta ke wa Baban ta Ambasada magana. Ba tare da ta san maanar abinda take furtawa ba.

"Ni kai na Daddy (ban san hakikanin abin da ke damuna ba), rayuwar ce kawai na gaji da ita. Na fi so in mutu in huta. Ji nake kamar ni kadai na yi saura a duniya, kamar rayuwata ta zo karshe.........

Kamar babu wani sauran farin ciki da zan cimma a karshen ta, kamar duniya ta ta kare. Ji nake kamar wani tsuntsu ko kuma shaho ya zo daga sama ya tattare dukkan farin ciki na da burika na ya tashi sama firrr! Da su".

Wani irin murmushi Ambasada Shehu ya yi, irin nasu na manya da suka karanci halayyr dan adam, kafin ya ce,

"Kuma wannan TSUNTSU ko SHAHO ba kowa ba ne, HABIBU ne!!!.

He ran away with all your hopes and happiness... (ba tare da sanin ki ba ya tafi da dukkan fata da farin cikin ki).

Habibun da ki ke gujemawa da gangan, amma ruhin ki da zuciyar ki na tare da shi da Dan da ki ka haifa masa..

It's either two options; ko dai ki yi hankuri ki ba wa zuciyar ki abin da ta ke so don samun farin ciki da kwanciyar hankali, ko kuma ki ci gaba da horar da kan ki da kan ki a bisa kuskuren ki.
Allah Ubangiji mai afuwa ne, Annabi (S.A.W) mai afuwa ne. Allah Ubangiji kuma yana son masu afuwa.

Amma Rahinatu ke kin ce ba za ki yi afuwa ga Habibu ba a kan kankanin laifin da ya yi miki. Wanda ku kadai kuka san abin ku. Don haka sai ki koya wa zuciyarki juriyar rashin su, in har kina nan a kan bakanki, ki fuskanci rayuwar da ke fuskantar ki.
Kina da babban aiki a gaban ki wanda ba ya son damuwa da rudani (karatun ta). A matsayi na na Baban ki, shawarar da zan ba ki ita ce ki koma addu'a, idan rabuwar ki da Uban dan ki ita ce mafi alkhairi, Allah ya ba ki zuciyar dangana.

Idan dawowar su cikin rayuwar ki shi ne alkhairi Allah ya sanyaya miki zuciya su dawo cikin rayuwar ki ba da jimawa ba".

Raheenah ko kadan ba ta son yarda da abin da Ambasada ke fadi, wai- wai wai Habeebu ne tsuntsun da ya tashi da farin cikin ta. Za ta fi yarda in ya ce rashin dan ta Abdallah! Don haka ba ta ce komai ba, amma tana can tana kokawa da zuciyar ta a kan shin abin da Daddy Amb. ke fadi shi ne hakikanin damuwar ta ko kuwa?

Wato rashin Habibu Nahuce???

Idan kuwa shi ne zuciya ba ta yi mata adalci ba, domin Habeeb bai bar wani (green momeries) ba cikin rayuwar ta da ya cancanci ta bishi da kewa, sai (black memories and black episodes...) wadanda da su ne kullum take kallon sa, suka kuma sa ta kasa bashi gurbin masoyi, wane irin rashin adalci na zuciya ne zai sa rashin sa ya dagula lissafin ta har haka, ya hana ta ci gaba da harkokin rayuwar ta?

Daga wannan ranar Raheenah ta yi aniyar fighting da zuciyar ta, mai neman kai ta ta baro, har sai ta manta da Habibu da Dan sa, dan da bata taba zaton ma za ta so ba har sai bayan da ta haife shi. Wannan wani kudiri ne da ta ke fatan Allah ya ba ta nasara da iko a kan sa, wato gusar da duk wani burbushi da Habibu ya bari cikin rayuwar ta.

Daga wannan ranar, Rahinah Omar ta maida hankali a karatunta, don in ba karatun ba wa za ta kama? Ranar da babu su Ambasada? Habibu ko sunan garinsu ba ta sani ba, balle inda ya fito, bare ta sa ran watarana za ta je ta kwato danta.

Abin da ta sani a kansa kawai shi ne dan kasarta Nigeria ne.
Bayan wannan bata san komai akan sa ba. Sannan Nigeria kasa ce ba gari ba.

Da sabon zango ya zagayo. Ta sake maimaita takardun da ta fadi, kuma cikin ikon Allah ta haye wannan karon. Da taimakon nasihohin Yafendo, Ambasada da lallashin Nene Balki.




*NA HUCE.* ...is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank
Shaidar biya 07030137870
: Ana gab da hutun summer Ambasada ya karbi passport din ta ya hada da nasu don yi musu shirin zuwa Nigeria hutu, kamar yadda suke yi duk karshen shekara.
Ta shiga dakin Yafendo a wani dare, sai ta tadda ita tana daure kaya. Tsibi-tsibi tana daurewa tana ajiyewa kamar in ta tafi ba za ta dawo ba. Raheenah ta ce,
"Yafendo? Wannan kaya ina za ki kai su haka? Ai sai ki karar mana da kilo"
Yafendo ta ce, "Duk tsaraba ce da na ke tarawa tsayin shekara guda ta mutanen Bichi. Sannan ke ma na yi sayayya ta musamman don ki kai wa 'yan uwanki in Allah ya sada mu da su".
Wani dadi ya ratsa Raheenah, sai ta ji tamkar Dadanta ce a tare da ita. Allah ya sa wadanda Yafendo ke hasashe su kasance su ne dangin nata. Da duk wasu matsaloli da damuwoyi sun karasa zama tarihi a gare ta. Habibu ya je ya dafa dansa ya cinye.

A washegari ita ma ta hada nata kayan, amma ba ta dauki sun fi kala bakwai ba. Don Daddy ya ce ita sati daya za ta yi ta dawo ita da Safeenah don ba ya so gidan ya zauna babu kowa. Safeenah kuma ba ta son zaman Bichi ko kadan, a cewarta zafi ke damunta.

Daddy Ambasada dan garin Bichi ne ta Jihar Kano, kowa ya san 'yan Bichi 'yan boko ne na ga-ni-kashe-ni. Gidan iyayensa har gobe yana garin Bichi, suna da family mai tsohon tarihi.
Sun sauka a Kano da daddare, daga filin jirgi wadanda suka zo tarensu kannen Ambasada ne su uku suka dauke su suka wuce dasu Bichi.
Kwanan su uku suna zaga dangi Yafendo da Nene na rabon tsaraba, suna kuma shan tambaya a kan bakuwar fuska Raheenah, cewa ta ke Daddy ke rikonta a Jamus, karatu ta zo. Sai da suka kwana hudu Yafendo ta kira Muqaddas kanin Daddy kuma cousin a gare shi, ta ce ya shirya mota gobe zai kai su Girei ita da Nene da Raheenah, Daddy Abuja zai wuce akwai taron da zai halarta na Ambasadodin Najeriya kafin nan da dawowar su daga Girei din.
Ambasada ya yi musu fatan alkhairi na Allah ya sa a dace ya kawo kudin fetir da na kashewa ya babbasu.
******

GIREI, ADAMAWA
T
afiyar su daga Bichi zuwa Adamawa ta basu wahala ba kadan ba. Musamman dake tafiyar mota ce zuwa Adamawa daga Kano. Sun jigata sun jijjiga wuni guda sur don ma motar lafiyayya ce.
Sai magriba suka shiga garin Girei, inda Yafendo ta ce Muqaddas ya tambayi gidan sarkin Fulanin Girei can za su je.
Raheenah sai rarraba ido kawai ta ke yi, tana jin wani irin nutsuwa da wani irin kwanciyar hankali na shigar ta, tun ma kafin a ce ga dangin Daadan ta. Kasar Girei da mutanen cikin ta kawai ta ke ta bi da kallo, irin feeling din da dan Adam ke ji lokaci na farko da ya taka fatherland din sa.

An kai su har gidan Sarkin Fulanin Girei mai ci a lokacin. Farin dattijo, siriri dan shafal da shi. Yana zaune a karkashin bishiyar darbejiya da ta yi wa kofar gidan sa rumfa. Suka sauko daga mota suka taka zuwa inda yake zaune, sai binsu yake da ido har suka karaso.
Tun daga nesa Raheenah ta kura wa siririn dattijon ido gaban ta na tsananta faduwa domin sosai yake kama da Dadarta.
"Jabbama-Jabbama (maraba-lale)". In ji Sarkin Fulani, su kuma suka tube takalman su suka karasa inda yake zaune a kan makekiyar tabarmar kaba, suka gaida shi ya amsa da madaukakiyar fara'a, sai kallon Raheenah yake yi da mamaki, domin da ganinta ka ga Sarkin fulani mai rasuwa, wato Umaru Modibbo. Fuskar ta sak ta jikoki sa dake cikin gida.
Yafendo ta kara gaishe shi, sannan ta gabatar da su daya bayan daya,
"Wannan sunanta Rahinatu, wannan Nene Balki, nikma Yafendo Mairama, mun taho tun daga Bichi ta jihar Kano don mu yi tambaya a kan tsohuwa (Rahin) da dan ta Modibbo Umaru Sarkin Fulani na nan Girei mai rasuwa shekaru kusan talatin da suka wuce.
Tunda na san shi ne a matsayin dan Rahin kuma sarkin fulanin Girei, shi ya sa kai tsaye na ce a nuna mana gidan sarkin Fulani mai ci a yanzu, wai an ce matambayi ba ya bata, hakane ko ba haka ne ba? Dadin dadawa muna da hoton ita marigayiya Rahin tare da mu".

Har ta kai karshen bayanin ta dattijon bai katse ta ba, sai ya kalle ta sannan ya kalli Raheenah, sannan ya kalli Nene, sai da ta dasa aya sannan ya ce,
"Allah mai iko, ikonSa da girma yake. Bana raba daya biyun wannan yarinyar jinin Adda Rahin ce. Don shi jinin mu karfi gare shi ba ya buya a ko'ina, balle a idanun mu.
Kwarai kun zo gidan su Adda Rahin, wadda ta kasance Yaya a gare ni. Kafin mu tattauna ku shiga cikin gida wajen iyali na a ba ku ruwa, ku yi sallah ku sha fura sannan mu zauna".
Suka mike suna godiya, farin ciki fal zuciyar Raheenah, ta kasa tashi daga gaban dattijon sai da ya ce je ki bada farali tukunna kin ji? Suna tafe zuwa cikin gida amma ba ta bar waiwayen dattijon ba don tsoro ta ke kada su shiga su fito su neme shi su rasa.
Har sai da ta ga ya dauko butar sa ya biyo bayan su sannan hankalin ta ya kwanta. Ta sa kai cikin gidan.
Matan aure hudu ne a gidan, Fulani duka farare sol da su kamar mijin su. Uwargidan na da tsagin kalangu a fuskar ta wadda Rahina ta ji an kira Dudu, sai Baba Amina da Goggo Tani da amaryar Sarki, Surbajo.
Cikin fulatanci ya yi wa matan nasa bayanin bakin, wadanda kowacce da aikin da suka samu tana yi a tsakar gida, ga yara da matasa suna ta shige da fice. Nan suka hau rige-rigen ba su ruwan alwala suna masu sannu da zuwa cikin karamci da girmama bako irin wanda Fulanin Girei suka gada.
A dakin uwargida Dudu aka shimfida musu karauni suka yi sallah, sannan kowacce cikin matan gidan ta shigo musu da kwanuka cike da kabakin abin da ta dafa wa iyalin ta, kasancewar 'yar tukunya ake yi a gidan wato kowacce tukunyar ta daban, Sarki kuma ya aiko musu da damammiyar fura ta ji kindirmo kwarya guda, da gasasshen nama mai laushi. Nan suka baje suna ci suna hirar karamcin mutanen gidan a tsakaninsu.
Rahinah kam farin ciki da doki sun hana ta iya cin komai, sun cika mata zuciya da ruhi taf! Sai furar ta sha bai fi ludayi uku ba da Nene ta matsa.
Sai da suka huta Sarkin Fulani ya shigo har tsakar gida aka shigo masa da kujerar shan iskar sa a waje tsakar gidan, ya zauna sannan ya ce Surbajo ta zo da bakin sa.
Sai da suka sake sabuwar gaisuwa sannan ya ce,
"Ko me ye dalilin su na zuwa neman gidan su Rahin?"
Yafendo ta nuna masa Raheenah da dan alin ta ta ce, "Domin mu sada wannan yarinya da dangin ta na uwa da uba, jikar Rahin ce, ba ta san kowa nata ba bayan Rahin, Allah bai sa Rahin ta taba gaya mata asalinta ba. Ni ma zance ne ya yi zance...to ka ji".
Ta ba shi labarin yadda aka yi ta yi zargin diya ce ga Umaru Modibbo, ta kwashe duk yadda suka yi da Raheenah shekarar baya ta fada masa, sannan ta dauko hoton Dada da Raheenah ta ba ta tun lokacin ta boye ta mika masa.
"Tsarki ya tabbata ga sarki Allah, wannan Yayata ce Rahin, uwarmu daya ubanmu daya. Ita ce ta haifi Umaru da Usmanu da Dije mai rasuwa.
Abinda ya faru shine, Umaru ya kasance bayan haihuwar wannan yarinya Raheenah uwar ta ta koma, sai ya auro wata mace daga zuwa ci rani Shagamu, ya taho da ita nan Girei, ya kawo ta gidan nan inda a da nan ne gidan da yake zaune tare da mahaifiyar sa (Rahin).
Wannan mata da ya aura babu tarbiyyah ko kankani a tare da ita, ta yi ta azabtar da Rahin da 'yar marainiyar Allah ba tare da sanin Umaru ba. Ko abinci ba su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login