Showing 12001 words to 15000 words out of 110913 words

Chapter 5 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

haihun kamar yadda ta yi alkawari? Shi kuma zai yi komai don dawo da ita cikin rayuwar sa cikin martaba da mutuntawa, dadin dadawa soyayya mara yankewa har fiye da wadda bata tsammani. Daga wannan ranar yake bincike, wani irin bincike na yadda ake tafiyar da soyayyar mata. A rubuce-rubuce na masana ilmin psychology (self-help books and self-reflection). Ya samo wasu tips guda goma wadanda suka ce (How to keep your woman and make her love you forever). Marubucin ya ce; cikin abubuwanda zasu rike maka soyayyar matar ka sun hada da;
-work on yourself ; ka yiwa kanka self-evaluation; ka cancanci ta so ka ko a'ah?
-listen to her (and i mean really-really listen); ka saurareta akan duk abinda ta zo da shi da cikakken attention ka bata hankalin ka a lokacin da take bukatar hakan.
-learn how she prefers to be loved; ka duba abinda tafi so ka nuna mata soyayyar ka da shi.
-give her gifts (ka kasance mai yawan yi mata kyauta, kyauta tana kara dankon kauna).
-be honest with her (ka zamo mai gaskiya da kyakkyawar manufa akan ta).
-respect her (ka girmamata) and treat her with this respect.
-find creative ways to tell her that you love her (ka zama mai iya kirkirar hanyoyin gaya mata yadda kake son ta in your own special way).
-allow yourself to be vulnerable; wato ka dinga nuna mata raunin ka. (Allow yourself to make mistakes and admit to them. Allow yourself to be real and true and not hide any of yourself from her.
Don't be afraid to cry in front of her. And don't be afraid to let her cry, too.}?Vulnerability allows for deep connection and bonding}?in a relationship. If you can't be yourselves}?in your most raw forms, how are you supposed to feel safe building a whole life together?"

Habeeb Nahuche sai ya ga cewa duka wadannan tips din da wannan masanin ya zano duk zurfin ilmin sa shi bai mallaki ko daya ba! Bai taba nuna wa Rahinah dayan su ba, yet yana blaming din ta da kasa son shi duk cancantar sa.
Ita soyayya ta gaskiya ba ta ta'allaka da appearance din mutum, but the way he demonstrates himself.
Ya yarda duk ilmin ka ilmi baya taba karew a a duniya, saidai ka dauki iya wanda zaka iya ka bar ragowar.
Inama! Inama! Inama Rahinah ta yarda ta sake bashi dama koda sau daya ne a rayuwar su???
****



*NA HUCE* is not for free,
It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara FirstBank
: A daren bata yi wani isashshen barci ba sabida taraddadi da ya cika ranta, ashe tana da rabon ganin wanda zai ce ya san wani nata ma bayan Dada? Excitement ya cika zuciyar ta, ta dokantu shekara ta zagayo ta bi iyalin gidannan Najeriya.
Washegari da safe ta yi shirin makaranta, ta hada tea a dining din kitchen zata sha, kawai sai taji zuciyarta na tashi kuma ba abinda take so sai ramar Yafendo.
Da sauri ta suri jakar ta ta nufi dakin Yafendo. Ta idar da sallahr walha kenan, ta shigo dakin kamar an jefo ta, "Yafendo don Allah don annabi ki sammin rama da kuli, in ban ci ba yanzun nan mutuwa zan yi".
Yafendo ta katse lazimin ta jin abinda Rahinah ke cewa, kafin kuma ta bata amsa ta hau daddaga shirgin Yafendo tana neman Ramar, Yafendo tace "Rama da safiyar nan 'yar nan? Ki tafi makaranta kafin ki dawo zan kwada miki, yanzu ki nemi ruwan dumi ki zuba a cikin ki""na hada na kasa sha, tashin zuciya bambita yake sa ni, don Allah ki taimakeni".
Da sauri Yafendo ta dauko ramar, tace "jona ruwan dumi a butar can" cikin minti biyar tayi mata kwadon ta bata.
Nan ta hau ci ba kakkkautawa hannu baka hannu kwarya. Yafendo tana ta mamaki a ranta, anya lafiyar ta?
Data dawo daga makaranta ma kai tsaye dakin Yafendo ta zarto. "Na kwaso yunwa Yafendo, zan samu kwadin ramar ki?' Kawai sai ta ga Yafendo ta zaro kwano a rufe ta mika mata, already ta kwada tun kafin ta dawo".
"Allah ya kara nisan kwana Yafendo nagode" ta soma ci a urunce. Yayin da Yafendo ta tsura mata ido.
Ta koma dakin ta ta sunce zata yi wanka, amma sai ta bige da kallon kan ta a mudubi, a take ta hango wasu bakin sauyuka a halittar jikin ta. Abinda ya fi daukar hankalin ta shine karuwar girman kirjinta sosai, sannan tayi wani irin fari dau! Kamar babu jini a jikin ta.
Rahinah bata damu ba ta cigaba da wankanta tana fadin mutum na kara girma ai dole kirjin sa ma ya kara girma.
Tana fitowa Ahlan ya shigo da gudu, "Aunty Rahina Nene tace wai yau baki ci abinci ba ko lafiya?" Ta ce "Ahlan ka gayawa Nene wallahi kwanan nan ban iya cin komai sai RAMA".
Ba jimawa sai ga Nenen da kanta, tayi sallama ta shigo, tace "Rahinah me kika ce a gaya min? Ban gane hausar Ahlan ba, Jamusanci ya masa yawa" nan ta maimaita mata. Tace "ke a ina kika ga Ramar?""Wajen Yafendo, tana da ita mai yawa" Mami ta tsura mata ido, a take ta hango sauyukan data ke son gani. Tace "Rahinah kina yin period kuwa?" Kanta tsaye ta amsa "ai ni rabo na da shi har na manta, amma kin san i'm too busy to notice that ba don kin fada ba".
Nene tayi mata kallon tausayi, sannan ta ce yanzu idan ramar ta kare ya za'ayi?"
"Nima ban sani ba Mami,na dai san in ina so ban samu ba mutuwa zan yi, yanzu kam na koshi sai kuma gobe in Allah ya kaimu".
Mami ta juya ta fita tana fadin "on weekends zaki raka ni asibiti, mutum baya period ai gara a duba shi a san dalili".
Cikin damuwa tace "Nene, is there any problen with that?" Nene ta dafa kafadarta tace "don't worry". Sannan ta fita.
Nene ta ce kar ta damu, amma sai ta ji ta damun, ko wata cuta ce rashin yin period din?
Nene na fita dakin Yafendo ta nufa, ta samu kujera ta zauna, tace "Yafendo ko kin lura da abinda na lura da shi game da yarinyar nan?"
Yafendo ta ce "kwarai kuwa, kallon ta kawai nake, in kuma jira in ga ko zaki kula da kiwon da Allah ya baki. Shi aure dama in Allah bai nufi karewar sa ba wa ya isa ya karar da shi? Da zata ji shawara ta gara mata ta koma gidan mijin ta ta cigaba da hakuri irin wanda kowacce mace ke yi a gidan auren ta, ba namijin da yake cikakke a komai dukkan su suna da gibi, amma yadda na lura tafi jin dadin rayuwar ta da mu a haka bata ko so a dago mata zancen sa". "Kwarai wannan haka ne, bari in je in samu Daddy muyi magana a kan ta".
Yana sauraron radio Jamus a 'yar karamar rediyon sa lokacin da Nene tayi sallama ta shiga. Ya amsa mata, sannan ta samu gefensa ta zauna.
"Ranka ya dade magana ce ta kawo ni, akan yarinyar nan Rahinah".
Ya rage sautin rediyon sa ya bata hankalin sa. "Ina zargin ciki ke gareta". Radeyon hannun Ambasada ce ta subuce kasa, tace "wallahi alamu sun gama nunawa, amma duk da haka ban tabbatar ba""kuje asibiti a tabbatar pls" Mami tace "insha Allahu, amma in ya tabbata cikin ne yaya zamu yi da ita ga karatun ta mai tsayi?" Ambasada ya nisa yace "yadda zamu yi da Safeenah, idan irin haka ta same ta".
****
Rahinah bata san me ta rako Nene yi a asibiti ba, amma tunda suka zauna a gaban likita ya kuma ce ta bashi fitsarin ta komai ya fara kwance mata.
As a medical student ta san awon fitsari na nufin abubuwa da yawa.....awon cuta ko awon ciki! Don haka kafin sakamako ya taddasu, ta yi ligib cikin tashin hankali da tararradi.
"She's two months pregnant". Likita ta fadawa Nene ita kadai, bayan ta ce Raheenah ta je reception ta jira ta. Sannan ya bata shaidar hakan a rubuce.
Nene ta yi masa godiya, sannan ta fito ta tadda ita suka tafi, a hanya take gaya mata an ga shawara (jaundice) cikin fitsarin ta.
Raheenah tayi wani ajiyar zuciya, feeling relieved. Har suka zo gida zancen rama take wa Nene, wai yanzu idan ranar Yafendo ta kare ina zata sa kanta? Nene tace "sai ki ci salad, ai shima ganye ne""amma bai da dan tsami-tsaminnan kamar na rama" murmushi Nene tayi, tace "sai a masa vineger".
Suna sauka a mota kuwa ta tafi dakin Nene cin rama.
Kwana bakwai kenan bata iya cin komai banda ramar, har yau gashi rama ta kare, babu kuma inda za'a sameta a Jamus.
Don haka tun safe take cikin kunci, haushin kowa ta ke ji, da Ahlan ya shigo yana mata surutu sai ta shige toilet ta rufe kanta don bazata iya korar sa ba.
Nene ta shigo dauke da plate a rufe ta sameta, "Rahinah yau bazaki makaranta bane? Yara duk sun fita sun barki, ga wannan ko a mota sai ki ci kada ki tsaya ci ki makara, kin dai san kina da nisa".
"Nene yau ban iya zuwa makaranta" ta fada hawaye na ciko idon ta. "Sabida me?""I'm not feeling well, sabida tun jiya ban ci rama ba, Yafendo ta ce ta kare""try this" ta fada tana mika mata plate din hannun ta.
Bata yi musu ba ta karba ta bude, salad ne Nenen ta hada mata da kanta, yaji kuli da vinegar da tumatur, cocumbrr da albasa. Wani mugun yawu ya gudana a bakin ta, ta karba tun daga tsayen ta soma ci kafin ta zauna. Amma ko loma hudu bata yi ba ta dinga kwaro amai kamar zata amayar da hanjin ta.
Tun daga ranar komai ta ci sai ya dawo, ta galabaita matuka, karfin jikin ta ya yi kasa sosai. Ambasada yace da Nene ta kaita asibiti, koda taimakon da zasu yi mata abinci ya dinga zama a cikin ta.
Suna asibitin likita ya riketa, domin yace she's 60% dehydrated. Aka sa mata drip nan take. A ranar ne Ambasada ya kira Habib a waya.
"In ka samu lokaci kazo 'Sachsenhausen Hospital' da daddare ina son ganin ka". "Insha Allah i will". Ya fada cike da girmamawa.
Karfe takwas na dare a Sachsenhausen ta yi wa Habibu Nahuche. Yana sanye da Native Hausa Attire dinsa na shadda sharaton ruwan makuba, ya kafa hula a gaban goshin sa ruwan toka mai turuwa sosai (deep grey), yayi kyau kamar koyaushe amma kallo daya Ambasada yayi masa ya gane muguwar ramar da yayi cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba.
A wajen parking motoci suka hadu, direba ya sauke ambasada, shikuma taxi ta sauke shi. Ambasada ya bashi hannu sannan tare suka taka zuwa dakin da aka kwantar da Rahinah. Daga ita sai Nene a dakin. Kamshin turaren sa ne ya fara shiga hancin Raheenah, wani kamshi mai tasirin da bazata taba mantawa ba....da sauri ta juya kai zuwa bakin kofar shigowa. Idanun su suka hadu, wanda hakan ya haifar da wani irin shock ga Rahinah dake kwance, domin ta ganshi ne ba zato ba tsammani.
Yayin da Habibu Nahuche ya tsura mata ido, gabadaya ta zabge ta lalace, maimakon ya zo ya ganta very healthy and jovial tunda ta samu rayuwa yadda take so? Ta karbi 'yancin ta da take ikirarin ya danne mata? Banda girman idanun ambasada da yake gani babu abinda zai sa shi amsa wannan kiran, don bai ga dalilin sa ba. Tunda komai ya kare a tsakanin su.
"To zauna mana kun tsaya kuna kallon-kallo kamar zakaru" Ambasada ya furta masa sounding fatherly. Ya nemi guri can nesa da gadon da take kwance ya zauna. Wani irin abu na hankoro a zuciyar sa, ta shiga bugawa fat-fat-fat, bai san idanunsa sun yi kewar ta ba, sai yanzu da suka ganta kwance a gaban su, hatta zuciyar sa neman fitowa take daga tsakiyar kirjin sa....shikadai ya san halin ragaitar da ya samu kansa cikin wadannan watannin biyu masu kama da jiran tashin alkiyama a gare shi.
Rahinah ta dauke kai daga kallon sa, ta mayar wani gefen daban, tunda suka rabu ko sau daya bata ji kewar sa ba. Bai bar mata wani abun tunawa a zaman da tayi da shi ba na kwanaki bakwai, banda kyakkyawar fuskarsa ta Rumawa data zauna a zuciyarta ta ki fita.
"Na kira ka ne Habib, don in sanar da kai Raheenah na da ciki na watanni biyu".
Daga Habib har Raheenah, a tare zuciyarsu tayi wani irin dokawa, ta doka ta sake dokawa ta ci karo da bango. Idanuwan Rahinah kamar zasu fado kasa.....jin maganar tayi tamkar saukar aradu a kunnuwan ta, zata rantse ko mutuwar Dada da aka gaya mata a waya bata firgitata ta ruda ta kamar abinda Ambasada Shehu ya fada yanzu ba...

Yayin da Habib, Mustapha Nahuche ya wani irin lumshe idanunsa.
Wani albishir ne zai ce ko bushara da ba'a taba yi masa kwatankwacin sa ba.
Wani irin maganadisu ya ji yana fizgar zuciyar sa akan Raheenah da abinda ke cikin ta..
The feeling is so sweet da bai taba jin mai dadi a zuciyar sa kamar sa ba...nitsatstsen SO!
A hankali ya bude idanun sa akan Raheenah, wadda ta tamke nata idanun tamau, hawaye na zirara ta gefe da gefen su.
Which means she's not happy at all, she's mourning kaddar da ta afka mata rana daya.......ta tabbata ta rasa farin cikin ta daga yau, bata ga amfanin sauran rayuwar ta ba..
Ashe dai ta yi gudun gara ne ta tadda zago..... Habib Nahuche bai shigo rayuwarta don ya fita a lokacin da take so ko yake so ba.
Kaddara bata kare tsakanin su ba, mai hada eternal dangantaka ya riga ya hada wato gamayyar jiki, wadda a yau ta maida ita matar Habib a karo na biyu har sai ta haife masa dan sa ko 'yar sa wanda take jin ba abinda ta tsana a duniya sama da kawo shi duniya...
A fili ta fada ".......bai yi sa'ar mahaifi ba, he's but selfish by nature wato mutum ne mai son kan sa da yawa (tana nufin Habib din).
Muryar Ambasada Shehu ta cigaba da ratsa mugun shirun da ya ratsa kamar daukewar ruwan sama. "My dear Son and Daughter isn't it high time you reconcile? Tunda kun ga yadda kaddara tayi daku, kowanne Da yana burin ya tashi tsakanin iyayensa biyu, broken home shine babbar matsala ga tarbiyya da rayuwar kowanne yaro, rayuwa duka 'yar afuwa ce, in kuka afuwantawa juna kuka kuma zauna kuka gano matsalolin ku i'm sure zakuji dadin zama da juna tunda har ga rabo a tsakani...".
Habibu yasa hanky dinsa ya goge gumin fuskarsa da hawayen da suka cika masa ido, wadanda yake da tabbacin na farin ciki ne. Ya dubi Raheenah wadda ta kautar da kai gefe tana jin tamkar Daddy na diga mata narkakkiyar dalma a kirjin ta da ya ce wai ta komawa auren Habibu. Ya ce "ranka ya dade ni bani da matsala da hakan in har ta amince, abinda ba zanyi ba shine sake zaman aure da ita ba tare da amincewar ta 100% ba".
Rahinah ta juyo a hankali zuwa side din da yake, a hankali ta ce "to in dai ko amincewata kake bukata to har abada bazamu koma ba, once beaten twice shy. Ba ciki ba ko 'ya'ya goma ne suka bayyana tsakani zan baka abin ka, yadda bana son ka haka bana maraba da duk abinda ya fito daga jikin ka...."
"Rahinatu!"
Ambasada ya kira ta sounding fatherly, "banda cin fuska ga wanda ya girme miki, balle mijin auren ki, wanda har yanzu kike cikin zummar auren sa, har sai idan kin haihu bai ce ya mayar dake ba. Tunda baki amincewa komen ba shikenan, amma ki janye munanan kalaman da kika yi masa".
Tana kuka sosai, kukan kaddarar da ta sameta, tace "ka yi hakuri Daddy na maida kalamai na, amma har abada bazan koma masa ba".
"Shikenan zance ya kare, shima cewa yayi ai in kin amince. Kinga kuwa yasa tagociya kenan ga maganarsa. Don haka ki kwantar da hankalin ki kina hannun Daddyn ki, har Allah ya sauke ki lafiya".
Ya juya ga Habib, wanda tuni ya mike tsaye ya zuba hannayen sa cikin aljihun caftan din shi yana nufin barin dakin don in ya cigaba da zama zuciyar sa na iya fashewa ko tayi bindiga, a yiwa uwarsa da 'yar uwar sa asara! Ya gama saduda Rahinah bata son shi, kuma har abada bazata so shi ba, tunda rabon bazata da Allah ya kaddara a tsakanin su bai sa ta so shi din ba. Ya sha jin ance mace na fara son mijinta ne daga lokacin da rabo ya gifta a tsakanin su. Wanda ke nufin ita Rahinah is exceptional and extraordinary daga sauran mata.......
"Daga wannan watan zaka dinga raba albashinka biyu kana bata rabi don ciyarwa har sai ta sauka. Ba don bazan iya daukar dawainiyar su ba sai don in baka damar ka ta uba da addini ya baka. Ka kuma koyi daukar responsibility na iyali tun daga yanzu".
Kansa a kasa idanunsa sun kada sun yi jazir yace babu damuwa insha Allahu. A turamin account number din ta".
"Kana iya tafiya Habibu, Allah yayi muku albarka, yasa hakan shi ya fi alkhairi tsakanin ku".
Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji tayi zuciyarta na son karyewa (rauni irin na diya mace) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta.
Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya.
Shikuma yasa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa bazai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwar sa ba.
****
Sai da ta kwashe kwanaki bakwai kafin ta samu karfin jikin ta, kuzarin jikin ta ya dawo ko ba duka ba. Har tana jin zata iya zuwa makaranta a gobe monday.
Tana canza kayanta na barci zata kwanta Nene tayi sallama a dakin. "Rahinatu kin yi barci ne?""Yanzu dai nake shiri Nene""to zo mu yi magana irin ta uwa da 'ya" tayi murmushi, don Nene ta canza mata bakidaya tundaga samun cikin ta, sosai take janta a jiki yanzu, tana tausaya mata, domin gani take tayi kankanta da haihuwa kashin jikin ta kamar bai gama kwari ba. Sabida bata da manyan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login