Showing 51001 words to 54000 words out of 110913 words

Chapter 18 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

wadda ta biyo su har gurin mota.
Abdallah ya ce da Habib bayan ya fito daga wankan da ya sa shi dazu, yana goge sumar kan sa da karamin tawul.
%??m just like her Daddy, and i don%??j know why I admire her from the first glance%???.. (Kawai na ji ina son ta, ban san kuma me yasa nake son nata ba, daga sanda na fara ganin ta, ta kwanta min a rai Daddy).
Wacece ita? A ina take? She%??j beautiful. Ina so in koma gidan Mummy don in kara ganin ta%???.

A wannan lokacin Habibu rasa amsar da zai baiwa Abdallah yayi, sabida ya san howsmart yaron nasa is, sai ya yi taka-tsan-tsan kwarai wajen gaya masa ko wacece Rahinah gare shi, dole ya bashi gamsashshen bayani, son samu ya gaya masa abinda zai dakusar da tasirin data samu haka nan da nan a ran sa, don kalaman da yaron ya yi amfani da su a kan ta sun bashi mamaki matuka, kasancewar sa wanda bai son bakin fuska bai kuma sakin jiki da su sam.
Sai ya shiga shafa kan yaron cikin wani hali na tausayin kai, tare da da tasowar wata irin KEWAR Rahinah Omar, ya samu kan sa cikin wani hali na kaka-ni-kayin SO mai wahalar da zuciya, da kuma bakuntar wadannan tsofaffin feelings dinnan da yake dasu tuntuni a kan ta, a dalilin ganin da yayi mata yau; (she%??j more beautiful and looking more ravishing than ever before).
A baya ya dauka ya dade da rasa sha%??jwar sa ta Da namiji a kan mace, tun daga kan ta, ya dade da rasa mazantakar sa a kan rashin Rahinah Omar, kudi kawai yake nema sune kadai bukatar sa a rayuwa. Har sai yau da ya ga RahinahOmardin ganin idon sa%???a ji muryar ta jin kunnen sa%???. Ya gan ta more mature, more ravishing and more sexy than before.
Sai komai ya dawo masa sabo fil, ya ji shi ya koma yaro matashi danye mai tashen balaga da tashen kuruciyar nan, wannan Habibun dan kimanin shekaru ashirin da tara ba arba%??jn din da yake da su a yanzu ba, wato lokacin da ya fara ganin Rahinah a Jamus. Wani abu mai kama da tsoro kuma ya zo ya darsu a ran sa a dalilin maganganun yaron a kan Uwar sa.
Daga bisani ya ga bashi da mafita, domin Abdallah ya tsatstsare shi da Almondshapedidanun nan nasa irin na uwar sa, wadanda ke tado masa da tsofaffin abubuwa da ya riga ya manta da su, suka shude tun wani karni can da ya shude, amsar sa kawai Abdallah yake son ji. Sai yalumshe ido na tsayin lokaci kafin ya bude su a kan Abdallah ya ce.
"Ka yi hakuri sai gobe Abdallah, zan gaya maka ko wacece ita, amma in ka yi min alkawarin duk runtsi; ni zaka zaba a kan ta!%???.
Cikin mamaki yaron ya kalli mahaifin nasa da kyawawan idanun sa sak na Rahinah, in da abinda Abdallah ya dauko a jikin ta guda daya kwakkwara, to kwantattun idanun ta ne masu gazar-gazar eye-lashes, har sai da Habibu ya ji wani irin abu ya tsirga a zuciyar sa da ruhin sa a dalilin kallon da Abdallah ya yi masa, domin exactly irin kallon da Rahinah Omar ta yi masa dazu ne yaron yayi yanzu. Wato kallon tuhuma, amma na Abdallah mai cakudeda kauna irin ta Da da mahaifi.
Sai ya tuna idanun ta dake kallon su dazun,a bakin kofar shiga falon gidan Uncle Usman,cikin ragaita da rashin sanin abin yi%???.. gani ya ke kamar Abdallah zai zabi Rahinah ya bar shi in ya ji ko wacece ita a gare shi, shine abinda ya ke tsoro, to gashi ya ce yana son ta (from the first glance) ba tare da ya san ko wacece ita ba, ina ga ya ce masa ita ce ta yi nakudar sa?
Shi kuma yaron sai ya russunar da kwayar idon sa kasa, bai ce komai ba.
Bai ce komi bane saboda bai fahimci dalilin Baban sa na cewa hakan ba. Amma duk da kasancewar sa yaro to fa ya digawa maganar Baban sa a kan bakuwar matar nan katotuwar ayar tambaya....cewa da Baban nasa ya yi,
%???....in ka yi alkawarin ni za ka zaba ba ita ba!%???.
A haka Habibu ya samu yayi barci, ya karanta addu%??jr barci ya shafe shi sosai, lokacin ne kiran Rahinah ya shigo masa.

"Hello!%???
Habibu ya sake fada, wannan karon da kwantar da murya, jin tana numfarfashi kawai cikin bala%??j ta kasa cewa komai. Ta rasa ta ina za ta fara. A yadda ya san ta da ego da boldness, bai zaci zata kasa voicingout maganarda ke cike a bakin ta ba. Wata irin mace ce mai tsayayyar zuciya.
"In ba kira bane please zan ajiye in kwanta, ina da sammako gobe da safe%??? ya fada da harshenGerman. Maimakon Hausa ko Ingilishi. (German Language) shine harshena biyu da ya san Rahinah ta fi sabawa da shi. Wannan ya tada tsigogin jikin Rahinah, wani abu yamm! Kamar tashin tsigar jiki ya soma bin tafin kafar ta, sakamakon tuna baya. (The way he kept on%???. raping her daily a tsayin KWANAKI BAKWAI kamar ya samu kuyanga) ya dawo sharr! A zuciyar ta da yayi magana da harshen German. A wancan lokacin duk sanda ya kusance ta da harshen Jamusanci yake mata sambatu. Zuciyar ta ta tuna mata ko waye Habibu, don haka kada ta bari kwantar da muryar sa ya kassara ta ta fasa kudirin ta na kwatar Dan ta, zaluncin sa ya fi da haka.
Ba%??j kidnapping Da kawai ya kware ba, har da kidnapping zuciya da ruhin diya macen duk da ta yi hadarin fadawa hanyar sa.
Da wannan tunanin, Rahinah Omar ta kwarara kan ta, ta hanyar tattaro dukkan kuzarin ta da karfin zuciyar da ya rage mata. Hankalin ta da nutsuwar ta ta hada su wuri guda ta dunkule su cikin tafin hannun ta, ta sani kwarai cewa da babban mutum take magana a yanzu, mai amsa taken (Young Nigerian Hotelier) wanda ya kama kasa, ya ajiye Naira da kwalayen boko, ba dan saurayin dalibin nan na 'Cologne University%??? da ta sani ba. Don haka dole ta yi taka tsan-tsan. Ta kuma iya takunta.

"Kana magana da Rahinah Omar!%???.

"I%??j aware". (Wato ya sani)
In ji Habib kamar cikin rada, muryar sa na nuna halin ko in kula.
A ran sa ya ce "the happiness destroyer, the cruel lady in action, and also a heart breaker (mai tarwatsa farin ciki, muguwar mace mara tausayi ma%??jbociyar karya zuciya)!". Rahinah ta hadiye bacin ran ta, tana kara baiwa zuciyar ta hakuri. Ita ke nema a wajen sa dole ya wulakanta ta yadda ya ga dama.
Zata shanye komai in dai eventually zai bata Dan ta, gudan ran ta Abdallah ta tafi da shi gidan ta a Abuja. Ta sanya shi makaranta, su kwana gado daya suna hira, tana koya masa karatun Alqur%??jni daga kwance. Me zai fi wannan moment din dadi a zuciyar uwa? Ba abinda zai kara gama su ko a hanya (bayan ta karbe Abdallah) balle yayi mata wulakancin sa da ya gada nau%??j-nau%??j.
"Ba Hotel nake so a bani in sauka ba Yallabai, balle a zaci bara ce ko maula suka kawo ni. I don%??j care ka gane mai magana ko a%??jh?
Da na, Abdallah, wanda na haifa a kasar Jamus ba tare da taimakon kowa ba, wanda aka bi dare aka dauke mini, nake so a bani yanzu, kamar yadda Shari%??jh ta bani, cikin aminci da salama, ba tare da mun taba mutuncin juna ba ko wani thirdparty ya shiga.
In ya so idan ya balaga sai ya zabi wanda zai zauna da shi tsakanin ni da kai din, tunda haka shari%??jh ta tanadar mana%???.
%??mllah ko?%???
Habibu ya tambaya cikin izgili da shagube. Kai har da tsagwaron raini. Kafin ya ce.
"Baki san hanyar kotu bane da zaki neme ni da salamar in baki Dan ki? Na dauka komai bisa doka da doron shari%??jhr yafi bada ma%??jna? Ai Dr. Rahane kike ko wa? Ba Otorlaryngologist ba ko shugabar likitocin Najeriya da Jamus aka baki kin yi kadan ki karbi yaron nan daga hannun Uban sa. Muguwa kawai, azzaluma!!!%???.
Yana fadin haka ya kashe wayar sa. Ya cusa kan sa a karkashin filon da yake kwance a kai, zuciyar sa na hankoro a cikin kirjin sa kamar zata fito ta bakin sa.

Sabuwar soyayya ta zo ta lullube shi, tamkar numfashin sa zai bar gangar jikin sa. Tamkar ruhin sa zai bar cikin numfashin sa.
Ko me ya tuna? Sai ya dago kan sa daga karkashin filon, idanun sa sun kada sun rine, gara a ce hawaye yake da launin da suka koma. Ya dauki wayar sa ya rubuta sako (text) ya turawa lambar data kira shi yanzu.

%??melete my number from your phone Rahinah, don%??j ever attempt to call me again, daga ni har Abdallah we don%??j need you in our lives anymore!%???.

(Ki goge lambata daga wayar ki Rahinah, kada ki kara kokarin kira na, daga ni har Abdallah bama bukatar ki cikin rayuwar mu ko kadan).

Yana tura sakon ya goge lambar da sakon bakidaya.

(Saidai ashe ya goge lambar ne a kan fuskar wayar sa kadai, amma tuni kakkaifar kwakwalwar sa ta haddace lambar Rahinah Omar ba tareda yin shawara da shi ba, kamar yadda ya haddace karatun sallah a cikin kwanyar sa).

Da asubahin washegari ta gan shi at a smart pace (afujajan) babu ko wankan safe ta san wani muhimmin al'amari ya taba zuciya da ruhin Habibullahin ta. Tabawar da aka dade ba%??j yi masa irin ta ba. Habibullahin ta dan gayu da kwalisa yau babu ko wanka ya kamo hanya. Idanun sa sun yi luhu-luhu na rashin barcin daren jiya, sun kada sun yi jajir dasu.
Ilai kuwa suna gaisawa abin da Habibu ya fara fadi shi ne.
"Hajiya, ga Abdallah nan na kawo miki shi ya yi miki sallama, zan kai shi makarantar kwana a duk garin da Allah ya nufa%???.
Da jin haka Abdallah ya dago da sauri, nan da nan ya soma turjiya yana shura kafa irin na 'ya%??jan gata shagwababbu "...ni gaskiya Daddy ban yarda ba, bana son boardingschool, wallahi bana so, ni wajen Mummy zan koma gun su Yaya Musaddiq, kuma na ce maka zan koma in ga wannan balarabiyar matar baka maida ni ba%???.
Bai san sanda ya kai ma Abdallah duka ba, ji kake gab! Ya gabje masa baki, dama zuciyar a kusa take. Hajiya ta yi maza ta tare dukan don ya sauka a nata hannun amma tuni ya samu Abdallah, bakin sa saura kadan ya fashe. Habibu ya hau fada kamar ba shi ba, ta inda yak e shiga ba ta nna yake cfita ba.
Hajiya ta manta yaushe rabon da ta ji Habibu ya daga muryar sa irin haka, (he is always calm, cool and smart) amma yau ya ma manta da Hajiyar sa yake magana.
"daga yau kada a kara kai shi gidan Yaya Badiya, na hana daga yau, in dai don makaranta ne zan nemi boardingschool da ta dace da shi in kai shi goben nan, amma ya gama zuwa Kaduna, yagama har abada ba zai kuma zuwa ba".
Hajiya da sakakken baki ta ke kallon sa.
"Kan ka daya kuwa Habibullahi? Me Badiyar ta yi maka haka da zafi? Allah dai ya sa ba shaye-shayen zamani kuma ka fara ba"
Mikewa ya yi yana balle links din hannun rigar sa yadda zai ji dadin yin alwala yayi sallahn nafila ko zuciyar sa ta lafa daga tafarfasar da take yi masa, wanda ba kowa ya janyo ba sai RAHEENAH OMAR, haka kawai -kawai yana rayuwar sa lafiya ta dawo ta hargitsa shi, ba tare da ya baiwa Hajiya Kaltume amsa ba, ya sa kai ya fita daga dakin.
Duk wanda ya yi wa Habibu Nahuche farin sani kamar Badiyya da Hajiyar sa, kallo daya za su yi masa su gane daga jiya zuwa yau har wata 'yar kwarya-kwaryar rama ya yi, sabida damuwa da azabar tasowar soyayyah, ramar da ganin Rahinah Omar ce ta haifar, ya kuma tada tsohon tsumi da tsohon miki wadanda suka dade da warkewa don haka a yanzu bai san ya ya zai yi da su ba.
Haka Hajiya Kaltume ta rabu da shi ya yi alwala shi ma Abdallah ya yi, don ya tsorata sosai da dukan da Daddyn ya kai masa, wanda wani abu ne da bai taba faruwa ba sai yau, don haka sosai ya shiga taitayin sa, suka tafi masallacin gidan tare (wanda shi ya gina wa al'ummar unguwar) don samun jam'i.
Kuma har suka je masallaci suka dawo suka zauna shi da Hajiya suna sallama bai gaya mata maqasudin dalilin sa na rabo dan sa da gidan Badiya ba, Badiyar da ta zame wa yaron UWA a lokacin da yake tsananin bukatar kulawar Uwa. Hajiya Kaltume ta dube shi sosai, alal hakika a matsayin ta na uwar sa, ba ta taba ganin Habibullahin cikin kwatankwacin irin wannan birkitaccen yanayin ba.
"Ka ki gaya min me ya faru? Laifin me Badiyar ta yi muku da za ka ce haka? In duniya da amana har kana iya nuna wa Badiya iko a kan Abdallahi? In da alkawari ruwa ba zai dafa kifi ba".
Hajiya ta fada da sanyin murya.
Habibu ya yi kasa da ido, cikin kasalalliyar murya ya ce, "In tana son ganin shi ta zo nan ko ta je Lagos ta gan shi, amma na raba shi da gidan ta daga yau. Ra'ayi na ne kawai hakan Hajiyar mu, ba don sun mana wani laifi ba, ita ko maigidan ta alkhairi ne kawai tsakani na da su. Allah ne kuma zai biya su alkhairin su ga Abdallah ba ni ba".
Hajiya ta yi masa kallon, %?7oo ba ka isa ba%???, sannan ta gyada kai ta ci gaba da jan carbin ta. Daga haka ba ta kara ce masa komai ba, don ita duk abin da zai raba kan 'ya'yan ta biyun nan (Badiya da Habibu) da Allah ya ba ta tana neman tsari da shi.
Ba ta fatan 'ya'ya su raba wannan kyakkyawan zumuncin na Habibu da Yayar sa Badiya har bayan ran ta. So take su rungume juna %??ja%??jan su su dunkule su zama abu guda. Allah SWA ya yi gaskiya da ya ce (%??ja%??ja da dukiya fitina ne).
Bazata zuba ido %??ja%??ja su yi sanadin wannan zumuncin ba.

Washegari suka wuce Lagos a jirgin sama da zummar zai je ya yi masa cuku-cukun samun gurbi a (British International School) da ke Lagos. Gara shima ya hakura da ganin Abdallahn, da dai RAHINAHOMAR ta samu access din sake ganin sa!
******


DR. RAHEENAH OMAR
A
can Kaduna kuma ko kafin jama'ar gidan su tashi daga barci Rahinah ta kama hanyar Abuja a washegari. Ita kadai cikin motar ta kiapicanto, sai sharara gudu take yi kamar zata tashi sama, don tsabar rashin nutsuwa a can ta baro Baba Sahura ta manta ma tare suke. Hukuncin Allah ne kawai da kiyayewar sa ya kawo ta Abuja lafiya amma ba nutsuwar tuki ba.
Tana shiga Abuja gidan ta ta nufa, cikin gidajen likitoci na %?ljational Hospital%???, ta shige ta kulle kan ta. Ta kuma kashe dukkan wayoyin ta.
Nutsuwa ta ke so ta samu ko ya ya ne, kafin ta yanke shawarar abun yi, amma nutsuwar ta ki zuwar mata sama ko kasa.
Ta kwanta rigingine tsakiyar lallausar gadon ta da niyyar ta yi barci, ko ta samu rangwame, amma barcin ya ki zuwa shima. Gabadaya jin kanta ta ke wani irin a birkice, upset, kuma upside-down. Ko ta ki ko ta so, kuma hakan na da nasaba ne da muggan kalaman dan mutanen Nahuche a wayar da suka yi jiya, bayan wucewar shekaru goma.
To dama ita soyayya tana rikidewa ne farat daya ta koma kiyayya? A sanin ta har suka rabu bin ta yake da kokon barar SO. Yaushe wsannan son ya rikide zuwa kiyayya? Itace dai bata da tabbaci akan tata zuciyar, amma kalaman sa sun sa ta gano da gaske ba ya bukatar tata, amma ita tana da bukatar tasu (Uban da Dan sa) in su basa bukatar ta (kamar yadda yace).
Sai dai kuma ko da bukatarta ta dawowar su cikin rayuwar ta ita ce zata yi ajalin ta%??? a haka zasu kare wutsiya a zage. This self-esteem da yayi takingfor granted a baya, yanzu ta fara maintaining din sa.
Ta tuno sunan da Habibu Nahuche ya kira ta da su a karshe,
".....Muguwa-Azzaluma!!!%???.
Rahinah kamar tayi hauka, kalaman sun rikita ta, ita kadai a uwardaki sai kai da komo take kamarf zararriya tana tambayar kan ta,
"da gaske ni muguwa ce? Azzaluma ce ni? Me na yi masa na zalunci? Me na yi masa na mugun ta? Ni ban kira shi da duka wadannnan sunayen ba sai shi zai kira ni da su?
A wurin ta mata suna sarayar da ESTEEM din su akan %??ja%??ja da SOYAYYAH su bari maza su taka su son rai, su keta alfarmar su. Su danne %??jancin su da hakkokin su da addini ya basu. Hujjar su da taqamar su shine zasu zauna sabida %??ja%??jan su. Annabi SAW mai girmama matan sa ne da mutunta bukatun su, mai nuna musu soyayya ne, ya yi umarni ga mazan aure kada su zowa matan su ba tare da dan aike ba, kada su aure su bisa tursasawa, ya yi umarni da fahimtar juna kafin aure.
Wadannan su ne hujjojin ta na kin barin soyayyar Habibu ta yi galaba a kan ta, amma ba don bata son shi ko ba ta son Dan su ba. Ta fara son shi immediately bayan rabuwar su, ta yadda har ta dinga bibiyar al%??jmarin shi, amma sai bata dauki soyayyar matsayin priority ba sama da goalattainment.
A yanzu all her dreams have come true. The goals are well achieved and properly actualized. Abu biyu ya rage mata yanzu a rayuwa; soyayyar miji da soyayyar Dan ta (family life).
%??mole in yi amfani da kuduri na na biyu, da na ki da na so, in ba haka ba HABIB NAHUCHE zai sha ni basillah! Bazai bani Dana ba, sannan na cigaba da bin sa ta lalama zai cigaba ne da wulakanta ni ne da bata min lokaci.
Rahinah ta shigo garin Abuja ne daga Kaduna absent-minded don haka ta manta cewa ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login