Showing 69001 words to 72000 words out of 110913 words

Chapter 24 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

kunya, ka zauna lafiya da uwar dan ka, domin dukkan ku kuna bukatar juna%???.
Bai ce komai ba, domin duk jikin sa ya yi sanyi, sai ya samu kan sa yana mai tambayar kan sa da gaske yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa ta yanzu ko kuwa Anty ta dai fada ne don ta ji dadin bakin ta???

Daga can kasan ransa sai ya ji wani sako na amsawa da cewa "YES! Har gobe yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Irin bukatar da nisan shekaru ko tsufa ba ya taba canza ta.
Iyayen sa da %??ian uwan sa basa bukatar komai daga gare shi duk da Allah ya bashi wadata, burin su kadai ya zama cikakken mutum ta hanyar yin aure da wadda suka tabbatar ita kadai yake so.
Ko don albarkacin Hajiya, Yayar sa Badiya da Uncle Usman zai sassautawa zuciyar shi, zai karbi Rahinah da duk irin fuskar da ta zo masa; da tsiya ko da arziki. Wato duk irin rayuwar da ta zaba musu ita za su gudanar.
Aunty ce ta katse masa tunani da cewa %? nn aka zaba mata ta zauna?%???
Ya dan zakuda kafada yace %??m have no idea. The choice is her%??j (wato zabin nata ne). Tunda ni ba mazauni bane na wuri guda ba%???, Aunty ta ce,
%?na san ma Abuja za ta zaba, ko don saboda ayyukan ta%???.
Dan kyabe baki yayi irin na ba matsalar sa bane wannan.
A daren yayi musu booking din jirgin da zai juya da su Adamawa a washegari har da Mr. Rasak wanda ya nemi alfarmar halartar auren Ogan su, don Aunty ta gaya masa tun jiya da ya dauko su.
%??malan bai gaya muku cewa ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????shi ango bane ko? Maman Abdallah za ta dawo!%???.
%??mongratulations Oga, congratulations Boss!%???
Inji duka ma%??jikatan gidan.
"May yours be among the best!".
Kowa sai da ya fadi irin fatan alkhairin sa, domin hakika sun yi farin ciki.
Washegari tun sassafe gabadayan su suka biyo Arik-Airdaga Ikko zuwa Adamawa.
******





ADAMAWA, GIREI
A
saukar sa a Adamawa, ba abinda ya fara zuwa ran sa illa, da ya samu nutsuwa abu na gaba da zai sa a gaba shine zai samar da Nahuche Hotel a jihar Adamawa, tunda Adamawan ta zama wani bangare nasa yanzu.
Ita ce tushen mahaifiyar Abdallah kuma garin kakannin sa na wurin uwa, ko don su samu wurin sauka idan suka zo garin. Ilyasu Uncle ya yiwa waya, ya dauko motar sa da ya bari a Girei ya zo ya dauke su zuwa Girei. Basu tsaya a ko%??jna ba sai kofar familyhouse din su Rahinah, wato gidan Sarkin Fulani.
Tuni labari ya riski jama%??jr gidan, da ma ita Rahinar kan ta, cewa Angon Rahinah ya iso daga Lagos. Safeenah ce ta shigo mata da wannan labarin, wanda ya sa ta saurin runtse idon ta a ahankali tana ambaton sunan Allah. Ba don ta yi farin ciki da zuwan nasa ba sai don faduwar gaban da ta bakunce ta.
Tana so ta tambayi Saffeenah ko tare da yaro Abdallah suka zo? Sai dai ta daure ta yi fulako ta yi shiru.
Yau wace rana ta gwada kawaici akan Abdallah. For the first time a tarihin rayuwar su da ta ji zuciyar ta ta dan rankwafa akan Habibu Nahuche, tunda dai har ya sauke girman kan sa ya biyo ta garin iyayen ta.
*****

S
ai biki ya koma sabo dal sakamakon zuwan Angon. Dan Nahuche jikan Nahuche. Habib, Mustapha, Bilyamin Nahuche. Biki yayi biki, biki irin na fulanin Girei wadanda suka hade da Zamfarawa suna nuna musu irin nasu culturesandtraditions din, wannan ya sa mutanen Nahuche suka dauki aniyar in suka dau amarya zuwa Zamfara sai sun kai ta har garin Nahuche ta gaida Kekun Nahuche da Uban Dawakin Nahuche suma su nuna irin nasu al%??jdun. Tunda burin iyayen Rahinah shi ne su nuna ita %??iar asali ce %??iar dangi ce suma dole su nuna Habibu dan asali ne dan dangi ne, ba%??j fi su jela ba baza%??j fi su iya taka rawa ba, kamar yadda ba%??j fi su kwarkwata ba baza%??j fi su iya susa ba.
Allah kadai ya san irin farin cikin da duk family din nan ke ciki na kowanne bangare. Habibu kuma da zuwan sa ya bude bakin aljihu ga dangin amarya da iyayen ta, komai sai da aka sauke mota guda tun daga kan ruwan sha. Lemo kuwa kamar a wanke gidan sarkin Fulani da shi. Kaji da zabbi kamar a tuka a yi tuwon su. Mutanen Girei sun dade basu ga biki irin na Rahinah ba, gashi dai a al%??jdance aka yi komai babu surkin modernity, amma komai ya wadata sannan tun daga fara bikin har zuwa karshen sa traditionalattire wato kayan saki na gargajiya Rahinah ke sawa irin na Fulanin usli, wadanda cousins din ta %??jammata sa%??jnnin ta suka kakkawo mata matsayin gudummuwar su.
Habibu da Rahinah basu hadu ba ko sau daya a garin Girei, sai ana I gobe za su wuce Zamfara. Aunty Badiya ta yi kokarin su hadu, ko sau daya ne su gaisa a Girei, kowanne ya nuna mata ba ya bukatar hakan.
Yau kuma da suka hadun, Sarkin Fulani ne ya kira kowannen su da kan sa zuwa turakar sa, kusan a tare suka iso, Rahinah ta sha ado, sanye da wata guntuwar rigar Karen miski ruwan hanta, ta yi dauren zanin daga can saman cikin ta ta yi lullubi da yalwataccen mayafi fari, an yi mata wadansu irin kananan kitso wadanda aka lankwaso jelar su ta gaban goshin ta zuwa bayan kunnen ta, kitson ya saka fuskar ta tayi fresh tayi cute da ita ya fito da kyawun fuskar ta na halitta. Kan ta babu kallabi sai lullubin babban mayafin da ta yi.
Habibu sanye yake da yadin voyel mai taushi fari sol, da gani yau ya soma saka su, %??iar ciki da babban riga wanda aka yi wa sassaukan aiki da farin zare. Komi nasa a saukake, kwalliyar sa mai sanyaya idanu, amma kallo daya zaka yi masa ka san ya kama kasa, kuma komai da yake sanye da shi mai daraja ne. Sassaukar rayuwa ra%??jyin sa ce kawai amma kada kaso ka tona tsadar sittiru da takalmin da agogon da ke jikin sa.
Tana saka kai a kofar dakin sarkin Fulani shima yana sawo kai, saura kadan su yi karo da juna, itace ta yi saurin ja da baya ta bashi hanya ya fara wucewa bayan sun jefi juna da mummunan kallon da kowanne ya kunshe cikin idanun sa.
A ran ta ta ce %?&nmh, mutum har mutum, fuska da zubi irin na salihai amma halin sa da zuciyar sa irin na mutanen farko (jahiliyya period).
Shi kuwa Habibu gani yayi gabadaya Rahinah ta canza a idanun sa, kuruciya ta karu mata, duk ta danyance masa kai bazaka ce ta taba haihuwa ba, balle katon yaro kamar Abdallah mai neman cika shekaru goma sha biyu. Kwatankwacin abinda ta fada a tata zuciyar shima haka ya fada a nasa ran, kamannin ta, innocent fuskar ta, zubin halittar ta duk basu yi kama da behaviours din ta na rashin tausayi ga mijin auren ta, na rashin compassion a zuciya da rashin karbar kaddara.
Ta fi kama da salihan mata masu sanyin rai, masu tausayawa da tallafawa mijin auren su, ba kamar nata halayen na zahiri ba. Ga ta stubborn ga ta unforgiving and wicked.
%??mu shigo daga ciki%??? inji sarkin Fulani, suka zauna suna fuskantar sa shi yana daga gaban su, sai da ya tabbatar sun bashi dukkannin nutsuwar su sannan ya fara da addu%??j suka shafa, kafin ya maida hanklin sa kan Habibu Nahuche.
%??muk abinda ya faru da ku a baya, mun ji labarin sa, Ambasada ya gaya mana. Ina so ku dauka kaddarar ku kenan ta haihuwar wannan yaron, don haka ku maida komai ya zama tarihi, ku fusknci rayuwar da zaku fara yanzu.
Habibullahi na aika an kirawo ka ne domin in baka amanar marainiyar Allah RAHINATU wadda Allah ne ya hada ku ba mu muka hada ku ba, bata da uwa bata da uba a duniya sai mu da muka rage a raye, idan ka cutar da ita Allah ba zai barka ba.
Ke kuma Rahin, kin gama sanin gidan nan ba%??j yaji, ba%??j kawo kara, sannan ba%??j zawarci. Don haka ne ma bana gaggawar aurar da %??ia%??ja na sai ga mazan da na tabbatar suna son su kuma zasu rike min amanar su ko bayan rai na. Sannan ya zamanto cewa soyayya ta hada su ba tursasawa ba.
Saboda haka na hore ki da yi wa mijin auren ki biyayya da zama uwa ta gari ga %??ja%??jan ki. Mahaifiyar ki matar kwarai ce mutuniyar kirki ce da har ta koma ga mahaliccin ta babu wanda ya taba jin kan su ita da Modibbo Ummaru.
Bai taba kara aure ba sai a bayan ranta, inda ya auri Kulun da ta yi sanadin barin ku gida har duka wadannan kaddarorin suka faru%???.
Habibu ya muskuta kadan, murya cikin sanyi yace %?:oacece Kulu?%??? Sarkin Fulani ya bashi labarin komai daga farko har karshe har yadda Rahinah ta hadu da su ta sanadin Yafendo, Habibu ya saci kallon ta kadan, (she have never know her parents), sai yaji tausayin ta kadan ya kama shi, gara shi ya girma da Hajiyar sa har gobe yana jin dadin ta, ya dukar da kai yana magana a hankali,
%?na karbi amanar ka da hannu bibbiyu Baba sarki, Allah ya bani wuyan dauka da hannun saukewa%???.
Kawai sai Rahinah ta ji kuka ya zo mata. Wanda tun fara bikin bata yi shi ba. Don a baya komai ganin sa take kamar almara ko mafarki wanda anjima kadan za ta bude ido ta ga ba haka ba. Amma yanzu da Habibu yayi Magana da bakin sa ta yarda ta amince zahirin kenan.
Ta sake zama matar Hotelier (Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche). Bambancin shine wannan auren ba irin na baya bane, wannan auren na mutunci da daraja ne, ya aure ta ne a hannun iyayen ta da kakannin ta, aure na adalci da martaba, to amma anya sauran tabban nasa da lahanin da ya yi wa zuciyar ta zasu taba gogewa daga zuciyar ta?
%??mu ta shi ku je, suna jiran ku za ku wuce. Allah yayi muku albarka%???.
Nene Balki da Inna Dudu ne suka shigo dakin sarkin Fulani suka tafi da ita, a motocin Nahuche Hotels zasu wuce zuwa Zamfara wadanda tuni PA Rasak ya sa an kawo su manya-manyan Highlanders har guda 4. Sai wadanda %??ian Nahuche suka zo a ciki dama ba su koma ba.
Wadanda Mr. Rasak ya kawo matan sarkin Fulani su duka hudun aka dauka a ciki da %??ia%??jan su mata, cousins din Rahinah da sauran %??ian uwan su aka dauka a ciki. Rahinah da Nene da Aunty Badiya da Inna Dudu suna mota guda, a gidan gaban motar kuma matar Baban Nahuche ce haka suka kama hanya daga Girei zuwa Zamfara.
Habibu da PA din sa tare da Uncle da yaran sa suka wuce, suna tafe a hanya yana ta buge bugen waya yana bada order na yadda yake so PA Mr. Atiku ya tsaya a kan gyaran gidan sa na %?riife Camp%??? duk da gidan baya bukatar komai, amma yanzu mace ce zata zauna a cikin sa akwai bukatar abubuwan da babu cikin gidan. Su Uncle kuma sun ce ya basu dakuna zasu zuba kayan gado da kicin zasu zuba mata kayan girki. Yana ta gargadin PA Atiku kan ya tsaya ya ga cewa komai (is in place). Uncle na ta sauraron sa a fakaice yana ta mamaki, in ya ji kudaden da ake ta ciniki na abubuwan da za%??j sa a cikin gidan. Murmushi yayi, a ran sa ya ce,
%?nannu sannu ai bata hana zuwa saidai a dade ba%??j je ba, yaro wa ya gaya maka Borno gabas take? Wa ya gaya maka ana yi wa matan gidan mu pretending?
******







KOFAR JANGE, ZAMFARA
U
nguwar Kofar Jange ta karbi bakin motocin wajen guda goma a jere da yammaci lis, lokacin da majalisar samarin Kofar Jange ta ke cikke taf! Kamar kullum. Nan da nan samarin masoya Habibu Nahuche suka soma tambayar junan su ko me ake yi? Don kafin isowar motocin wani makwabcin Hajiyar Nahuche ya kawo musu labarin akwai fa kishin-kishin din cewa NAHUCHE ya yi aure duk suka karyata shi, ta yaya zai yi aure bamu ji a media ba? Bayan kwanannan suka gama shari%??j da tsohuwar matar sa a Abuja?
Sai ga wadannan bakin motocin nata fakewa a kofar %??mIDAN NAHUCHE%???.
Mata ne suka rika fitowa kafin su fito da amarya nannade cikin alkyabba, suna shiga gidan Hajiya Kaltume, ai kuwa nan suka gasgata labarin da Kalla ya kawo suka gwale shi, nan wajen ya kaure da sowa da surutun su.
Dai-dai da isowar sa cikin motar karshe, motar Alh. Usman Girei. Suna yin fakin samarin na yanyame motar fadi su ke;
%??mllah ya bar mana NAHUCHE%??? %??mllah ya taimaki NAHUCHE%??? shi kuma sai murmushin da ya saba ya ke yi (broad smile) cikin ginshira irin tasa. Ya kawo ihsanin da ya saba yi musu ya yi musu bayan ya basu hannu daya bayan daya, abinda suka samu yau ya zarta na kullum shikan sa bai san dalili ba, don ba zai ce farin ciki yake ba.....addua suka shiga yi a kan auren da suka samu labarin ya yi, tare da roka masa zuri%??j mai albarka.
Wannan daban.

Kasancewar Gidan Hajiya Kaltume babban gida ne mai wadatattun dakuna don haka tsaf ya dauke bakin Nahuche da na Girei. Aunty Badiya bata zauna ba suka shiga hidima ta bajinta da surukan su. Sabida yadda gidan ya cika da mata Habibu bai samu ganin Hajiyar sa ba suka wuce Hotel shi da su Uncle da PA Rasak.
Har dakin Haj. Kaltume su Nene suka kawo Rahinah, aka bada amana ta ce Allah ya taya mu riko. Yau ga Hajiya ga Rahinar Habibu! Duk da bata yi nasarar ganin fuskarta ba daga goshin ta da sumar ta ka san kasaitacciyar mace ce dole Habibu ya kasa aure akan wannan bafullatana.
Duk yadda suke boye maganar auren don kada %??ian jarida su samu a daren ranar ta yadu a garin Zamfara, kasancewar Habibu sananne kuma fitacce wanda kiris a ke jira a kan sa. Washegari bayan kowa ya karya ya kuma kimtsa motocin suka sake kwasar su zuwa Nahuche.
A Nahuche 'yan Girei sun ga karramawa inda aka kai ta gidan su mahaifin sa kowa nasa ya zo ya gan ta, ya sa albarka, kowa sai Masha Allah yake ambato matar Habibu ta kai ta kawo, daga nan suka wuce fadar Nahuche suka gaida Kekun Nahuche wanda amini yake ga Kakan sa Bilyamin Nahuche.
Kwanan su daya a Nahuche suka wuce da amarya gidan ta.
******





ABUJA (Life-Camp)
G
idan Habibu na nan a sabuwar unguwar Life-Camp wadda ke gaba kadan da Gwarimpa. Madaidaicin gida na zamani zubin (Pent House) mai hawa biyu wato sama da kasa, Habibu ya dauko samfur din sa ne daga kasar Jamus bai jima da kammala ginin sa ba. Ba kasafai yake zama agidan ba idan yana garin Abuja rayuwar sa ta fi yawa a %?tiahuche Hotel%??? na garin Abuja. Rahinah could%??jbelieve cewa yau ita ce a gidan miji, mijin kuma ba kowa ba face her ex husaband; Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche. Wanda ta sha cin alwashin har abada bazata koma masa ba.
To an ce kana naka Allah na nasa kuma na san shine gaskiya. Bawa bai isa ya tsarawa kan sa rayuwa yadda yake fatan ta ba.
A yau da ta daga kai ta yi duba ga al%??jmuran duniya bakidaya, sai ta ga cewa (nothing is constant), komai canzawa yake kamar wahainiya, kuma rayuwar kanta garawa take da gudu kamar gare-gare abin wasan yara. To haka al%??jmarin ta da uban dan ta ke nasa juyin cikin hikima da iradar Ubangiji. Yanzu kam ta yarda ta amince a cikin kundin kaddarar su, har da na sake zama da juna.
Abinda bata da idea a kai yanzu shine irin zaman da zai gudana tsakanin ta da Habibu Nahuche. Wani kwayan mutum guda daya da ke ta walagigi da duniyar ta (for almost a decade) tun haduwar ta da shi a jirgi. Har gobe, har jibi har gata zuciyar ta ta ki aminta da shi, ta ki kwanciya da shi a kan nakasu guda daya, a kan laifin baya, ta ki yarda soyayyar sa isgenuinekuma soyayya ce yake mata ta tsakani da Allah.
Kullum da abubuwan da baudaddiyuar zuciyar ta ke gaya mata daban - daban akan sa, wanda laifin sa na farko duk shine sila, mafari kuma tushe na sanya duhun sa a zuciyar ta, duhun da ya lullube soyayyar da ke kwance lambam, ta zabi su kare rayuwar su cikin challenging juna.
Su Nene da sauran %??ian uwan ta na Girei basu kwana gidan ba duk suka juya gidan Ambasada a daren, inda a can za su kwana, washegari kowa ya koma inda ya fito, cike da farin cikin an yi biki lafiya an kare lafiya.
Ita kadai tsakiyar makeken gadon ta wanda Uncle Usman ya yi mata, ta saka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login