Showing 39001 words to 42000 words out of 110913 words

Chapter 14 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

Musaddiq ke gayyatar ka get together dinner iya mu i'mu na gama degree din Musaddiq and zaa yi hotuna da bidiyo don tarihi, don haka presence dinka is very vital".

Habibu ya yi dan murmushi, zumunci da 'yar uwar sa ba ya hada shi da komai, don ba shi da wanda ya fita a duniya bayan mahaifiyar su. Ya ce, duk muhimancin uzrurrukan sa yana bari sabida hidimar Aunty Badiya da iyalin ta.

"Zan yi squeezing time don ina da muhimman abubuwa a gabana a weekend din nan".

"A bar komai a zo mana, in babu kai abin ba zai yi armashi ba".
"I know Maman Abdallah". Da haka suka yi sallama.


Kusan a tare Habibu Nahuche da Raheenah Omar suka shigo garin Kaduna, shi a jirgi daga Lagos, ita a motar ta daga Abuja. Sahura na gefen ta tana zuba mata hira, amma ga mamakin ta ta kasa ce mata komai. Yau jin kan ta ta ke kamar an dinke mata baki, an cire dukkan kuzarin ta. Ba ta san hakikanin abin da ke damunta ba.

Raheenah ta riga Habibu isowa gidan Uncle, kuma kai tsaye sai ta wuce dakin ta na gidan ta kwanta, don duk yaran gidan Aunty ta kwashe su ta kai su gidan aminiyar ta a Malali, ta ce sai takwas na dare za ta turo a dauko su. Musaddiq ne kawai a gidan, don haka bayan sun gaisa da Aunty ta ce ba ta jin dadi, kwanciya za ta yi kamin Uncle ya shigo gida. Da ma kuma tana hutun sallah.

Ba a fi awa guda da kwanciyar Rahinah ba Habibu ya iso, karkashin rakiyar ma'aikatan Nahuce Hotel na garin Kaduna, wadanda suka dauko shi daga filin jirgi. Motoci uku jibga-jibga kamar su fashe don koshi da sheki, kowacce dauke da logo na NAHUCE GROUP OF HOTELS. Sanye yake cikin (black-grey-German-Suit) wadda ta fiddo zahirin ilhama da cikar zatin sa, kwarjininsa ya fiddo zahirin matashin miloniya mai tashe, HABIBU MUSTAPHA NAHUCHE wanda kallo daya za ka yi masa ka tabbatar Allah ya gama yi masa kowacce irin ni'imar rayuwa.

Kallo daya ba zai gamsar da idon ka a kan HABIBU NAHUCHE ba, ba tare da marmarin ka yi masa kallo na biyu ba. Idaniya ba sa taba gajiyawa da kallon sa sabida wani sassanyan sirrantaccen kyau da haiba da Allah ya yi masa.

"The successful business tycoon of Zamfara".

Kamar yadda kafafen yada labarai ke kiran sa.

Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche, ya fito daga motar hotel dinsa yana taku majestically, zuwa cikin gidan Aunty Badiya.
Musaddiq ne ya fara taren sa a bakin kofar shiga falon, da runguma mai karfi yana fadin.

"Welcome Uncle Habib!"

Muryar Musaddiq ce ta fiddo Aunty daga kicin, murmushi fal bakinta ta ce, "Ban zaci za ka sauka haka da wuri ba. Musaddiq ka je ka taho da su Abdallah".

Musaddiq ya ce, "Aunty da kin kyale Abdallah sai Uncle ya ci abinci ya huta, yana zuwa zai ishe shi da zance da dumi ba comma ba full-stop".

Aunty ta ce, "Sai kuma Uncle din ya ce maka bai son ya cika shi da dumin? C'mmon je ka dauko su maza gidan Anty Hassu".
Habibu na jin su amma rabi-da-rabi don hankalin sa ya tafi ga wayar da yake ta amsawa akai-akai.

Kafin dawowar Musaddiq Uncle ya dawo, ita kuma Aunty da mai aikin ta ba su zauna ba sun dukufa shirya abinci bisa makekiyar darduma da aka shimfida a falon Uncle. Fita goma ko shiga goma za ta yi sai ta kalli Habibu ta yi murmushi, ba abin da ta ke tsananin so irin ganin reaction din da zai nuna idan ya ga Raheenah yau a gidan ta. Ko za a kashe ta ta san Raheenah ce ta farko, kuma ta karshe a zuciyar Habibun, ko da kuwa su duka a yau sun nuna musu ba su taba sanin juna ba.

Uncle Usman ya bi Aunty kicin ya ce, "Tana ina ne?"

Aunty ta yi dariya ta ce, "Tunda ta zo, tana daki a kwance ba ta fito ba, kamar wadda aka yi wa duka".

Uncle ya girgiza kai ya ce, "Bari in je in yi serving din sa abinci ya ci, idan ya gan ta ba zai iya cin abinci ba, ga shi ban san yadda kowannen su zai karbi dan uwan sa ba".

Ya juya ya fito, ita kuma Aunty ta hau kiran Musaddiq a waya don ta ji ko sun taho?

Uncle da kan sa ya zuba ma Habibu duk abin da Aunty ta dafa a kan plate guda yana ta jan shi da zance yana loda abincin a kan faranti har sai da Habib ya ce, "Abincin nan ya yi min yawa fa!".
Uncle Usman ya ce, "So nake ka tada komada daga wannan ramar taka, kai kenan kullum kamar a bushe ka fadi?"

Murmushi ya yi, ya ce, "Yaya dan Adam zai yi kiba alhalin rayuwar sa ba ta taba hutawa ba? Kullum cikin kujuba-kujubar nema yake, sannan babu iyali a gefe wadanda taimakon su zai sa ya yi kibar?"

Baban Musaddiq ya ce cikin halin ko'in kula,
"I can relate, I see".
Sannan ya tura masa plate din abincin gaban sa. Bayan ya aza cokali da fork akai.
Gab da zai gama cin abincin Abdallah da Zarah suka shigo, Abdallah ya yi kan sa da mugun gudu yana,
"Daddy na, oyoyo!"Ya rike shi sosai cikin jikin sa tamkar zai maida shi cikin sa yana sunsunar sa, ya ce, "Junior, me ka ke ci haka? Ni girman ka tsoro yake ba ni".
Dariya Abdallah ya yi daidai lokacin da Aunty ta shigo, ta ce, "Junior, je ka dakin Zarah za ka ga bakuwa tana barci, ka taso ta, ka ce ta zo in ji Daddy ya dawo".

Da gudu Abdallah ya fita don shi yaro ne mai bin umarni, yana fadin, "Daddy kada fa ka je ko ina, yanzu zan dawo".
Aunty ta zauna gefen Habibu tana yanka mishi apple, Daddy kuma na diban sa da zance.

Barci ta ke sosai, lokacin da Abdallah ya shiga dakin. Yatsun kafarta ya hau ja yana fadi da karfi, "Bakuwa ki taso ki zo in ji Maman mu, Daddy ya dawo".

Kamar a mafarki 'yar siririyar muryar yaron ta ke ratsa kunnuwan *Rahinah Omar.* Jin muryar ta yi tamkar busar sarewa cikin kunnuwan ta, ga shi sai kara maimaitawa yake yi. A hankali ta ke bude fararen idanun ta, wadanda barci ya sa suka canza launi tana kallon kyakkyawan yaron. Har idanun ta suka gama washewa sosai a kan sa.

The cute face looks so familiar... and the feelings for him is not a strange feeling. Abin nufi ji ta yi ba yau ya ginu a zuciyar ta ba. Wani daddadden feeling ne wanda babu irin sa (maternal love) irin wanda kowacce uwa ke da shi a kan dan ta, walau ta san shi ko ba ta san shi ba.

Amma a halin da ake ciki, Rahinah Omar ta ji kaunar yaron ne kawai a ranta ba tare da ta san daga ina kaunar ta keto ta fito daga karkashin zuciyarta ba.

Murmushi ta yi masa, sannan ta yunkura ta tashi daga kwanciyar ta sa hannu ta yafito shi. Matsowa ya yi gaban ta ya tsaya, a kintacenta zai yi shekaru goma, amma ba ta taba ganinshi cikin gidan ba, don haka tunaninta ya ba ta shi ne Junior da suke yawan ambata. Hannu ta sa a kan lallausar sumar kansa ta ce,

"Kai ne Junior?"

Gyada mata kai ya yi, sannan ya juya zai fice.
Raheenah sai ta samu kanta da cewa cikin rawar murya,
"Junior ya ya sunanka na gaskiya?"
Sai da ya kai bakin kofa zai fice ya juyo ya ce,

"Sunana Abdallah Habibu Nahuche!!"

"ABDALLAH NAHUCHE!!!

Rahinah ta maimaita a fili. A ina ta taba sanin wannan sunan?
Tamkar wadda aka fizga a zuciya ko kuwa aka tsikara sai ta samu kan ta da mikewa wuf! Ta bi bayan sa ko kallabin ta ba ta tsaya daurawa ba.

Dakin Aunty Badiya ta fara zuwa, babu kowa! Da sauri ta fito zuwa inda ta jiyo tashin muryoyin jama'ar gidan, wato falon Daddy.

Nan ta tadda su complete family yadda sukan zauna koyaushe. Amma a kusa da Aunty a tall, giant, handsomeman, ya bata baya, wanda duk hayaniyar da ke tashi a falon babu tashin muryar sa. It's either kamar bai falon, ko kuma akwai abin da yake yi da ya hana shi magana. Waya ce a hannunsa yana daddannawa, sallamar Rahinah Omar ta sanya shi wani irin dagowa in a slow motion.

Ita kuma ba tare da ta lura da shi ba ta nufi inda Junior yake can gefen Musaddiq yana ta zuba masa zance. Tamkar wadda ake controlling da remote haka ta nufi gurin yaron absentmindedly ta tsugun na a gaban sa, tafin kafarsa ta kama tana son tantance abin da ke cin ta a zucci.

Tawwadar Allahn data ke son gani tana nan a kan babban yatsar kafar sa, sai girma da fadi da ta kara.

"ABDALLAH!"

Habibu ya fada da karfi tamkar ya ga wani abun da zai cutar masa da Da. Irin tsugunnon da ta yi a gaban yaron, irin sa ta yi a gaban Ambasada Shehu Bichi tana rokon sa ya karbar mata 'yancin ta daga hannun sa. Bafullatanar mai yawan sumar kai, da hasken fatar da ko a cikin farare ita fara ce lamba daya tsugunne gaban dan sa, wadda cikin kowanne hali ba zai kasa gane ta ba, image din kyakkyawar fuskar ta ba zai taba gushewa daga zuciya da kwakwalwar sa ba.

Balle ma cikin shekaru goman da suka gabata, canjin da Rahinah Omar ta samu na halitta ba wani mai yawa ba ne. Canji ne kawai irin wanda nauyin shekaru ke haifarwa diya mace ba tare da ya canza appearance na kuruciyar ta ba. She is still that ravishing, glowing and sparkling lady fiye da yadda ya baro ta a Germany.

Sai ma wata 'yar kiba-kiba da ta kara mai nuna sukuni, wadata da kwanciyar hankalin da ta ke ciki.

Kiran da Babansa ya yi masa haka da karfi ya firgita shi, don haka da sauri ya kwace kafar sa daga hannun Rahinah ya nufi baban sa yana buya a bayan sa.

"Daddy boye ni, ni ma ban santa ba".

Ya yi daidai da lokacin da Rahinah ta juyo, ta sauke ragaitattun idanunta a kan Habibu Nahuce, wanda ke kallonta babu ko kiftawa. Her Ex- Habibu ne! wanda ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane shi ba, balle dan da ke tsakaninsu.
Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Habibu Nahuche da Rahinah Omar, kallon da ke rewinding duka incidents din shekarun can baya a Jamus, abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun su.

A take Rahinah ta soma ja da baya cikin tsoro da kidima. Tsoron da ya haifar mata da karkarwar jiki da ta zuciya, amma ga Habibun, ba zan iya cewa ba.

Domin kuwa bayan idanun sa sun farfado daga shock din ganin ta a inda bai taba tsammani ba, wato a gidan Yayar sa, ya kara yi mata kallo na biyu, kallon da ya tattaro duk wani kundi da ya lullube a karkashin zuciyar sa. Ya bude shafukan sa filla-filla, shafukan tun shigowar Raheenah cikin rayuwar sa, and the roles she played in shattering it (da rawar da ta taka wajen yagalgala ta).

Eh, ya kira shigowar ta cikin rayuwar sa ba komai ba sai kacaccala ta (shattering dinta into pieces) tunda har yau ga shi nan a gantale bisa titi yana ragaita babu iyali, in an kuma bi salsala wannan bafullatanar ita ce sila.

Domin kuwa soyayyar ta ce har gobe ke azabtar da shi ko na second daya bai taba hutawa ba. The marital physical relationship din da ya wanzu tsakanin su, will forever remain green a zuciya, gangar jiki da kwakwalwar sa, wanda ya dusar da hasken duka sauran mata daga idanun sa yake musu kallon ba bambancin da nasa jinsin, sai ita kadai ce mace a idanun sa.
Ba zai gaji da cewa ba Rahinah Omar... ta tafi da dukkan farin cikin sa, sannan dawowar ta a yau ya san yana nufin abubuwa da dama in bai yi wa tufkar hanci ba.

Tunda ita tamkar mala'ikar daukar rai ta ke, ba ta zuwa ta tafi, ba tare da ta kashe zuciyar mutum ba.

Ta zame masa tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba ALHERI ba.

Yana cikin tattala 'yar ragowar rayuwar sa da ta riga ta kashe ya samu control din ta a yanzu, shi ne kuma ta dawo cikin rayuwar sa ta inda bai zata ba.

A wannan karon, a wannan lokacin, a wannan 'yan dakikan, Habibu Nahuche, ya kudiri aniyar yaki da dawowar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Ba zai bari ta sake yin galaba a kan sa ba. Ko da wacce ta zo zai tarbe ta kyakkyawar tarba irin ta yakin ceton rai.

Ko da ma can ya san tana existing a garin Abuja matsayin cikakkiyar *otorlaryngologist* din National Hospital da NIZAMIYE. Yadda aka yi ta zo gidan Yayar sa ne bai sani ba, watakila wani ya gaya mata ga inda dan ta yake shi ne ta zo, za kuwa ta sha mamaki in ya ce mamaki, yana nufin mamaki mai gigita kwanyar diya mace. Domin daga yau Abdallah zai bar gidan Badiya.

Hannu ya sa ya janyo Abdallah da ke faman buya a bayan sa, ya yi masa kyakkyawar mafaka a kirjin sa, ya rungume shi sosai idanun shi a lumshe.

"Don't be afraid Abdallah, I'm here with you babu mai taba ka sai ruwan sama".

Daga nan ya mike tsaye rike da hannun yaron, kyakkyawan kallo na biyu wannan Rahinah Omar ba ta samu daga gare shi ba,

"Maza Abdallah debo kayan ka tafiya za mu yi".

Daga Aunty Badiya har Daddy bin sa suka yi da kallo, kallo na mamaki. Domin ba haka suka yi zato ba.

Yayin da Dr. Raheenah ta sunkuyar da kai, hawaye fal idanun ta. (Between happiness and excitedness) ba ta san wanne ta ke dulmiyewa tana nutso a cikin sa ba. Abdallahnta... her only son Abdallah... after a decade, yau shi ne tsaye a gaban ta gidan Uncle din ta.
To ta ina ya zo? Wannan na nufin... shi ne Junior din, dan kanin Aunty Badiya... wannan na nufin Habibu Nahuche... shi ne kanin Aunty Badiya... Ta wani irin lumshe idanun ta a hankali, tsigar jikinta na tashi, ko kafin ta farfado daga shidewar wucin gadin da ta tafi, babu Habibu babu dan sa Abdallah a falon.

Ta ina za ta bari Abdallah ya sake kubuce mata A KARO NA BIYU? Ai ko yakin duniya na biyu ( *World War II* ) za su yi ita da Habibu wannan karon sai ya ba ta dan ta!!!.

Da gudu-gudu ta bi bayan su tana kiran sunan "ABDALLAH". Yayin da jamaar falon duka suka bi su da kallo. Ba ta cimmasu ba sai a harabar gidan yana kokarin saka katuwar jakar kayan Abdallah a bayan jibgegiyar motar da ke ajiye a ma'adanar motoci.

Sai ta rasa kwarin gwiwar karasawa gare su, sabida kallon dibar karen mahaukaciyar da Habibu ya yi mata, ta tsaya daga bakin kofar shiga falon Daddy Usman tana kallon su kawai suna shiga mota, kaunar Dan ta na kara bunkasa a zuciyar ta kwatankwacin ta ranar da ya zo duniya, hanyoyin da zata bi ta karbi Abdallah ta take tunani, koda hakan shine *struggle* na karshe da zata gudanar a rayuwar ta. Daga nan har *supreme* *court* ! Wato kotun *daga ke sai Allah ya isa!!!*


Ganin sa da ta yi yau matsayin kanin Aunty Badiya matar Baban ta, ta san Allah ke nufin farawar sababbin al'amura da dama a gare su, wadanda a iya kintacen ta da tsinkayen ta bata hango farkon su balle karshen su ba. Na baya duk shimfida ne, wato wanda ya faru a Jamus, yanzu ne zasu fara ta babu dadi ita da dan mutanen Nahuche. Domin ko sama da kasa zata hade sai ya bata dan ta.

Abu daya ta sani shine (maintaining self-esteem) din ta yanzu ta fara, ko da soyayyar ita ce ajalin ta, amma tana da right din ta na rikon Abdallah wanda addini da shari'ah suka bata har sai ya balaga in ya so ya zaba tsakanin ita da shi.

Idan a da bata da gata shi yasa yake walagigi da ita da dan ta yadda yake so to a yanzu tana da gata kamar koma fiye da kowa. Sannan ta tsaya da kafafun ta, ta wuce wargin kowanne da namiji. Wata fuskar......yanzu ta fi gaban Mari. Don haka ita da Habibu a je zuwa..wai mahaukaci ya hau kura



*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI KE CEWA, MU KARASA LABARIN "NAHUCHE. (DAGA FUSHI NA) A LITTAFI NA 3 NAN BA DA JIMAWA BA INSHA ALLAHU.*
20/2/2022

: *SUMAYYAH ABDULKADIR*



*NA HUCE*

PAID BOOK




Daga wannan kallon shakulatin bangaron da ya yi wa Rahinah, Habibu ya ja hannun yaron ya saka shi a gaban mota ya rufe har da murza key, ya zaga daya bangaren ya shige ya rufe, ya yi juyi (reverse), ya ci taya sannan ya zugi motar da mugun gudun da ya sa Maigadi wangale masa kofar ba shiri, saura kadan ya bi ta kan yatsun Hashimu mai gadi.La-shakka da dai a ce ba (interlocks) ne a wurin ba da Habibu ya bule Rahinah da kura, kurar da watakila in ta koma cikin gida baza su gane ta ba. Shi kan sa Abdallah ya tsorata da wannan jan mota da Baban sa ya yi kamar za su tashi sama, kamar zai bar Kaduna dasu a mota zuwa birnin Sin.

Sai ta tsaya daga inda take tsaye cikin mutuwar jiki, da matsanancin bacin rai,gawaniirin sagewar guiwa da ya same ta duk a lokaciguda, tana mamaki da al'ajabin abin da Habibu ya yi mata kamar ko a hanya bai taba sanin ta ba.
Tadade da saninkobajimako ba dade watarana dole zasu hadu tunda Abdallah ya riga ya yi tying alaqar da bazata kankaru har abada ba, amma bata zaci in sun hadun irin reaction din da zai nuna kenan ba. Ai ko Habibu bai taba sanin ta ba yau ya fara ganin ta ba zai mata wannan wulakancin da tozarcin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login