Showing 3001 words to 6000 words out of 110913 words

Chapter 2 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ya yaye, jirgi ya daidaita akan hanyar shi, ba jimawa suka sauka a birnin Cologne, Germany.

Kunyar abinda ta aikata kuma ta zo ta lullubeta, ta kasa sake hada ido da shi, ta nemi hanya ta sulale abin ta, cikin nasihohin Daada kafin ta taho har da cewa kada ta yarda jikin ta ya rabi na kowanne namiji haramun ne in ba mijin auren ta ba, yau ba raba ba kadai ta kankame namijin da bata san daga inda yake ba, tana tafe tana waige-waigen neman abokan tafiyar ta.

Bafulatanar Adamawa ce kyakkyawar gaske, doguwa sambaleliya, siririya, shekarunta sha tara da haihuwa, tana cikin dalibai masu hazaka da gwamnatin jihar Adamawa ta zaba tayi sponsoring karatun su na likita zuwa kasar Jamus akan likitancin fidar kunne, hanci da wuya (ENT surgeon) wadanda sunyi karanci a Nijeriya, specialization din su shi ake kira (Otorhinolaryngology).

Ta tashi ba tare da iyayen ta ba, sun mutu tun tana kankanuwa, a hannun kakarta Daada wadda ta haifi mahaifin ta ta tashi, don haka duk wani wayo irin na yaran da suka tashi gaban iyaye bata da shi, goyon kaka ce ziryan, mai tarin yarinta, wauta da shagwaba, amma a fannin karatu zaqaqura ce. Daada ita tasa ta a makaranta, hazakarta tun tana karama daban ce data sauran tsararrakin ta. Bata san kowa ba a danginta sai Dada, Dada ce kawar ta, uwar ta uban ta komai nata.

Hazaqarta ce ta sayo mata kauna a gun malamanta, bayan kammala sakandire wadda ta gwamnati ce, tafi kowa cin WAEC da NECO, B2 guda biyar rus, da A1 a biology, physics, chemistry da lissafi, wannan yasa hukumar makarantar ta bada sunanta a gurbin sukolaship na dalibai biyu masu hazaka 'ya'yan marasa karfi da gwamnatin jiha ta basu.

Komai za'a yi musu, sannan za'a dinga basu alawus na cin abinci, har su gama karatunsu a Jamus wanda zai dauke su tsawon shekaru biyar zuwa bakwai har specialization din da a ka tura su su yi. A karshen kowacce shekara zasu zo gida su yi hutu su koma.

Ba karamin dauki ba dadi aka yi da Daada ba, kafin ta barta tahowa Germany, sai da shugabar makarantar su ta zo har gida da kanta ta same ta, ta roketa ta kuma kwantar mata da hankali, ta gaya mata yara irin jikanyar ta ba'a wasa da talent din su, irin su ake nema don a farfado da harkar kiwon lafiya a Najeriya, sannan karatun da zata yi (Otorhinolaryngology) babu mai irin shi a fadin Najeriya a wancan lokacin, tayi wa jikanyarta addua ta bita da fatan alkhairi ta bar ta taje, ita kuma zata kula da rayuwar ta acan, akwai kanwarta dake aure a kasar.

Sannan ne Daada ta hakura, amma tace abu na halin rai da tsufa, ko a ina ta samu damar yin aure tayi, koda wanene, in dai musulmi ne, babba ko yaro, in dai zai rike maraicin ta, sabida bata da tabbacin zata dawo ta sameta a raye.

Don haka ne da jirgi ya kusa kifar dasu tafi kowa nadamar wannan tahowa, da ta yi hakuri ta yi zamanta bayan Daada, akan gadon bonon ta, da wannan ajali ya dauketa ne a bayan Daada cikin kwanciyar hankali. Don ta san mutum baya tsallake ajalin sa, saidai inda ajalin kowa yake ne daban.

Suna saukowa daga jirgi ta hau raba idanu, abokan tafiyar ta duk sun kama gaban su, taimakon da Allah yayi mata tana da adireshin jami'ar data zo da duk wasu muhimman takardunta a tare da ita.

"RAHINA OMAR! RAHINAH OMAR!! RAHINAH OMAR!!!"

Taji an kira sunan ta daga baya, da sauri ta juya don ganin mai kwala mata kira haka, nan da nan ta gane shi, shine agent wanda aka turo daga Embassy yayi musu jagora a komai har su gama registration dinsu. Kuma tana da hoton sa. Sannan principal tace shi zai kaita wajen kanwarta Dr. Laura wadda lakcara ce anan Cologne take aure. Gara ta zauna gidan ta madadin zaman (students hall of residence).

Murmushi ya subuce mata, data hango abokan tafiyar ta tare da shi, suka rankaya cikin babbar mota suka wuce cikin gari.

Sunan ya cigaba da wata irin amsa-kuwwa a kwanyar sa, ba tare da sun ankara da shi ba, sabida a lokacin ya basu baya ".......Raheenah Omar.......". Ya ji amsa-kuwwar wannan suna har cikin bargon sa. Kamar yadda har zuwa yanzu yake jin ta cukuikuiye a jikin sa. Surar ta bazata taba gushewa daga idanun sa ba, domin bai taba ganin kyakkyawar surar data manne a ruhin sa irin tata ba, sannan innocentlooks dake cikin fararen idanun ta wani sign ne daya makale a zuciyar sa.
****




*FIRST ENCOUNTER (HADUWAR FARKO)*

"The Cologne Public Library" babban dakin karatu ne na jami'ar Cologne wanda yake lamushe dubunnan dalibai komai yawan su, yawanci daliban anan suke assignments din su, kuma idan kazo a matsayin sabon dalibi dole ne kayi register da Labirare, a matsayin ta na sabuwar daliba mai yin registration yau ta shigo labirare tunda wuri, bata kai ga tarewa gidan kanwar principal ba ta zauna tare da abokan tafiyarta a (hall of residence) har zuwa sanda zata kammala da registration.

Bayan ta kammala abinda ya kawo ta ta juya zata fita, accidently ta bugi mutum wanda ya juya baya yake jera littatafan Encyclopaedia Britannica a bookshelves na library din. Littafan hannunsa suka fadi kasa.

Da sauri ta sunkuya tana tsince masa, ta mika masa cikin cewa "i'm sorry......." sorry din ta makale a makoshin ta sakamakon ganin makwabcin ta na jirgi. Wanda ta sulalewa.

Ga dukkan alamu ma'aikacin library din ne. A very handsome figure din data zauna mata a rai sati biyu da suka wuce, ko na kwana daya bata fasa tuna shi ba.

"You?"

Ya fada yana nuna ta da dan yatsa. "...... matsoraciya mai tsoron mutuwa" ya sake fadi cikin harshen hausa. Murmushi ta yi tayi gaba tana fadin "wa ke son ta? Da jirgin nan ya kifa da ni Dada na ma mutuwa zata yi". Dariya yayi ya bi bayan ta har kofar labirare. "Daga wane gari kika zo?" Bata san meyasa ta samu kanta da kantara masa karya ba tace "Benue" kallon mamaki yayi mata don ko kusa bata yi kama da kabilu ba, face zallar fulani, bafullatana cikakkiya, ita kuwa ta fadi hakan ne sabida Dada ta ce mata never trust a stranger. Sai yayi tunanin watakila zama ne ko aiki ya kai su zaman Benue din.
Bai cika ta da tambaya ba, suka yi sallama ta wuce ya wuce, amma da ya koma dakin sa na accomodation din dalibai sai ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ta yi masa karan -tsaye a zuciya a kan dalilin da bai sani ba. A kuma yadda ya lura bata da wayau, wayau na fahimtar abubuwa muhimmai irin wanda ya samu kansa akan ta, bai taba tunanin aure nan kusa ba, amma yau ji yayi in bai mallaki yarinyar nan ba bazai iya rayuwa ba. Ya manta da abinda ya kawo shi karatu ne kuma a yanzu ne ya fara masters din sa, ya samu part time job da labirare don ya taimaki kansa, kasancewar kudin da PTDF take basu ko kusa baya isar sa sabida tsadar student accomodation.

A yau da ya sake haduwa da Raheeenah, sai ya tuna cewa ashe shima namiji ne, ashe yana da bukatar mahadin rayuwa duka shekarun nan biyar da ya kwashe a Jamus, ashe bai taba haduwa da wadda zuciyar sa zata aminta bane, shiyasa bai taba son aure ba, sai akan Rahinah. Wadda ganin shi da ita bai fi a kirga ba. Gabadaya ya rikice ya birkice ya rasa inda zai sa kan sa. Aure kawai yake so yayi kuma ba da kowa ba sai Rahinah Omar.

Yana da Ubangida limamin masallacin musulmai na jami'ar Cologne wanda ke karatun doctorate, mutumin kasar Maghrib ne, shine ya samar masa aikin da yake yi a library yanzu, duk da albashin ba mai yawa bane amma bai nemi komai ya rasa ba, har ya bar cikin jami'a ya kama private gida karami a wajen makaranta.

Rigimar son aure data shige shi a yanzu harda kuruciya domin kuwa abinda bai sani ba infatuation ke damun sa akan Raheenah ba soyayya ba. Kyawun ta ne ya riba ce shi. He just wants to have her as a spouse at the age of 27 a lokacin da ya kamata ace karatun sa ne a gaban sa ba mace ba. Ga Hajiyar sa ta dade da samar masa mata a kauyen su, Nahuche. Wadda take matukar so, don 'yar kanin baban sa ne. Jira take ya kammala masters ya dawo ayi musu aure.

Amma haduwar sa da Raheenah ta rikita shi ta hargitsa shi, gabadaya ya rasa lissafin sa, bai taba tunanin yin zina a rayuwar shi ba duk da cewa ita tafi komai arha a Cologne, amma ji yake kamar zai iya raping Raheeenah in bata yarda ta aure shi ba, laifin da ya san zai iya kai shi ga hukuncin kisa a kasar turai, ji yake in bai yi aure da Rahinah ba a daidai wannan lokacin zai iya rasa ransa, al'amarin da ya kawo shi gaban ubangidansa at a smart pace (afujajan) yana neman mafita.

Dr. Sayyed ya dube shi sosai bayan ya gama jin damuwar sa, da yake malamin Psychology ne a take ya gama fahimtar halin da Habib yake ciki (infatuation/lust), yace masa "ita yarinyar tana son ka, kuma ta amince zata aure ka? Annabi SAW yayi umarni da ayi wa samari aure a lokacin da suka bukaci hakan, in ba haka ba barna bazata gushe ba a doron kasa. Don haka in ta amince ni zan daura muku aure (ba tareda tunanin abinda zai biyo baya ba)".

Cikin rauni Habib yace "ni ko dosarta da zancen bazan iya ba, i'm sure ba abinda ya kawo ta kenan ba, she's very naive and innocent, ni kuma zan iya cutar da ita idan ta ki yarda ta aure ni, i just want to marry her...... or rape her.....in ba haka ba Dr mutuwa zan yi. Na yarda bayan dayan wannan in kare behind bars!".

Dr. Sayed ya gama gane inda Habib ke fuskanta, infatuation ne mai tsanani ya kama shi ba soyayya ba, yace "ba zaka mutu ba insha Allahu, kuma bazaka aikata zina ba har karshen rayuwar ka, sannan bazaka je kurkuku akan laifin fyade ba, kaje ka gwada sa'ar ka, in har ta amince ni kuma zan yi kasadar daura muku aure, ai karatu baya hana aure".

Tun daga lokacin yake tunanin ta inda zai bullo mata, sun sha haduwa a wurare daban daban musamman labirare data ke yawan zuwa. Amma kwarjininta ya hana ya tunkare ta. Until that fateful day.....da ya ga an daukota ranga-ranga a sume an yi asibitin jami'ar Cologne da ita a ambulance.

Abokan karatun ta sun tabbatar wa da likita cewa basu san me aka gaya mata a waya ba, ana cikin lecture ta ansa waya sai gani su kayi ta zuba kara ta zube a wurin a sume.

Ya makale a asibitin nan a kofar dakin da aka shiga da ita, ya ki matsawa ko nan da can, lokacin da likitoci suka yi nasarar dawo da numfashin ta shi suka ce ya zauna tare da ita kasancewar duk abokan karatun ta sun koma makaranta. Sun dauka shima coursemate din ta ne.

Tana bude ido da sunan DADA ta bude baki.....tana kuka tana fulatanci, fulatancin da bai san me take fadi ba, a karshe ya tsinci kalmar hausa. ... Dada ni da ke shike nan? Dada kema kin tafi kin bar ni ba uwa ba uba a kasar da bani da kowa? Dada kin kyauta min kenan? Meyasa baki ce mutuwar ta dauke mu tare ba? Me yasa baki jira na zama Otorhinolaryngologist ba na saya miki gida mai kyau da mota?"

Ta soma zabura tana fizge karin ruwan ta, da sauri ya rike ta ya kuma danna kararrawar kiran likitoci suka zo suka zurmuqa mata allurar barci.

Kwana uku cif Rahina na cikin wannan halin na tsananin firgita da dimuwar rasa Kakar ta. Ko na minti daya Habib bai bar asibitin nan ba, da nasiha da banbaki da janyo ayoyin Al'qurani masu tabbatar da kowanne mai rai mamaci ne "kullu nafsin za'iqatul maut" Habib ya samu ta soma dawowa hayyacin ta. A ranar data kwana biyar a gadon asibiti, cikin dare ta farka yana sallah, ta hada kai da gwiwa tayi kukan ta ta koshi, yana jin ta har ya gama nafilfilin sa ya juyo don ya kara bata baki.

Sai gani yayi ta mike, ta dauki mayafin ta ta yafa, tana shirin barin dakin. Yayi maza ya sha gaban ta "Rahina ina zuwa? Likita bai sallame ki ba tukunna, ya ce sai gobe, kiyi hakuri ki kwanta ki kara nutsuwa zuwa gobe, ni da kaina zan maida ke gidan ku".

Cikin kuka ta ce "Najeriya zan koma na fasa karatun, passport dina zan je in dauko a gidan aunty Laura, dama sun tsane ni, a dole nake zaune a gidan, bazan iya rayuwa babu Daada ba, don Allah.....don Allah ka fadawa hukumar makaranta na koma gida".

Wani matsanacin tausayin ta ne ya kama shi, yace "Rahinah in kin bar karatun ki, kuma babu Dada, kin koma gida, menene madafarki a gaba? Gara ki karbi reality na cewa Dada ta rasu, ki tsaya ki gina future din ki, wanda ya riga ya mutu baya dawowa, kiyi hakuri zuwa gobe likita ya sallameki in raka ki gidan Antin ki, in kuma san gidan naku don yanzu ni Yayanki ne wanda bazai bari ki ragaita a rayuwa ba".

Da haka ya samu ya kalallameta, da tausasan lafuza, har ta yarda ta koma gado ta zauna. Saidai yadda suka ga rana haka suka ga dare. Kowanne abinda yake sakawa a ransa daban ne. Ga Habibu, tunani yake wannan dama ce Allah ya bashi ta auren Rahinah cikin sauki, tunda bata da gatan da zai zame masa cikas, ba sai ya wahalar da kansa wajen neman soyayyar ta ba.
Raheenah kuwa tunanin ta irin zaman data fuskanta ana yi a gidan anty Laura ne; zama na kafirci da rashin tuna dokokin ubangiji, ta tsani zaman gidan don dai bata da yadda zata yi ne, sabida basu da kirki ko kadan, Anty Laura tana da wani Da Yasir fitinanne mai ruwan 'yan iska, wanda ta gama gane take-takensa na banza da wofi a kanta, don haka tunda ta yi sati a gidan ta fahimci zaman gidan bazai yiwu mata ba domin 'ya'yan anty Laura ko sallah basa yi. Yanzu tunanin ta shine taje ta kwashe kayanta ta dauki passport din ta ta koma makaranta da zama yadda ta fara tun farko. Tunda Habib ya ce komawar ta gida ba amfani.

Gari na wayewa likita ya sallame su, suka fito tare zuwa bakin titi, ya tare musu taxi suka hau zuwa gidan Dr. Laura wanda ba shi da nisa da makarantar su.

Cikin halin ko'in 'kula Dr. Laura ke tambayar ta inda ta tafi har kwana biyar, bayan an gaya mata kakarta ta rasu, shi kuma wannan saurayin ina ta samo shi?" Kamala da kwarjinin Habib yasa ta kasa ci masa mutunci yadda tayi niyya, a take ya kara fahimtar cewa dan sauran gatan da yake tunanin tana dashi a kasar ma babu, wannan matar da gani ba jinin ta bace ba.

Nan yayi mata bayanin daga asibiti suke, ya gaya mata duk halin da Rahina ta kasance, ga mamakin sa sai ta kyabe baki, "don tsohuwa ta mutu ne kike neman kashe kanki? Ai kawai yarinya ki zauna kiyi rayuwa mai 'yanci a Jamus ki tarawa kanki ilmi da dukiya, kin ganni nan tun da na bar Africa na huta da wahala, aure kuwa na yi ya kai goma, yarannan da kike gani duk uban su daban, bana daukar bakin cikin namiji, in kika samu kwalin Cologne kin gama tsallakewa, ki tsaya kiyi karatu ki nemi rayuwar 'yanci kawai".

Rahina ta saki baki tana kallon ta, Shikuma Habib tsoron matar ne ya kama shi, ya tabbata barin ta da Rahinah hatsari ne babba, don haka ya yi gaggawar cewa shi yana son auren Rahina, a bashi auren ta.

Aunty Laura tace "ai ba 'ya ta bace, ba kuma 'yar uwata bace, student din yayata ce kawai, don haka zan mata magana, in ta amince kuma kanada sana'ar da zaka rike ta ko gobe zan wakilta muji na ya daura muku aure".

Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, domin principal cewa tayi Dada ta bar mata wasiyyar idan Rahina ta samu miji musulmi, wanda zai rike maraicin ta ayi mata aure shine babban kwanciyar hankalin ta a kabarin ta.

Dr. Laura tace "ai gashi kam ta samu, har da tabon sallah a goshin sa karewa, kuma ga yadda na lura yana son ta sosai, zan gaya wa baban Nihal ya zama waliyyinta ranar jumaa a daura musu aure".

Baban Nihal mijin Anty Laura da Dr. Sayed suka zaunar da Raheena suna nuna mat??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a amfanin tayi aure shine martaba da kwanciyar hankalin ta, Rahina ta kasa musa musu sai kuka, daga Sayed ya dinga lallashin ta, daga bisani suka daura auren a masallacin Cologne bayan an idar da sallahr jumaah, akan sadakin da Dr. Sayed ya biya masa in Euros. Kudi tsababa masu yawa duk don ya taimaka ta amshi auren domin ta kafe kai da fata bayan daurin auren tace bata so, duk da convincing din ta da Dr. Sayed ya bata lokaci yayi, har mari ta sha a wajen anty Laura tace "ubanki ya ce ki kwaso min shi? Ba tare na gan ku ba? To in baki son shi sai dai ki bar min gida na, ko ki auri Yasir ya sha cocaine dinsa ya lakadaki ba ruwa na".

Ta debi kudin sadakin ta watsa mata, tace "kije ki hada kayan ki da daddare zasu zo su tafi dake, Allah ya gani ni taimakon ki na yi, don nasan in bakiyi auren bama karshenta ki zama international prostitute.
A Jamus kike yarinya ba a Najeriya ba".

Tana kuka tana komai Anty Laura dasu Nihal suka loda mata kayan ta a bayan taxi din da Habib ya zo a ciki, kamar dama zaman ta tare dasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login