Showing 84001 words to 87000 words out of 110913 words

Chapter 29 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

tashin hankali. Amma dukkan su are talking bitterly to each other ba tare da sun san ya dade tsaye yana jin komai ba.

A daren wannan ranar an yi drama ba 'yar kadan ba, hakurin Habibu ya gaza, yayi lallashin duniya Rahinah ta ki, musamman tunda yayi maganar gatsen zai kara aure, hakan ya kara fusata ta, ya kara gishiri akan danyen gyambo, bayan a da ta fara dan sakkowa.
Shi kuma Rahinar sa yake son kasancewa da, anyhow, wanda abinda ya sanya shi dawowa daga PH kenan ba tare da ya gama abinda ya kai shi ba, ba don alkawarin da ya yi wa kan sa ba, na har abada bazai kara ba, ba akan Rahinah kadai ba, akan kowacce diya mace, sabida tunanin nasa yaya matan da zai iya Haifa a gaba, (after knowing the consequences of marital rape), da babu abin da zai hana shi maimaita laifin sa a yau, sai dai ko me zai faru ya faru.

Ya yi kwanan bacin rai ba dan kadan ba, yau ko gafarar bai roka mata ba, bacin ran da ya sa da asubahin washegari ya buga wa Aunty Badiya waya.
Wayar sa a daidai wannan lokacin ta fadar mata da gaba, idar da sallahr Asubar su kenan ita da Uncle, sai ta fito daga inda Uncle Usman yake zuwa dakin ta, ta amsa wayar tasa a nitse, don ba ta san ko me ta kunsa ba.
Suka gaisa shi da Badiya, amma ba'a kai karshen gaisuwar ba Habibu ya ce,
"Maman Musaddiq aure nake so zan kara. Ina neman taimakon ki".
A zaune Aunty ta ke, amma sai ga ta tsaye a kan kafafun ta.
"Amma ba karamar yarinya ba, bazawara nake so wayayya ba mai karatun boko ba, wadda ta doshi shekaru arba'in haka".
Aunty ta nisa, kafin ta ce,
"To Habibu za a bincika, amma ba yanzu ba. Duka-duka yaushe wannan ta koma? In ka kasa zama da guda daya zama da biyu ba naka ba ne. Find the root cause of the problem first, tackle it then, I'm sure ba dadi ne ya kawo bukatar karin auren ba sai akasin sa.
Daman ina da niyyar zuwar muku cikin satin nan in ga lafiyar ku, amma yanzu gobe zan zo insha Allah.
Ka ba ni sati biyu zan gana da Rahinah tukunna. Bayan nan in karin auren shi ne solution na tabbatar maka zan mara maka baya".
Da wannan suka yi sallama.
Kamar yadda ta alkawarta masa a washegari Musaddiq ya dauko ta zuwa Abuja.
Ba ta gaya wa Rahina za ta zo ba, yau din ma suna tsaka da rikicin su a falon kasa, wanda duk rikicin Habibu da Rahinah kashi tamanin cikin dari in ka bincika a kan Dan su ne".
"Ni na ce ki dinga kai shi makaranta? Ko ko salon samun hanyar gantali a kan titi? Ban ajiye masa direba ba?"
Cikin tsananin zafin rai yake magana. Wanda kin sa da ta yi daren jiya shi ne sila.
Rahinah ta ce, "Ka ajiye, kaishin da nake yi ganin dama ta ne. Wai me ka ke nufi da ni ne Malam a gidan nan?
Auren kulle za ka koma yi min? Ka ce aiki, na bari, sannan ka ce ba inda zan je don in mike kafa ta sai dai kawai in zauna in sharba kiba a cikin daki?"
"Za ki rantse da Allah sabida ki motsa kafa ki ke kai shi ba don ki yaudare shi ba? In motsa kafa ne ina gymnasium din gidan? Kawai so kike ya saba da ke, ya so ki, ya so ci gaba da rayuwa da ke, ki zo ki sake guje masa!
Ai mumini maciji ba ya saran sa a rami guda. Mun dade da sanin wace ce ke, mayaudariyar Uwa, muguwa, azzaluma......!"
Fushin nasa ba a kan kai yaron makaranta da ta keyi bane kawai, har da kwalelen talalar data yi masa daren jiya.

"Habibu!"
Ya ji muryar Aunty Badiya daga bayan sa cikin fushi.
"Me nake gani haka? Me nake ji haka? Ku kalla nan...".
Ta nuna Abdallah da ke mannewa a bayan labule jikin sa yana ta rawa da karkarwa, ko kadan ba ya son fadan nan da suke yi kullum, ba abinda ya tsani gani irin sa'in sar su, da sunan nan da Habibu ke kiran Rahinah a duk sanda ya bushi iska; muguwa-azzaluma.
Don a dan zaman sa da ita su biyu a cikin gidan ya fahimci abubuwa da dama a kan ta, tana son shi ita ma, kwatankwacin yadda Baban nasa ke son shi, har ya fi jin dadin kulawar ta a kan ta Baban sa.
Bai ga mugunta ba, bai ga zalinci a Maman nasa ba!
Daga shi har Rahinah ba su san yaushe Abdallah ya zo gurin ba. A tunanin su sun kaucewa idon sa tunda yana dakin sa yana barci.
Aunty ta karaso cikin falon tana cewa, "To tunda kalar rayuwar da ku ke yi kenan, ni a ba ni yaron in tafi da shi, da ma ba ku san kalar kashin sa ba balle na fitsarin sa, bayan na haihuwa. Kada ku bata masa tarbiyyah a banza".
Aunty Badiya ta fadi a hassale tana janyo Abdallah jikin ta daga bayan labulen.
Rahinah sai ta haye sama da sassarfa. Tana ji Aunty na ta yi wa Habibu fada, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba.
Ga shi kuma yana jin nauyin ta, yana kuma kare sirrin auren sa, ba don haka ba da ya gaya mata dalilin da ke tunzura shi a kan Rahinah ba Abdallah ba ne, the more mace ta yi denying husband dinta in bed, the more zuciyar sa ta ke a kusa, the more ya ke zama frustrated, duk wata kyautatawa da zata yi masa ba ya gane ta in ba wannan ba.
"Ki yi hakuri".
Kawai ya ce kan sa a kasa, sannan ya ce cikin sanyin murya,
"Ni zan fita, ina fatan a nan za ki kwana?"
Badiya sai ta ji kanin nata Habibu ya bata tausayi. Ta ce.
"In kwana gidan da babu fahimtar juna da kwanciyar hankali cikin sa a kan me? Ka san dai ina da masauki na, me zai kai ni kwana gidan ku alhalin har gobe ba ku gama sanin ciwon kan ku ba? Ba ku iya rike amanar Da guda daya da Allah Ya ba ku ba sabida wautar ku?"
Kan sa a kasa ya ce, "Hakurin nan dai nake kara ba ki Maman Musaddiq, ba za ki gane ba ne. Kuma maganar aure da na yi miki I'm very serious yanzu nake son sa ba gudu ba ja da baya".
Aunty ta ce, "Tau! ai ka san inda zawarawan suke sai ka je ka bincika da kan ka. In ji dai Rahinar ma ba ni na gano maka ita ba?"
Ta haye sama ta barshi a nan tana fadin, "In ka so ka bai wa Musaddiq daki ya huta yana waje yana fidda kaya a boot".
Ta kama hannun Abdallah suka bi bayan Rahinah zuwa dakin ta. Sai ta same ta ta hada kai da gwiwa a gefen gadon ta, ita ba kuka ta ke ba, amma idanun ta sun kada sun yi jajir.
Abdallah ya ce, "Mummy, ki yi hakuri".
Sai ta yi dan murmushi ta gyara zaman ta, ta ce, "Aunty sannu da zuwa, ya hanya?"
Ta mike don ta dauko mata ruwa a firjin gefen gadon ta, Aunty ta ce, "Bar ruwan ki Rahinah. Yau tafiyar nan tawa takakkiya, taki ce. Na rantse ban barin gidan nan sai na ji tun farko mene ne matsalar ku ke da mijin ki. Me ya hada ku kuma me ya raba ku shekara goma?".
Ta dubi Junior, ta ce, "Junior maza tafi wajen Musaddiq yana dakin baki, ga choculates din ka na zo maka da su. Har da kelloggs".
Ga mamakin Aunty Badiya, yaron bai nuna zumudi ko farin ciki ba, kamar yadda ya ke yi a duk lokacin da ta bashi chocolate ko kelloggs din, jikin sa a sanyaye ya ke idon sa sai kallon Rahinah yake yi wani iri, domin ba ya son ganin ta a irin yanayin nan da ta ke ciki tun dawowar Baban sa gidan.
Hatta fara'ar da ta ke wuni ciki yanzu ta dauke, koyaushe cikin yanayin da ta ke kenan; ido jajir babu fara'a.

"Maza je ka Abdallah, ka ce ina gaida Yaya Musaddiq".
Da wannan ya juya ya fita jikin sa duk a sanyaye, ko ledar tsarabar da Mummy ta kawo masa bai dauka ba.
Aunty ta maida hankalin ta kan Rahinah, ta ce, "Rahinah, ba komai ya sa na ce ina son sanin hakikanin matsalar ku ba sai don Habibu da ya kira ni jiya yana batun yana so ya kara aure, shekara goma da ba kwa tare bai yi auren ba sai yanzu da ku ke tare Rahinah? And he sounds serious ban ji alamun wasa yake yi ba, don na fi kowa sanin sa.
Idan ki ka bari Habibu ya auri irin matar da yake nufi, kin kade har ganyen ki".
"Aunty ko kyankasassar 'yar bariki yake so ku aura masa don Allah ku aura masa...". Sai kuka ya kubuce mata.
Aunty ta ce, "Rahinah may I know your problem as a mother not an inlaw? Na yi alkawarin ko Baban ki ba zai ji ba, ba zan saka third party a tsakanin mu ba.
Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, na tabbata rashin SO ba shi ne matsalar ku ba, akwai wani boyayyen dalilin amma ba shi ba.
Ko ban kawo solution ba ko ban hana shi kara aure ba zan taimaka miki da shawarwari matsayi na na mace yar uwar ki wadda ta fi ki yawan shekaru da sanin halin maza, wadanda insha Allah in muka bi su za mu yi maganin matsalolin komin yawan su. Hausawa suka ce barin kashi a ciki baya maganin yunwa Rahinah".

Lokaci na farko da Rahinah Omar ta ji zuciyar ta ta amince ta fada wa wani abin da Habibu ya yi mata. Wanda ya sanya mata tsanar sa, ya kuma lullube soyayyar sa wadda ta zo ta same ta bayan rabuwar su. Ko babu komai ita wannan shakikiyar sa ce, 'yar uwar sa ce ta ciki daya, duk wani mataki da za ta dauka ko shawarar da za ta bayar wanda zai amfane su ne su duka, kuma ba ta taba mutuncin sa a idon wani ba. Idan kowa zai kalli da abin da ya yi din a baya ya hada shi da matsayin sa na yanzu da wani ido na daban, Badiya ba za ta kalle shi da haka ba.
Sai ga Rahinah yau tana voicing out damuwar ta ta shekara da shekaru tana yi tana kuka.
"He has been sexually abusing me in my adolscent ages da sunan aure. Auren da aka yi ba da cikakkiyar yarda ta ba, a gantale babu martabar iyaye a ciki.
Abin da na fahimta ya saka karfi ya aure ni ne kawai a lokacin don biyan bukatar gangar jikinsa.
A lokacin da ni kuma ina da abin da na saka a gaba, abin da ya kai ni kasar Jamus. Ban gama sanin hakikanin me aure ya kunsa ba sai a hannun sa.
Sannan bai tsaya ya fahimtar da ni ta hanya mai kyau ba. Bai samar da fahimtar juna da kyakkyawar dangantaka ko kankani a tsakanin mu ba. Abinda ya sanya a gaba a wancan lokacin kawai shine ya sadu da ni anyhow, disregarding my feelings, my well being, my health and my humanity
A yanzu kuma da na girma na mallaki hankalin kai na da tunanin kaina, sai na gane cewa, a rayuwa ta ina son miji ma'abocin soyayyah.... (I want my husband to be loving, caring and romantic who is not given sex priority), don na fahimci ina da karancin bukata.
Na fi danganta hakan da psychological trauma din da Habibu ya gina a kwakwalwa ta a baya. Kwatakwata yanzu bana so ya kusance ni duk da na fahimci yana son canzawa ne...
To Anty kin ji abinda ke sanya mu samun sabani.
Ta karasa fadin hakan cikin tsananin jin kunya da runtse idanun ta, tana mai sunkuyar da kai tana share hawaye. Amma yau sai ta ji ta sakayau, tunda ko ba komai ta amayar da abin da ba ta taba amayarwa kowa ba, abinda ta dade tana fama da shi ita kadai a ran ta, sai ta ji tamkar an zare mata kaya daga zuciyar ta.

Aunty Badiya ta yi mamaki a kan labarin da Rahinah ta bata, kuma a kasan ran ta ta ji kunya sosai kamar ita ce Habibu Nahuchen, eh, dole Habibu Nahuche ya yi gummm da bakin sa in aka ce Rahinah ce autar mata da ya ki yin aure sabida ta ki shi, har wani lokacin ya bige da hawaye, ashe shi ya san danyen aikin da ya aikata mata, alhaki kuma yasa alamarin ya rikide masa zuwa soyayyah ta ce,
"In kin duba shekarun sa a wancan lokacin za ki gane sha'awa ce ta sa shi auren ki, irin ta tashen balaga, a irin wadannan lokutan maza kalilan ke tsallakewa hadarin zina ko masturbation. An gode Allah da ya bada sadaki aka daura muku aure bai bi ta wata hanyar ya same ki ba, kin san kuma in a can kasashen da ku ke ne hakan ba wani abu ba ne, na tabbata addu'ar UWA da tsayuwar daren ta a kan sa ne ya sa a ka kare a haka.
In kuma da ace yayi raping dinki ne ba auren a can Jamus yadda suka dauki rape case da muhimmanci fiye da kasar mu hukuncin sa a shariance mai girma ne. Banda hukuncin da yafi na kowanne wato na lahira.
Amma a addinance mijin ki bai aikata haramun ba tunda a wani kaulin karbar sadaki na nufin amincewa, but zamu kira abun deviance tunda ya saki kyakkyawar koyarwar sunnah. Ayar da tace matan ku gonakin ku ne bata nufin ku afka musu babu dan aike babu amincewar su. (Allah shine mafi sani)
Don haka don Allah don Annabi Rahinah ki bar wannan ya shige daga zuciyar ki, na yarda Habibu yayi laifi kuma na tabbata duk da bai gaya min ba a halin yanzu da girma da hankali suka game jikin sa yana ta nadama, ki dubi Allah kani na ya ci darajar aure da ta alfarmar ya biya sadaki, ki ba shi dama ki ga irin repenting din sa.
Allah Ubangiji muna masa laifin da ya fi wannan, amma kullum cikin afuwanta mana yake in mun nemi gafara. Allah ya ce ka yi wa musulmi uzuri sau sabain kafin ka kamashi da yi maka laifi, ki yi masa uzuri da tsoron Allahn da ya ji bai nemeki da zina ba a inda yake da duk wata dama ta samun hakan.
Maimakon haka sai ya alkinta ki a dakin aure domin ya zama garkuwa kuma suttura a gare ki. Ki yafe masa Rahinah, ba don ni ba, ba don shi ba. Ki duba albarkar dan da Allah ya ba ku a sanadin hakan ki yi hakuri, ki sa a ran ki kaddarar zuwan Abdallah duniya ne ya janyo auren naku ma gabadaya".
Rahinah ta sa habar zanin ta tana share hawayen ta cikin shessheka, ta ce,

"Na hakura Aunty, wallahi daga yau na yafe masa, ba zan kara tada zancen nan ba".
Aunty Badiya ta rungumota jikin ta. "Na ji dadin jin wannan. Allah ya yafe miki ke ma, tare da mu bakidaya, da iyayen mu da suka kwanta dama. Kuma ki nemi gafarar sa kan hakkin sa da ki ke ta dannewa ba tare da ya san me ye hakikanin matsalar ki ba.
Yanzu ai Rahinah zamani ya ci gaba, bayan psychological trauma na abinda ya faru a baya akwai magunguna na zamani da na gargajiya da zasu gyara wannan matsalar, baa barin irin wadannan kananun matsalolin sakaka su hana zaman aure armashi, tuni ake maganin su.
Mostly cutar sanyi ita ke kawo karancin sha'awa, akwai magunguna na gargajiya da na Bature wadanda za su daidaita sexual behaviour din ki, musamman na kasashen Indonesia da Asia.
Nan Africa ma kasashenmu irin Nijar, da garuruwan Sokoto da Katsina suna sarrafa su don amfanin ma'aurata. Na yi alkawarin kawo miki wadanda za su daidaita wannan sabanin.
Shi kuma Habibu ki ba shi dama, ki kwantar da hankalin ki da shi, don ta haka ne kadai za ki gane ya canza ko bai canza ba. Amma kina ta rikici da shi kullum a kan Da, yaushe ki ka san yadda yake in bed a yanzu? Bana ko tantamar har da bakin cikin hakan yake tunzura shi yake tono abin da zai sa ku hau sama ku fado a kan yaro, wanda babu ruwan sa. Maza a wannan fannin basu da ragowa Rahinah kuma ba sa uzuri.
Dubi yadda walwalar Abdallah ta canza, amma ba ku kula ba, kun fi maida hankali ga tonon juna babu gaira babu dalili, yaro na ba haka yake ba, duk kun canza min shi. (He is healthy and energetic) kan ya zo hannun ku".
Murmushi ta yi, a ranta ta amince ta karbi duka shawarwarin Aunty Badiya, da niyyar za ta ba shi dama ta gani ya canza ko bai canza din ba?
Idan ta yarda ya canza din, sannan ne ita ma za ta yi amfani da daya shawarar ta Aunty, wato yin amfani da taimakon da za ta kawo mata.
Tare suka shiga kicin da Aunty kamar kanwar miji ba Yar miji ba. Girki na musamman suka shirya suka aza a dining, sannan suka yi wanka suka yi sallah, suka zauna a falo suna kallo suna jiran dawowar sa.
Amma sai waya ya bugowa Aunty ya ce, ba zai samu dawowa ba, ya wuce Lagos. Ran Aunty ya baci ta hau fada,
"Haba Habibu? Wannan wacce irin rayuwa ce? Da da yanzu da ka ke shawagin ka duk inda ka ke so babu notice din kowa da yanzu da ka aje iyali daban.
Kada ka kara tafiya wani gari ba tare da cikakken sani da cikakkiyar sallama da iyalin ka ba, this is sheer nonsense".
Murmushin da ya yi har ta cikin wayar ta ji sautin sa. Ya ce,
"Maman Musaddiq ke nan! Matar da ta ke son ka, ta kuma damu da kai ita ke damuwa da zaman ka a gida, sometimes gara ma ka tafi inda ayyuka za su mantar da kai cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login