Showing 96001 words to 99000 words out of 110913 words

Chapter 33 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

da maganin ta na gargajiya amma kun ki"
Hajiya ta koka, tana yamutsa fuska.
"To in ba kya sha a kan kari Hajiya ai bazaki warware da wuri ba su sallame mu a kan lokaci, ki koma wajen maigidan ki Abdallahn ki da kullum ki ke damu na da zancen sa".
Hajiya ta dungure mata kai, ta ce, "Abdallahn da ku ka sabauta min? Bawan Allah! Allah kadai ya san irin izayar da ku ke gana masa da sunan soyayya".
Dariya Rahinah ta hau yi. Wai izaya. Fada kawai suke yi shi kuma Abdallah ran sa baya so, ya sanyawa ran sa damuwar hakan har hakan ya taba masa kwanya. Amma ai lelen sa suke yi ba ita ba ba Uban ba, wannan na wane wannan a son Abdallah, kowanne so ya ke ace shine gwarzon mahaifi a wajen Abdallah dayan ya gaza; wato dayan ne a baya.
Kuskuren da suka yi shine kwakwalwar yaron ta yi kadan da daukar matsalolin su. Rahinah na wannan tunanin taba ballewa Hajiya magani ta sunkuya domin dauko gorar ruwa a firji sai ji suka yi an murda kofar dakin nasu tare da sallama a natse.
Muryar da ta ratsa har kasan zuciya da ruhin Rahinah Omar, ta sanya ta dagowa abruptly kuma cikin (slow motion).
Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche ya bayyana a dakin asibitin sanye cikin (Black - Grey German Suit), wadda ta taimaka ainun wajen kara fito da ilhama da cikar zatin sa na cikakken Bazamfare mai jini a jika. Kafar sa cikin rufaffen takalmi (cover) samfurin (Bloomingdale's) wanda ya dace da launin sutturar jikin sa, wato black/grey. Agogon rolex dake daure a damtsen hannun sa ma (Bloomingdale's) dinne na bakar fata. Agogon ya kwanta luf ya nitse cikin tarin lallausar sumar dake kwance a hannun sa ta Zamfarawan usli. Fatar jikin sa lub-lub mai nuna yanayin hutu da kwanciyar hankalin da yake ciki.
Wannan sardidin matashin bazamfaren da a kullum ta gan shi ko ta ji muryar sa tun daga kuruciyar sa har zuwa matakin da ya ke kai a yanzu (at his fourteith), sai ya tafi da kafatanin numfashin ta na wucin gadi ya kuma tada tsigogin jikin ta.
Daga ita har Hajiya babu wanda ya yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin, don haka suka bi shi da kallo na mamaki da al'ajabi, na Rahinah cakude da boyayyen farin cikin ganin sa har kasan ran ta. Irin farin cikin da ta dade bata yi ba, kuma idanun ta sun nuna hakan. Ta saki wata siririyar ajiyar zuciya.
Sai da Habib ya tabbatar ya sanya kwayan idanun sa cikin na Rahinah duk da yadda ta yi kokarin kaucewa hakan saboda Hajiya da ke zaune a gefen su, sannan ya karasa gaban gadon Hajiya da sassarfa.
Hajiya ma ta kasa boye farin cikin ta na ganin sa, ta ce,
"Baban Abdullahi zuwa ba sako ba sanarwa? Amma ka shammace mu".
Hannayen ta duka biyu ya kama ya rike cikin nasa ya dora a kan kwantaccen sajen fuskar sa, ya ce, "Hajiya ina sane na ki gaya muku zan zo, don cewa za ki yi ba sai na zo ba kin warke".
Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta zare hannayen ta daga cikin nasa, Habibu ba ya girma in dai a gaban ta ya ke, ta ce,
"To ai shi ke nan, ka zo lafiya ya ya hanya, ya Abdallah da jiki?"
Suka koma gaggaisawa irin ta Da da mahaifi. Yana gaya mata rikicin Abdallah na cewa sai ya biyo shi. Hajiya ta dubi Rahinah da duk ta kasa sakewa ta takura a dakin sakamakon kallon da Habib ke mata na kurullah duk lokacin da tayi kuskuren dago kan ta sai idanun ta sun fada cikin nasa ta ce,
"Ke kuma haka ake karbar bako babu sannu da zuwa babu ruwan sha?"
Murmushi ta yi cikin jin kunya, kan ta a kasa ta kara nutsuwa hadi da takurewa, murya can kasa ta ce,
"Sannu da zuwa Baban Abdallah".
Habibu ya yi mata kallon tsaf, kafin ya ce. "Rike sannu da zuwan ki tunda sai da a ka roka min". Ya fadi hakan ne cikin gimtse fuska da nuna rashin jin dadi.
Yadda ya gimtse fuskar sai ta ga ya kara wani irin kyau a idanun ta. Ko kuwa ita kadai ta ga hakan don tana murna da zuwan sa? Ba zan iya sani ba.
Tana murmushi ta nufi firij ta rasa lemon da za ta dauko masa, sai ta tuna ya taba cewa ba ya shan zaki, kawai sai ta bige da dauko ruwan roba mara sanyi da tambulan ta kawo masa.
Gabadaya ta rikice ta rude sosai da zuwan Habibu. Amma tana kokarin sarrafa kan ta saboda idon Hajiya da nasa idanun da ke ta bin ta.
Tana bashi ruwan ba tare da ta bari sun hada idanu ba ta juya musu baya ta tada sallah.
Bai sha ruwan ba ya mike yana fadin, "Hajiya zan karasa masauki in yi sallah sai dare zan dawo in ga likitocin ki".
Hajiya ta dubi Rahinah da ke ninke sallayar ta bayan ta idar da sallahr ishai da idanun kulawa da kauna, kamar mai magana da karamin yaro cikin lallashi ta ce.
"Rahinatu sai ki raka shi masaukin ko, kun dawo tare zuwa goben, ni bana bukatar komai alhamdulillah kullum lafiya karuwa take yi, barci ma zan yi yanzu haka, Allah ya yi miki albarka yasa yayan ki su yi miki ninkin abinda kika yi min"
Rahinah ta zaro ido ta ce, "Hajiya ba za mu barki ke kadai ba...".
Kallon da Habib ya yi mata ya sa ta hadiye sauran maganar ta har ta kware. Domin kallo ne da bata taba gani a idanun sa ba.
Hajiya kuwa sai ta hau fada,
"To in kin zauna goya ni za ki yi? Kin bani magani kin bani abinci barci kawai ya rage min. Mijin naki da ya taso kasa ya kasa ki ce ba za ki raka shi masauki ba, haka ake yi Rahinatu? Bayan ni bana bukatar komai? Duk wata kulawa kin gama bani, shima kulawar ki ya ke so. Tashi maza ku tafi, Allah ya yi muku albarka".
Shi tuni har ya kai bakin kofa ran sa kal da farin cikin kalaman mahaifiyar sa. Da tace da Rahinah shima kulawar ta ya ke so. Da gaske ne Hajiya ta fi kowa son sa, ta kuma fi kowa sanin sa da fahimtar sa.
Ba abinda yake so a lokacin sai kadaicewa da Rahinah Omar. Ba kuma wai don wani abu ba, kawai so yake ya gan su daga shi sai ita a kebantaccen muhalli shine babban abinda yake sa masa nutsuwa a yanzu. Son samu ya dan runguma ta cikin jikin sa ya ji dumin da ke kasan dogon wuyan ta, wanda ya san ba mai yuwuwa bane.
Rahinah ta gama 'yan mutsu-mutsun ta na jin kunyar Hajiya, sannan ta dauki kayan ta kala daya ta sanya a leda da rigar barci daya, da duk abin da ta san za ta bukata a daren zuwa gobe ta bi bayan sa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Tana ficewa daga dakin tana ce da Hajiya %??najiya ki kunna waya ki bar ta a kunne%???. Hajiya tace,
%?7oo Rahinatu, ga nurses din nan ma suna ta bakin kokarin su ai, bana jin sai na kira ki, mu kwana lahiya cikin alheri%???.

Direban hotel din da ya sauka wanda da ya dauko shi zuwa asibitin yana waje yana jiran sa bai tafi ba, shi ya bude musu gidan baya na motar duk suka shiga, ya mayar ya rufe ya ja su a hankali suka shiga cikin garin Bonn.
Bonn City makociyar Cologne ce. Daga ita har shi, ba mai iya kallon dan uwan sa. Wata bakuntar juna ce ta zo ta lullube su. Zukatan su kadai ke aiki da wani irin emotion na zama jikin juna a kujerar baya na motar. Kwakkwaran motsi wannan daga shi har ita ba wanda ya yi har suka iso hotel din da Habibu yayi masauki.
Meriotte Hotel, Bonn.

Shi ne hotel din da Habib ya yi masauki.
Ta lifta suka haura zuwa dakin da ya sauka a hawa na goma. Abin da Rahinah ta gani shi ne, Habib bai cika kallon ta ba tunda suka taho, karewa ma, ignoring haduwar idanun su yake yi, ko mai ya sa? Ko Habib ya daina son ta ne shine dalili?
Tun shigowar su dakin yake sabgogin sa, ya yi wanka ya sauya kayan jikin sa zuwa na barci, ita kuma ta haye saman kujera ta yi zugum, kamar tsohuwar da ta yi wa Sarki karya. Tana kallon sa ya jona kettle ya dafa shayi ya sa lipton din %?sjetley Tea%??? mai kamshin na%??jna%??j da kanimfari ya zauna a gefen gadon dakin yana sipping (kurba) a hankali, yana yi yana amsa wayoyin da ke ta shigo masa a kai a kai daga ma'aikatan sa na gari-gari a Najeriya da sauran abokan kasuwancin sa. Ta raja%??j sosai a kallon sa yadda yak e yin komai nasa cikin nutsuwa da class burgeta ya ke yi.
Tana bukatar wanka, don haka ta hakura da kallon mijin nata wanda ya nuna bai san da wanzuwar ta ba, ta mike da kayan ta cikin leda zuwa bathroom din dakin cikin mutuwar jikin yin biris din da Habib ya yi da ita, kamar bai san tana cikin dakin ba.
Ai ko laifi ta yi masa tunda ta kashe kunyar Hajiya ta biyo shi masaukin sa ya sassauta mata yayi mata kallon rahma su yi celebrating ganin juna. Watakila bayan tahowar ta komai ya gama kankama tsakanin sa da bazawarar sa. Shiyasa yau Habibin ya ke share ta. Kawai sai ta ji idon ta sun cika da kwallah.
Ta gaban sa ta wuce tana tafiya kamar macijiya. Ta kasan idon sa ya bi ta da kallo har ta shige ta rufo kofar.

A hankali Habib Nahuche ya sauke kwayar idanun sa kasa, daga kallon bayan matar tasa Rahinah, yana jin wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali har da gamsuwa na ratsa shi. Ji yake kamar ya bi ta toilet din amma hani kan sa yin hakan, domin hakika ya azabtu da rashin ta a kwanakin nan duk da ko suna taren ba wani abu ke shiga tsakanin su ba, amma atleast yana ganin ta ko fada suke yi dadi yake ji, idan ya tuna Rahinah Omar ce ta dawo cikin rayuwar sa.
Amma haka ya daure ya hana kan sa bin nata, domin ya riga ya alkawarta wa ran sa komawa SABON Habibu a gare ta daga yau har karshen rayuwar su, sabon mijin Rahinah wanda komai nasu sabo zai koma wato (from the beginning).
A yanzu sabuwar rayuwa yake musu kwadayin ginawa wadda babu komai sai zallar soyayya, kauna da fahimtar juna a cikin ta. Ta baya ta riga ta shude. Sabon gini ya ke musu fata mai inganci da karko mai kuma meaningful direction.
A sabuwar rayuwar da ya shirya musu shi da Rahinah, ya kuma ke musu fata yanzu; fahimtar juna da soyayya zallah ne zasu jagorance ta, sex will now be their last priority at the convenience and desired time of each other.
Love and mutual understanding will prevail.
Tunanin da Habib Nahuce ke ta yi ke nan har Rahinah ta fito daga wankan ta, sanye da wata lallausar nightie (pusher pink) a jikin ta. Amma rigar doguwa ce sosai har kasan idon kafar ta, hannun ta ne kamar na shimi, suka hada ido, tayi saurin kawar da nata. Rauni irin na diya mace na son mamayar ta, ya fallasa halin damuwar da biris din da Habibu ya yi da ita ya sanya ta a ciki duk da yadda take daurewa, ruwa na yarari daga cikin lallausar gashin kanta ta fulanin usli da ta wanke da kumfar (head&shoulder).

A hankali kamar wadda aka yi wa umarni Rahina ta tako zuwa gaban sa, kawai sai ta samu kan ta da tsugunnawa a kan gwiwoyin ta, sannan ta sunkuyar da kai, ta kasa cewa komai. Hawaye na son bada ita.
Habib ya ajiye kofin shayin da ke hannun sa, ya kai makura wajen shariyar da yake mata shima ba da son ran sa ba, sai don dai kawai don ya koyawa kan sa hakuri da yakanah, ta yadda zai tabbatar mata da cewa ya canza zuwa yadda take son sa, take fatan ya koma.
Yau Rahinah ce tsugunne a gaban sa a cikin yanayin da shi mijin ta kadai zai iya ganin ta, this scenario touches him to such an extent. Ya dube ta sosai cikin raunin murya wadda har shakewa da sarkewa ta ke yi, jikin sa na dan rawa ya ce,
"Ya ya aka yi Maman Abdallah? Irin wannan durkuso haka kamar mai neman gafara? Baki yi min komai ba kin ji? Im only too much tired. Na kwana zaune a jirgi sannan tun da na sauka ban zauna ba. Tashi dawo nan daga gefe na.." ya nuna mata saman cinyoyin sa. (Ba ya son ya yi wani action wanda zai nuna cewa bai canza daga yadda take so ya koma ba).
Don haka ya ke cigaba da kaucewa idanun ta kada su lalata masa ajin da ya shiga.
Maimakon ta ba shi amsa, kawai sai ta samu kan ta da kwantar da kai a kan gwiwoyin sa, ta rungume kafafun sa ta fashe da kuka.
Kuka sosai mai sauti Rahinah Omar ke yi mai taba zuciyar masoyi, masoyin kuma ba kowa ba ne HABIBU ne, wanda ba narka zuciyar Habib kadai ya yi ba, hatta jikin sa rawa ya hau yi, tsigar jikin sa ta mimmike duka, share tan da ya yi fa daurewa yake yi gas hi tana so ta lalata komai.
Ya sa hannu ya dago habar ta daga kan gwiwoyin sa, ya dubi yadda hawaye ke gudu bisa fararen kundukukin ta, wadanda nan da nan suka koma jazur, ya ce,
"Rahinah... why? Rahinah dube ni... don Allah".
Ba ta iya ta dube shi ba kamar yadda ya bukata, ya ke kuma kan cigaba da rokon ta yi hakan, sai ma kara sautin kukanta da ta yi tana kara kankame kafafun sa.
Ta sani ta azabtar da shi da yawa kuma yayi hakurin da har ya kai shi makura yanzu ya daina damuwa da ita irin da, ya daina sha%??jwar tama bakidaya.
Ta rasa ta ina za ta fara cewa Habib ya yafe mata. Ta rasa ta ina za ta fara cewa tana so su canza akalar rayuwar su daga rana irin ta yau.
Tana so ta gaya masa cewa ta mallaka masa ranar yau baki dayan ta, ya yi yadda ya ga dama da gangar jikin ta, ruhin ta da zuciyar ta bakidaya a yau ta mallaka masa su, ranar yau bakidayan ta tasa ce, tana so ta yi amfani da ita ta wanke dattin data jima tana yaba masa tsayin shekaru goma a daren yau bakidayan sa.
To amma ba za ta iya fadin hakan kai tsaye ba, banda kasancewar ta bafullatana har gobe ba su yi irin wannan sabon ita da shi ba har yau. Sannan har gobe ita Rahinah ce mai aji da kiyaye darajar ta.
Babbar yatsar sa sabbab ya sa yana dauke hawayen da ke sauka a kan fuskar ta wanda hakan ya sa Rahinah wani irin lumshe idanun ta, tare da sauke ajiyar zuciya, da kyar ta ce,
"Habib ka yafe min!".
"Da ki ka yi min laifin me?" Ya tambaya yana dago ta daga durkuson da ta yi a gaban sa irin na mai neman gafara ya azata saman cinyar sa, ta rasa inda za ta sa kan ta da soyayyar sa da ke kara-kaina a tsakiyar kirjin ta.
Habib bai ankara ba kawai ya ji Rahinah ta shige jikin sa a hankali bakidaya ta kanainaye shi, ta cusa kan ta a kirjin sa da iyakacin karfin ta.
Ta saki kakkarfan kuka mai tsananin sautin gaske wanda ya tafi ya ratsa har cikin brain din sa.
Shidewa ya yi na wucin gadi domin hakika rungumar ta zo mai bagatatan, wani abu ne da bai taba tsammanin samu daga Rahinah Omar ba, sai ko cikin sa mafarkan sa da hasashen en sa masu yawan gaya masa cewa rana irin wannan na zuwa komai daren dadewa....
Ita kan ta Rahinah ba ta san lokacin da ta yi hakan ba, shauki ne ya debe ta, ta bi umarnin zuciyar ta da gangar jikita ne kawai, wadanda a wannan lokacin ba abin da suke so suke marari kuma, face kasancewa cikin jikin mijin ta Habibu Mustapha Nahuche.
Ji ta ke duk wani ban hakuri na duniya ya yi kadan ya nuna nadamar ta. Ta hakan ne kawai zata iya nuna masa ta yi nadama she%??j begging for change. Kwarai Habib ya yi mata laifi, laifi kan laifi yayi mata a baya, but her punishment to him is severe.
Yau watanni nawa da maida musu aure ko sau daya bata taba bashi hakkin sa na aure ba, yet yana jin dadin zama da ita a hakan don dai ya nuna mata ya canza....
Habibu na son rike Rahinah cikin jikin sa, wata zuciyar na hana shi. Rahina a wasu lokutan Zuma ce ga zaki ga harbi, kada ya yi saurin nuna weakness din sa ta bashi zuma ta dawo ta harbe shi (ta guje shi). Wannan tunanin da ya yi ne ya sa tsaya mata kamar gunkin da ba ya motsi, bayan kuma ji yake tamkar zuciyar sa za ta fito daga kirjin sa with excitedness, ita kuma bata san hakan ba sai kara kankame shi ta ke yi tana sakin kuka mara sauti tana bashi hakuri. Tsigar jikin sa ce ta soma tashi sanadin jin ta lambam cikin jikinsa.....
Zuciyar sa ke gaya masa...
"Rahinah Omar ce fa!"
Wadda ko na sakan daya bugun zuciyar sa bai taba gudana ba tare da ita a ciki ba. Rahinah ce Maman sanyin idaniyar sa wadda ta yi nakudar nan a kan idanun sa, ita ce wadda tsayin shekaru goma sha biyu daidai da rana daya zuciyar sa ba ta taba hutawa a kan ta ba.
"Please hold me Habibi!". Ta fada cikin tsananin kuka, wato "ka rike ni Habibi!".

Yana son ya rike tan, amma yana hana kansa hakan, sabida sanin ko wace ce Rahinah, bakidaya ta tado tsofaffin al'amura cikin jikin sa da a baya yake zaton sun gushe, sun shude, they are no longer

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login