Showing 66001 words to 69000 words out of 110913 words

Chapter 23 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

ba, it became something that they are all bitter about (wato wani abu ne da ya zo su duka biyun ya musu ciwo) amma yanzu ba rigima da Habibu ce a gaban ta ba, yadda za ta samar da kyakkyawar dangantaka ta mu'amala da soyayya tsakanin ta da Abdallah shine a gaban ta, yana da damar fadin duk abinda yake so bazata tanka ba, in dai a karshe zata yi winning ya dawo mata da Abdallah.
"Alright, kin ci darajar masu daraja (Hajiya da Badiya) Abdallah zai dawo. Amma bayan na gama gaya masa how cruel his mother is, how selfish sheis da ta zabi boko akan rayuwa da shi da uban sa.
Sai bayan ta gama watangaririyar ta a boko ne ta san da shi, ta zo da mayaudariyar soyayya a gare shi don ta shiga tsakanina da shi kamar yadda ta shiga tsakanina da farin ciki na na baya.
Sai in ce mu je zuwa Dr. Rahinah tsakanin ni da ke yaron da kan sa zai gane wa ke son sa da gaskiya. Ni dai na san ba ka taba son Dan da ka san ba ka son uban sa kaddara ce ta samar da shi a tsakanin ku. Sabida su 'ya 'yan da aka haifa ta hanyar soyayya daban suke".
A wannan karon ma bata tanka masa ba, domin yau azumin magana ta ke yi in dai da Habibu ne. Ya gama fadin duk bakaken maganganun sa tana jin sa bata ko tada kai ta dube shi ba, ta lura kallon bakin ta yana motsi ko yana magana yana da tasiri sosai a kan sa.
Ita kuma bata zo gidan nan don sake zama abar hutawar sa ba, ko sex toy din sa kamar baya, ko kissing utensil din sa, ko matar sa, ko partner din sa a komai ba, sai don gyara tsakanin ta da dan ta, da nemowa kan ta soyayyar Abdallah da ta rasa shekara goma. Don haka shi yanzu ta dauke shi ta ajiye shi a gefe, ya gama duk bakaken maganganun shi ya kara gaba in dai a karshe Abdallahnta zai dawo gidan.
Haka ya karaci mitar sa ya gaji ya tafi, sosai ya so ta tanka din don ya samu damar sumbatar ta ko yaya ne, kamar ta san kudirin sa da abinda yake yi mawa sai bata tanka din ba har ya fice.
Tana kallo ya aje mata ATM card tareda rubuta pinnumbers din a jikin complimentary card din sa mai dauke da dukkan lambobin wayoyin sa ya ajiye mata sannan ya juya yana fadin.
"Gara in bar miki gidan ki, kafin kuma ki yi waya ki ce da Hajiya na yi raping din ki".
Da ta tabbbatar sun shiga mota sun bar gidan shi da PA din sa da wasu daga ma%??jikatan sa da suka zo tafiya da shi filin jirgi, ji tayi kamar an zare mata kaya a kafa, kamar an raba ta da dutsen da ya danne mata zuciya, sai ta mike ta shiga sha'anin ta cikin gidan.
Da farko kicin ta shiga ta shirya cefanen kayan abinci a inda take son kowanne ya kasance, sannan ta dafa noodles, da ruwan blacktea, ta zauna akan island din kicin din tana ci, da ta gama ta fito zuwa upstairs wato inda dakunan barcin su yake, dakin da ke tsakiyar nata da nashi ta bude domin mukullin yana jikin kofar, nan ta kara sakankancewa da kaunar da Habibu yake yi wa dan sa Abdallah.
Komai da ke cikin dakin (light blue and yellow) ne, ga gadon yara yan shekara sha biyu haka zuwa kasa mai gadon sama da na kasa, an kawata dakin da duk abinda yaro mai wadannan shekarun zai bukata, a gefe ga study-table na yara wanda aka jera masa littafai kala kala akai na daidai shekarun sa. Ga Alqur'ani mai hizfi dai - dai zuwa goma mai manyan rubutun hafsu, na'ura mai kwakwalwa ta yara bisa tebirin ta. Da kuwa ta bude wardrobe din dakin sai da ta ajiye ajiyar zuciya.
Sittirun sa ne dankare a ciki rukuni rukuni, bangaren dinkakku (traditional attire) daban haka na englishwears shima daban, ga takalma kala kala an jera masa a shoerack din sa.
"Abdallah dan gata!".
Ta fada a ran ta, sai ta ji duk damuwar ta ga son dawowar sa cikin gidan ta karu, da gaske uban sa ya gama saye shi da kowacce kalar kauna, duk wanda zai zo da wata kaunar daga baya sai dai ya bi bayan sa kamar yadda ya ce.
Amma zata yi kokarin ganin cewa ya gane ba rashin kauna ya sa ta bar shi ba. Har karatun nata ta jingine na shekara guda don ta kula da shi (in his first year of life). Yaudarar ta yayi ya dauke mata shi, ita kuma ta yi zuciya ta bar masa.
Amma daga sanda ta sake ganin shi ai bata sake nutsuwa ba, bata sake komawa cikin hayyacin ta ba sai tunanin ta hanyar da za ta dawo da shi gareta, wanda shine sanadin dawowar ta gidan su a yanzu.
Kasa fita tayi daga dakin Abdallah a ranar kusan a dakin ta wuni don yana da toilet din sa karami makale da dakin, har sallolin ta na farillah na ranar a kan dardumarsa ta yi.
******


D
a Habibu ya sauka a Lagos al'amuran gabansa ya shiga, sai bayan sati biyu ya je makarantar su Abdallah ya bada hakuri kan cewa zai cire yaron kasancewar Kakar sa bata amince ba.
Malaman British International School basu ji dadin tafiyar Abdallah Nahuche ba domin a yan satittikan da yayi tare dasu hikimar sa da hazakarsa sun fito fili, yaro ne mai kokari don haka yake da shiga ran malamai gashi da bin maganar malaman sa don Badiyya ta tsaya sosai akan tarbiyyar yaranta ciki har da Abdallah.
Amma shi ko da aka ce masa Daddynsa ya zo tafiya dashi murna yayi ta yi, don dama bai son makarantar kwanan.
Duk inda Habib yasa kafa suna tare a Ikkon tsayin sati guda. Yana gudanar da harkokin business din sa na hotels yadda ya saba, in suna gida kuma musamman lokacin da zasu kwanta barci sai ya dinga sako masa zancen mahaifiyar sa, sai dai kamar yadda ya alkawarta mata, ba alkhairi yake gayawa yaron a kan ta ba.
%??mbdallah wannan Antin ta dawo gidan mu fa, tana Abuja, Hajiyar Nahuche Ta ce in kai ka wajen ta%???.
%??mace Antin Daddy?%???
%??madda ka gani a gidan Mummy, ka dame ni kana son sake ganin ta%???.
Yaron ya fadada far%??jr sa %?ni kuwa I like her%???. Cikin takaici Habibu ya ce.
%??mbdallah za ka so wanda ba ya son Baban ka?%???
%??mamar yaya bata son Baba na?%???
Habibu ya mike zaune, shima yaron sai ya tashi daga kwancen da yake. Seriously yake kallon yaron sannan with a serious tone yake magana.
%??ma yi alkawarin gaya maka ko wacece ita, idan ka yi alkawarin bazaka zabe ta akai na ba%???.
%??ma yi alkawari Daddy, ta yaya zan zabe ta a kan ka?%???
%??maboda MAHAIFIYAR KA ce!%???.
Shiru mai yawa ta ratsa tsakanin uban da dan. Dan na kokarin %??iigesting%??? maganar uban yadda zai fahimce ta cikin dan kankanin tunanin sa, domin ta yi masa girman da ta gagare shi ganewa.
%??madday, ina da wata uwa bayan Mummy ne? (Badiya)%??? yaron ya tambaya cikin karyewar murya.
Bai bata lokaci ba ya amsa masa.
%??mummy su Musaddiq ta Haifa, Yaya ta ce, uwa daya uba daya, ita kuma wannan din ita ta haife ka a Jamus mun je karatu muka yi aure. Amma wallahi bata son mu, tunda ta iya barin mu shekaru goma, muna watangaririya da ragaita cikin maraicin ta, bata taba neman mu ba.
Da wannan nake gaya maka ko mun koma gidan ba ruwan ka da ita, ko me zata yi maka kada ka yarda da ita, bata zo don ta zauna da mu har abada ba, sai don ta kwace ka dagahannu na ta kara gaba.
Imagine Abdallah har kotu ta kai ni, don a kwace ka daga hannu na a bata. Wannan abun ya mun ciwo, it really hurts me!%???.

Haka yayi ta turawa yaron negative thoughts a kan mahaifiyar sa Rahinah, of course ya san abun da yake yi dinnan ba daidai bane, bai kuma kamata ba, ba%??j raba hanta da jini, amma ta wannan hanyar kadai zai bi ya rama bakin cikin da Rahinah Omar ta cusa masa ya rayu da shi tsayin shekaru goma, tunda ya bayyana gare shi ba abinda ta ke so ta rayu da shi a halin yanzu sai Abdallah, kamar yadda shima a wancan lokacin ba abinda yake so ya rayu da shi sai ita, bata duba Abdallahn ba, a wancan lokacin da suka fi bukatar ta, ta ajiye kowanne laifi ta ke ikirarin yayi mata, ta sadaukar da nata farin cikin da burukan don ta rayu da dan ta???
Sai yanzu da dan ya zama gotai-gotai da shi karkashin tashi kulawar da nashi tashi-fadin shi kadai? A duniya akwai mai SON KAI (sunan littafin TAKORI mai zuwa) irin Rahinah Omar?%???
Gabadaya ya rikita yaron ya hargitsa masa tunani akan mahaifiyar sa Rahinah, ta yadda yaron ya koma ganin ta da wata fuska ta daban, tun kafin ya ganta.
A washegari suka bi jirgi mai zuwa Abuja.
*****


Y
au tunda ta tashi da kewar komawa aiki ta tashi, duk da cewa sun kara mata kwanakin hutun a matsayin hutun aure da na karshen shekara, amma kadaici yayi mata yawan da take bukatar zuwa asibiti. To amma ya kyautu ne ta fita batare da sanin sa ba? Da da yanzu akwai banbanci, duk da takun sakar da ke tsakanin su, bazata so fitaba da iznin sa ba.
A bisa rashin sanin ta a lokacin ma su tuni sun sauka a Abuja, suna cikin mota sun taho zuwa %?riife %??? Camp%??? daga filin jirgi.
Kamar daga sama ya ga kira daga bakuwar lambar da bai yi saving ba tun a wancan lokacin da ta fara kiran sa, amma ga mamakin sa duk da bai yi saving ba lambar ta dade da zama a cikin kan sa.
Cikin ginshira da shariya yaki dagawa, ya sake kishingida a kujerar sa, cike da mamakin yau Rahinah ta kira shi ai kuwa za%??jyi ruwa har da kankara, koda yake ita kiran ta ba alkhairi bane don kuwa ta riga ta zame masa tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alheri ba. Ko dai tata ce ta kawo ta, ko ta kira don ta gaya masa bakar Magana, ba kuma ya so ta san sun taho sai dai kawai ta ga Abdallahn.
Da ta tabbatar ba zai daga kiran ta ba sai ta daure ta tura masa gajeren sako (text).

%??man shiga NIZAMIYE%???..%???.

Ji ya yi tamkar ta caka masa mashi a kahon zuci da ya tuna a NIZAMIYE din nan wanda ta kira da Dr. Irshad yake, kuma he%??jahead of her a mukamin aiki.
Bai san sanda hannun sa ya bi bayan kiran nata ba, ita kuma bata bata lokaci ba ta daga, don ta gama shiryawa tsaf hatta labcoat din ta na rataye a hannun ta.
Muryar da ke kassara ta a kullum sabida coolness din ta da zurfin ta, ta kwararo cikin kunnnuwan ta babu ko sallama.

%??mi rubuta resignation letter ki kai musu ki dawo, ina jiran ki%???.

Rahinah ta kankance ido ta rasa mezata ce, sakamakon wani irin bacin rai da ya yunkuro mata.
%??me kake nufi?%???
%??mna ce da Hausa nayi Magana? Ko sai nayi da Jamusanci?%???
Rahinah ta cizge mini hijab din ta ta ajiye, sakamakon jin gumi ya yanko mata, ta bar aiki fa ya ce, a sanin ta he%??j frank and straight forward baya fadin abinda ba haka yake a zuciyar sa ba, kuma baya wasa da furucin sa.
%??min gama aiki a Nizamiye, daga ranar da kika yi kuskuren sake amsa sunan MATAR HABIBU NAHUCHE, shima na gwamnatin ina tantamar cigaba da yin sa, zan iya biyan su scholarship din da suka biya miki, ki zauna ki yi bautar aure da kula da yara kamar kowacce mace.
Ba kin ce don ki kula da danki kika dawo ba? To gashi nan na kawo miki. Sai ki zaba ko shi ko aiki, don ni ba na barin da na a hannun %??ian aiki. I come in peace!%???.
Yana gama fadin hakan ya kashe wayar sa.

Ya yi daidai da jin dirin shigowar motoci da ta yi harabar gidan. Da sauri ta karasa ta daga labule bayan ta wancakalar da lab-coat din ta. Kamar ta yi hauka sabida yau ta kara tabbatarwa Habibu Nahuche ya fi ta iya mugunta. Ta hango su shi da ABDALLAH suna fitowa daga mota.....

The tall, slim, chocolate complexioned boy, Abdallah Nahuche, looking so handsome and obviously cheerful like the replica of his father. Ya kara tsayi da kyau gwanin sha%??jwa da shi har fiye da ganin farko da ta yi masa bayan wucewar shekaru goma.
Fatar jikin sa lub-lub a kwance kamar ba girman kasar nan ba, kamar yadda sumar kansa ta ke kwance lub-lub itama ba tare da aski ko saisaye ba, daga gani tana samun kula ta musamman da tsadadden mai na gashin maza Arganavita, gashinan dai exactly yadda Habibu ke barin nasa gashin kan ba aski ba saisaye sai taza. Ita a rayuwar ta bata taba ganin kamanni na kwabo da kwabo irin na Habibu Nahuche da dan sa Abdallah ba.
Babu ko digo nata da Abdallah ya dauko banda almond shaped eyes din ta, wadanda suka taimaka wajen karawa yaron cikar halitta da cikar zati.

Ta saki labulen a hankali jin takun su suna hawowa upstairs din a tare, da taku na energy wato na sassarfar tafiya cikin koshin lafiya da kuzari, suna tafe suna hira har da dariya cikin nishadi irin na Da da mahaifi, kai da ganin su ka san basu da sauran matsala a rayuwa, hannun su makale cikin na juna kamar abokai ko Wa da kani. Dukkan su sanye da (Black-Grey German Suit) wadda ta dace da launin fatar jikin su mai salki da sheki.
Tsigar jikin ta ta ji ta soma tashi da jin sautin muryar ABDALLAH NAHUCHE, wadda ke tsirgawa tana ratsawa tana shiga cikin kunnen ta har zuwa cikin brain din ta, tana hudo wani irin sabon son Dan ta da kaunar sa a zuciyar ta, cikin wani yanayi na soyayyar uwa da bazai fassaru ba, irin feeling din da uwa kadai ke iya jin sa a kan Dan ta kwatankwacin koma fiye da na ranar da ta kawo shi duniya tana kwance kane-kane cikin halin nakuda a kan cinyar Habibu Nahuche.

NA HUCE is not for free. It's 1000 via 3094856450
Sumayyah Kabara Firstbank

A hankali ya sunkuyar da kai, kafin ya dago ya dubi Yayar sa da mijin ta.
%??mu yi min alfarma ku ci abinci ku yi sallah ku natsa%??? yace da su finallycikin muryar sanyi, bayan ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, daga Aunty har Uncle basu katse masa hanzari ba sun bashi dama yayi tunanin sa positively.
%??ma zan iya cin wani abinci ba sai ka tabbatar min zaka bi mu zuwa Girei Habibu%???. Inji Badiya.
A hankali ya gyada mata kai alamar zai bi sun. Uncle ya ce, %?"no alhamdulillahi, ina Abdallah? Cikin kunkuni ya ce.
%??ma zan gaya muku inda yake yanzu ba don ban shirya ba da shi ga uwar shi ba%???.
Dariya Aunty ta yi, sabida farin cikin ya yarda zai bi su zuwa Girei kadai ya karbi auren sa da kan sa ya wadatar da ran ta.
%??man ta matse muku, a bamu masauki mu je mu huta%???. Inji Aunty.
Waya yayi wa mai kula da share-sharen gidan ya zo ya tafi dasu sassan baki, Kuku kuma tuni ya shirya musu abinci ya kai, ya san ba wanda zai yi masa wannnan karambanin na kawo su Anty Ikoyi sai Mr. Rasak.
Amma bai ce masa komai ba don shima yanzu ya ji dadin zuwan nasu, domin ya yaye masa damuwar da yake ciki kaso tamanin cikin dari 80%. Kuma shine babbar maslaha ga mutuncin sa aidanun iyayen Rahinah, dama ita Rahinar kan ta.
Ba wai sulhu yake nema da ita ba, illa shi mutum ne mai yawan submissiveness, wanda idan yayi laifi ya kuma gane daga baya yayi laifin, ko aka nusar da shi, yake gaggawar mika wuya nan da nan ga gyara wannan laifin.
Sun tattauna sosai a daren shi da %??iar uwar sa. Duk abinda suka kashe ita da Hajiya da Uncle da su Baban Nahuche wajen hidimar auren sai da ta kwashe ta labarta masa, don ya san ba a banza ya samu Rahinah ba wannan karon.
Tace atampopin %??iuddaje%??? kawai daga Super sai Holland muka zuba, sauran da suke kanana %??ian uwa ne suka baka gudummuwar su har da Shafa%??jtu".
He felt loved! Sabida ko kana da shi, idan %??ian uwan ka da iyayen ka suka yi maka aikin zumunci da kara irin wannan dadi ka ke ji. Ya ce da Anty zai maida mata kudin kayan suddaje din da na lefe cikin account din ta, Aunty ta harare shi nan ta hau shi da fada, inda ta ce,
%?na ji min yaro, lefe ai gudummuwata ne dama, suddaje gudumuwar Hajiya, Paute gudummuwa ne daga gare mu zuwa ga zuri'an amarya, sauran hidimdimun kuwa duk daga %??ian uwa na Nahuche suka fito, fatan mu Habibu kada ka bamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login