Showing 9001 words to 12000 words out of 110913 words

Chapter 4 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

tsaya miki kamar Babanki, domin hakkin walwalar duk wani dan kasar Najeriya dake Jamus yana wuya na, amma hujjar ki bata isa hujja da za'a kai kotun Jamus ba, sannan baki da kudin da zasu nema. Don haka in zaki bi shawara ta in ma sakin zaki nema to ki nemeshi ta hanyar sulhu saki na addini tunda auren musulunci kuka yi ba tareda kin kai shi kotu ba.

Ni zan kira yaron mu zauna mu uku, gara ya baki saki bisa doron musulunci tunda shi kika zaba amma ba ta hanyar kotun bature ba. Hakan zai jawo babbar matsala ga karatun ku ku duka, don dukkan ku ba abinda ya kawo ku ba kenan. Kuma in gwamnatin garin ki ta ji a inda kika kare a kotu zaki yi disappointing din ta ga kara sponsoring yara mata, sannan jami'ar ku zata shigo zancen wanda duka matsala ne ga karatun ku. Don haka ki barni in ganshi mu zauna mu duka.
Idan rabuwar ku ita ce mafi alkhairi ya sake ki ta ruwan sanyi bisa doron saki na addini".

Jikin Rahina yayi sanyi sosai, kuma tana hango rashin yiwuwar hakan a idanun ta; Habib bazai yarda ya sake ta ta ruwan sanyi ba, ta gama gane mutum ne mai naci akan abinda yake so, kuma hargagi ko barazana basa razana shi. Shiyasa ta so ta kai shi kotu. But who is she to argue with this humble ambassador?"

"Na amince a kira shi in roke shi ya sake ni, a bisa hujja ta bana son sa".

Ta fada cikin matsananciyar faduwar gaba, tana mai jin tamkar hukuncin data yanke bai yanku ba, kamar zai dawo watarana yayi ta haunting din ta (evocative feelings).
*****


NA HUCE....is not for free. It's 1000 via;

3094856450
Sumayyah Kabara
FirstBank
: SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI


*NA HUCE* ....(Daga Fushi na)

PAID BOOK



Sati uku kenan tana karatun ta conveniently online. Natsuwa ta soma shigar ta yadda ya kamata. Tunda bata ganin Habibu A. Bilyamin Nahuche bata da bacin rai, kuma bata da damuwa.
Ciki dai har mantawa take yana makale a jikin ta, in banda mugun kwadayi da yake sa ta, kamar ta cinye Nene da Yafendo sabida dafa min kaza, dafa min kaza.

To haka rayuwa take, komai lalacewar zamani baka rasa mutane na kwarai masu zuciyar taimako saboda Allah, iyalin Ambasada Shehu Bichi, ba abinda zata ce dasu sai addua da fatan Alkhairi.

Hutun farko na summer mutanen gidan duka zasu je Paris, amma Ambasada yace banda ita da Yafendo, su zauna suyi kadin auduga a gida, ta sha jarabawa tana bukatar zaman waje daya ta nutsu, don su kam in sun tafi sai sun kwashe sati hudu suna yawo.

Sun tashi ranar lahadi, gidan ya rage daga ita sai Yafendo, don haka ta lokewa tsohuwar, ba hirar data ke so su yi sai ta garin Girei da mutanen cikin sa. Duk yadda Yafendo ke son ta nusar da ita gara ta koma gidan ta taga gara ta kyaleta, tana cikin walwala da farin ciki a gaban nasu, kamar bacin ranta shine ace ta koma gidan Habibu Nahuche.

Ita kuma haka kawai yaron ya shiga ranta, yana da wata irin Charisma da ba duka maza Allah ya mallakawa ba. Zuwan sa biyu gaida Daddy suna haduwa da Yafendon a falon saukar bakin Daddy, tayi ta zolayar sa wai biko yake zuwa a inda ba'a son sa. Shikuma baya shiru ramawa yake yi, yace yanada kamar ta me zai yi da wata Rahinah? Shi Yafendo ta ishe shi rayuwar duniya. Ya zo ne ya ji lafiyar dan sa a wurin Daddy he's not here for RAHINAH!

Bata jima da dawowa daga dakin Yafendo ba ta ga wayar ta na haske, alamar shigowar sako text. Ta dauka ta duba sai taga cewa alert ne na kudi Euros '???3000. Daga Habibu Aminu Nahuche. Ya cika alkawari na farko da Daddy yasa shi ya dauka na ciyar da ita har sai ta haihu.

Bata san ya aka yi ya aka yi ba kawai ta ji kwalla ta cika idanun ta.
****



Rayuwa ta cigaba da gudana yadda suka tsara ta, sai dai kuma sau tari ta kan zo wa dan adam da sauye-sauye; abin nufi, cikin ta na girma ra'ayin ta na canzawa akan sa. From negative to positive. A kullum ta ji shi yana wutsilniya sai ta ji gabanta ya fadi, sannan kauna irin ta UWA ta soma kanannade ta ba tareda ta yi shawara da ita ba. Bata son uban cikin, amma tana jin zata iya yin komai don tsira da wannan dan na cikin ta. Shi kadai ne ya rage wanda zata kalla ta kira jinin ta, tunda har gobe bata da wanda zata kira nata a gefen ta.

Ta yi sallama a dakin Yafendo, ta sameta tana murza goge a magogi tana hambudawa, Yafendo tace "yau tun safe ban ji motsin ki ba, inji dai lafiya kuka tashi?" Ta zauna gefen Yafendon, tace "lafiya na tashi Yafendo ina wani group discussion ne da 'yan class din mu via zoom. Sai yanzu muka gama kuma dole yau zan shiga makaranta akwai littafan da zan karbo a library". Yafendo tace "a wannan yanayin da kike 'yar nan? Zaki niki hanya ki bar gari zuwa makarantar nan taku mai nisa?" Tayi murmushi ta dora hannunta akan na Yafendo tace "kada ki damu tawan, ina jin karfin jikina sosai, kuma direba zan kira mu tafi tare". Yafendo tace "in kin ga wannan naman da ake cusawa cikin fulawa ki sayo min, irin wanda kika kawo min wancan zuwan naki makaranta" tayi dariya tace "bakin Yafendon mu akwai son cin dadi, zan kawo miki shawarma, nima yau ita nake son ci". Da haka suka yi sallama ta daga wayar ta ta kira Yohana direba.

Suna tafe akan titi tana nazarin wani practical da zasu yi cikin ipad dinta, tayi shigarta islamically cikin abaya ruwan makuba da mayafinta kirar kasar Oman, cikin ta ya fito sosai yayi toro don ta shiga wata na bakwai. Sake-sake take a ranta ko yaya haihuwa take? Is it painful? Shikuma raino da breast feeding ya suke? Kamar amsa ga tambayarta dan cikin ta yayi wani uban juyi da yasa saida tasa hannu ta dafe shi, tana mai addu'ar Allah ya raba su lafiya.

Ta nunawa Yohana inda zai ajiyeta, wato parking lot na Cologne Public Library. Ta bude kofa ta fito a hankali tana taku irin na masu ciki, ta shiga library din da kafar dama domin kuwa shima shigowar sa kenan. Kamar kullum yana cikin kayan sa na hausawan usul jamfa da wando na farin boyel, amma yau bai sa hula ba, ya tara suma mai yawa akansa ta yadda farin gilashin da ya sanya ya nitse cikin gashin kansa. Yana zaune a kujerar sa cikin wani dan cabin na glass inda yake kula da bangaren ajiyar littafai masu muhimmanci (reserve section) ya ga wucewar ta amma ita bata lura da shi ba, kuma gabadaya ta manta a wajen da yake aiki kenan.

Taje ta zabo littatafan da take bukata, amma bata samu guda biyu ba an ce suna reserve section.
Ta tako a hankali zuwa reserve din, ya juya baya yana fuskantar allon kwamfutar dake gaban sa, kwarai ya ga sanda ta taho, kuma ta taho ne tare da bugun zuciyar sa. Ta kara wani itin kyau da sulbin fata tabbacin tana cikin kwanciyar hankali, sabanin shi da rayuwar sa ta jirkice bakidaya tun shigowar ta cikin ta. Rahinah muguwa ce mai son kanta da la'akari da maslahar kanta kadai. Idan wani barin na zuciyar sa ya so kare ta, wani baya mata uzuri cewa yake bata da hujjar kin koma maka...... tunda ka ce zaka canza zuwa yadda take so.

Babu wani bangare na zuciyar sa dake yarda wai Rahinah bata son sa.....tana amfani da kalmar ne don biyan bukatar kanta.

"Hi, can you please check these for me?%???;
-Diagnosis in Otorhinolaryngology
-New Aspects of Fundamental Problems of Laryngology and Otology
Pediatric Otorhinolaryngology....Scott-Brown's Otorhino....." sauran maganar ta makale gabadaya a makoshin ta sakamakon juyowar sa gabadaya. Saura kadan numfashin ta ya bar gangar jikin ta sabida wani mummunan kallo da Habib ya jefa mata. Dadi da cewa bata tsammaci ganin sa ba a daidai wannan lokacin. Sannan dadewar da ta yi bata ganshi ba ya dada haifar mata da faduwar gaban. Tayi kokarin maida numfashinta amma ya gagara isa huhunta.

Daga sanda ya taso daga mazaunin sa zuwa isowar sa gabanta Rahina bata farfado daga suman tsayen data yi ba. Haka kama hannun ta da yayi suka bar cikin library din bata iya ta kwaci kanta ba. Saboda gabadaya bakin ta ya mutu ta kasa saita kanta a gabansa, ta kasa kuma yin kowacce irin hobbasa ta kwace hannun ta daga cikin nasa.

A sanin ta da shi dai bashi da mota, amma ya bude bayan wata mota opel-astra ya sanya ta ciki ya rufe harda mukulli. Ya zagaya ta barin mazaunin sa ya zauna kuma ya tashi motar da wani irin mahaukacin gudu, bata raba daya biyun yau tata ta kare. Don ta san Habibu akan ta wani mahaukaci-mahaukaci yake komawa.

Har kofar flat dinsa ya shiga da motar, ya kashe ta sannan ya dube ta da idanun da suka kada, suka kuma sanya hantar cikinta kadawa. "Ki fita mu je, magana kawai zamu yi in mayar dake inda na dauko ki".

Rahinah ta soma hawaye, tace "babu inda zani, nida shiga wannan gudan sai dai akai gawata""ko? Zaki shiga ne kuma da ran ki da lafiyar ki, ko ta tsiya ko ta arziki, kina sane da cewa har yanzu matsayin matata kike?"

Wani karfin zuciya ne ya zo mata, ta ce "wallahi ko ka bude min na fita, ko nayi maka ihun da zaka fada hannun hukuma, nace bana yi, bana so kuma bana auren dole ne?"

Ya kwantar da kai akan sitiyari yana kallon ta, masifa take yi tun karfin ta amma zakin muryarta kamar busar sarewa yake jin sa a kunnuwan sa. Haka mace mai cikin take komawa? Danya sharaf? Komai fresh? Idanuwan sa har wani kanakancewa suka yi suna dubanta da siga mai nuna bukatuwar miji zuwa ga matar sa......
"You can scream.... (kina iya yin ihun) amma ki sani nima inada nawa 'yancin da musulunci ya bani, kuma zan tabbatar miki shi yanzu". Ya karasa maganr ta hanyar kamota da karfin gaske ya rungume ta, tana mutsu-mutsun kwatar kanta. Yace "Rahinah ki dubi Allah ki tausaya mun......my life is shattered without you. Ko me kike so zan miki, ko me kike so zan zama. Nayi alkawarin fin Romeo iya soyayya. One more last chance.... ko don albarkar dana dake karkashin marar ki. Rahinah ko a lahira wani kan ci albarkacin wani. In kika barni gabadaya bazan iya kara aure ba. Zan yi ta zama da dan ki ne yana debe min kewar ki har karshen rayuwata......".

Rahinah ta ga cewa hargagin ta ko cika bakin ta bai kwatar ta hannun Habibu a yau, he's ready to face anything don ganin ya kusance ta a yau, wanda hakan na nufin maida hannun agogo baya. Tun farko ita wane tsautsayi ya kawo ta library bayan ta san anan yake? Ta soma kuka tana rokon sa "don Allah ka amida ni inda ka dauko ni, kaga bani da lafiya, bazan iya wannan abun ba zan mutu, da na ma zai mutu, wallahi nayi alkawarin zan saurareka da duk abinda ka zo da shi amma bayan na haihu....". Habib ya sassauta rikon da yayi mata, shima bazai so wani abu ya samu dan sa ba, dan da yake jin duk duniya ba abinda yake so kamar sa in ka dauke Haj. Kaltume.
"Kin yi alkawari zaki saurare ni in kin haihu?"

Ya tambaya in a subdued voice.

Da sauri ta gyada kai, ba don ta yarda ta yi alkawarin a karkashin zuciyarta ba, fatan ta ta rabu da Habib lafiya ba tareda ya maida ita gidan nan nasa ba, data yi alkawarin ita da shi sai dai a kawo gawar ta.

Sai jin Habibu tayi yana dauke hawayen fuskarta da halshen sa, wani al'amari tamkar electrical shocking ya bakunce ta. Ashe ba a iya nan zai tsaya ba? Al'amarin da ya biyo baya mai tsauri da nauyi ne da ya shallake tunanin ta. He began to kiss her passionately wani abu da bai taba faruwa tsakanin su ba. Ko ya manta a inda suke, ko kuma ita ta manta cewa sakakkiya ce a wurin sa. Wani incident da ya dauki tsayin mintuna masu yawa da bazai taba gogewa daga kwakwalwar Rahinah Omar ba. Ya kuma goge tabon abubuwa masu yawa da suka samu muhalli tuntuni akan Habibu Nahuche a zuciyar ta.....


Wayarta ce ta dauki tsuwwa....kira ake akai-akai. Da sauri ta ja baya.... tana wani irin hararar sa tamkar idanun ta sa fado kasa. Habibu ya shafa kai, yana kallon ta da dukkan kauna da soyayya na zuciyar sa, idanun sa har shigewa ciki suke sabida azabar soyayya. Shi kadai ya san azabar da yake dandana. Komai ya dawo masa sabo, ji yake tamkar bai taba kusantar Rahinah ba sai a wannan lokacin. Amma ya san ko shi maye ne Rahinah bazata sake bashi wannan damar ba, idan har ba ya ya yi yaqin kwatowa kansa soyayya ba.

"Nene!"

Sunan da ya bayyana akan screen din kenan. Gabanta yayi wani irin faduwa. Me ta aikata? Me take aikatawa rayuwar ta? Dadin bakin namiji ne zai sa ta gurbata kyakkyawan ginin data faro? Ya su Nene zasu ji in suka ji tana tare da Habib ne a kofar gidan sa cikin motar sa ba tasu ba? Bayan ba yadda basu yi da ita ba kan ta koma masa amma tace a'ah? Me yasa ta yarda ta biyo shi? Shin idan Nene ko Ambasada suka san tana tareda Habibu ba zasu zargeta da raina musu hankali ba?

Da wani irin zafin nama ta bude murfin motar ta fice, Allah ya so ta ya saki lock din, ta leko ta window tace cikin muryar kuka.
"Allah ya isa taba ni da kayi, Allah ya saka min!".

Habib Nahuce. Bai san sanda dariya ta kwace masa ba duk da halin da yake ciki. Yace "Allah ya saka mana tare Rahinatu! Akwai mugu a duniya irin ki? Kin ci albarkacin Baby na, na rantse da sai kin kunshi wani sabon cikin a yau kin haifo su tare sun zama biyu.......". Bata tsaya sauraron mugayen kalamansa ba masu kama da sabon Allah a kunnuwan ta ta nufi titi da mugun sauri tana tare taxi.

Yohana sai ganin ta yayi taxi ta sauketa a gefen sa, ita da tace library zata shiga ta karbo littafi ta fito. In ya kirga daidai ta kwashe akwalla awanni biyu kenan. Ba wannan ne ya bashi mamaki ba sai yadda ta bude motar ta afko kamar wadda aka biyo.

"Are you okey Madame?"

Ya tambaya calmly.

"I'm okey Yohana let's go, kada ka tsaya a ko'ina sai mun isa Frankfurt".

"Is someone following us? So that i report to police?"

"A'a babu mai bin mu, kaidai ka tafi da sauri ka bar harabar wajen nan".

Ya ja motar suka bar wajen yana cewa "alright Madame, but kowanne karamin abu ki dinga gaggawar sanar da police".
Ita dai tace masa ta ji.

Sun yi nisa sosai wayar ta ta sake kara, tayi ajiyar zuciya sai yanzu ta fara samun nutsuwa data tabbatar sun fita daga shiyyar birnin Cologne. Sun kama hanyar da zata kai su Frankfurt.

Da ta duba sai ta ga 10 missed calls daga Nene.

A take ta kira ta jikin ta har rawa yake, ji take kamar Nene ta ga komai da ya faru, ita da Habibu a mota suna kissing. Wani hawayen bakin ciki ya zubo mata, ta ji ta tsani kan ta, ta tsani karatun da ya fiddo ta daga gidan Ambasada, in bata yi wasa ba Habibu na gab da sake rusa mata rayuwa.

"Nene wallahi ina cikin library ne wayar kuma na barta a mota"
"Meyasa kika je makaranta baki jira ni na dawo mun je tare ba idan zuwan ya zama dole? Kinsan Dr. Yace ki daina zirga-zirga" ta share wani uban gumi daga kan goshin ta, tace "Nene i'm sorry littafai na je amsow na clinical assignment dina, kinga ma ban samo su ba, bazan ma kara zuwa ba har sai na haihu. Zan gayawa Daddy a nemomin na saya kawai" Nane tace "better, me zan dafa miki kan ki iso?" Tayi murmushin samun relief tace "anything traditional""to shikenan zan miki tuwon alabo miyar ugu leaf da alayyahu da ganda da busashshen kifi, yayi miki?"
Wani hawaye ya bullo mata, ashe haka soyayyar UWA ke da dadi? Allah ya barta da danta itama ta bashi kauna irin wannan. Allah yasa kuma kada mutuwa ta raba su yana karami sai ya mallaki hankalin kansa ko da zata mutu. Ya zamo cewa ta gama bashi duk wata kulawa da tarbiyyar da ya kamata ya samu daga gareta.

A wannan daren, daga Habibu Nahuche har Rahina Omar, babu wanda ya iya ya runtsa. Dare ne mai matsanancin hazo, cikin watan Nuwamba, Habibu na nannade cikin bargo sanyin kasar Jamus na shigar sa, ba abinda yake so yake bukata a lokacin sai dumin matar sa Rahinah. Amma ta wace hanya zai bi ya dawo da damar da ya samu a baya? Masu iya magana dama sun ce opportunity comes only once in life! Ya bata komai, ya dade da bata komai, ya riga ya bata rawar sa da tsalle. Haduwar su a yau ta maida masa komai sabo in itsown special unique way..... girman Rahinah da soyayyar ta sun karu sun ninku sun hauhawa a zuciyar sa, ya fahimci abubuwa da dama wadanda a baya bai sani ba; Rahinah na daga cikin kasaitattun mata da samun kamar su sai an tona. Irin matan nan ne one in million wadanda duk namijin da Allah yayiwa baiwar mallakar su ya gama bashi rabin addini sa, ya gama bashi farin cikin rayuwa, da duk wani jin dadi dake cikin ta.

A yau???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ya amince da abinda a baya ya ki believing da gangan. Cewa zai iya rayuwa babu Rahinah, zai iya hakuri da rayuwar sa single ba tare da Rahinah cikin ta ba. A yau ya yarda ya amince rayuwar sa bazata taba zama straight ba ba tareda Rahinah a gefen sa ba. Ko zata yarda ta saurareshi idan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login