Showing 48001 words to 51000 words out of 110913 words

Chapter 17 - NAHUCE BOOK COMPLETE BY Sumayya Abdulkadir Takori Kabara .doc

addu%??j ce ban yi masa ba? Don haka tunda dai wannan din ita ce uwar Abdallah kuma mu duka shaida ne a kan cewa ita kadai yake so, sannan kai ne madaurin auren ta, to mu taru mu gyara sunnah, in ba su shirya don Allah ba sa shirya albarkacin dan su. Ku tashi yanzun nan komin dare mu wuce Nahuche in gaya wa madaura auren sa".
Ba karamin jin dadin shawarar Hajiya Daddy Usman da maidakin sa suka yi ba. A take ya kira Ambasada Shehu ya gaya masa duk abin da yake faruwa da hukuncin da Hajiya Kaltume ta yanke.
Ambasada sabida sanin da ya yi wa Habibu da Rahinah sai ya ga cewa shawarar su ba mai billewa ba ce idan har ba Rahinah da kan ta ta amince za ta koma wa Habibu ba, to fa baza%??j haifi da mai ido ba, don haka ya ce su ci gaba da abin da suka tsara, shi kuma zai zauna da Dr. Rahinah formally ya tattashe ta a kan komen ta gidan Habibu don ita ce mai babbar matsala ba Habibu ba. Duk suka yi na%??jm da shawarar Ambasada.
*******



A Nahuche, baffanin Habibu sun ji dadin batun da Uncle da Hajiya Kaltume suka zo da shi. To kowa a kan gwiwa yake da damuwar rashin auren Habibun. Dadin dadawa an ce uwar dan sa Abdallah. Don haka kowa ya yi na%??jm da a maida auren.
Amma zasu jira Ambasada tukunna kamar yadda yace sai ya zauna da Rahinah officially akan maganar komen nata, matsayin ta na bazawara wadda addini ya baiwa damar zaben mijin aure.

Suna kan hanyar dawowa Zamfara daga garin Nahuche wayar Ambasada ta shigowa Uncle Usman, da sauri ya amsa cikin fara%??j yana gaya masa nasarar tafiyar su Nahuche da matsayar da aka cimma idan Ambasada ya gama Magana da ita Rahinah. Ambasada Shehu sai ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya sannan yace da Usman,
%?nunna data ka duba WhatsApp, na turo maka wani abu yanzun nan da %?giaily Trust%??? suka fitar cikin makon nan%???.
Da sauri Uncle ya hau duba dayar wayar sa.
Salatin da ya yi ba Aunty kadai ya firgita ba har Hajiya Kaltume. Sai ya kasa Magana kuma, sabida kunyar Hajiya Kaltume, a lokaci guda yana kissima irin yadda zai saka kafar wando guda da Rahinah, ana ganin ta mai ilmi ashe bata da hankali ko kankani? Kuruciya bata bar ta ba a shekaru 29?
Kasa fada musu ya yi, yayi shiru, duk da tambayar sa ko lafiya da suke ta yi yake jera salati? Sai ya ga gara su ji a bakin sa akan su ji a media. Ya gaya musu Rahinah ce ta yi karar Habibu a kotu, gobe zasu shiga Federal High Court ita da shi su fara Shari%??jh akan dan su, amma su kwantar da hankalin su (he will never let this happen) insha Allah in dai yana raye kuma shine uban ta, zai yi maganin Rahinah.
Jikin su duka sai yayi sanyi, a lokaci guda kowacce ta soma tunanin ko dai a hakura ne? Allah kadai ya san abinda ya boye a karkashin wannan takun-sakar na Habibu da Rahinahr sa, sai kuma su da suka aiwatar da rayuwar su ta dan lokaci tare a Jamus.
Har suka iso gida jikkunan su a sanyaye suke. Aunty Badiya bata kai Uncle Usman jin ciwon abinda Rahinah ta yi ba, domin ya nuna bacin ran sa a fili, fada ya ke ta yi kamar Rahinar na ganin sa har suka isa Zamfara.
Hajiya kam ta fi kowa jin babu dadi, Habibullahi a Kotu! Wani abu ne da bai taba faruwa da shi ba, kuma wai da uwar Dan ka wannan terere da bankada da me ya yi kama. In Rahinah na son karbar dan ta ta bi ta maslaha mana ko ta zo ta same ta ta gaya mata sai kawai ta sa su a bakin duniya?
Dama can Hajiya Kaltume tana jin haushin Rahinah, a bisa ganin cewa, sabida ita Habibu ya ki aure, balle yanzu da ta yi wannan danyen aikin, ana cikin kokarin gyara aure.
Sai Hajiya ta ji Rahinah ta kara sire mata, amma zata ci albarkar Usman don miji ne har miji ga %??iar ta, wanda ba%??j taba jin kan su da Badiya ba shekaru ashirin da doriya, sannan zata ci albarkacin dan ta. A yadda ta san Habibullahi, da son da ya ke wa Abdallah, to ba kotu ba, ko ina Rahinah zata je zata gaji ta bari babu mai iya raba shi da Abdallah.
Uncle Usman yayi kwafa %?nanda hauka irin na Rahinah? Wa ya gaya mata ana jayayya a kan Da? Da, na kowa ne kuma ajiyar Ubangiji ne ga iyayen sa, zamu gamu da ita, sai ta gwammace bata taba sanin Usman Girei ba%???.
Ko da suka isa Zamfara, anan ya bar Aunty Badiya. A daren ya dawo Kaduna, washegari ya nufi %??iirport%??? ya bi jirgin %?siax Air%??? zuwa Abuja don hanyar Abuja ta kazanta a wannan dan tsukin, ba%??j fiya bi da mota ba, balle shi da yake a kagauce da yin tozali da Rahinah, ko a waya bai kira ta ba, burin sa ya bude ido ya gan ta gaban sa, yana kuli-kulin kubra da ita. A sanin da ya yi wa Habibu ko kadan bai son tashin hankali balle abinda zai taba mutuncin sa.
******


*RAHINAH*

Abinci ta ke ci a dakin Yafendo, abinci mai rai da motsi da Nene Balki ta dafa mata na musamman, tana ci suna hira ita da Yafendo hankalin ta kwance ya tsumma a randa. Tana fadi cikin ran ta jibi I yanzu suna gaban alkali ita da dan Nahuche. Har Lawyer ta dauka mai zaman kan ta daga Chambar Lauyoyi masu zaman kan su na garin Abuja.
Sai ganin Daddy Ambassada ta yi tsaye a kan ta rike da jarida, tsabar bacin rai ko sallama bai yi musu ba. Ya ce
%??mahinatu, me na ke gani haka?%???
Ashe baki da hankali baki da tunanin dana ke ganin kina da shi?%???
Ya jefa mata jaridar %?giaily Trust%??? akan cinyar ta sannan ya ce %?naza-maza ki je ki janye karar nan, kafin in kifta ido na, wa ya ce miki ana jayayya a kan yaro? Kina so Ubangiji ya yi hukuncin sa a kan sa? Kina son ku rasa shi gabadaya ko? In kina son rayuwa da yaron da gaske, me zai hana ki koma gidan uban sa?%???
Rahinah ta sunkuyar da kai, bata ce komai ba, ganin yadda Ambasada ke tafarfasa, ko wa ya kai wa %??ian jarida labarin kuma? Bata yi don ta bata ran iyayen ta ba da masu kaunar ta, ko don a yayata su a mediasai don kwatarwa kan ta %??iancin ta da Habibu ya bi ya danne ya ke kuma kan dannewa, domin so ya ke har ta mutu ba ita babu dan ta.
Ita ba don a sa a media ta kai Habibu kara ba, ta kai shi ne don shari%??jh ta kwatar mata dan ta, tunda ta bi shi ta lalama ba wanda ya ji ba wanda ya gani amma ya bi ta da gatse da bakar Magana. Ya raina mata hankali.
%??maza-maza ina umartar ki da ki tashi ki je ki janye karar nan, yanzu yanzun nan kafin isowar Usman, ya gaya min ya taso a jirgi, zai saba miki yadda ba kya zato. Don ta ni kin sani mai sauki ne, har kullum Uba nake mai fahimtar ki da bin ra%??jyin ki, mai yawan yi miki uzuri, hadi da baki damar da Allah ya ce a baki. Amma a wanan karon bana bayan ki Rahinah.
Akwai muhimmiyar Magana da dama nake so mu yi a yau, kawai na ci karo da wannan shirmen naki ana sayarwa a hanyar motoci, tashi maza-maza ki je ki janye ki dawo kafin isowar Usman don ya gaya min kan azahar zai sauka a garin nan.
Rahinah ta dan tsuke baki da fuska cikin alamun gardama, karo na farko da zata yi wa Ambasada musu, Yafendo da bata gane akan me ya ke ta fadan ba ta ce.
%??me ke faruwa ne Jakada?%???
Nan Daddy yayi mata bayani a takaice %??mahinah ta kai Habibu kara kotu, a kan ya bata dan ta!%???.
Sai ga Nene Balki ma ta shigo, ta tsinkayi karshen maganar da yake fadawa Yafendo, salati suka hau yi a tare, Nene na fadin %??mahinah kan ki daya?%??? Yafendo ta ce %?no kin fara shaye-shaye ne bamu sani ba? Don an ce min yanzu a kasar nan mata sun koyi shaye-shaye, kuma kika kunshe baki kika yi shiru kina sabgogin gaban ki hankalin ki kwance kamar kin kashe rai, sai zabga lomar abinci kike, Allah ya raba mu da kotu, ko makiyin mu kada Allah ya kai kotu balle Baban Abdullahi, %??iar nema, ja%??jra.%???
Nene kuma ta ce %??mahinah ki komawa uban sa mana! In kin san kina son yaron ki da gaske? Ki rayu da su har abada cikin salaama da aminci, wannan taurin kan da girman kan ba naki bane a matsayin ki na %??ia mace, na rasa ina kika koyo su, ita %??ia mace da rauni aka san ta da yafiya ga mijin auren ta, ki tashi maza ki bi umarnin Abba Jakada, kin ga shi bai iya fada ba, kada ki sa yau a kan ki ya koya%???.
Cikin bacin rai Ambasada ya ce %?ni ni bata dauke ni Uba ba shi yasa ina ta Magana tana ji na ta yi kunnen uwar shegu da ni, ku bari uban ta na halali ya zo, shi in ya sa ta za ta yi, ya ce min har da dorina sai ya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?buge ta wallahi%???.
Kalaman Ambasada Shehu na %?nata dauke ni Uba ba, ku bari uban ta na halali ya zo%??? sun taba zuciyar Rahinah sun kuma karya ta. Ta mike tana hawaye ta isa gaban Ambasada ta durkusa, cikin rawar murya take magana.
%??ma ni da uban da ya fi ka Daddy, ka yi min abinda kowanne uban halali yake yi wa %??jar sa. Ka yi hakuri zan je in janye yanzun nan. Saboda kai!%???.
Ambasada ya juya ya fita sakamakon kiran sa da ake ta yi a waya duk akan maganar, wadda ke kara yaduwa kamar wutar daji a garin Abuja. Ita kuma ta dauki Jilbaab din ta da mukullin mota jikin ta na rawa ta fita.
Lawyer data dauka wato Barr. Hanifa Suraj Kumo (AMANATA) ta fara kira tana hawaye tana tuki, ta gaya mata Baban ta ya ce ta janye karar, so ta janye, amma kudin da ta riga ta bata ta bar su. Barr. Hanifa ta ce baza%??jyi haka ba, zata maido mata da ko rabi ne. Sannan ta karasa kotun, cikin dan lokaci ta janye karar.
Al%??jmarin da bai yi wa %??ian jarida dadi ba, don sun so samun kudi sosai da issue din Nahuche da ex-wife din sa. Kasancewar Habibu Nahuche wani matashin miloniya mai farin jini a kasar Najeriya. Tana hanyar dawowa gida, Uncle Usman ya iso, Ambasada ya tura direban sa ya dauko shi daga filin jirgi, suna falon saukar bakin sa suna kara tattaunawa akan al%??jmarin.
%??ma tura ta yanzu kan ta je ta janye%??? inji Abba Jakada.
Sai ga wayar Habibu ta shigowa Uncle Usman, inda ya gaya masa %?na shi ya sauka daga Lagos shima yanzu, an aika masa SAMMACI, wai wata mahaukaciyar Likita ta kai karar sa, zai halarci zaman kotu jibi tare da ita%???.
Uncle ya kasa gane halin da muryar Habibu ke ciki a wannan lokacin. Sai ya ji sunan da ya kira Rahinah da shi ya ba shi dariya, ya kuma dace da ita ya ce masa,
%? nna gidan Ambasada yanzu haka, nima ban dade da shigowa garin ba, ka bar duk abinda ka ke, ka zo ka same ni a can. Maitama ne%???.
Habibu ya juya yayi wa PA din sa na Abuja Magana wanda shi ya dauko shi, ya bashi umarnin su fara zuwa gidan Ambasada Shehu kafin ya kai shi gidan sa na Abuja da ke a %?riife-Camp%???.
A dai-dai wani shatale-tale (roundabout) na kan titin da zasu bi su dauki hanyar unguwar Maitama, danja ta tsayar da su.
Kusan a tare suka tsaya da motar da ke barin daman su kirar KiaPicanto fara sol, kamar an ce da shi ya kalli matukin motar, sai ya dan janye jaridar %??iaily trust%??? da ke hannun sa yana dubawa, wadda ke dauke da kanun labarun kai shi kotu. A gefen nasu mace ce fara sol ke jan motar, sanye da (Egyptian Jilbaab) ruwan kasa-kasa, hannayen ta biyu da ke dafe da sityari sun sha zobban zinare guda uku-uku, bai dauki %??ian sakanni ba kwakwalwar sa da kyawawan idanun sa suka gane ta; Dr. Rahinah Omar Girei.
Itama jin alamun idanu a kan ta, sai ta waiwaya kadan, motar su kirar bakar %?eihevrolet-Volt%??? wadda bata da yawa ko a cikin Abuja ba itace ta dauki hankalin ta ba, kamar HandsomeMan din, mai wani irin sassanyan kyau da aji na musamman, wanda ke kwance cikin lallausar farar shaddah Wagambari a bayan motar.

Ko mutuwa ta yi ta dawo wannan fuskar bazata taba bace mata ba, lumsassun idanun nan masu son shigewa cikin nata a yawancin lokuta, har yanzu suna nan yadda suke farare kal, a lumshe, cikin farin glasses tar-tar da shi kamar ba glass ne a idon sa ba sabida garai-garai din sa; Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche, shi ke kallon ta cike da wata irin lumsassar %??isana%??? kwance cikin kyawawan kwayan idanun sa.
Yatsun ta masu dauke da zobban zinare ta kai tana danna maballin dake jikin motar ta, glassai bakake suka maye gurbin masu haske su ka yi sama zuuu! Kamar yadda ta kautar da kai itama, cikin tsananin faduwar gaba marar misaltuwa.
Dai-dai lokacin danja ta basu hannu, ta wani irin zugi motar da gudu ta tsere musu. Ashe an yi ba%??j yi ba, an gudu ba%??j tsira ba.
Domin kuwa kusan a tare su duka suka isa gidan Ambasada Shehu Bichi da ke unguwar Maitama, ta riga su shiga, har ta adana motar ta a ma%??jdanar motoci kafin su iso, akan idon ta mai gadi ya bude musu kofa suka sulalo cikin gidan kamar ita kan ta motar tasu tafiyar takama take yi tamkar Ba-Rumen ubangidan nata (dan kabilar Rumawa).

Kafin PA Mr. Atiku ya gama parking ya fito don ya bude masa, ya bude da kan sa ya fito.
Rahinah bata tsaya ba, kusan da gudu-gudu ta karasa shigewa cikin gida, bata sani ba ko da ace ta tsaya din sun jera, ko alfarmar kallo ba zata samu daga Habibu ba.
Dakin Nene Balki ta fada ta shige toilet ta rufe, don ta san nan ne kadai waje na karshe da za%??jyi tunanin neman ta cikin gidan. Addu%??jr ta daya kada ya kasance wani ya ga dawowar ta, balle a neme ta.
Sai dai kuma tana shiga toilet din Nene na shigowa dakin, ta kuma ga rufo kofar toilet din data yi, sannan kamshin turaren ta %?tiina Ricci%??? shi ke fallasa ta a duk inda ta s higa.
Nane bata kawo komai ba a ran ta, ta dauka ta shiga ne don yin alwallar sallahr azuhur.
******


Is not for free. It's 1000 via
3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank

SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870



Ga dai kiran ya shiga, ga wayar tana ta ruri, amma sai ta nemi dukkan karfin gwuiwar da ta tattara take tinkaho da shi na jin cewa zata iya tarar sa gaba da gaba ta rasa, ta nemi kalaman data harhada a fatar bakin ta don yin magana da Nahuche ta rasa, ta nemi boldness din da jajirtacciyar ego din ta suma ta rasa%???. A lokacin da ta ji calm, cool muryan nan ta Habibu Nahuche cikin kunnuwan ta tana kwarara mata sallama, kamar wanda dama ya ke jiran kiran nata ya amsa impatiently,

"Hello, Ma%??jm, ina kan layin!%???.

Duk sai ta kara daburcewa ta rikice gabadaya.
Ya ya san cewa ita ce ta kira shi?
A ka%??jdar sa bai amsa kiran da bai san ko na waye ba, amma already ya san Rahinah zata kira, psyche din sa ya dade da bashi zata kira din, da wacce fuskar zata kira ne bai sani ba; da tsiya ko da arziki.
Don haka tuntuni Habibu yana jiran kiran nata ne, shi ya sa yaki yin barci, yayi mamaki ma da ta kai har sha biyun dare bata kira ba, a yadda ya san ta da wutar ciki a kan Dan ta, ya san yadda ya kasa barci itama yau bazata iya ba, watakila har gara shi, tunda yana makale da dan sa rabin ran sa a gefe abin debe masa kewa (apple of his eyes), ya fi kyautata zaton kiran nata bana arziki zai kasance ba, kuma ya shirya mata da duk irin wacce ta zo masa.
Shi yasa koda ya ga bakuwar lambar da aka nuna daga cikin Kaduna kiran yake ya san cewa; ita ce. Dr. Rahinah Omar Girei. Don haka bai yi nawa ba wajen dagawa a ginshire, ya amsa a kagauce. Yana magana a kasaice.
He is expecting her rigimammen call a daidai wannan lokacin orbefore. Jin dadin sa daya Junior ya yi barci. Zai ji dadin caccaba mata Magana yadda yake so.
Bayan ya sha jerin tambayoyi masu dimbin yawa daga wayayyen yaron nasa mai kaifin basira da wayayyen kai, da kalaman da suka bashi mamaki, akan BAKUWAR FUSKAR da ya gani ta gidan Mummy Badiya a yau,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login