Showing 1 words to 3000 words out of 112633 words

Chapter 1 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

2986

 *DAURIN GORO*

SHAFI NA DAYA (1)

©️HAFSAT RANO

ALKALAMI TV
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

WATTPAD: HafsatRano


**********
*MAFARIN KOMAI*.

A guje ta fito daga dakin jikin ta cikin shigar kayan ma'aikatan jinya, da sauri duk suka mik'e ganin ta nufo su

"Ta sauka Dr!" Suka tambaya a rude kuma a tare

"Ina maigidanta?" Ta maida musu ba tare da ta amsa tambayar tasu ba.

Matsowa yayi da sauri yace

"Gani."

"Ok muna so ka saka hannu ne, ba zata iya haihuwa da kanta ba dole sai dai ayi mata aiki."

"Innalillahi, aiki kuma Dr?" Ya tambaya a kideme

"Shine kadai abinda zamuyi mu ceto rayuwarta data abin cikin ta. Kayi hakuri babu lokaci."

"Shikenan, Allah sa ayi a sa'a."

Bin bayan ta yayi, suka je ya saka hannu sannan ya dawo wajen sauran ya tsaya yana kaiwa da komawa.

Bayan shafe tsawon mintuna arba'in da shigar su ta sake fitowa, wannan karon akwai alamun nasara a tattare da ita. Kafin ta k'arasa garesu sukayi saurin isa, fuskar su dauke da alamun tambaya, hannun ta ta mika alamun abata tukwuici kafin tace

"Congratulations Your highness, an yi nasarar ciro muku dan saurayi."

Da sauri ya kalle ta kamar be ji me tace ba, gid'a masa kai tayi alamun gamsarwa, maida kallon sa yayi wajen sauran da duk fuskokin su ke cike da farin ciki yace

"Alhamdulillah ya ALLAH!" Ya furta da karfi

A duniya bashi da wani buri da ya wuce yaga an haifa masa d'a namiji, yau sai gashi Allah ya cika masa burin sa, ba ma shi ba, duk wani makusancin sa yana masa sha'awar haka. Duba da irin tarin dukiyar da Allah ya bashi. Ya hakura ya barwa Allah zabin sa, sai gashi ya bashi a lokacin da beyi zato ko tsammani  ba.

A take wajen ya kaure da murna, babu wanda ya tsaya tambayar lafiyar mahaifiyar, tuni kowa ya hau kokarin kiran waya domin sanar da yan'uwa da abokan arziki.

THE ONE AND ONLY HEIR To *MARWAN DIKKO* FAMILY IS BORN.

A daidai lokacin Inno na kwance a gadon asibitin, babu tazara tsakanin dakin da take da babban dakin da aka ajiye Matar Alhaji Marwan, saboda haka tana jiyo hayaniyar mutane me cike da tsantsar farin ciki, kallon jaririyar dake kwance kusa da ita tayi, zuciyar ta tayi rauni, anya? Anya bata zalunci yarinyar ba kuwa? Kallon gefen ta tayi taga jakar da aka hado mata tare da jaririyar, soyayyar ta da kudi abu ne me girma, babu abinda ba zata iya aikatawa akan su ba, sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo gaba, gashi babu ko digon soyayyar yarinyar a zuciyar ta. Abu daya ta sani shine rayuwar jaririnta, rayuwa me inganci da tsananin gata da zai taso da ita. Idan ta tuna wannan sai ta ji ta samu sauki, sai dai fa tana da kudurin komai daren dadewa sai ta karbo shi.

Shigowar su Yalwati da sauran jama'a ne yasa ta ɗan saki ranta, suka shiga daukar jaririyar kowa yana yaba kyawun ta, ita dai Inno jin su kawai take ba tare da ta tanka ba, ganin zasu cigaba da chaja mata kai da hayaniyar su yasa ta rufe idon ta alamun bacci take yi, hakan ya bata damar cigaba da yin tunanin da take akan wannan babban al'amari ne cike da tarin matsaloli a gaba.

Hmm

****

*AMINATU*

Kowacce rayuwa cike take da kalubale, sai dai ni tawa rayuwar da wani salon na sarkakiya tazo min.

Rayuwa ta cike take da abubuwa masu yawa. Duk da haka  bazan ce nafi kowa shiga matsin rayuwa ba, sai dai ina da tabbacin ina cikin sahun farko na mutanen da za'a kirasu da wanda rayuwa tayi *Daurin Goro*.

_Eh daurin da nake tunanin babu wani mahalukin da zai iya warwareshi, na riga na sare, na barwa Allah ikon sa, ina kuma kyautata zaton zai kawo min yankewar sa kafin barin numfashi na._ Ajiyar zuciya na sauke ina bitar Rayuwa ta daki-daki kamar a lokacin komai yake faruwa.

Zaune nake a faffad'an tsakar gidan mu wanda ke dauke da dakuna hudu falle falle sai madafi daga gefe, randunan ruwa manya, daga dayan bangaren rijiya ce babba da makewayi a gefenta, gidan gidane babba daya hada da mutane da yawa sai dai kowa yana ɓangaren sa inda babban zauren gidan shi ya haɗa kowa da kowa.

Dakin farko ya kasance dakin Baba, sai dakin Inno daga chan gefe, dakin yara matan gidan ne a kusa dana inno, daga dayan barin dakin Yalwati ne sai dakin samari dake daura da hanyar fita daga shashen namu.

Tsintar shinkafa nakeyi tun kafin rana ta fito gashi har ina neman makara ban samu na gama ba, a gurguje nakeyi saboda lokacin makaranta kar na makara, cikin sa'a na kammala nayi saurin zubawa a ruwan waken dake ta tafasa bayan na tabbatar da dahuwar waken saboda gudun abinda zai je yazo. Gyara wutar nayi ganin ta fara zarewa na karasa gaban rijiya domin yin kwaskwarima. Cikin sauri sauri na zura uniform d'ina wanda duk ya tsofe wani wajen ma ya yage na sake fitowa, lokacin har yaran gidan sun fara fitowa ana layin alwala. Haka dabi'ar gidan mu take, tun tasowa ta kawo yanzu hakan bata chanja zani ba, kafin su gama alwalal sai sunyi fada kashi dari. Murmushi kawai nayi na fada dakin Inno dan gaishe ta, a tsaye na ganta tana kokarin daura dankwali tana ganina ta tsaya.

"Ina kwana Inno.?" Na durkusa har kasa kamar ko yaushe. Bata amsa ba sai kallon kayan jiki na da tayi kadan kafin tace

"Kin gama aikin naki ne da zaki wuce makaranta?"

"Eh." Nace ina kallon ta.

"Kin zuba ko kin gama?"

Iya sani na Karime ke karasa wa idan na zuba, tun da ita ba makarantar take zuwa ba, a darare nace

"Na zuba karasawa kawai zatayi a kwashe Inna."

Dan bata fuska tayi tana yatsine baki kafin tace

"Jeki jira ta karasa yau babu me karasa miki Karime bata jin dadi."

"Toh."

Kawai nace na mike jiki a sanyaye na koma bakin dakin mu na zauna ina kallon yadda rana ta d'aga sosai alamun na makara, ina nan zaune kowa ya fito aka hau hada-hadar shan koko, ban bi ta kai ba ni dai buri na na ganni a makaranta. Sai bayan wajen rabin awa sannan na kammala na sake dauraye kafata na fice daga gidan da sauri kafin Inno ta ankare ta kawo abinda zai hana ni zuwa duk kuwa da na kan yi mamakin dalilin da yasa inno take bari na zuwa makaranta, bayan haka bama kowa ne a yaran gidan ke samun zuwa makarantar ba.

A babban zauren gidan naci karo da Nura, da alama lokacin zaiyi sallah, gaishe shi nayi na wuce ba tare da jiran amsar sa ba.

Tafiya ce mai tsawo kafin ka isa makarantar guda daya jallin jal dake a kauyen,  Kamar kullum babu malamin daya shigo har nazo, haka dabi'ar makarantar take, a rana sai ka samu malami daya ne kawai zai shiga duk suna zaune a staff room suna hira, a haka dai muke dan samun abinda muke samu wanda bamu da tabbacin daidai suke koya mana sai dai saboda ba gane wa zamuyi a lokacin ba yasa muke binsu a haka. Musamman ma ni da na taso da son karatu da kuzun zama wani abu a kauyen namu tun bayan ganin da nayi wa jikokin mama Ladi makociyar mu dake zaune a birni, sun kawo mata ziyara, tun daga lokacin na sawa raina zama kamar su, sai dai hakan ba mai yiwuuwa bane duba da irin gidan dana taso.

***
Haka rayuwa ta cigaba da garawa, babu abu daya daya sauya na daga al'adun gidan mu, tun da na taso nasan Inno ita ke ciyar da gidan mu ko nace shashen mu, shiyasa ko babanmu baya mata musu, Yalwati kuwa ta zama kamar ba kishiiyar ta ba, dan bayan na gama girkin shinkafa da waken da karime take fita dashi wajajen sha biyun rana, Yalwati ce zata dora alala, sannan tayi dambu da wake shima a sake fita dashi, duk kuma jarin na Inno ne.

Inno mutum ce wadda tasan darajar nema, bata taba zama haka nan, yau ta buga nan gobe ta buga chan, bayan sana'ar saida abinci har kiwon akuyoyi take yi da kaji, ga sana'ar abin kad'i dangin su kuka da su kubewa, da sauran abubuwa, sai ya zama ma a kaf kauyen namu babu wanda zai kama kafa da ita Indai a samu ne, shiyasa kaf gidan mu suke shakkar ta, babu wanda ya isa ya daga mata yatsa balle Baba da Yalwati da suka zama kamar yaranta, sai abinda tace musu ake aiwatar wa.

*******
Kiran da Karime ke kwala min yasa na ajiye kibiyar hannu na na fito, riko ni tayi da sauri tana haki

"Lafiya dai?" Nace ina kallon yanayin ta

"Ina fa, dalla kowa yana chan kallon bak'in gidan Bature sun zo ke kina nan kina tsifa."

"Dan Allah!" Nace ina fad'ad'a fara'ar fuska ta

"Wallahi ana chan duk ana ta kallon su abin sha'awa, na duba ban ganki ba shine nazo kirankii, kinga motar da suka zo acikin ta, har da wata yarinya kamar girman mu, kinga kayan jikin ta kuwa? Wayyo yan gayu sun ji dadi wallah"

Ta fada tana rik'e haba, da sauri na koma ciki na dauko dankwali na na daura muka fice da gudu, dukkannin mu sirara ne babu kibar arziki, yadda muke gudun kadai zaka tabbatar da yarintar mu, dudu du a lokacin ba bazan bi shekaru goma sha biyu ba, tsiran mu da karime shekara daya ne saboda haka ba zaka gane wani banbanci me yawa a tsakanin mu ba.

Tun kan mu karasa muka ga ana juyowa, hanne ce ta tsaida mu tana dariya

"Ina zaku wai, kallo ya barku ai sun koma gida, sai wani jikon kuma."

Haushi ne ya kamani, duk zuwan  da zasuyi ban taba samu na gansu ba har su tafi, a take na kudurce a raina wannan karon babu abin da zai hanani ganin su, ko nima na samu na dorar da labarin su.

Kullum da safe idan na tashi ta kofar gidan nake bi, haka ma idan na dawo, ban taba samun nasarar ganin ko da cikin gidan bane. Gida ne me girman gaske, hade da babban gidan gona da tsayawa fasalta yanayin girman sa ba mai yiwu wa bane. Duk da karancin shekaru a lokacin da kuma yanayi na duhun kai da kauyanci na gane cewa ba karamin masu kudi bane mamallaka wannan wajen, duk a irin wannan lokacin suka zo gaba d'ayan su su jima sosai, idan suka tafi kuma shikenan sai wani lokacin me tsawo.

Gidan Bature kamar yadda mukayi wa gidan da lakabi, sai dai a zahiri ba haka sunan me gidan yake ba, tsari da yanayin gidan da bamu taba ganin kamar sa ba yasa muke kiran gidan da gidan Bature.

***
Tun gabanin magriba garin yake ta hadewa, alamun za'a iya samun ruwa a kowanne lokaci, muna daga kofar dakin mu dasu hanne muna hira da karad'i Inno ta kwala min kira, tashi nayi na karasa wajen ta ina kallon hannun ta

"Yi maza kije shagon Umaru ki siyo min maganin sauro yanayin garin za'a iya ruwa kowanne lokacin."

Karba nayi na juya da niyyar kiran me rakani, dakatar da ni tayi ta hanyar cewa

"Ina kuma zaki koma?"

"Su karime zan kira su rakani Inna."

"Saboda ku tsaya min shiririta a hanya ko? Kin wuce da sauri ko sai na bugo ki?"

Da sauri na juya nayi hanyar waje zuciya ta duk babu dadi, duk yawanmu na rasa dalilin da yasa ni kadai Inno take takurawa.

Sanda na isa shagon ya riga ya rufe, juyawa nayi ina tunanin yadda zanyi, sama na sake kalla naga yadda hadarin ke sake hadewa nayi saurin daga kafata na kara sauri don zuwa shagon dake chan kasa kadan.

Sauri sauri nake nabi ta wani lungu ina kokarin ganin na isa kafin ruwan ya sakko, cikin sa'a na samu shagon yana bude shima yana kokarin rufewa, da sauri na bashi kudin na karbi maganin sauran na juya na kamo hanyar gida a lokacin garin ya kara hadewa.

***
*Gidan Bature*

Dukkanin su suna zaune a babban falon gidan, kallo suke suna hira gwanin sha'awa, sun kusa a ƙalla su goma maza da mata, Ja'afar ne ya kalli Farouk da tun da aka fara hirar yana rike da waya be tanka musu ba, magana suke akan fitar da zasuyi gobe dan zaga gari.

"Ya Farouk." Ya kira sunan shi yana kallon sa

"Uhum?" Ya amsa yana yin kasa da wayar dake hannun sa

"Maganar fita gobe, U haven't said anything bayan kuma kai kadai ne zakayi convincing Dada ta yadda."

Be tanka ba ya sake maida kansa kan wayar kamar ba zai ce komai ba, ganin haka yasa Ja'afar zungurar Amal ya nuna mata bangaren Farouk din, duk ciki tasu tafi zuwa d'aya, babu wani abu da zata nema beyi mata ba sai dai idan bashi dashi din.

Tashi tayi tsam ta isa gefen sa ta zauna ta marairaice murya

"Dan Allah Yah." Hade hannayenta tayi waje d'aya tana sake kallon sa, hararar Ja'afar yayi kafin ya mike yana ware hannayen sa, duk sun maida hankalin su kansa suna jiran su ji me zai ce, takawa yayi a nutse har gaban window dake makale a falon ya zuge curtains din, sama ya kalla yaga yadda garin yayi, murmushi yayi ya tura hannun sa gaba daya waje yana kama sanyayyiyar iska dake kadawa a hankali. Wajen mintinan biyu yayi a haka kafin ya zaro hannayen nasa ya juyo ciki yana kallon su.

"Zan yi magana da Dada, shikenan?"

Ihu suka sa gaba daya cikin murna, yana jin su ya juya da sauri ya fada dakin su, ƙatuwar rigar ruwa ya dauka ya saka hade da takalmin sa na ruwa ya fito ya fice daga gidan gaba daya.








ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

DG
Shafi na biyu (2)


******
Lokaci daya iska me karfin gaske ta taso, gaba daya bana ganin gaba na, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ni, na sani sarai idan har na bari ruwan nan ya taba lafiyar jiki na kashi na ya bushe, ganin da gaske bana ko ganin hanya yasa na makale gefen wani shago na kudundune kaina ina jin matukar tsoro. Ina nan makale yayyafi ya fara sauka a hankali, tsoro na ya dadu, zuciya ta tayi rauni sosai, kamar daga sama naji an dafa kafada ta, cikin tashin hankali na dago kaina,ban samu nasarar ganin fuskar kowaye ba, saboda tsananin hasken torch light din da aka sa aka haske ni. Cikin muryar tsoro na furta

"Waye!"

Be amsa ba, ba shi kuma da niyyar amsawar, illa sake dalle ni da yayi, take hasken yayi tasiri rage kaso tamanin cikin dari na gani na, baya da ƙurar da ta riga ta cika min idon nawa, da sauri na mike ina kokarin daidai ta zaman riga ta, na fara alamun barin wajen, hannu naji an saka an riko ni, cikin wata iriyar murya mara fasali ya furta

"Gidan uban wa zaki? Ai wallahi kinyi kadan tsuntsu daga sama gashashshe."

Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskata jin muryar Garbati, mutumin da ko a mafarki bana fatan hada hanya dashi, waye be san shi ba kaf kauyen nan namu, tantirin dan iska ne, lamba daya, gashi babu wanda ya isa dashi kaf kauyen. Da sauri na ja da baya ina kokarin sake shiga cikin ruwan sosai, damko ni ya sake yi nayi kara da karfi jin zafin rikon da yayi min, ja na ya shiga yi yana kokarin turani cikin shagon da tun zuwa na wajen na lura da yar kofar dake bude, amma banyi tunanin akwai mutum ciki ba, da karfin gaske na hau kokarin kwatar kaina, sai dai ko kusa da hakan ban kai ba , duba da yanayin karfin ba daya ba. Tuni na hau kuka ina magiyar bashi hakuri, tunda ayi ƙarancin shekaru na nasan hakan da yake me yake shirin aikata min. Be saurara ba, ko ma nuna alamun yaji abinda nace, haka ya tura ni ta karfi ya maida kofar ya tura yana sakin wani shu'umin murmushi.

Tuni na watsar da aiken Inno, na shiga ihu da dukkannin murya ta ko Allah zai sa a jiyo ni, dariya ya shiga yi ba kakkautawa.

"Yarinya da kin hakura babu shegen da zaiji ki, uban me ya fito dake a wannan lokacin shegiya."

"Aike na akayi wallahi." Nace ina sharbe hawaye da majina.

"Daidai kenan, idan na ci ubanki zaki gane shayi ruwa ne."

Ya fada yana kokarin matsowa kusa dani.

Sosai na kara karfin murya ta, cikin tsananin tashin hankali, magiya nake masa ina rokon sa, sai dai hakan ba sa ya fasa aiwatar da abinda ya kudurta a ransa. Tun daga nan bansan me ya kuma faruwa ba😭😭

***
***
Tafiya yayi sosai yana mai jin dadin yanayin garin, kafin zuwa lokacin da iskar ta taso, sauri ya kara don ganin ya isa gida, be yi tunanin ruwan zai zo da iska haka ba. Saukar ruwan ne ya rage karfin iskar sosai, hakan ya bashi damar cigaba da tafiyar sa cikin kwanciyar hankalin ruwan na dan taba fuskar sa kad'an-kad'an. Kamar daga sama yaji ihu, ihun ma na mace me karancin shekaru, sai dai karar saukar ruwan yayi tasiri kwarai wajen kasa tantance daga ina ihun yake, hankali ya tashi ya hau neman ta in da muryar ke fitowa, kamar mahaukaci haka ya shiga kai kawo a cikin ruwan, hankalin sa ne ya kai wajen, da wani irin mugun guda ya nufi dan karamin shagon daya gama tabbatarwa daga nan ɗin ne yake jin kukan, beyi wata wata ba yana zuwa ya daki kofar da dukkan karfin sa. Abinda ya gani yayi mugun daga masa hankali, da gudu yayi kansa ya shiga dukan shi, duka me cike da tsantsar bacin rai. Yanayin rashin karfi da a tattare da Garbatin ya hana shi katabus, sai daya yi masa duka sosai sannan ne hankalin sa ya dawo kanta, tana kwance kamar mara rai, abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login