Showing 72001 words to 75000 words out of 112633 words

Chapter 25 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7450

suka dade da mantawa da yadda farin ciki yake."

Madaidaicin study room din sa suka nufa, daga shi sai Farouk da Anty Safiyya, yaran na falo kowannen su ya samu abin tattaunawa da zuciyar sa, cikin gamsasshen bayani Farouk ya warware musu komai na abubuwa da zai iya sanar dasu, har zuwa lokacin da yayi bankwana da kowa.
    Babu digon mamaki ko tashin hankali a tattare da uncle Aliyu bayan ya gama sanar dasu komai, a yadda ya nuna ma kamar dama yana da masaniya da dukkan abinda ya faru ɗin.
   Da kyar suka barshi ya koma gida da niyyar zai dauko abubuwan bukatuwar sa ya dawo nan ɗin, sai a sannan ya tuna da maganar supervisor din sa daya ke kiran sa, a gaggauce ya tura masa mail na ban hakuri da bayanin uzurin daya riƙe shi, babu komai yace masa ya kuma sake bashi lokaci akan yazo ya ganshi gobe idan Allah ya kaimu.

Kwanan sa biyu ya gama tattare komai ya dawo gidan nasu, Anty Safiyya da duk ta tashi hankalin ta ta dauka ba zai dawo ba, sai data ganshi sannan hankalin ta ya kwanta.
Karatun sa daya zo gangara ya bada himma wajen hattama shi, shi kanshi a yanzu hankalin sa ya soma komawa gida, yana ji a ransa wannan lokacin zai hadu da Aminatu, duk da babu wani labari daya samu tun bayan zuwan sa game da komawar ta Shagari, amma kowanne lokaci cikin bibiya yake yana fatan Allah yasa ta koma.
Shirye shiryen komawar su ya kankama, gefe guda yana cigaba da zuwa shagon dan ba karamin sabo yayi da mutanen wajen ba, tun da suka ji zai tafi suka shiga tashin hankali, barin ma Mr John daya sakar masa kusan dukka ragamar wajen shi sai dai ya dan duba abinda yake ganin zai iya amma komai a wajen Farouk ke kula dashi cikin kwarewa da kaffa-kaffa.

***
Tsawon kwanaki hudu kenan tun bayan da akayi min aikin, sai dai ba'a cire ba sai zuwa karshen sati idan mai duka ya kaimu.
   Kowacce uwa zata fuskanci yanayin tashin hankalin da nake ciki, batan d'a ba abu bane mai sauki, na rasa inda zan saka kaina, babu wani labari game da batan Iman, duk da kwantar min da hankalin da suke hakan bai saka hankalin nawa kwanciya ba, ji nake kamar na gudu daga asibitn na tafi neman ta da kaina,sai dai nasan daga Anas har Kamal suna iya kar kokarin su wajen ganin an samu ko da wani hint ne akan haka, kullum cikin jiran kiran su muke amma shiru kake ji kamar malam yaci shirwa, babu wani bayani gamsashe. Addu'a muka dukufa yi babu dare babu rana, ba ta kaina nake ba, buri na kawai naga yata, ita kadai ce dangin da nake dashi na kusa, duk wani da zai rabe mu da sunan kauna ba kamar ni da itan ba.

***
Ranar da za'a cire min abinda aka saka aka nannade idon dashi duk jikina yayi sanyi da tunanin abinda zan tarar. Dishi-dishi na soma ganin komai, nayi saurin runtse idon ina jin kamar sun sake kankancewa akan yadda suke a dah, a hankali na sake bude su ina duban mutanen da ke dakin daya bayan daya, har lokacin bana ganin su tar sai dai ina iya banbance komai da kowa, glass likitaan ya saka min hakan ya taimaka wajen kara karfin ganin nawa, sai dai babu kaso hamsin ciki dari na gani na adah.

     Kuka nake so nayi amma babu hawayen ma balle har na saka ran zasu zubo, da zuciya ta na shiga kokawa cikin yanayi mara misaltuwa, an cuce ni an lalata min rayuwa yanzu kuma an kashe min baban jigo na rayuwar mutum, idan aka taba maka ganin ka an gama da kai, makanta babbar musiba ce sai wanda ya sami kansa a ciki ne kawai zai gane. Kai tsaye na yanke wa kaina hukunci na kira kaina da Makauniya, eh makauniya mana tunda menene banbanci na da wanda basa gani gaba daya, illar ido daga ranar da ya riga ya tabu toh daga lokacin sai dai hakuri saboda yadda zai tayin gaba.

***
Kai tsaye gida muka wuce bayan an sallame ni, babu Anas babu Kamal sai keke napep muka samu ya kaimu dauke da kayan mu, waya ta dake saman cinyata tayi kara, na dauka ina duban screen din, bazan iya karanta rubutun ba, dole na jawo glass din na saka na shiga bin rubutun a hankali ina kokarin karantawa, ji nayi idon ya fara ruwa, dole na rufe na kira shi kai tsaye ina manna wayar da kunne na

" Kina ji? Gamu nan tare da Daddy da Uncle Kabir, zasu duba ki sai kuma yayi miki maganar Iman, ina tunanin zai iya taimakawa idan yasa baki a kara tsaro sosai wajen neman nata, sai mun ƙaraso."

"Ai an sallame mu ma, muna gida."

"Kash, shikenan bari na fada musu, zan kira ki."

Kashe wayar yayi ya juyo baya

"Daddy Ashe an sallame su ma, wai suna gida."

"Toh, babu damuwa sai muje station din da kace case din na hannun su, idan yaso sai muji yadda za'a yi."

Kallon Daddyn su Farouk yayi yace

"Friend ban taba ganin Kamal ya zama so serious akan abu irin wannan lokacin ba, shiyasa nake so nayi supporting nasa with all I can."

"Hakan nada kyau, ban taba tunanin yara na bukatar support dinmu ba sai bayan na rasa Farouk, ban taba bashi dama yayi wani abu da kansa ba, i always find fault a kansa bansan me yasa ba, sai da kuma ya matsa nake dana sani."


"Suna bukata sosai, idan yaro yazo ma da abu ka fara bawa abun big thought,idan kaga akwai fault a ciki sai ka zaunar dashi ta cikin hikima ka fahimtar dashi illar abin, amma idan kace zaka zama tough toh yaran ka zasu na tsoron ka, ba kuma zaka taba sanin halin da suke ciki ba, komai a boye zasu dinga yin sa sai abu ya kwabe kuma sai kaji ana wallahi wallahi."

"Haka ne." Yace yana girgiza kansa.

Hirarrakin su suka cigaba har suka isa station din, waya Daddy ya daga ya kira commissioner of police na gaba daya Kano state ɗin ya sanar masa abinda yake so ayi, kai tsaye ya amince ya kuma hada su da head na station din da case din ke hannun su, a take aka chanja case din zuwa Babbar headquater su.

Dukkanin su a gajiye suke dan ba karamin yawo suka sha ba akan case din da kuma wasu harkoki na bussiness da suka shigo dasu garin na Kano, a gidan Dadah suka yada zango la'asar likis, zarewa Kamal yayi ya nufi gidan Aminatu dan tare zasu koma da Daddy sablda yadda ya ke kokarin ganin ya dora kamal ɗin akan komai na kasuwancin sa.
Har dare suna gidan sai da suka ci tuwo sannan suka tafi driver ya ajiye su a airport, abin ka da tafiyar manya cikin yan mintuna suka isa Abujan.
Dukkan abubuwan daya saba gabatar dasu sai daya kammala su kafin yayi shirin kwanciya, be iya zuwa ganin mahaifiyar sa ba yau kamar yadda ya saba idan ya dawo yakan je suyi hira yaji bukatar ta, har ya kwanta ya tuna da wani mail da wani abokin cinikayyar sa dake birnin London yayi masa tun rana, ya kuma kirashi akan lallai ya duba a yau din dan abin nada muhimmanci.
Tsam ya mike Ammi dake kwance ta bishi da ido tana gyara kwanciyar ta, hutun sa koda yaushe kadan ne, daren da yake samu ya huta ma sau tari yana kwanciya zai mike ya shiga wata sabgar kuma da na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Shiyasa wani lokacin akan ce mara arziki yafi mai shi kwanciyar hankali da nutsuwa.
Zama yayi yana dora computer a saman dan karamin table din dake cike da tarkacen takardun sa, kunna tayi ya runtse idon sa yana jin kansa a cunkushe. Email ɗin sa ya shiga ya fara dubawa a hankali yana nazarin komai.
Tsawon lokaci ya dauka yana dubawa kafin ya kashe komai, wayar sa dake ajiye saman bedside drawaer ya dauka yana kokarin sata a flight mood sakon dake yawo a saman notification bar din sa yaja hankalin sa, budewa yayi ya soma karantawa

_"Cikar buri shine samun abinda zuciya ta kwadaitu dashi. Haka ma abu mai matukar muhimmanci na faruwa na da mutane masu muhimmanci.Kunyi tarayya akan abu guda, ba tare da sanin ku ba, saboda ku ɗin wawaye ne mayaudara. A yau abinda yafi komai muhimmanci a gareku kai da wanda kake kira aminin ka na hannu na. Ina fatan ku samu karfin zuciyar iya fuskantar abinda ke tunkaro ku!"_

Be fuskanci abu daya da sakon ke nufi ba, sake karantawa yayi ko zai samu wata amsa aciki, sai dai a yadda sakon yazo babu wani abu da zai iya fassarawaa ciki har ya gane inda maganganun suka dosa.

Menene sukayi tarayya da aminin sa akai? Abu kuma mai muhimmanci gare su? Dole yasa a bibiyar masa number sakon da safe idan Allah ya kaimu.
Gaba daya sai yaji dan guntun baccin dake idon sa ya kaurace masa, dole ya nufi toilet ya dauro alwala ya shiga nafilfili yana rokon ALLAH ya kare su daga sharrin masu sharri.



*Rano**DG*

                       *32*

★★★
Da safe ya tashi yana shiryawa sakon na cigaba da yi masa yawo a kwakwalwa, be wani tsaya karya wa ba ya karasa ya gaida Hajiya Turai a tsaitsaye ya fita.
   Daddy shirye yake shima tun bayan da sukayi waya saboda haka yana fita suka hadu suka dau hanya, wayar sa ya ciro ya mika masa ya duba sakon, shi din ma bai wani gane komai ba, sai ya kashe ya mika masa yana kallon sa

"MD ban gane komai akan sakon nan ba."

"Nima hakan ce, kuma iya tunani na na kasa gane waye zai tura dashi?"

"Shine, hanya mafi sauki ayi tracing sakon,daga nan sai mu san yadda zamuyi."

"Shikenan." Yace yana lumshe idon sa, daren jiya bai wani runtsa ba, ba wannan ne karo na farko daya fara cin karo da irin wannan sakwannin ba, sai dai na yanzu yasha banban da sauran, idan har ya fahimta komene yana da alaka da abokin sa, hakan ya kara saka shi a taraddadin waye zai masa wannan?

Lokacin da PA d'insa ya bashi statement din dake kan sim card din yayi mamaki kwarai, suna da duk wani information da akayi register sim din dashi bashi da alaka da wanda ya rubuto sakon, ga dukkan alamu ma irin sim card masu register akan su ne sai dai kawai ka siye su a haka.
Shafa kansa yayi ya mikawa Daddy result din yana sake resting sosai akan kujerar office din nasa, dogon nazari Daddy yayi kafin yace

"Ina ganin so ake ayi wasa da hankalin mu, a shagaltar damu da abinda yake mai muhimmanci, karka damu zan san yadda za'ayi."

"Ok duk yadda kace haka za'a yi."

Wayar sa ce ta hau burari, duba wa yayi ganin KAMAL ne yasa ya dan tura hular sa baya

"Kamal ba zai barni na huta ba idan ban tashi tsaye akan case din nan ba."

"Da gaskiyar sa, atleast he's willing to help."

"Haka ne."

Yace yana bin kiran, magana sukayi kadan ya ajiye wayar ya cigaba da duba abubuwan da zai duba suna hira jefi jefi.

***
Duk motsin Farouk na kan idon Anty Safiyya, gani take kamar zata sake rasa babbar damar da take ganin ita kadai ce zata sata komawa ƙasar ta, ta gaji ainun, tana bukatar wani dangi a kusa da ita, ace rayuwa daga kai sai miji sai yaya. Tunanin da kachokam ya tafi akan Ja'afar, kullum kwanan duniya da tunanin sa take kwana take tashi, ba abu bane mai sauki a raba uwa da danta tun be san waye shi ba,tana bukatar ji daga gareshi, tasan matsalar sa, abinda yake so da wanda baya so.
Karatun Farouk ya kare, saboda haka uncle Aliyu ya shiga shirye shiryen dawowar su a boye ba tare da sanin kowa ba sai shi Farouk din.
Sai da komai ya kankama sannan ya sanar ma Anty Safiyya, ranar bata iya runtsawa ba kwana tayi tana duban ticket din tana hawayen farin ciki

Jirgin karfe sha biyun dare zasu hau, saboda haka sai bayan sun gabatar da sallar isha sannan suka fito, yaran duk basu da walwala idan ka cire mahaifiyar su da har nema take ta manta wasu abubuwan nata sai da Uncle Aliiyu ya ankarar da ita.
Duk da Farouk ba a wannan lokacin yaso ya koma ba, amma shima yana bukatar jin amsoshin dake dan kare a zuciyar sa.


***
Kuka nake na zuci na rasa wanda zan fadawa damuwa ta, yau tsawon mako guda kenan da kwanaki biyu babu labarin ta, Hajiyar su Anas sunzo sun duba ni ita da Ramlah da wata kanwarta sai dai yadda naga Hajiyar tayi min sai nake jin kamar akwai lauje cikin nad'i, ina kyautata zaton ba a son ranta ta amince wa Anas ba. Hakan kuwa be dame ni ba, dan ni yanzu ba ta aure nake ba, buri na daya shine naga yata na kuma san wanda yake kokarin kassara mana rayuwa ba tare da mun aikata masa komai ba.
    Duk da Kamal ya bani tabbacin maganar tana hannu manya amma na kasa aiwatar da komai, magana ma idan ba Baba Altine tayi da gaske ba sai na wuni bance komai ba, daga uhum sai um um.
    
Murmushi na saki me matukar ciwo, bayan na dawo daga dogon zangon dana tafi na tunanin rayuwa ta,tun daga lokacin dana budi ido na na ganni a wannan duniyar me cike da mutane marasa tausayi da imani.
    Mutane biyu masu matukar muhimmanci a rayuwa ta a yau na rasa su, ciwon da zuciya ta ke ciki ba zai misaltu ba, da kyar na mike daga kwanciyar da nayi,waya ta dake yashe a saman gado ta dau ruri a karo na uku, karamin tsaki naja kafin na mika hannu na dauka, kamar yadda na zata shi din ne kuwa, *Kamal*. Murmushi nayi daya fi kuka ciwo  na katse kiran ina jingina da jikin dan madaidaicin fridge din dake daura da kofar shigowa dakin.
   Sake shigowa kiran yayi na daidai ta zaman glass din ido na ina dagawa cikin muryar data fi kama da wadda bata da gata ko galihu nayi masa sallama cikakkiya kamar yadda manzon Allah (SAW) ya koyar damu.

"Ina ta kiran ki tun dazu."

Yace kai tsaye bayan ya amsa sallamar tawa.

"Sorry na tafi wani dogon tunani ne kamal."

"Zaki fara ko? Gani nan zanzo na dauke ki muzo nan station din, Daddy ma sun kusa ƙaraso wa shida Uncle Kabir."

Dan dum naji gaba na ya fadi nan da nan, dakewa nayi na amsa masa da toh na fito falon, Baba Altine na zaune tana tunani gefen ta karamar jikar tace data dauko ta tun zuwan da tayi ganin gida zaune tana barar gyada.
  Zama nayi a gefe ina juya wayar hannu na, tunanin haduwar da zanyi da mahaifin kamal nake, duk sai naji na damu, kasan zuciya ta cike take da tsoron haduwar mu, ina jin karar tsayawar mota a kofar gida duk sai naji kamar an tsaida gudun jinin jiki na, a kasalance na mike ina kallon kiran sa ba tare dana daga ba na yi hanyar wajen.
Yana zaune ya zuro kafuwan sa wajen motar ya dago jin fitowa ta, bai tsaye wata doguwar magana ba ya tada motar muka bar layin.
Mun riga su isa station din saboda haka muka samu waje muka zauna zaman jiran su, basu iso da wuri ba sai bayan mun dade da isa, a waje Daddy ya tsaya yana amsa waya baban su Kamal ne kawai ya shigo, kaina a kasa ina kara jin abu mai kamar tsoro tsoro na fizgata, wuce mu yayi kai tsaye ya shige office din DPo ɗin, a dan rada rada nace ma Kamal

"I'm nervous."

Dariya ya saka yana duba na

"Kin cika tsoro."

Shiru nayi ina tunanin abinda yasa nake jin hakan, takun tafiya muka ji nayi saurin sake nutsuwa har suka ƙaraso gaban mu, a hankali na dago yayi daidai da duba na, kura min ido yayi cikin wani irin yanayi me kama da kallon sani, da sauri na furta

"Ina wuni?"

Kada kansa yayi a kajarce ya amsa yana maida hankalin sa kan Kamal

"Itace?"

"Eh itace Daddy."

"Ina iyayenki?" Ya wurgo min tambayar a bazata, da sauri Kamal yayi karaf yace

"Sun rasu ai Daddy."

Boyayyiyar ajiyar zuciya na sauke, ina jin dadin yadda Kamal ya cece ni, bansan amsar da zan bayar ba hakan kuma na iya jefa shakku a zuciyar sa, ina ji suka cigaba da magana da Dpo akan yadda za'a yi.
Daidai lokacin Daddy ya gama wayar da yake ya shigo ciki, dukkan su suka mike cike da girmamawa suka sara masa, hannu ya daga musu ya ƙaraso inda muke yana kokarin fahimtar maganar da suke.

"Ina fatan akwai wani improvement akan batar yarinyar?"

Da sauri na dago jin irin maganar Farouk, sai dai wannan girma ya yi mata rufi sosai inda kai tsaye zaka gane mamallakin muryar Baba ne, yawun bakina ne ya kafe a diririce nace

"Daddy?!" Sai a lokacin ya lura dani, ware idanun sa sosai yayi akaina cikin tsananin mamaki yace

"Kamar Aminatu ko?"

Sai na fashe da kuka da karfi ina daga mishi kai

"Ikon Allah." Ya furta yana dubana duban tsanaki

"Ko zuwan mu wajen Dadah sai data yi min maganar ki, ina kika shiga tsawon wannan lokaci?"

Ban iya bude baki nayi magana ba, sai kuka na daya karu sosai, ganin duk mutanen wajen sun juyo suna kallon mu yasa Dpo yace mu koma office din sa. Alhaji Marwan da Kamal sun shiga tunanin abinda ya hada mu, saboda haka muna shiga ciki Alhaji Marwan yace

"Me yake faruwa ne Kb? Ka santa ne? Ko shi yasa nake ji kamar na taba ganin ta tun shigowa ta wajen nan."

"Matar Farouk fa, wadda muke maganar ta ranar da Dadah."

"Ikon Allah."

Yace yana bi na da kallon tausayi, kamar an mintsini Daddy yayi saurin cewa

"Yarinyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login