Showing 30001 words to 33000 words out of 112633 words

Chapter 11 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7403

tausayin yar uwarta. Mayafinta ta dauka, ta dauka yan kudaden ta tayo waje, yara tasa suka kira mata Nura, suka nufi in da zasu samu mota. Har suka isa makarantar bata bar sake-sake ba, wani irin tausayin ta take ji, tabbas tasan ita ce Ummul abaisin halin da Aminatun ke shiga, sai dai tayi nadama, duk da nadamar bata da amfani, amma tabbas tayi dana sanin abinda ta aikata, gashi Baba tun lokacin daya ji komai ya kwanta ciwo, saboda tsabar kaduwar da yayi take barin jikin sa ya shanye, ko a iya haka Allah ya barta ta gane kuskurenta, ballantana tasan akwai wasu sakamakon masu zuwa nan gaba.

***
Ina kwance kamar wadda aka zare wa dukka kashin jikin ta, cikina ke ta ya mutsawa kamar kayan cikin shi zasu fito, a wahalce nake fitar da numfashi ina murkususu. Budo kofar akayi na zuba musu ido, principal ce a gaba sai Inno da Nura, ganin su yasa na saki kukan da nake ta kokarin tsaida shi, da sauri suka ƙaraso wajena Inno tayi kokarin sani jikin ta.

"Sannu kinji." Principal tayi maganar tana ajiye takardun a gefe na. Da sauri na runtse ido na ina jin kamar ta ajiye garwashi tunawa danayi da abinda ke ciki. Ina ji ta hau yi musu bayanin komai,

"Naji dadin zuwan naku, dama muna ta tunanin yadda za'a yi, tun da kunzo sai asa hannu ku tafi da ita, Allah ya kara lafiya."

"An gode Allah ya saka da Alkhairi."

"Amin, dan Allah a kula da ita sosai, akwai karamin ciki a jikin ta, damuwa zata iya haifar mata da matsala, duk tsanani yana tare da sauki, komai zai zamo tarihi in Sha Allah."

Da kallo Inno ta bita, ta kasa magana sai daga kanta kawai da take a hankali, har principal din ta juya ta fita.

"Ni Nura a takardar nan ba yace babu abinda ya shiga tsakanin su bane?" Tayi tambayar tana kallon sa

"Tabbas haka yake a rubuce."

"Allah ya kyauta." Kawai tace tana kokarin tashi

"Ki daina kuka kin daiji me firincifal ɗin tace ko?"

Shiru nayi suka tattare komai da magunguna na Nura yasa hannu muka dau hanya.

***Tun da muka soma tafiyaa na jingina da kujerar motar, na lumshe ido na kamar mai bacci, babu wanda yayi min magana a cikin su har muka isa kauyen namu, sanda muka iso daidai gidan Bature, na bude ido na, jikina ya hau rawa na kura wa babban gate din gidan ina ganin kamar zai bude, gani nake kamar zai fito, kamar zan ganshi tsaye yana daga min hannu, sai dai kash, har muka wuce babu motsin kowa, babu alamun ma akwai mutane a ciki. Muna isa gida Inno ta gyara min hijabi na ta riko ni, ta taimaka min na fito, hannun ta cikin nawa muka shiga gidan, da sauri Yalwati ta taso, tana mana sannu da zuwa. Amsawa Inno tayi ta bude min dakin ta.

"Jeki kwanta." Kawai tace ta rataye mayafin ta saman igiya ta nufi dakin Baba. Ina shiga na tarar da Karime da jaririnta, ta sauri ta taso ta rungume ni,sai a sannan naji wani sabon kuka ya taso min, kukan muka saka baki daya a tare, babu me yunkurin rarrashin wani, sai da mukayi me isarmu, sannan muka samu waje muka zauna, sai a lokacin Inno ta shigo, kallon mu tayi kadan ta wuce wajen daukar abu,har zata fita sai kuma ta tsaya tana duba na

"Taso ki watsa ruwa kafin magriba tayi, ke Karime miki min yaron nan a goya shi magriba ta gabato."

"Toh." Muka amsa a tare, ta karbi jaririn ta fita, cikin rashin kwarin jiki na mike, na rage kayan jiki na, na fito tsakar gidan, ruwa me dumi na tarar a bandakin na watsa na fito. Kayan Karime na saka na sake kwanciya a saman gadon Inno, har aka kira sallah sannan na tashi nayi na sake kwanciya, gaba daya bani da karfin jiki dana ruhi, komai baya min dad'i. A gefe na Karime ta zauna tana jijjigen yaron, kallon ta kawai nake ina hasaso hakan akai na.

"Ya sunan shi?" Na tambaye ta ina mika mata hannu ta bani shi

"Abubakar aka sa masa, amma saddiku za'a dinga ce masa."

Shafa kansa nayi wasu hawaye suka zubo min, nima haka zan haifi abin ciki na, na raine shi ni kadai ba tare da uba ba, bansan wanne irin rayuwa kuma zan sake yi nan gaba ba,  hannu na dora a saman shafaffen ciki na bayan na mika mata shi don ta bashi nono. Na shiga tunanin kalar rayuwar da zanyi. Abinci Inno ta kawo mana, na d'an ci kadan dan har lokacin cikina babu dadi, na haye gadon na kwanta ina fatan bacci ya dauke ni

***Cikin dare na kaasa bacci juyi kawai nake, na rasa abinda yake min dadi, har aka kira sallah na mike da kyar na je nayi alwala,. Bayan na idar na zauna saman abin sallar ina fadawa Allah damuwa ta, nasan shine kadai zai kawo min sauki a dukkan al'amari ne. Sai da gari yayi haske sosai sannan na kwanta, bacci ya dauke ni a take. Ina cikin baccin ne naji hayaniya sosai kamar a tsakar gidan mu, da sauri na mike zaune, Karime na gani a zaune gefe na tayi wanka tana cin dumanen tuwo.

"Sannu da tashi, ya karfin jikin?." Tace tana min murmushi

"Da sauki, ya kwanan Saddik?"

"Alhamdulillah."

"Su waye nake jin hayaniya a waje?" Na tambaye ta ina sake kasa kunne na sosai, tabe baki tayi kafin tace

"Dan iskan Garbatin nan ne yazo zai wa mutane hauka, amma Inno tayi maganin su ma ai, bashi da hankali wallahi sam."

Gabana ne ya fadi nayi saurin lek'awa, lokacin suke fita daga gidan, hannu naga Inno tasa ta goge fuskar ta, ganin ta nufo dakin yasa nayi saurin komawa na zauna. Shigowa tayi tana maganganu kasa kasa, chan sai ga Nura yayi sallama a dakin.

"Wai kina kirana ko?" Yace yana zama kasa.

"Waye yayi maganar juna biyun da take dauke dashi? Kasan dai ni dakai kawai muka san maganar."

Zaro ido yayi cikin rashin gaskiya

"Wallahi dazu ne da asubah muke maganar dawowar Aminatun da su Iro(sauran samarin gidan) shine nake basu labarin abinda ma ya faru."

"Toh gashi nan zance ya fita gari, har mutane sun zo neman ba'a si."

Dafe kirjin sa yayi da sauri

"Toh waya fitar da maganar kenan?" Ya tambaya yana zaro ido

"Kaine, da baka fada ba ya za'ayi har a yada, tashi kaje ni kana abu kamar ba namiji ba."

Sum sum ya tashi ya fita, Inno tayi tsaki ita ma ta bar dakin. Kallo na Karime tayi cikin son karin bayani

"Me ya faru Aminatu? Bayan sakin akwai wani abu ne?"

Share hawayen fuska ta nayi na zauna sosai zuciya ta na min daci, a hankali na ce

"Bansan wacce kaddara ce ke tunkaro ni ba Karime, a lokacin da na gama tabbatar wa kaina da tsananin soyayya da nake ma Ya Farouk, a lokacin ya datse igiyar alakar dake tsakani na dashi, ya ruguza dukkan tanadin da mukayi wa juna. Kinsan bayan sakin har cewa yayi babu wani abu daya shiga tsakani na dashi? Bayan a daidai lokacin gwaji ya tabbatar min da ina dauke da ciki har na sati bakwai, Karime ya zanyi da rayuwata da abinda yake ciki na, bayan wanda zai tsaya min ya tabbatar da cewa babu abu tsakanin mu, ina kenan na samo cikin jikina? Wa zai karbe ni dashi?"

Kuka yaci karfin mu dukka, tasowa tayi ta zauna daf dani tana sharen hawayen fuskata

"Kiyi hakuri, tabbas ba'a kyauta miki ba, kuma an zalunce ki, amma bak'ya tunanin akwai sa hannu wani a cikin wannan al'amarin? Kina ganin Farouk zai miki haka kuwa?"

Girgiza kai na nayi cikin kuka nace

"Idan ma sharri akayi masa, yana ina yanzu? Me yasa be zo ya wanke kansa ba? Bayan haka rubutun dake jikin takardar nashi ne, rubutun sa ne Karime, ya kike tunanin bazan yarda ba?"

"Duk da haka, ya kamata ayi bincike sosai."

"Babu wani bincike da za'ayi, aikin gama ya riga ya gama, abu daya na kasa ganewa, laifin me nayi masa da har zai min wannan hukuncin? Menene matsalata?"

Share hawaye nayi na mike ina komawa jikin tagar dakin,

"Amma ba komai, na gode masa sosai da dukkan sadaukarwar sa gareni, hakika ba zan taba mantawa dashi a cikin jerin mutane masu matukar muhimmanci a rayuwata ba, ina jin kamar nunfashi na zai bar gangar jiki na Karime, zuciya ta tana min zafi."

"Kiyi hakuri, karki tsananan ta damuwa ko dan abinda ki cikin ki."

Sosai Karime ta shiga rarrashi na da ban baki, haka dai nake bin ta da ido kamar mutum mutumi, bata hakura ba har sai da saddiku yayi kuka sannan ta kyale ni. Wanka na fara yi na sha kunu wanda shi kadai ne zai iya zama a ciki na a halin yanzu. Wajen azahar sakon kiran maigari ya riske mu. Sai da akayi la'asar sannan Inno tasani a gaba tare da k'anin Baba muka tafi, duk inda muka wuce sai munga ana kallon mu ana magana kasa kasa. Haka muka isa wajen, daga gefe muka zauna muka gaida maigari sannan ya soma magana cikin dattaku."

"Jiya wasu mata sunzo har nan sun same mu, sun gabatar da takardar sakin Aminatu daga wajen mijinta Farouk, bayan nan suka dora da bayanin su kafin sukayi sallama suka tafi. Toh bayan tafiyar su, nasa an karanta min abinda takardar ta kunsa, daga nan na yanke shawarar kiran mahaifin yaron, dan jin abinda yake faruwa, tunda ance ta inda aka hau ta nan ake sauka. Toh bayan kiran shi ne yake nuna min shi sam be san da maganar ba, hasalima shi rabon shi da yaron an kwana biyu, sai dai ya bani hakuri da alƙawarin zai samu lokaci ya shigo. Toh kuma yau sai ga maganar juna biyu ta riskeni, sai na sake komawa baya abinda yake rubuce a takardar nan da suka kawo, in da yaron ya nuna babu wata alaƙa data shiga tsakanin su, shine abin ya daure min kai, na bukaci naji daga gareku, kafin zuwa Mahaifin yaron ko yaron, mu san abinda ake ciki."

Runtse ido na nayi ina karanto duk addu'ar datazo baki na, idan har Farouk be zo ba, be kuma ƙaryata abinda ya rubuta ba, ana nufin za'a sheganta min abinda ke cikina kenan? Wannan wacce irin masifa ce ta kunno min?

"Aminatu..." Maigari ya kira sunana, ban iya amsawa ba sai dagowa da nayi kawai ina goge fuskata.

"Abinda mijinki ya rubuta shin gaskiya ne ko ba gaskiya ba?"

A hankali na bude baki na cikin tsananin kukan da ya soma cin karfi na nace

"Ba... gaskiya bane."

Gid'a kansa yayi cikin gamsuwa yace

"Shikenan, in Sha Allahu komai zai warware kinji, kiyi hakuri."

Da kai na amss kawai, ya karasa bayanin sa sannan ya sallame mu.

***
Ransa a matukar bace yake kutsa kansa falon, tana zaune hannun ta rike da babban tasbah tana ja, tana ganin shi ta fadada fara'a ta

"Soja mazan fama."

Yake yayi kawai ya ƙaraso ya samu waje ya zauna

"Dadah, me yaron nan yake so ya zama?"

Ya ambata yana jan karamin tsaki

"Wanne yaro hala? Ja'afaru ko wa?"

"Farouk!"

"Toh me kuma Babana yayi ehe?"

Cire hular kansa yayi ya ajiye yana goge gumin kansa

"Wallahi wai ya saki yarinyar nan."

Da sauri ta dafe kirjin ta

"Innalillah wa inna ilaihi raji'un! Saki!!! Yaushe?"

Tsakin ya kara ja yana duban kofa

"Dazu maigari ya kirani wallahi, kuma abin takaice wai aikawa yayi da takardar,ba shine da kansa yaje ba, gashi duk numbobin sa na kira a kashe balle nasan ta ina zan fara, ni rabona ma dashi tun zuwan da yayi karshe yace an tura shi wani aiki."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yau me zanji, wanne irin abu ne wannan? A lafiyar sa kuwa? Kai da sake gaskiya, bana jin Babana zai aikata makamancin wannan."

"Dadah dan yau fa, halin su sai su."

"Duk da haka Kabiru, sam ban yarda Farouk zai aikata ba, aikuwa ba dan dare yayi ba a yau zan bar garin nan, amma tabbas gobe da izinin Allah ina chan, hankali na ba zai kwanta ba sai na ji komai, ka cigaba da kiran wayar tasa ko zaka samu kaima."

"Allah ya kaimu, nima zuwan ya kamani, ina ganin ki fara zuwa sai na biyo ki jibi, dan akwai ayyukan da zan karasa goben, amma idan na koma zan shiga gidan Aboki, zan sanar masa abinda yake faruwa, shine me yabon faruk yanzu sai yasan abinda ya sake aikata bayan na dah, idan yaso sai mu tafi taren musha kunyar a tare, dan bazan iya kallon mutanen nan ba wallahi, da kunya ana ganin mutuncin ka."

"Duk yadda kayi yayi, amma ni kam gobe zan isa da izinin Aallah."

"Allah ya kaimu, sai ku tafi Ja'afar da driver ko?."

"Amin, yayi hakan." Ta amsa har lokacin bata bar mamaki ba, ina alkawarin da yayi mata na cewa duk ranar da Aminatun ta gama karatu zai dawo da ita wajenta, su zauna tare har zuwa lokacin da shima zai nemi transfer ya dawo nan ɗin, me ya faru da babban alkawarin da yayi na taimaka mata wajen hada ta da dangin ta? Kai akwai lauje cikin nad'i, tabbas wannan makirci ne aka shirya, sai dai kai tsaye Mum ce ta fado mata arai, tasan zata iya aikata fiye da hakan ba, amma dai koma menene, zata je taji.

***
Alhamdulillah, nagode kwarai da addu'oin ku 🙏💯 Allah saka da Alkhairi.

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
 
                 
: ©️ HAFSAT RANO

    THE HEART BREAK💔💔💔💔

                (14)




***Dauke nake da Saddiku ina dan jijjigashi, rabi da kwata na hankali na yana kan tunanin abubuwan dake faruwa dani, sallama Karime tayi daure da zanin wanka ta lullube saman kanta da wani, kallo na yayi ganin yadda nayi firgigit jin sallamar ta.

"Tunanin dai ko Aminatu, kifa saukaka ma ranki kar ki jawo wani ciwon kuma."

Yake nayi wanda aka ce yafi kuka ciwo na zauna sosai ina kwantar da Saddiku, zaman tayi itama ta hau shiryawa bata sake min magana ba, tashi nayi na fito, nayi fitsari na dan leka dakin Baba, yana kwance idanun sa a bude, na k'arasa na tsuguna gaban sa

"Sannu Baba." Nace ina maida kwallar ido na, bina yake tayi da ido babu halin magana, shiru nayi ina tunanin yadda mutum zaiyi rayuwa a haka, tabbas ba karamin jin jiki yake ba, gashi babu wanda zai taimaka masa da  zuwa asibiti, Farouk ne ya fado min, na tuna da yananan yanzu, xan iya neman alfarmar sa ya taimaka masa. Na jima a dakin ina zaune dashi har saida Inno ta kwala min kira, da sauri na tashi na fito, sai nayi turus ganin Dadah na kokarin shiga dakin Inno, gani na yasa ta dakata, ganin haka yasa nayi saurin isa gareta, bansan sanda na fada jikinta ba, na saka kuka sosai. Rike ni tayi muka karasa shiga dakin har lokacin kukan nake, gaishe ta Karime tayi ta tashi ta fita don bamu waje. Tabarma Babba na dauko na shinfida mata, na fita da sauri na debo mata ruwa na ajiye a gaban ta sannan na zauna ina sauke kaina kasa.

"Aminatu, sannu kinji."

Hakan data fada yasa naji zuciya ta ta sake yin rauni, tabbas ni ɗin abar a tausaya min ce,

"Sannu da zuwa Dadah, ina wuni?"

"Lafiya kalou Aminatu, mun same ku lafiya?"

"Alhamdulillah."

Nace ina wasa da hannu na. Inno ce tayi sallama ta shigo Yalwati na bin bayanta, a mutunce suka gaisa kafin su tashi su fita. Muskutawa tayi kadan tana dubana sosai.

"Aminatu me yake faruwa? Me ya hada ki da Babana."

Ta jeho min tambayar ta na riga nasan da ita, kallon ta nayi zan cigaba da kukan da nake ta dakatar dani,

"Kul kina kuka, akan me? Fada min gaskiya me ya faru, kunyi fada ne ko kin masa wani laifin ne?"

"Allah banyi masa komai ba, hasalima rabona dashi tun ranar daya maida ni makaranta, yace sai ranar da muka gama exams zai zo, toh kuma ni tun bayan nan sau biyu mukayi waya, daga nan bamu sake magana ba."

"Zaki iya dauko min takardar da aka kawo miki?"

"Eh."

"Toh bani na gani."

Tashi nayi na bude jakar da nazo da ita na dauko, na fito da takardun guda biyu, kura musu ido nayi a tare, sai kuma na juya na mika mata su dukka ina jin wani iri, karba tayi ta bude ta farko me dauke da sakamakon test result dina, a fuskar ta naga yanayin da take ciki, sosai naga ta sake sakin fuskar fiye da yadda take a baya, ninkewa tayi ta ajiye ta bude dayar, ta jima tana dubawa kamar ne son gano wani abu kafin ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya.

"Waye ya kawo miki wannan?" Ta nuna takardar sakin

"Bansan waye ba nima, nasan dai wata mota ce ta shigo makarantar mu, ina kallo ta bawa security man din dake wajen shi kuma ya kawo min, sai dai tabbas mace ce dan naga hannun ta."

"Baki ga fuskar ta ba kenan?"

Girgiza kai na nayi

"Ban gani ba, amma ance tazo gida ma bayan ta je makarantar."

"Nan gidan?" Ta tambaya da sauri.

"Eh ance tazo, kuma maigari ma yace sunje chan wajen sa sun kai masa."

"Good, kira min Maman taku."

Tashi nayi tsam naje na kira Inno, a tare muka shigo na samu gefe na zauna.

"Ko zaki iya gane matar data zo dan Allah?" Tayi maganar tana kallon Inno

"Zan gane ta."

"Yawwa."

Ciro wayar ta tayi ta budo wajen hotuna ta fara nuna wa Inno, duk wadda ta nuna mata sai tace ba ita bace. Ajiye wayar tayi tana murmushi

"Aminatu samu yaro yaje waje ya kira min Ja'afar, suna nan a mota."

Tashi nayi na fito, babu yaro ko daya duk Inno ta kora su waje, hijabin jikin Karime na karba na leka da kaina na kirawo shi. Gabana ne ya fadi da ya fito, sosai yayi min kama da Farouk, sai dai shekaru da Farouk zai fishi da girman jiki.

"Sannu, Dadah ke kiran ka."

"Owk." Yace yana biyo bayana, tsayawa yayi a tsakar gidan na shiga na fada mata gashi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login