Showing 105001 words to 108000 words out of 112633 words
Chapter 36 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
yana gogewa wlhia: *DG*
45
©️Hafsat rano
★★★★
"Officer ku tafi da ita "
"Hajiya you are under arrest "
ya saka mata handcuf, jujjuya kanta kawai take cikin tsananin tashin hankali, a gaba suka sata Kamal na bin bayan su, kukan da take yana shiga cikin kunnuwan sa yana masa amsa kuwa, tsayawa yayi daga nesa yana duban motar, da gudu Karime tayi inda yake tsaye ta durkusa ƙasa tana kama kafuwan sa
"Dan Allah karka yi mata hukunci data aikata...Mahaifiyar ka ce ka taimaka bata da lafiya."
Dauke kansa yayi dacin da yake ji na sake taso masa, ko tantama babu ita ɗin kanwar sa ce, sai dai bashi da hurumin hana hukuma aikin ta, na hukunta duk mai laifi.
Ciki ta koma da gudu tana kiran Aminatu, tare suka fito yana ganin su ya yi saurin buɗe mota ya shige dan ba zai iya jure ganin su ba. Duban Farouk tayi, magana suk' da daya daga cikin yan sandan, kenan duk sun san da plan din kamasun shisa ma ko a ciki Ammi taki cewa komai duk kuwa da magiyar da tayi ta mata.
Karasowa akayi Garbati da Ila aka watsa su ciki suma, jan hannun Karime tayi suka koma ciki tana kuka, suna jin sanda motar ta daga ta bar unguwar, yara da manya aka samu abin magana.
Daki suka shiga, ta hau rarrashin Karimen da maganganu masu dadi, sosai take jin zafin Farouk da Kamal har ma da Ammin shisa da suka ce ta taso a tafi taki, tace zata tawo.
Babu wanda ya matsa mata tunda dama a garin zasu kwana. Suka tattara suka tafi suka kyale ta. Da tashin hankali Nura ya shigo gidan labari ya kai masa, lokacin jikin Baba ya kara rikice wa saboda abinda ya faru, mota ya tafi ya kirawo suka kwashe shi zuwa asibiti.
Duk abinda za'a bukata Aminatu ce ta biya, kudade ba kadan ba saboda ba karamin asibiti bane, ganin za'a iya bukatar wasu kudin gashi bata dashi yasa ta kira Kamal, lokacin yana zaune duk abin duniya ya dameshi
"Kudi nake bukata muna asibiti da Baba."
Tace kai tsaye,
"Ina ne asibitin? zanzo."
"Ok." Tace tana kashe wayar
Cikin kankanin lokaci ya isa asibitin, a barandar ya hange ta tana tsaye ta zuba wa gate din ido, karasowa yayi ta nuna masa wajen biyan kudin bata ce mai komai ba, zuwa yayi ya biya abinda ake bukata ya dawo in da take, da hannu ta nuna masa dakin da Baban yake ta koma wajen da Karime ke xaune.
A darare ya bude dakin da aka kwantar da Baban ya kura masa ido, idon sa ne ya cicciko da kwalla ganin mutumin da ya kasance mahaifi a gareshi cikin tsananin wahalar talauci da tsananin ciwo.
Har gaban gadon ya taka ya na kare masa kallo, bacci yake me wahalarwa numfashin sa na fita da kyar ta cikin oxygen.
Dukkan su ba'a yi musu adalci ba sam duba da yadda abubuwan suka kasance.
Lallai Aminatu nada karfin zuciya idan wata ce ba xata kalle su ba balle har ta tausaya musu, sai gashi har fushi take dasu akan abinda ya xama dole.
Sai da Ammi ta kirasu sannan suka bar asibitin, har lokacin Aminatun na fushi dasu.
Washegari suka sake dawowa asibitin, ta bawa Nura kudin da Kamal ya bata sannan ta bawa karime wani abu tace ta rike a wajen ta ko zata bukaci wani abu sannan suka tafi.
Taso kwarai su kara kwana amma Ammi taki. Dole suka hakura suka tafi.
Kwanan su biyu da komawa rai yayi halinsa, mutuwar Baban ta girgiza both Aminatu da Kamal, be san mahaifin shi ba, magana ta fatar baki bata taɓa hada su sai gashi Allah ya karbi ransa a lokacin da yake da burin sanin sa.
Dole suka tattaro suka sake dawowa garin na Shagari amma wannan karon su biyu, sai Farouk da Ja'afar da suka biyo bayan su sukayi taaziyya.
Da zasu tafi kwarai Karime ta bawa Aminatu tausayi, ashe mijin ta ya rasu har tayi takaba, inda dangin mijin suka karbe dansu akan taki ta auri kanin mijin nata. Hakan ya kara wa Aminatu tausayin ta ba tare da shawara da kowa ba tasa ta haɗa kaya ta bisu saboda tana bukatar hutu sosai.
Bata ki ba, ta amsa tayin ta dan dama zaman yayi mata zafi gashi babu Inno tun da har yanzu ba'a shigar da case ɗin nasu kotu ba.
Zuwan Karime Abujan ya kasa ta dan saki jikin ta, tayi mamakin girma da Yalwar gidan da ya kasance mallakin su Aminatun, ta kuma kara karaya da lamarin shari'ar ganin ba kananan mutane innar ta tabo ba.
Duk yadda taso ta shige wa Kamal ya bata damar da zata yi masa maganar Inno yaƙi.
*****
Safa da marwa Ya Anas ke tayi a tsakiyar falon ya gaza cewa komai. A kufule Hajiya tace'
"Wai Anas menene haka? Ka sani a gaba ka gaza cewa komai, me ya faru?"
"Hajiya Aminatu ce."
Tabe baki tayi
"Dama nasan tatsuniyar gizo bata wuce kok'i, wai har yanzu ba zaka hakura ba?"
"Hajiya hakuri ya zama dole ai, Aminatu tayi min nisa sosai, bayan haka kuma da mijin ta."
Tashi tayi rai bace tace
"Dama rashin jin magana ne irin na dan yau, abinda na dade ina hasaso maka kenan, wahalar banza."
"Hajiya bama wannan ba, ko da ace babu wani, zanji tsoron shiga saboda mahaifin ta ba karamin mutum bane, kina ji ana maganar Alhaji Marwan dikko?"
"Eh! Inaji, me ya faru?"
"Shine mahaifin ta."
Da sauri ta dafe kirji
"Kana nufin uba mahaifi?"
"Eh Hajiya."
"Na shige su ni Bintu, kasan kuwa me kake cewa?"
"Wallahi Hajiya."
"*Hukumullah, kaji ikon Allah ko? Kai masha Allahu, amma ya akayi haka?."
"Yadda kika ji haka yake Hajiya, ni kaina abin ya dauren kai."
"Alhamdulillah, Allah na gode ma da babu wani abu dana taba mata, shiyasa aka ce karka wulakanta mutum wallahi."
Murmushi yayi kawai,yana duban Hajiyan, sai ya kada kansa kawai ya bar falon, har yaje kofa tace
"Allah yasa tana da kanwa kaga sai ka shiga kawai ko dan hallacin da kayi wa yar su xasu baka, su kuma daga ka kaima ka samu wani abun."
Sarai yaji, bece komai ba kawai ya karass barin dakin yana mamakin chanjawar Hajiyar,kudi masu gidan rana kenan.
★★★★
Cikin shirin farar shadda kal, ya dora hular jaddara, sosai ya fito a cikakken bakatsine me cike da kamala da haiba.
A gurguje ya shiga bangaren Dadah,ya gaishe ta ya sanaar da ita abinda yake shirin yi, addua tayi masa da fatan alkhairi.
Bayan mota ya fada, ya zauna sosai yana hasaso yadda xasu kwashe da ita, sai dai duk runtsi ba xai sake barin ta ba.
Sanda suka isa kadunan be ma sani ba yyi xurfi a tunani, sai da motar ta tsaya a kofar gidan sannan ya dago yana karewa unguwar kallo.
"Oga xamu shiga ciki ne?"
"No ka tsaya anan."
Yace yana fitowa, da kafa ya isa gate din ya tura, da Iman ya fara cin karo tana wasa a harabar gidan kan sabon keken ta. Murmushi yayi ganin ya samu weak point din gimbiyar tasa. Kai tsaye falon ya nufa, yayi knocking yana maida hannayen sa baya.
Ta gama tattare duk ayyukan da ta yi kenan taji ana knocking, fasa shiga ciki tayi,ta nufi kofar a tunanin ta ko Iman ce ta gama wasan, turus tayi ganin shi taja ta tsaya ba tare da ta ce komai ba
"Ba zaa ce na shigo ba?"
Sai ta matsa masa,tana jingina da bango, har ya kai ya zauna bata motsa ba, sai daya sake magana sannan ta karaso ta zauna a darare.
Hakuri ya soma bata,cikin kankan da kai ya kuma yi mata alkawarin ya chanja xai dinga xurfafa bincike kafin ya zartar da hukunci.
Da fari taso kin bashi fuska, amma daga karshe sai ta sakko,dama chan tana son shi, kawai yadda ya rufe Ido ya wulakanta ta ne ya kasa barin zuciyar ta.
Be baro gidan ba sai dare bayan yayi dinner cikin farin ciki da annashuwa, anan sukayi maganar komawar ta, tace ya bata lokaci, kin yarda yayi yace mata sati daya kawai ya isa tun da yanxu su ba yara bane. Dole ta amince akan babu yadda ta iya.
Dadah ya fara sanarwa yana isa, sosai tayi murna dan dama babban burin ta kenan.
A daren ya sanar da MD, ji yake kamar lokacin xasu fara aure. Sati daya kuwa na cika aka daura auren Alhaji Kabir da Hajiya Abidah a karo na biyu. Babu wata bidia da akayi ta tare a sabo kuma tsohon gidan auren ta.
****
Gadan gadan aka shiga kotu bayan hankalin su ya kwanta, babu bukatar dogon zama da bincike tun da dukkan su sun amsa laifin su, adam yayi laushi sosai ya kuma gane ramin kura ba wajen bakin yaro bane, iyakar horo da wahalarwa ya shata a hannun yan sandan da ba wani isheshen imani ne da wasun su ba musamman akan mai laifi, hakan ya sashi gane kuren sa ya shiga magiya da ban hakurin da bashi da amfani.
Aminatu duk ta damu shi yasa ta tsaya kai da fata wajen ganin Inno ta samu sassauci, kamar yadda aka gindaya wa kowannen su iya adadin shekarun da zai yi gidan kaso ko tarar kudi, kai tsaye ta hau shirye shiryen biyan kudin da aka gindaya wa Innon ba tare da sanin kowa ba.
*Sati biyu*
****Bangaren Farouk da Aminatu wasan buya kawai ake, sam Ammi ta hana shi ganin ta,hadaddiyar me gyaran jiki aka kawo take mata. Wani irin kyau da sheki take,santsi da kyawun fatar ta ma abin kallo ne. Ita kanta sai ta zauna tayi ta kallon kanta a mudubi, komai ya chanja a dan kankanin lokaci, haka rayuwa take dama.
Gidan ya soma cika sosai, da yan uwa da abokan arziki. Karime da Hanne sun zo tun kwana biyu, hakan yayi mata dadi sosai, da farko sunki sakin jikin su ganin girma da haduwar gidan basu taba ganin irin shi ba ko da a mafarki ne, a hankali suka saki jikin su aka shiga hidimar bikin dasu.
Walima kayatacciya aka yi a harabar gidan, in da aka gayyato wata babbar malama tayi fadakarwa akan zamantakewar aure.
Washegari akayi mother's eve, in da aka hada manyan matan kusoshi da masu fda aji na kasar nan.
A gajiye take sosai, sai dai ba zata iya ketare kiran Dadah ba, dole ta sauya kayan ta xuwa marasa nauyi ta ja hannun Karime.
Gidan babu hayaniya sosai hakan ya basu damar isa kai tsaye bangaren Dadah. Amal ce ta amsa sallamar su, cikin sakin fuska tace
"Amarya."
Mamaki ne ya kama Aminatun ta , zatayi magana Dadah ta fito, hannun ta, ta kama suka shige bed room. Nasiha sosai tayi mata akan rayuwa sannan ta bata kyautar sarka da yan kunne masu azabar kyau. Taji dadin kyautar, soyayyar da take mata daban ce, tun bata san kanta ba, tun tana abar kyama ta nuna mata soyayya. Bata da bakin da zata gode mata,sai dai tayi mata adduar gamawa da duniya lafiya.
Part din mummy suka shiga, sanyayyen kamshi ne ke tashi, komai tsaf, mummy ba karamar yar gayu bace, shisa komai na falon sai da aka chanja shi, ya tafi daidai da zamani.
"Amarya." Tace tana murmushi, karon farko data fara sakar mata fuska.
"Barka da dare Mummy."
"Barka dai Aminatu, ya hidima?"
"Alhamdullah."
"Masha Allah, ashe tafiya xakuyi? Sai jiya nake samun labari."
Shiru Aminatu tayi ba tare da ta gane me take nufi ba. Tashi Ammin tayi ta shiga kitchen.
Harde hannun sa yayi a kofar yana kare mata kallo, jin kamar ana kallon ta yasa ta dago, da sauri Iman ta kwace daga rikon da yayi mata tayo wajen ta.
"Ummi na."
Shafa kanta tayi tana murmushi.
"Iman, kin manta dani ko?'"
"Eh... Ina wajen Mummy, tan bani kayan dad'i."
Murmushi tayi
"Lallai kinji daɗin ki."
"Ummi baki gaishe da Daddy na ba." Tace tana nuna mata shi da yake tsaye
"Zan gaishe shi ai anjima." Tace tana basarwa
Fitowa Mummy tayi rike da tray sheke dq snacks. Kallon Farouk tayi
"Son tsaiwar me?"
Sosa Kansa yayi
"Fita ma zan yi Mummy."
Ya juya sai ya makale a waje
"Zamu tafi Mummy."
"Toh shikenan sai kun shigo sallama kenan?"
Murmushi tayi suka fita, da sauri yabi su, takun tafiyar sa sukaji a bayan su, Karime ta tsaya ya ƙaraso tana rike da hannun Iman, gaisawa sukayi idon sa akan Aminatun kafin suyi wata magana.
"Kuje wajen Ammi kinji dota?" Ya shafa kan ta
"Tohm Daddy."
Tace sukayi saurin wuce Aminatu. Da sassarfa ya k'arasa gareta, yasa hannu ya jata, be tsaya ko ina ba sai a bangaren su, tura ta yayi ciki ya maida kofar ya rufe, ya jingina da jiki yana dariya kasa kasa
"Kin gama guje gujen kenan?"
"A ah." Tace tana dariya
Matsowa yayi ya manna ta jikin sa, murya kasa ƙasa yace
"U look very beautiful, the soft skin, the perfume and everything are very nice!"
Dukan chest dinshi tayi ganin yadda yake yawo da hancin sa ko ina yana lumshe ido.
"Naughty boy." Tace tana dariya.
"Kira ne koma mene, i just can't hold it anymore, haba babu tausayi ne? Kalle ni fa duk na zama maraya."
"Yafi ai." Tace tana ture shi
"Please ki taymaka min I'm dying."
"Ka yi hakuri Please."
"Shikenan." Ya janye jikin sa yana matsawa gefe alamun yaji haushi
"Akwai dama yarinyar da muka hadu a Nottingham, Dr Teema gabas, kuma ta nuna interest dinta akaina sosai, tunda baki sona zan neme ta, dama ina da contact d'inta."
A razane ta kalle shi, zatayi magana ya juya ya shige daki da sauri,p tsaye tayi saroro cikin rashin sanin abin yi, tana tsaye Ja'afar ya shigo, a kunyan yace ta amsa gaisuwar sa, tana ganin yadda yake blushing tasan akwai wata a kasa, sai ta juya kawai ta bar part din zuciyar ta babu dad'i.
Tun da ta koma take gwada kiran sa amma wayar a kashe, dole ta hakura suka cigaba da hira dasu Karime.
Ko da tazo kwanciya ma sai data kara kira amma a kashe, duk babu dad'i, sai ta dinga hasaso budurwar da yace, tasan tabbas me aji ce ta karshen karshe, kishi ne ya taru ya cika mata zuciya har ta kasa baccin ma.
***Sai data makara sosai, sanda ta tashi har su Karime sun gama shirin komawa, duk sai ta sake jin babu dad'i. Sukuku ta dinga yin komai har zuwa sanda zasu tafi, da kyar suka rabu bayan Ammi ta haɗa su da sha tara na arziki tun daga kan dangin sutura zuwa kudi. Sunji dadi sosai, har mota Kamal ya rakasu sannan ya kara musu da nashi. Tasha aka kai su suka tafi cikin kewar Aminatu da sabuwar rayuwar ta.
***Waje daya Ammi ta hade mata komai, duk abinda zata bukata ta haɗa shi a cikin jakar.
Tana kwance tayi rigingine Ammin ta leko ta kira ta, falon Daddy suka je, yana zaune daga shi sai doguwar jallabiya fara yana kallon news, remote ya dauka ya rage volume din yana duban su cikin kulawa.
"Maraba da Uwata."
Sunne kanta tayi ta zame ta zauna a kasa tace
"Daddy ina kwana?"
"Lafiya lou mamana, ya sabon waje."
"Alhamdulillah."
"Toh Masha Allah, mamana abubuwa da yawa sun faru, wanda dukkan mu babu wanda ya ke da ikon hana faruwar su tunda Allah ya riga ya tsara, toh Alhamdulillah duk da haka mun gode wa Allah, dan bamu san abin da hakan ke nufi be, ina fatan komai da ya faru ya zama tarihi a wajen ki, sannan ina horon ki da ki zama me hakuri da juriya a duk yanayin rayuwar da kika riski kanki."
"Ki riƙe addinin ki, ki riƙe mutuncin ki, ki zama uwa ta gari ga yayanki, ki girmama mijin ki,ki kiyaye dokokin Allah, ina fatan ki shiga sabuwar rayuwar ki cikin amincin da yardar Allah, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka."
Kuka ta saka, yau ita ce a gaban mahaifin ta yake mata faɗa irin wanda iyaye ya kamata suyi wa dan su, abun da ta rasa a rayuwar ta kenan, lallai babu abinda zata ce sai godiya ga Allah, shi ya ƙaddara mata komai.
"Menene na kuka kuma? Kinji sokonta Ammi."
Murmushi Ammin tayi dan itama zuciyar ta ta karaya, ta kuma gane dalilin kukan nata.
"Auw kema kukan zakiyi? Toh bari na gyara zama na sha kallon uwa da 'ya suna kuka."
Dariya ya basu gaba daya, hakan yayi masa dad'i ainun, sai ya mike yana cewa
"Bari kiga mamana, akwai sakon ki da ya kamata na baki."
Ya shige daki, jim kadan ya fito rike da manyan files ya aje gefen sa, ya hau bude su daya bayan ɗaya, sai daya gama dubawa sannan ya mike mata
"Gashi uwata, wannan shine kyautar ki, abubuwa da kika rasa a baya ina fatan zai isa ya rufe komai."
Hannun ta na kakkarwa ta karba ta bude, jiri ne ya soma dibar ta ganin tarin abubuwan da files ɗin suka kunsa, da sauri ta dago ya sakar mata murmushi cike da gamsar wa yace
"Karki yi tantama dama chan naki ne.
*DG*
*Fourty End *
"Nagode Allah ya saka da Alkhairi.".
Tace Muryar ta na sarkewa. Murmushi yayi cikin jin dadi yace
"Allah yayi miki albarka."
"Amin." Suka amsa baki daya.
Daga nan gidan su Farouk ta shiga wajen Daddy, yayi mata nasiha sosai ya kuma bata kyautar kudi masu tsoka, daga nan sukayi sallama da Mummy ma, ita yar madaidaiciyar leda ta bata me kyau tace zata kira ta a waya, godia tayi ta wuce shashen Dadah, anan ta shantake ganin Ja'afar ya kuma ta kwasar ta da hira tun tana basarwa har ta saki jiki dashi, Amal na gefe bata sa musu baki sai dai tayi murmushi kawai ,Aminatu na lura da ita, tayi laushi sosai kamar ba ita ba, hakan yayi mata dadi, ko da ma chan tasan vata da matsala, kawai anyi amfani da ita ne da kuma yarintar ta.
Da kyar ta bar shashen Dadah ta wuce gida rike da Iman da ke ta faman bata labarin abubuwan da suka faru wanda ma bata tambaye ta ba, ganin surutun na neman wuce gona da iri yasa ta dakatar da ita.
A tsanake ta hau shiryawa tun da Ammi tace mata jirgin karfe biyu zasu hau, tana yi tana tunanin Farouk, bata san zai iya fushi da ita har haka ba, ita sam bata ma ga abin fushin ba, haka ta k'arasa tana ayyana yadda zasu kwashe dashi tunda dai tare zasuyi tafiyar.
Juyawa tayi ta sake