Showing 111001 words to 112633 words out of 112633 words
Chapter 38 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
faman reto ta sa a handfree
"Maman Iman, hala har kin fita."
"Wallahi Anty Rahee, kinga amma da wuri zan dawo, snacks din ya zama ready ne?"
"Eh ya zama, nama yiwa oga magana ko zai biya ya aje, kinsan shi sai yace wai ba hanyar zai ba."
"Ya Anas hoo! shikenan ki ajiye anjima Kamal ko Ja'afar wani zai zo sai ya karba. Nagode."
Zata ajiye wayar kira ya kuma shigowa, dagawa tayi tana shan kwanar office din nata,
"Sis, kin fita ko?".
"Na fita Amal, anything?"
"Ok zanzo gidan nida Iman, akwai maganar da nake so nayi miki ne."
"Shikenan sai na dawo."
Ta aje wayar, tana kashe motar, da sauri messenger ta ya iso wajen yana bude bayan motar
"Sannu da zuwa Hajiya."
"Sannu Ila, ina fatan an yi duk abinda ya dace ko?"
"Anyi dukka, wasu mutane biyu ma da yar yarinya karama tun dazu suna zaune sunce wai wajen ki suka zo."
"Ok." Tace tayi hanyar office din, suna zaune rike da yarinyar suna hango ta suka tashi, da fara'a ta tarbe su, ta bude office din suka shiga ciki, ajiye komai tayi a muhallin sa kafin ta zauna ta ji me ya kawo su, duk da dama tatsuniyar gizo bata wuce koki, maganar dai daya ce kullum fyade wa kananun yara, zare glass din idon ta tayi,ta goge saman goshin ta tana duban yarinyar da dududu bata wuce 7years ba, she was raped by her own family member,kamar uncle ma yake a wajen ta..
Rubuce rubuce tayi sannan ta kira Dr Rumaisa ta tura su domin ta duba ta sosai ta kuma bata report na damage din da aka mata before tayi proceeding further.
Shekara guda kenan da kafa kungiyar tata me suna FAR-AM INITIATIVE (HELPING THE NEEDY AND FIGHTING AGAINST RAPE, VIOLENCE AND OTHER MARITAL ISSUES)
Alhamdulillah babu abinda zata ce sai godiyar Allah, sosai kungiyar ta samu karɓuwa ta kowanne lungu da sako na kasar nan, hakan kuma idan baku manta ba shine burin Aminatu, dan haka komai na tafiya cikin tsari, duk wanda ya kawo kukan sa wajen su suna kokarin share masa hawaye, da kanta take tsaya wa mata d a yara a kotu, ta kwato musu hakkin su ba tare da sisin su ba.
Wajen azahar ta samu barin office din, ta riga tayi wa Kamal text message na abinda take bukata na taron babban bakon nata.
Sai zata fara watsa ruwa domin ana rana, sannan ta sauko kasan, lokacin Amal tazo, abinci taci suna dan taba hira akan wanda zai auri Amal din turad, Kitchen suka wuce saboda lokaci na ja, anan suka ci-gaba da maganar wadda Amal din kece tayi wa Farouk magana akai dan bata so damar ta sake kwace mata, so take itama tayi aure gashi har an saka bikin Kamal da Ja'afar shisa itama take so a hada da ita dan ta soma gajiya da zaman.
Cikin kwarewa Aminatun ta shiga sarrafa hadaddiyar jollop rice me veggies, gefe guda kuma tana gasa kaza a gudar ta, sai hadin coleslow da yaji kayan hadi sosai. Kunun aya me rai da lafiya ta haɗa masa bayan ts rage aikin ta saka a freezer, (don't mind me yunwa nake ji yasin 😭😂😂😂) duk da aikin yayi sauri saboda taimakon Baba Altine da Amal amma basu samu gamawa ba sai la'asar lis, sama ta haye da ya zama out of boundary daga ita sai chubby dinta ke rayuwa a ciki, komai yana kasa saboda haka babu wanda yake hawar mata domin fadar ta wuce ajin kowa.
Kayan da zata saka ta ciro a wardrobe ta kunna hadadden turaren kayan data yi order a wajen Yerwa(Na Mss Xoxo) ta saka a kasan kabbasa ta shiga turara su, hatta undies da shegun nighties din da zata saka sai da komai ya dau kamshi, ajiye su tayi a saman bed ta wuce toilet domin gyara kanta, sai data fara rage pubic hair sannan ta wanke kanta da hadaddun mayukan wanke kai masu masifar kamshi, sannan ta yi wanka, ta bata kusan mintuna arba'in kafin ta fito ta jona handdryer ta hau busar da kan nata. Tana gamawa tayi oiling nasa da mayuka masu dadin kamshi sannan ta raba shi biyu tayi parking kowanne da ribbon daban.
A tsanake ta shirya kanta cikin wata ubansun half gown pink daga wajen kirjin anyi tattara da wani silk din zare, hakan ya fidda shape din wajen, sosai tayi kyau kamar yar tsana, parking din ya kara taimakawa ta fito kamar baby doll.
Hijabi babba ta ɗora a saman shigar ta,ta sauko ta tarar da Ja'afar, Kamal, Amal da Iman suna kwasar gara a saman dinning.
"Sai Anty!" Ja'afar yace yana dariya
"Anzo za'a cinye wa mijina abinci ko? Toh wallahi gwara a matso da bikin nan naku kowa ya kama gaban sa."
"Haba wa, Madam ai ko munyi auren muna manne da gidan Ya Farouk, wannan dabge haka."
Kamal yace yana kurbar kunun ayar da yayi sanyi sosai.
"Allah dai ya aurar damu nan kusa kawai alaji."
Suka saka dariya baki daya, tattare warmers din da ta zuba wa ya Farouk nasa tayi ta kai sama, sannan ta dawo lokacin sun gama, sallama sukayi mata suka tafi har Iman din da ta zama ta Mummy dan sam taki basu ita har sun hakura.
Sallar magriba tayi, ta sake gyara fuskar ta ta feshe jikin ta da wasu turarrukan ta sauko ta zauna jiran zuwan sa. Ganin shirun yayi yawa yasa ta kunna Tv tana kallon shirin dadin Kowa na arewa 24, sosai ta shagala da kallon har bata ji bude gate din ba sai tsayuwar mota, kafin ta isa kofar har ya turo kofar ya shigo, da sauri ta isa gareshi, ya bude mata dukkan hannun su ta fada ciki, rumfa yayi mata ruf yana sake kankame ta.
"Welcome home chubby."
"I missed you hayatyy.”
"Missed you more." Tace tana zare kanta, peck tayi masa a kumatu taja hannun sa suka haye sama, a gefen gado ta zaunar dashi ta zare masa takalmin da safa ta ajiye su a wajen daya dace sannan ta dawo ta zauna a gefen sa tana masa murmushi me tsada tace
"Sannu da hanya."
Mika yayi yana komawa baya kafin yace
"na gaji sosai wallahi."
"Sannu, ai dole, bari kasha ruwa sai ka yi wanka zaka ji dadin jikin ka."
Mik'ewa tayi ta kawo masa ruwa da kunun aya, ta zuba masa yasha sosai yana lumshe ido, ganin ya kusa shanye wa ne yasa ta matsar gefe ta rage masa kayan jikinsa sukayi bathroom, ita ta taimaka masa yayi wankan sannnan ta fito ta barshi ya karasa.
Bayan ya fito ya shirya cikin kaya marasa nauyi, alamun garin akwai hadari shiyasa zafin yayi yawa, sallah ya fara yi sannan ya hau kan food mat ta shiga serving dinshi.
Yana ci suna hira gwanin sha'awa, duk yawanci akan hirar inda yaje ne da kuma harkar NGO dinta. Yana gamawa ta tattare komai, ya jasu sukayi isha'a dan har an idar a masallaci lokacin an fara yayyafi kadan kadan.
A saman cinyar shi ta kwanta ya zura hannayen shi cikin gashin kanta dake fitar da wani annurin kanshi ya shiga ya mutsa shi a hankali cikin salo, hira suke gwanin sha'awar hannun su sarke da juna, a lokacin ta kawo masa maganar Amal, yace zai yi magana da Daddy, taji dadi sosai tayi addu'ar Allah ya bada sa'a, amin yace yayi kissing dinta a forehead kafin ya daga ta zuwa babbar fadar tashi data sha gyara da sabon lallausan zanin gado wanda ya dace da yanayin da masoya zasu kasance a ciki.
Da light and romantic kiss ya fara, a hankali xukatan masoyan biyu suka cika da muradin kasancewa da juna, a hankali cikin deep husky romantic voice d'insa ya kama kunne ta ya rada mata
"Ina son yanayin damina, ya kan haifar da wani yanayi me wuyar fassarawa, its all started bayan na fito daga gida, fitowar da ta zamar min abin alfahari, ƙaddara ce ta fito dani, ƙaddara me karfi da ba za'a iya ketare mata ba, abu na biyu haduwar gangar jikin mu waje guda, sanda ruwa yayi karfi a lokacin komai ya wakana, har Allah ya bamu rabon haihuwa ta sanadiyyar haka, ina ji a raina hakan zai sake kasancewa a daren yau, ina so naga wani babyn, wanda zai amsa sunan Farouk da Aminatu. Ina son ki har bansan iya yawan sa ba, I love You with all I am."
"I love you beyond everything Ya Farouk, ka soni a lokacin da bani da abinda za'a soni, ka inganta min rayuwa ka nuna wa duniya nima zan iya, i love You chubby nah."
"Shissh say no more, xamu yi rayuwa me inganci, tare zamuyi kuka, muyi dariya tare, I'm your best friend kema haka, we shared our sorrows and everything, for you are my eternal peace of mind, my everything, both of our hearts will be bound forever, together we will see tomorrow."
"In Sha Allah my chu...."
Dariya yasa yana kokarin hade bakin su waje guda yace
"Soon zan fara exercise gaskiya, I want to be slim again, ta karfi da yaji an samun chubby."
"No haka nake son ka."
"Shikenan, Allah ya barmu tare Mrs Farouk Kabir Shagari, soon to be Captain Kabir Shagari."
Kankame shi tayi sosai cikin jin dadi tace
"Allah ya tabbatar da Alkhairi."
"Amin."
Na amsa ina murmushi
********
Alhamdulillah ya ALLAH,ina godiya ga duk masoya ZAFAFA Biyar, na fili dana boye, Allah ya saka.da alkahiri.
Kuskuren da ke cikin littafin nan ina rokon Allah ya gafarta min. Allah ya bamu Sa'a ya biya wa kowa bukatar sa ta duniya yasa mu cika da imani.
Hafsat Rano ke cewa sai wani lokacin idan me dukka ya kaimu.
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_