Showing 93001 words to 96000 words out of 112633 words

Chapter 32 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7419

nuna wa Aminatun. Dago kai tayi jin an bude kofar, ganin wace yasa ta maida kanta ta cigaba da abinda take, gefe Aminatu ta samu ta zauna tana tunanin yadda zama zai yiwu ita da Amal a daki daya.
   Tana nan zaune har aka kira sallah, kofar dake nuna toilet dake manne a dakin ta nufa, murya a shake Amal tace

"Bana sharing toilet da kowanne trash."

Juyowa tayi da sauri ta tsaya tana mata kallon mamaki

"Amal nice trash?"

"Mu nawa ne a dakin?"

"Ok nagode." Tace sannan ta bude toilet din ta shiga, hakan ya bata wa Amal rai ta tashi tana fadan maganganu, tana jin ta sarai har ta dauro alwala ta fito, bata kula ta ba ta tada sallah a kan dankwalin ta.
  Tana zaune tana addu'a Mama ta leko

"Kin idar? Taso zaku shiga chan gidan."

"Owk tom." Ta mike

"Dota kema ki taso."

"Zan je gobe kaina ke ciwo."
 
"Ayya sannu, gajiya ce kisha magani."

  Fita tayi Aminatu ta tashi ta nufi kofar fita, har ta kama kofar sai kuma ta tsaya tana juyowa

"Wai ke bak'ya sallah ne?"

Waro ido Amal tayi, kafin tayi magana ta yi ficewar ta.

****
Tsananin faduwar gaba ne ya ziyarce ta sanda suke shiga cikin gidan, haske ne ko ina kamar rana, haka ya bata damar karewa tsarin gidan kallo da yafi kama da irin wanda ake gani a Film.
  Dukkan sautin sahun digadigan ta na fita ne tare da tsanantar bugun zuciyar ta, idan tace tasan musabbabin da yasa take jin hakan tayi karya, haka nan take ji kamar ta zura da gudu saboda tsabar zulumi
  Haka suka shiga wuce bangare bangare na tafkeken gidan a kasan zuciyar ta tana tuna yadda suka saba da Kamal bata taba tunanin girma da yawan dukiyar su ta kai haka ba sai yanzu.
   Babban falo ne daya kawatu da kayan more rayuwa, a hankali bakin ta dauke da sallama ta shiga takawa tana bin bayan su Dadah hannun ta damke dana iman.
   Ammi na zaune, tallafe da kumatun ta bayan ta sha kuka, zuwan Dr Ahmad yasa ta fitowa daga ciki ta zauna a falon tana dakon fitowar su da labarin halin da gudan d'an nata yake ciki.
   Zamewa tayi da sauri ganin su ta mike tana sakaya yanayin da take ciki ta maye gurbin sa da yar fara'a.

"Dadah!"

"Sannu kinji."

"Bismillah."

Ta nuna musu wajen zama, kamar munafuka haka Aminatu ta rabe a bayan Anty Safiyya, sam Ammin bata lura da ita ba, suka shiga gaisawa. A darare Aminatu tace

"Ina wuni?"

"Lafiya..." Maganar ta makale a makoshin ta, wani irin abu taji ya bige ta, ta kura mata ido sosai tana kallon ta, tsoro ne ya kama Aminatu ganin yadda matar take kallon ta, gashi daga ganin matar taji kamar ta taba ganin ta, kamar ta tashi ta isa gareta ta zauna kusa da ita.

"Wacece?" Ta tambaya still idon ta na kanta

"Oh wai Aminatu, matar babana ce ga diyar ta nan ma Iman, itace ai wadda Kamal din ke son gani."

"Aminatu..." Ta maimaita sunan

Sai ta bata rai ta nuna ta da hannu

"Kece ki ka samun rayuwar yaro a matsala ko? Kece mukayi waya nayi miki kashedin fita daga rayuwar sa, me kuma kika zo yi nan?"

"Me ya faru ne?" Dadah tace

"Gata nan tafi kowa sanin halin da take ciki da dalilin da yasa ya shiga, idan ba haka ba me yasa dukkannin farkawar da zai yi da sunan ta a bakin sa, me kikayi masa haka?"

"Haba Hajiya, ba haka bane Aminatu ba irin mutanen nan bace, kila baki fahimce ta ba."

"Haka ne ma, komai a bayyane yake yadda ya damu da al'amarin ta ko ni be damu dani."

"Kiyi hakuri." Tace cikin muryar kuka, hadiye abu Ammin tayi da ya tokare mata makoshi tace

"Please kije i can take care of him, an gode da dubiya."

"Haba Hajiya, haba Hajiya, bansan ki da son kai ba, karki manta ita ma mutum ce da iyayen ta, idan kika yi haka kamar baki yarda da ƙaddara ba."

"Kiyi hakuri Dadah na gama magana."

Tace tana kauda kanta gefe cikin son danne abinda yake taso mata kasan zuciyar ta, yadda take jin yarinyar a ranta ya sata cikin wani irin yanayi mara dadi.

Mik'ewa Aminatu tayi, ta rike hannun Iman,ta soma takawa ta nufi kofa, ta kasa boye kukan ta saboda haka sai ta sake shi kawai, ita kenan kowa baya son ta kowa kyamatar ta yake, idan ba haka ba menene laifin ta.

"Ummi ki daina kuka kinji?"

Iman ta fada tana son fara kukan, tashi su Dadan sukayi, suka mata sallama suka bi bayan Aminatun cikin rashin jin dadin abinda Ammin tayi.

Dr Ahmad ne ya leko yana duban Ammin da take jin kamar bata kyauta ba sai dai ta kasa yarda da hakan,

"Hajiya yaron ku ya farka..."

"Alhamdulillah." Tace cike da farin ciki

"Yana bukatar ganin ki, mahaifin sa sai kuma Aminatu, idan tana kusa ki kirata please."

"Aminatu!"

"Eh haka yace, dan yafi damuwa da ganin nata ma akan kowa, ko dan lafiyar sa ki kirata please."

Ya juya ciki, kanta ne ya hau juyawa, yanzu ya zatayi kenan? Da kunya ai ta koma tace suzo kuma, sai ta basar ta shiga ciki.
  Yana kwance idon sa a bude fes, da sauri ta karasa tayi saurin kama hannun sa.

"Allah na gode maka."

"Ya jikin naka? Me yake maka ciwo yanzu?"

"Ammi ina Aminatun? Dan Allah ki ce tazo."

"Kamal wai menene ka damu da sai tazo? Baka murnar gani na sai ita?"

"Inayi Ammi, sai dai..."

"Bana son maganar ta Kamal, ka bari ka sake samun lafiya sai kaje ka ganta."

Yake yayi ganin yadda ta dage, a hankali ya dora hannun sa a saman nata, ya kalli Alhaji Marwan dake tsaye bayan su ya harde hannun sa tun bayan shigowar Ammin yana duban su, baya so ya sa musu baki shiyasa yaki magana.

"Tabbas kinfi kowa bukatar maganar ta Ammi, saboda kinfi kowa chanchanta da hakan, ƙaddara ce ta haɗa ni da ita, haka ma ƙaddara ce ta kaini Katsina har na shiga cikin wannan halin, babu sanin ta ko izinin ta kamar yadda kike tunani, komai da ya faru tsarin Allah ne, idan ka duba yadda ya kasance. Dan Allah a tura tazo idan har tana nan, bana so nace komai sai a gabanta."

"Bari na kira ta son, sun iso yanzu ta bar falon nan bisa korar da mahaifiyar ka tayi mata."

Sai ya ciro wayar sa ya shiga neman layin Farouk, yana zaune a dakin sa tun zuwan su, gefe jakar akwatin Aminatun ce daya ajiye a wajen sa, yana shirya wani kuduri a ransa.
   Shigowar kiran ya katse masa tunanin da yake

"Ina gida, ok tom gamu nan."

Rigar sa daya rataye ya jawo ya saka ya fito, ganin part din Dadah a kunne da haske yasa ya nufi chan, sallama yayi ya tura kofar, duk sun zagaye Aminatun dake ta faman kuka suna bata baki, da sauri ya isa ciki yana neman ba'a si

"Me ya faru?"

"Matsala suka dan samu da Maman Kamal, kamar tana zargin ta da jefa Kamal din cikin halin da yake ciki."

Anty Safiyya ta amsa masa tana matsawa gefe

"Zancen banza kenan, akan me? Dan kawai ya taimaka mata sai kuma cin mutunci ya shigo? I can't tolerate cin mutunci daga kowa."

"Bata kyauta ba kam, na rasa kuma me ya sa ta hakan bayan ba halin ta bane."

"Tashi." Yace yana mika mata hannu, dagowa tayi ta kalli hannun kafin ta maida kanta kasa ta cigaba da kukan ta.
  Damko hannun nata yayi ya mikar da ita tsaye yana girgiza mata kai

"Karki sake kuka, kin bar kuka tun daga ranar dana dawo gare ki, wannan ya zama na karshe."

"Me yasa kowa yake min haka?"

"Muje." Yace yana nufar kofa da ita

"Me zakayi Farouk?"

"Alhaji Marwan ke kiran mu, yanzu zamu dawo."

Yace yana fita da ita.

*****
Shiru kawai Ammi tayi bata sake magana ba ta zauna tana matsawa Kamal din gefen kafadar sa.
Shigowar su yasa ta dakata, kallo daya tayi musu ta dauke kanta zuciyar ta babu dadi.
Fuskar Kamal ce ta washe sosai ganin ta, ya lura da yadda idon ta yayi, ya san kuma hakan na da nasaba da abinda Ammin tayi mata, duk da bai ji dadi ba amma yasan hakan baya daga cikin halayyar Ammin, be san me yasha kanta ba, har ta iya aikata abinda be yi tunani ba.

"Ammi, Daddy, Ya Farouk da Aminatu, ina so na sanar daku abinda ya kaini Katsina, da abinda yasa na takura da son ganin Aminatu da har ya jawo matsala tsakanin ta da Ammi."

"Go ahead, karka ji komai kaji, muna sauraron ka."

"Nagode Daddy."

"Duk da bansan takamaimai alakar Adam da ku ba, bansan me kukayi masa ba da har yake bibiyar rayuwar ku, ya kuma yi abinda yafi komai muni, Ammi ki dubi Aminatu da kyau, kiyi mata kallo ba irin kallon da kikayi mata a yanzu ba, zaki gane abinda zan fada."

"Daddy I'm sorry, I'm very sorry to say, ni din ba danku bane, baku kuka haife ni ba."

"Kamal!!!!" Alhaji MD ya daka masa tsawa

"Me kake so kace? Kana da hankali ko ka tabu, waye ya gaya maka wannan banzan labarin?"

"Daddy ka yarda dani, bani da ikon boye muku gaskiya tun bayan dana san gaskiya, Daddy wallahi ni ba danku bane, Aminatu ita ce yarku, yar da kuka haifa da cikin ku, aka chanja muku ita, duk a bisa umarnin Adam."

"Kamal me kake shirin cewa ne wai? Ban gane ba!"

"Ammi ki yarda dani, akwai kwararan hujjoji, komai na cikin waya ta nayi recording din sa, ina fatan idan kun gani zaku yarda dani."

Juyawa dakin ya hau yi, daga Aminatu har Ammi babu wanda yake iya tantance komai, komai na dakin ya shiga rarrabe wa Aminatu, lu tayi zata fadi Farouk da maganar ta dake shi shima yayi saurin tare ta, lumshe idon ta tayi tana son tantance mafarki take ko kuwa gaskiya ne?

"Baka da hankali Kamal, ka haukace ko ƙwaƙwalwar ka ta tabu?"

"Idan kuka duba wayar still baku yarda ba ,daga nan zaku iya daukata a mahaukacin ma."

"Bani wayar!" Ya karba a hannun Ammi da ta soma kuka ta kasa magana, hannun sa har rawa yake ya bude wayar ya shiga wajen, sautin muryar Kamal ɗin ce ta karade dakin cikin tattaunawar su da sister Asibi, zuwan sa Shagari, haduwar sa da Adam kafin accident din ya faru.
Da baya da baya Alhaji Marwan ya shiga ja har ya isa kujerar dake daura dashi ya fada yana dafe kansa.
Kuka sosai Ammi take, haka ma Kamal da Aminatu da bata masan a wanne matsayi zata ajiye abinda yake faruwa ba. Me ya kamata tayi yanzu? Me zata ce? Tsawon rayuwar ta tayi shi ne da tunanin ranar da zata hadu da iyayen ta, bata taɓa tunanin ta wannan yanayin zata hadu dasu ba, dukkan su kowa ya kasa motsawa daga in da yake, nauyi kunya da wani irin yanayi Ammin ke ciki, yarta! Yar cikin ta tayi wa abinda bata taɓa tunanin ko mai aikin gidan zata yiwa ba, ina tunanin ta ya tafi, ina hankalin ta, so take ta sake kallon ta, ta tabbatar da gaskiyar komai,amma ta kasa, ta gaza mik'ewa ta aiwatar da abinda yake cin ta.

Waje Farouk ya samu ya zaunar da ita ganin duk sun rikice ya isa gaban Kamal din ya dafa shi

"Me ya faru da har ya saka ka yin tafiyar?"

"File ɗin ta, file dinta dake dauke da sunan ta, Aminatu MD, sannan da passport din dake jiki na Ammi da Daddy, sai kuma labarin ta data taba bani, tabbas ba abu bane me sauki garemuba dukka, amma wannan shine gaskiya. Asibi, Adam, Inno kadai sun isa shaida, za'a iya neman su a tabbatar da haka."

"Na yarda da kai." Yace yana shafa kansa.

"Kira min mahaifin ku farouk, kira shi yazo nan na rasa yadda zan ɓullo wa al'amarin na."

"Ok tam."

Ya zaro wayar sa, ya kira Daddy.

"Daddy..."

"Ku taho nan Farouk, Adam na hannu yanzu haka, yana cikin gidan nan a dakin horo na, ka gaya wa MD kuzo yanzu, komai yazo karshe!"


***
Assalamu alaikum
Kuyi hakuri pls na shiga hidimar biki ne, kunsan yadda biki yake musamman idan aka ce naku ne..
Bikin best friend d'ina ne kuma zata auri dan uwa na. Ku sanya musu albarka da bakunan ku masu albarka Allah sa ayi a sa'a

Sai kuma ku shirya suburbudar Adam dan ni har na samu muciyar da zan sambade shi da ita.😂😂😂
Shegen Goraa: *DG*

                       *40*

©Hafsat Rano

★★★★

"Bani shi." Yace yana karbar wayar

"Ina ganin ko zaku zo nan ɗin saboda barin Kamal shi kadai anan ɗin matsala ne, idan yaso sai ayi komai nima akwai abinda ya shigo min yanzu haka, na ma rasa yadda zan."

"Shikenan ina ganin mu bari zuwa gobe, bari nazo yanzu ni."

Ya ajiye wayar yana nufar bangaren Dadah, yaji dadin zuwan da Adam ɗin yayi da daren dan hakan yayi masa sauki wajen kamashi.
   Kamar yadda suka saba ya shigo cikin gidan kai tsaye babu shamaki saboda matsayin sa na kanin matar gidan kuma sananne tsawon lokaci, Daddy na zaune a falo yana tunani yadda za'a yi ya turo kofar ya shigo, da murmushi ya tarbe shi kamar kowanne lokaci ya kuma bashi wajen zama yana tambayar shi kwana biyu. Bayan tattaunawa da sukayi kadan Daddyn ya tashi ya bashi wuri gami da kira Mama ta fito da mamakin zuwan nasa.
  Bangaren su Farouk ya nufa ya tura kofar, baya nan saboda haka ya dawo wajen securities din daya bawa umarni tun safe yace Ibrahim na fitowa su kama mashi shi, sannan ya koma ciki.

***
Kuka Aminatu take sosai wanda ta gaza boye shi, sam bata taba tunani ko kawowa a ranta wani abu makamancin haka zai ɓullo mata a irin wannan lokacin data cire rai da komai, mahaifiyar ta? Yau ita ce gaban ta cikin yanayin da ta gaza fuskanta yadda zata ajiye shi.
  Kadan kadan yake murza hannun ta cikin salon son rarrashin ta, sai dai ta gaza tsaida hawayen, idan da za'a fada mata cewa zata riski irin wannan ranar zata iya karyatawa, sai gashi ta risketa cikin yanayin da bata taba zato ko tsammani ba.
  Shigowar Daddyn ya tsaida komai, da sauri Alhaji Marwan ya tare shi da abinda ya ke faruwa, sosai maganar ta dake shi, ya tsorata ainun da lamarin Adam, ashe zai iya aikata haka garesu? Tabbas Adam yayi nisa cikin kiyayyar su, ya zama dole su ajiye duk wata alaƙa su hukunta shi hukunci me tsanani.

"Ina ganin dole a samu sauran mutanen da suka taimaka wajen bashi hadin kai, tabbas suna bukatar hukunci me tsanani."

"Abinda nayi tunani kenan."

"Dole gobe kowa ya zo, ya zama yana nan kuma ya zama dole Dadah ta fayyace wa kowa babban sirrin dake lullube a zuciyar ta."

"Ina fatan ya zama abu mai sauki da zamu iya dauka."

Alhaji Marwan yace yana kallon Aminatu da yake jin kamar ya dauke ta ya saka ta jikin sa, tun ranar daya fara ganin ta ya kasa tantance abinda yasa yaji wani iri game da ita, ashe jinin sa ne yake yawo a cikin jikin ta.

****
Tashi Ammi tayi da kyar bayan ta gama bawa kanta k'warin guiwar tunkarar ta, tashi Farouk yayi ya bata wajen yana komawa gefen Kamal.
  Da k'yar ta d'aga hannayen ta, ta ɗora su a saman kan Aminatun, kuka ya kuma kwace mata,

"Wacce irin rayuwa 'yata tayi, wacce irin wahala tasha? Wannan wacce irin ƙaddara ce."

Dago fuskar ta tayi wadda ta cika da hawaye ta rungume Ammin da dukkan sauran karfin ta, abinda take jira kenan itama tayi saurin sa hannu ta zagaye ta tana shafa bayan ta

"Ki yafe min, ki yafe min dan Allah, an cuci rayuwar ki, an saki maraicin karfi da yaji tun a karancin shekarun ki bayan baki da hakki akan kuskuren da muka aikata."

"Ammiiiii....!" Ta ja sunan cikin tsananin kuka da ta kasa tantance na farkin ciki ne ko na akasin haka?

"Shissshh! Karki yi kuka, kukan ki ya kare, ke yar gata ce ta kowanne bangare, ba zan taba yafe wa Adam ba, ya cuce ni cuta mafi muni, akan me zai raba uwa da yarta tun zuwan ta duniya, wannan wanne irin rashin imani ne? Akan kuskure daya? Daya tak? Waye baya kuskure a rayuwa dan Allah?"

Idon Alhaji Marwan ya kada sosai yayi ja, tabbas Adam yayi masa cuta mafi muni, ba zai taba yafe masa ba, ba zai taba kyale wa ba sai ya nuna masa akwai banbanci, matsawa yayi har gaban su ya riko Aminatu ya mikar da ita, girgiza mata kai ya shiga yi alamun tayi shiru, da sauri ta fada jikin sa tana sakin kuka muryar ta ta soma dashewa, murmushin karfin hali kawai yake dan yadda yake jin zuciyar sa zai iya kukan. Ta jima a jikin sa tana kokawa da zuciyar ta.
  Ta gefe Farouk ya rabe ya fita yana jawo musu kofar, kai tsaye gida ya nufa domin dauko Iman, a yau yafi kowa murna. Anty Safiyya ta gama shirya su kenan shirin kwanciya bacci ya shigo, dagowa tayi ta kalle shi

"Kar kace min dauke ta kazo yi."

"Anty!" Yace yana murmushi

"Naga aalama ne ai, yaran zamani."

Sosa kansa yayi yana dariya kasa kasa

"Zan kaita ne wajen Ammi da Anty!"

"Auw toh mana, na zata ko rashin ta idon ne ya motsa."

Murmushi yayi ya kama hannun Iman din suna barin dakin. Yanayin tafiyar sa kadai zata gamsar dakai da irin yadda yake ji,farin cikin sa ya gaza boyuwa kwata-kwata, har ya dangana ta da dakin da suke, yasa hannu kadan ya bude yana nuna mata ciki

"Shiga wajen Ummi kinji?"

Daga mishi kai tayi ta sa kai tana kallon ko ina, duk suka juyo suka zuba mata ido, da sauri Ammi ta tashi ta nufe ta tana goge fuskar ta

"Alhaji kaga, ikon Allah kalli Alhaji,."

"Alhamdulillah." Yace yana mika mata hannu ,

"Zo naji ki kusa dani, matso nan sabuwar amarya ta." Ya karashe cike da barkwanci, duk sukayi dariya har Kamal da yake jin kamar ya gama cika burin sa.

***
Dakin Ammi ɗin ta jasu, ta rasa ina zata saka su, komai ta dauko sai ta mayar, kamar a mafarki Aminatu take ji, yau itace tare da mahaifiyar ta cikin yanayi me dad'i beyond her imagination.
  Basu samu runtsawa ba, daren ranar ta fayyace mata dukka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login