Showing 3001 words to 6000 words out of 112633 words
Chapter 2 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
ya dade yana jin labarin yana faruwa ga yara masu kananan shekaru ne ya faru da yarinyar nan, yarinyar da dududu ba zata wuce sa'ar Amal ɗin su ba, da sauri yayi kanta ya dago ta, tuni ta sume saboda tsabar firgicin data shiga, wani irin kuka ne ya taso masa, wannan wane irin rashin imani ne?. Da dukkan karfin sa ya daga ta ya sata jikin sa, be bi ta kan Garbati ba da yake kokarin tare shi, har ya kai kofa maganar shi ta dakatar dashi
"Ni kayi wa wannan dukan? Akan wannan yar iskar yarinyar?"
A halin da yake ciki ba zai iya magana ba, saboda haka ya juya da sauri dan ganin ya ceto rayuwar yarinyar. Yana juyo hargowar Garbatin me cike da gargadin abinda zai aikata masa.
Gida ya wuce kai tsaye yana jin kamar zuciyar sa zata bar jikin sa. Har lokacin dukkan su suna falo ya shigo da sauri dauke da ita Baba maigadi na bin bayan sa, a tare duk suka mike suna kallon shi cike da mamaki.
"Yah Farouk..!
Amal ta fada tana zaro
"Bude min daki na."
Da gudu ta yi gaba suka take masa baya, dakin sa ya kaita, ya kwantar da ita saman gadon sa, sai a lokacin ya ga fuskar ta, kallon su yayi duk sunyi cirko cirko kamar sun ga abin tsoro.
"Kira Dada Ja'afar."
"Wacece ita Yah Farouk?" Ya tambaya ba tare da ya motsa ba.
Kallon sa yayi rai a bace daa karfi yace
"Will you go and call her or..."
Da sauri ya juya ya bar dakin, dafe kansa yayi ya sake dagowa yana hararar kowa.
"Duk ku fice min anan, Amal ki tsaya."
Yar rige rigen fita suka hau yi, kowa zuciyar sa cike da tambayar abinda yake faruwa.
Gefen sa amal ta zauna tana kura mata ido
"Yah bata da lafiya?" Ta fada cikin tausaya wa.
Daga mata kai yayi zaiyi magana Dada ta budo kofar cikin tashin hankali.
"Babana,me ya faru?" Ta fada tana shigowa dakin, ganin da tayi mata yasa tayi saurin ƙaraso wa wajen
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me zan gani haka?"
Hannun sa ya saka cikin na Dadan yana kokarin saita yanayin bugun zuciyar sa.
"Bani ruwa da sauri ke Amina."
Da sauri amal ta tashi ta dauko ruwan, karba ta shafa mata a fuska, sai data yi wajen sau uku sannan ta bude ido tare da sakin wani irin ihu wanda ya karade kusan kowanne lungu da sako na gidan.
Bude ido na nayi wanda yayi min matukar nauyi ina kallon kowa na dakin, a lokaci daya zuciya ta ta shiga tariyo min abinda ya faru, kuka sosai na saka ina jin tsananin zafi kamar an watsa min barkono, riko ni dattijiwar tsohuwar dake kusa dani tayi tana kokarin sani a jikin ta.
"Kwantar da hankalin ki, yi shiru, babu abinda zai faru kinji? Yi shiru karki karawa kanki ciwo."
Abinda kawai naji tana ta maimaitawa kenan yana shiga kunne na cikin wani irin yanayi dana kasa tantancewa.
"Dada asibiti zamu kaita, She's bleeding so Badly."
Muryar sa ta daki kunne na, kallon sa Dada tayi kafin tayi magana cikin harshen turanci.
"Who is she?"
"It's a long story, babu time zan sanar dake komai, for now let's help her please."
Ya karashe a marairaice.
"Owk, Amma Ina son sanin amsar, kasan dai mahaifinku, kasan kuma labari zai kai masa zuwa gobe, i just hope ba kaine ba."
Ta zura masa ido tana son ganin gaskiyar sa. Be yi magana ba, sai ma mikewa da yayi ya fice daga dakin, jim kadan ya dawo yana kallon Amal data makale a gefe tana mun kallon tausayi.
"Zaki rakamu ko?"
Da sauri ta daga kanta.
"Dada ga driver ya dauko motar, muje ko?"
" Shikenan."
A hankali ta daga ni zata mikar dani, wata irin kara na saki me cike da azaba, da sauri ya waiwayo ya fasa kokarin fita daga dakin, da baya da baya ya dawo ya daga ni chak ya fita dani suna take masa baya.
***
Tun Inno na zuba idon dawowa ta har hankalin ta ya fara tashi, ganin tasowar hadarin yasa ta sake shiga tashin hankali sosai, turawa tayi aka kira mata Nura a zaure ya bi bayana, lokacin iskar nan ta taso sosai. Safa da marwa Inno kawai take yi, duk wajen kowa yayi tsit ana jiran dawowar Nura, tsawon mintuna talatin ya dawo hankalin sa a tashe, babu ni babu dalili na, hakan kuma yayi daidai ta tsugewar ruwan, iya kar tashin hankali Inno ta shiga, bata fatan abinda zuciyar ta ke raya mata ya zama ya faru,bata da wata hujjar kare kanta a duk lokacin data shirya karbar muradin zuciyar ta, ko ma ba haka ba, baya cikin yarjejeniyar da sukayi tsakanin su, ko ba komai zata ci darajar nata dan.
Tuni su karime da sauran yaran suka fara kuka, babu me rarrashin wani, ana haka ruwan ya fara tsayawa, gaba daya suka fito dan zuwa nema na, lungu da sako babu alamun za'a same ni, tashin hankalin da ba'a sa maka rana kenan, gida suka dawo kowa yayi jigum jigum ana tunanin ta in da zan ɓullo, duk da zuwa lokacin kowa ya gama saddak'arwa wani mugun abin ya same ni.
Duk suna zaune sunyi cirko cirko, makotan da suka shigo duk sun tafi, yara sunyi bacci sai yan kadan, aka yi sallama a kofar gidan, da sauri su Nura suka fito tare da su Baba.
"Garbati?" Nura ya fada yana kallon su.
"Mune nan." Ilu ya amsa yana jingina a jikin garu
"Lafiya dai ko?" Baba yayi tambayar ganin basu ce komai ba.
Ilu ne ya kalli Garbati kafin ya shiga magana
"Dama akan Aminatu ne."
Da sauri a zabure suka hada baki.
"Kun ganta ne?"
Ilu ne ya dora
"Bamu ganta ba, sai dai mun san inda take, dan munyi iya kar kokarin mu wajen ganin mun taymaka mata, garin haka ne ma Garbati yasha wannan dukan da zaku ga jikin sa haka." Ya fada yana haske Garbatin
"Tana ina?"
"Ina bakin gidan Bature? Daya daga cikin su ne muka kama shi, dan a lokacin da muka je ko numfashin kirki batayi, garin kokarin mu ne ma yasa masu gadin su sukayi wa Garbati mugun dukan nan, sannan ya dauke ta ya tafi da ita."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan
©️Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
(3)
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Suka hada baki suka fada a tare.
"Yanzu ina ya kaita?" Baba ya tambaya cikin jimami.
"Wallahi muma bamu sani ba, mun dai zo mu sanar ne dan a sani, amma abunda yafi shine mu dunguma muje gidan su, idan yaso sai a sa ya fito da ita. "
"Abinda za'a yi kenan, kai Nura shiga kira min Yahya da Lawan duk mu dunguma, ba dan dare yayi ba ma wajen maigari zamu fara zuwa."
A tare suka fito, Inno na tambayar su yadda ake ciki babu wanda ya tanka mata, suna fita ta sulale kanta na juya mata, tsananin tsoro ya hana ta motsi, idan ta tuna abinda zai faru.
Babu kowa a hanya har suka isa gidan, haske fitilu ne tarwai kamar rana, buga kofar Ilu ya hau yi da dukkan karfin sa Garxali na taya shi, Baba maigadi ya taso a zabure yana tunanin ko sune suka dawo. Yana budewa yayi turus ganin mutanen da be wani waye dasu ba a wannan daren, kallon kallo sukayi wa juna kafin yayi karfin halin tambayar su
"Lafiya dai?"
Lawan da duk yafi zafi cikin su ya bata rai yana leken gidan
"Yarinyar mu da kuka sace muka zo ku fito da ita."
Da sauri Baba maigadi ya kalle su yana tuno abinda ya faru kafin isowar su, kar dai ace? Da sauri ya kauda tunanin yana mai tabbatarwa kansa hakan ba mai yiwu wa bane, yasan waye Farouk, yasan me zai aikata, duk da ance ba'a yabon yaran yanzu, sai dai yana kyautata masa zato ko ba komai yaro ne nutsattse.
"Kayi magana mana, wallahi ko a fito da ita ko mu nuna muku mune muke da garin nan dan uwar mutum."
Garbati ya katse masa tunanin da ya tafi na wucin gadi, kallon su yayi daya bayan daya yana yanke hukuncin abinda ya kamata ya sanar musu.
"Bansan me kuke magana akai ga gaskiya, babu kuma wata yarinya da tazo gidan nan, amma ku bari na shiga ciki na yi magana da masu gidan."
"Karya ne wallahi, karku yarda Malam Ayubah, yaran gidan ne a gaban idon mu ya sungume ta ya tafi da ita, bayan ya gama da ita, Allah ma yasa ba yan yankan kai bane wallahi."
"Subhanallah!"
Sai a sannan Baba yayi magana yana jan murya
"Kayi wa Allah idan diyata na hannun ku ku fito min da ita, hankalin mu gaba daya a tashe yake, dan Allah na roke ka."
"Wallahi Baba bansan komai akan maganar da kuka zo da ita ba, amma me zai hana mu bar maganar zuwa garin Allah ya waye, a lokacin masu gidan ma sun tashi, kunga sai ayi magana sosai."
"Kana nufin mu bar maganar yar mu har sai gobe, bamu san halin da take ciki ba, idan ma cinye ta za'a yi ko kashe ta zuwa goben kaga shikenan ko?saboda ba yarka bace ta bata ba. Toh wallahi ba'a isa ba."
"Ni dai kuyi hakuri dan Allah."
Zasu sake magana Baba ya dakatar dasu
"Mu bar wa goben idan Allah ya kaimu, ita kuma Allah ya bayyana mana ita, ku muje dare na sake yi."
Haushi ne ya taso wa Garbati, ba haka yaso a tashi wasan ba, so yayi su kutsa kai gidan ya samu damar cin uwar yaron nan, kwafa yayi a ransa yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai masa idan Allah ya haɗa su. Zai gane ya tana Gaza Boy.
***Karamin asibitin dake garin suka kaita, babu alamun ma ana aiki a asibitin, maigadi ne kawai yayi saura da yar karamar torchlight din sa babu isasshen haske, Farouk kamar zaiyi kuka haka yaji sanda maigadin ke musu bayanin babu kowa a ciki sai majinyata. Juyawa sukayi suka dau hanyar fita daga kauyen baki daya.
A lokacin jiki na ya kara tsami sosai, ko ina ciwo yake min zufa nake kamar wadda ta hadiyi kunama, babu abinda nake sai kuka Amal na tayani, Dada kam duk hankalin ta ya kara tashi, musamman ganin yanayin da na sake shiga daga fitowar mu zuwa yanzu.
Juyowa yayi a hankali yana kallon bayan motar be ce komai ba sai kura musu ido da yayi yana jin kamar ya bude motar ya fita, yasan Amal da raguwar zuciya da saurin kuka, kasancewar ta marainiya wadda bata san mahaifiyar ta ba yasa yake tausaya mata, baya son ko kadan yaji kukan ta, sai dai kukan yarinyar da yake ji yana neman danne kukan Amal din, har ya zama baya jin na Amal din sai nata kawai dake masa yawo a cikin kunnen sa, zuciya da ruhin sa.
Suna zuwa asibitin aka karbe su, suka zauna a reception aka shiga da ita ciki, Farouk kasa zama yayi ya shiga kai kawo a wajen yana ayyana rashin imanin wasu mazan, basu da maraba da dabbobi. Fitowar Dr Iman yasa duk suka mike, kallon su tayi sosai taga babu alamun kauyanci a tattare dasu, dan bata fuska tayi kafin tace
"Kuzo office Ina son magana daku ku biyu." Ta fada tana nuna Farouk da Dada, rufa mata baya sukayi suna shiga ta tura kofar tana jingina a jikin kujerar ta
"Menene alakar ku da patient din nan?"
Kallon Farouk Dada tayi zatayi magana yayi saurin katse ta
"We are Family Dr."
"Good." Tace tana zama
"Kenan my guess was right, kunyi wa yarinya karama at her age aure, sannan saboda rashin imani ka kasa hakuri da kankantar ta, kayi forcing kanka akanta ko?"
"A ah likita..." Dada tayi saurin katse ta, kafin ta k'arasa yayi maza ya sauke kansa kasa a hankali ya furta.
"Haka ne Dr, I'm very sorry, kuskure ne."
Biron hannun ta ta saka a bakinta tana kallon sa, shi a karan kansa ba wani babba bane, bata jin zai dora shekaru 20 idan ya dara to ba zai fi da biyu zuwa da hudu ba, yanayin jikin sa na girma da cika yasa zaka kasa tantance shekarun sa, sai dai duk da hakan ba za'a hada shi da yarinya yar shekara goma da doriya ba. Cire glasses din idon ta tayi ta fara magana a hankali cike da nasiha, dan a yadda tayi niyyar shigar dashi kara duba da yadda ta ga halin da ya saka yarinyar a ciki, sai dai yadda ya amsa laifin sa kai tsaye yasa ya sauko ta shiga nasiha da dukkan kokarin ta.
Hannayen Dada a makale da ita ta zuba su akan Farouk din, mamaki ne karara kwance a fuskar ta, bata gane nufin sa ba, bata gane inda ya dosa ba, tasan shi da tsananin tausayi amma bata taɓa tunanin zai iya aikata daukar laifi a ajiye akansa ba, tuni zuciyarta ta sake tsinkewa, idan har hakan ne kuwa ya tabbata Farouk din ne ya bata musu yarinya, in kuwa hakan ta kasance bata san ya zatayi ba.
Bayan sun fito daga dakin Dr yaki yadda su hada ido sam Dada, yasani sarai tana bukatar gamsasshen bayani, amma baya so ya sanar mata da komai sai ya samu nutsuwar zuciya.
Dakin da aka kwantar da ita suka tura suka shiga, Amal na zaune kan kujera tana bacci, drip ne a daure hannun ta, bacci take sai dai yanayin fitar numfashin ta ya nuna tsantsar wahalar da take ciki, karasa wa yayi gaban gadon yana sake kallon ta.
"Umar!"
Dada ta kira sunan sa, yanayin Muryar ta kadai yasa ya gane abinda zata ce, kasa juyowa yayi har sa data maimaita kiran nasa.
"Na'am Swthrt."
"Ba wasa nake maka ba, kasan kuma ni ɗin ba sa'ar tsohon ka bace balle kace zaka maida ni mara hankali ko wata chan daban, wacece yarinyar nan? Menene alakar ka da ita?"
Juyowa yayi yana fuskantar ta, ganin ta bata rai sosai babu alamun wasa yasa shi takowa har gaban ta. Sai da ya daidaita tsayuwar sa a gaban ta sannan ya fara magana cikin son gamsar da ita.
"Kiyi hakuri idan na bata miki rai, hakan da nayi ba wai nayi ne dan na bata miki ba, wallahil azim bani da wata alaƙa da ita,hasalima bansan wacece ita ba, bansan komai game da ita ba."
"Aina ka samo ta toh idan baka santa ba?"
"A daidai lokacin da Allah ya saukar mana da daya daga cikin ni'imomin sa, a daidai lokacin wani mara imani ya aikata mata wannan aika aikar, babu digon tausayi ko imani a tattare dashi, bansan shi ba, bansan waye ba, ihun ta kadai naji, na taimaka mata."
Kallon sa take har ya kai karshe, ganin bata ce komai ba yasa shi kama hannun ta
"Ki yarda dani, ba zan taba iya aikata wa wata mace makamancin wannan ba."
"Naji! Amma menene dalilin ka na amsa wa likitar nan a matsayin kaine mijin ta? Baka tsoron maganar ta fita, bayan kasan waye mahaifin kuma."
"Hakan shine daidai, karki manta wannan abun babban tabo ne a tattare da duk wata ya mace, da zai iya zama wani babban gibi a rayuwar ta. Banyi hakan da wata manufa ba face don kare mutuncin ta."
Turo kofar akayi, hakan yasa yayi shiru yana duban su, Dr Iman ce sai wata nurse a bayan ta.
Dan dube duben su sukayi suka juya, har ta kai kofa ta juyo.
"Af na manta, akwai alluran da za'a yi mata da safe gobe, , so ka zama around please."
"In Sha Allah."
"Good."
"Kai zaka kwana kenan?" Dada ta fada tana kura masa ido, har zai ce eh sai kuma yayi wani tunanin daban
"A ah, kece zaki taimaka."
"Amal fa? Kalli a yadda tayi bacci."
"Eh zanje na tambaye su idan akwai spare gado sai su bamu mu biya sai ku kwanta akai, dama dare yayi yanzu komawa hanyar nan akwai risk, in yaso ni sai mu kwana a mota."
Dan jim tayi kadan kamar zatayi magana sai kuma ta girgiza kanta kawai ba tare da tace komai ba ta koma gefen gadon ta zauna tana kura mata ido kamar me karanto wani abu a tattare da ita.
***
Da safe na bude ido na ina karewa dakin kallo, daidai lokacin aka turo kofar aka shigo hade da sallama, zuba masa ido nayi ina kallon sa har ya iso gaban gadon, shi din ma kallon nawa yake fuskar sa dauke da murmushi. Juyawa yayi yana kallon Amal dake bacci hankalin ta a kwance, karar ruwan da yaji a toilet yasa ya gane Dada na ciki. Sake matsowa yayi gaban gadon ya furta a hankali
"Ya jikin?"
"Da sauki." Na amsa da sauri ina kallo sa
"Sannu kinji."
"Toh." Nace ina sake bin fuskar sa da kallo kamar me son tuno abu. Murmushi ya sake yi yana kallon drip din dake shiga cikin jikina a hankali, file din dake ajiye saman drawer saka magunguna ya dauka yana dubawa har Dada ta fito.
***Yanayin horn din kadai ya tashi kowa na gidan, a firgice su ja'afar suka fito falo kowa ya tsaya, ba sai an fada musu ba sun san kowa ye, tsoron su daya abinda ya kawo shi a irin wannan lokacin, iya sanin su ma baya kasar baki d'aya. Motoci uku ne suka shigo a jere, kai kawo Baba maigadi ya shiga yi har suka daidai ta a harabar gidan. Cikin shigar sa ta Babban sojin kasa ya fito daga motar fuskar sa dauke da yanayi marar misaltuwa.
"Barka da zuwa." Kawai kake ji kowa na kawo gaisuwa. Jiki a sanyaye su Ja'afar suka dunguma zuwa harabar gidan kowa tsoro fal zuciyar sa.
A daidai lokacin aka fara bugo da mugun karfi kamar za'a balla gate din gidan, hayaniyar mutane ke tashi da alama ba mutane ne kadan ba. Da sauri ya kalli Baba maigadi Yana neman karin bayani.
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta