Showing 108001 words to 111000 words out of 112633 words

Chapter 37 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7432

kallon kanta a mudubi, shigar ta cikin ɗinkin lace white and red riga da zani yayi matukar yin kyau da dacewa da yanayin jikin ta, mayafi ta ɗora a saman red bayan ta daura dankwalin, tayi kyau ainun kamar ka sace ta, turo kofar akayi ta dakata da abinda take, Kamal ne hannun sa makale cikin dogon wandon sa, murmushi tayi ta zauna saman stool din gaban mirror tana duban sa har ya ƙaraso.

"Sis, kingan ki kuwa? Wannan ai sai ki rikita Ya Farouk din."

"Toh sarkin tsokana." Ta saka dariya

"Allah dagaske nake, kin fito a amaryar ki, ga angon chan a falo sai kizo muje wajen Old Woman kinsan tun dazu take zuba wa hanya ido, yau kafar ta matsa mata shisa bata fito ba."

"Allah sarki Hajiya, muje toh." Tace tana zura takalmin ta.

Idon ta akan sa suka fito, ya shirya tsaf cikin shigar manyan kaya da suka dace da tsari da yanayin sa, kamshin turaren sa ya gauraye ko ina na falon, idon sa akan Tv har suka gifta shi be kalle su ba, hakan ya kara sata a wani yanayi mara dadi, haka ta daure suka dangana da bangaren Hajiyan, sukayi mata sallama har da kwallar ta sannan ta fito.
   A tunanin ta zata tadda shi a falon, suna shigowa ta ga wayam babu shi, sai ta zame ta zauna a saman kujerar da ya tashi, ta soma tsorata da fushin nasa, amma babu komai zata san yadda zata bullo masa dan ba zata jura ba.
   Da suka tashi tafiya kowa ya fito, har gaban motar iyayen suka rako su, kowa yana musu fatan alkhairi, kasa duban kowa tayi zuciyar ta ta karye, kuka ta soma kasa ƙasa ba tare da ta bar kowa ya gane ba. Sai da driver ya kunna motar sannan ya ƙaraso wajen, yayi sallama da kowa ya fada bayan motar, sanyayan turaren sa ya cika kofar hancin ta, a dan kaikaice ya kalle ta, yayi murmushin mugunta ya maida kansa window yana duban hanya, har suka isa airport ɗin babu wanda yayi wa wani magana, shi ya fara fita ya sauke kayan su, sannan ya buɗe mata kofar yana duban chan wani waje, a kasalance ta fito tana kokarin sai ta kalle shi amma sam ya hana ta hakan, jan kayan nasu ya shiga yi ta bi bayan sa tana sake sake.
   Har aka gama duk arrangements din da za'a yi bata kara ganin sa ba, sau daya ta hange shi chan suna magana da wani agent, zuwa chan jirgi ya sauka suka dunguma zuwa ciki, She's feeling nervous saboda lokacin ta na farko kenan data tako cikin airport, jiri take ji ga wani mugun tsoro daya cika mata zuciya, daurewa tayi ta cigaba da bin sa a baya, har suka dangana da cikin jirgin zuwa lokacin tsoron ta ya dada karuwa.
    Bayan sunyi settling aka yi a announcing kowa ya saka belt jirgi zai tashi, hannun ta ne ya hau rawa, yana lura da ita, tana kokarin sawa taji hannun sa saman nata, ta dago da sauri, sunkuyowa yayi daidai fuskar ta, yayi mata kallo ɗaya ya maida kansa kasa, ya daura mata belt din, sannan ya saka nasa, ya zauna sosai ya kwantar da kanta saman kafadarsa kusan rabin jikin ta na saman nashi a hankali ya furta

"Stay still matsoraciya."

Tsit tayi kamar ruwa ya cinye ta, tayi lamo tana jin tsoron na barin ta a hankali, she feels so comfortable a yadda yayi mata, har bata san sanda jirgin ya daidai ta a sararin samaniya ba. Shi kansa ya kasa tantance yanayin da zuciya da gangar jikin sa suke ciki, be ki su zauna a haka ba.

"Ya Farouk." Ya tsinkayi muryar ta kamar me rada a saman kunne sa, lumshe ido yayi ya buɗe ya zuba mata su

"Uhum?" Yace ya kasa buɗe bakin sa saboda yadda yake ji

"Ina zamu je?"

"Siyar dake zan, Allah sa ma zakiyi tsada."

Shiru tayi bata kuma cewa komai ba, har zuwa sanda suka isa, hannun ta ya kama suka fito, yanayi da tsarin filin jirgin kadai ya isa ka gane ka bar Nigeria kasar mu ta gado, fararen Larabawan da suka yi wa airport ɗin ado yasa ta gane kasar da suke, bakin ta ya gaza boye farin cikin da take ciki, yau itace a birnin na Makka da take hasashe da burin zuwa, a hankali ta soma takawa a ƙasar me tsarki, tana biye dashi kamar ragumi da akala, taxi ya samar musu har zuwa masaukin da zasu sauka wanda ya riga yayi booking din sa tun kafin zuwan su kasar.  
   Da kallon manya manyan gine-ginen da suka kawata garin ta shagala, har bata san sun iso ba sai dayayi magana, a kunya ce ta sauko tana kara kallon ko ina cikin tsananin mamaki.
   Girman hotel din kaɗai abin kallo ne, ya tsaru ta ko ina, komai tsaf tsaf kamar ka kwanta a kasa, wani a cikin ma'aikatan ne yayi musu jagoranci zuwa masaukin nasu, wanda ya kasance aljannar duniya, falo ne babba sai bed room me dauke da madaidaicin gado.
  Sallah suka fara gabatarwa daga nan sukayi order abinci suka ci. Farouk ne ya fara wanka ya sauya kayan sa ya fita, hakan ya bata damar watsa ruwan ita ma, ta bi lafiyar gado tana jiran dawowar sa.
   Ya jima sosai kafin ya shigo dauke da manyan ledoji, kayan da zasu bukata na dan zaman da zasuyi ya samo, da sauri ta tashi ta karbi kayan, tana yi masa sannu da zuwa.

"Sorry na barki ke kadai."

"Ba komi." Ta ambata a hankali.

"Gobe idan Allah ya kaimu zamu fara Umrah, saboda next week zaki ga likitan ki, so get ready."

Yace yana wucewa daki, kwanciya yayi ya huta, ita kuma ta kunna Tv tana kalla duk kewar gida ta taso mata.
   Sai da aka kira sallah sannan ya fito, da alamu ma bacci yayi, alwala kawai yayi ya fita, hakan yasa ta tashi itama ta gabatar da sallar sannan ta dan sake cin abinci ta zauna tana cigaba da kallon.
  Makale da waya a kunnen sa yana magana ya shigo, zare wayar yayi ya mika mata, yana cewa

"Ammi ce."

Da sauri ta karba ta tashi tayi ciki ya bita da kallo yana murmushi, so yake sai yayi mata horon da zata kawo kanta gareshi, gashi duk ya soma gazawa amma haka zai daure dan yaga alamar wasan zaiyi dadi, mimmikewa yayi a saman kujerar har ta dawo ta mika masa wayar sa, chan gefe ta koma ta zauna tana satar kallon shi, ranshi fes yana ta danna wayar sa yanayin fuskar sa ya nuna yana jin dadin abinds yake, sosai ranta ya sosu ganin ya share ta, tashi tayi ta wuce daki tayi shirin kwanciya kawai dan ta ga abin nashi ba na kare bane.
   Anan falon yayi kwanciyar sa, tun tana sa ran shigowar sa har ta hakura ta kwanta.
  Washegari suka soma Umrah, hakan ya kara haifar da nisa tsakanin su, dukkan su sun shagala wajen Ibadah musamman Aminatu da take ganin dama ce da zata bautawa Allah sosai ta kuma yi masa godiya bisa sauya sauyan da ya samu rayuwar ta.
  Sati guda sukayi suna Ibadah, a ranar da suka sauke Umrah da daddare tana zaune tana duba wayar ta, gama maganar su kenan da Iman da Hajiya Turai ta zauna tana tunanin rayuwa, shigowa yayi ta bishi da ido, ya wuce kai tsaye wajen kayan su ya dauki bathrobe ya daura, ta gefe take kallon duk abinda yake yi, toilet ya fad'a ya jima a ciki yana wanka, ta lura dama yana da dadewa a toilet, tashi tayi ta fiddo masa doguwar rigar sa da boxer ta ajiye a saman gadon tayi hanyar barin dakin daidai lokacin ya turo kofar toilet din ya fito.

"Bani karamin towel."

Yace yana k'arasa wa gaban mirror, da baya ta dawo ta dauko ta mika masa kanta a ƙasa, kin karba yayi ya zuba mata ido, material ne a jikin ta silk anyi masa ɗinkin riga doguwa me fadi daga kasa, saman ta kuma ya tsuke, yawo ya  shiga yi da idanun sa, dagowa tayi da nufin sake mika masa idanun ta suka shiga cikin nasa, rage musu karfi yayi saurin yi zuwa kanana masu bayyana asirin zuciyarsa, da towel ɗin da hannun ta ya hade ya riga yana dage mata gira

"Taimaka pls, tayani rage ruwan kaina."

Zame hannun ta tayi, ta ja masa kujera ya zauna ta saka towel din tana share masa kai, lumshe ido kawai yake yana buɗe su tana lura dashi ta mudubin

"Na gama." Tace tana mika masa, langabe kai yayi cikin shagwabe murya yace

"Ki karasa ladan ki, get me dress ba zan iya ba."

"Sai kace Iman?" Tasa dariya

"Eh karki manta I'm the first and last born wajen Mummy da Daddy na, dole nayi shagwaba ai"

"Soon za'a haifo twins ai,ka daina feeling kanka, bayan haka ma ai Ja'afar ne dan gaban goshin Mummy not u."

Matso da ita yayi ta zauna saman cinyar sa, a kunne ya rada mata

"Kece zaki haifa mana twins ai, Mummy ta tsufa sai mu bata kawai, ko mu bawa Ammi daya itama daya mu karbe Iman."

Dariya tasa tana zamewa jin ya fara chanja salon, matse ta yayi gam ya hana ta motsi, kansa na saman kafadarta ya shiga aika mata da sakonnin sa, shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, ta gaza yin komai duk ya kanainaye ta, maganganu yake mata masu dad'i da sa kwanciyar hankali, sosai hakan yayi tasiri akanta. A hankali komai ya shiga chanjawa zuwa wani bigire me cike da farin ciki da kaunar juna, it was a memorable night a wajen dukkan su, hakan ya sake haifar da shakuwa mara misaltuwa a tsakanin masoyan biyu.

   Da safe suka tashi so happy and energetic, tsokanar ta yake taki kulashi, kunya da nauyin sa take ji, kasan zuciyar ta cike yake da kaunar sa, kauna me sanyi, mutunci da karamcin sa gareta abu ne me matukar muhimmanci a wajen ta, he's the perfect husband da duk wata mace zata yi muradin samu.
    Tare suka shirya suka wuce asibitin, domin ganin likitan idon nata da ya basu appointment yau, hannun su sarke da juna suka shiga asibitin, da fara'a ya karbe su, babban mutum ne dan a ƙalla zai girmi su Daddy, tests ya saka aka fara yi mata, daga karshe ya dora ta akan strong magunguna da zasu taimakawa idon wajen karo karfin ganin, kwana uku tayi tana shan magungunan suka koma, akayi mata aikin idon, cikin nasara akayi aikin aka gama, cikin hukuncin Ubangiji sai ga idon ta ya dawo ras tana ganin komai tar ba kamar da take amfani da glass ba, farin cikin da suka shiga mara misaltuwa ne, haka sukayi ta kiran mutane suna sanar musu cike da farin ciki.
 
Daga nan Dubai suka wuce, anan suka mori amarcin su sosai, suka yi yawon wajejen shakatawa kafin su tattaro su dawo.

****
Yana zaune bayan yaje sun Alhaji Marwan, yaji dadin yadda ya karbe shi sosai, ya kuma yi masa godia bisa alkhairin da yayi wa Aminatu, sannan yayi masa tayin aiki a kamfanin sa dake Kano, yaji dadi ssoai kuma ya amsa tayin babu wani dogon tunani don aiki a kamfanin sa aiki ne me kyau da tsoka, gashi kuma permanent and pensionable ne.
    Ji yayi yana bukatar yaje yayi shopping saboda gobe yake sa ran shiga Kano domin ya sanar wa Hajiya labarin, tashi yayi ya sauya shigar shi zuwa kananan kaya, ya fito. Kai tsaye supermarket din daya saba siyayya ya shiga, ya wuce direct inda yasan zai samu abubuwan da yake bukata.
   A daidai lokacin wata hadaddiyar beb ta turo kayan data siya tana ta mitar bata musu lokaci da wadda suke tare tayi,ji tayi tayi karo da mutum ta dago a zaton ta ameerah ce, bude idon sa yayi sosai akan ta, chubby cute little girl da ita, she looks so young and naive.

"Sorry." Yace mata a gajarce ya raba ta gefen ta ya wuce, da kallo ta bishi, zubin sa irin na first class guys din nan, masu nutsuwa da kamala, a take taji ta kamu, kamuwa me karfi, yayi mata 💯 ba karya, tana tsaye har ameerah ta karaso dauke da wani lotion da ta tsaya nema,

"Sheshe na samo shi fa, sorry nasan kin gama shaka." Ta kama kunnen ta tana dariya alamun ban hakuri

"Karki damu,jiran yayi amfani, muje." Ta tura bsket ɗin tana yin gaba. Cike da mamakin ta bi bayan ta, ganin sudden change a wajen Raheenat sheshe, kada kai kawai tayi ta san koma menene zata sanar mata.
  A wajen biyan kudin suka sake haduwa, satar kallon juna sukayi tayi har suka gama. Tare suka fito ya shiga motar sa suma suka shiga tasu, bin su ya dinga yi a hankali har suka isa gida, sai da yaga shigar su sannan ya fito ya karasa wajen maigadi ya tambaye shi akan ta,be boye mishi komai ba ya sanar dashi komai, kai tsaye ya nemi izinin ganin mahaifin ta, lokacin yana garden din sa yana hutawa maigadi ya sanar dashi, yace ya shigo dashi
    Bayan sun gaisa ya fada mishi abinda yake tafe dashi, tare da neman izinin magana da yar shi, hakan yayi wa mahaifin nata dadi kwarai, dan ba'a taba masa haka ba, yawanci sai sun gama daidai wa da yaran sannan iyaye ke samun labari.
   Hakan da Anas ɗin yayi shine koyarwa addinin musulunci, idan kaga yarinya kana so ka fara neman izinin iyayen ta. Tambayoyi yayi masa masu yawa, ya kuma fuskanci abubuwa game da Anas ɗin, yaron yayi masa sosai, zai kuma so ya hada shi da Raheenatu dama ita kadai ta rage duk ya aurar da yayyenta. Waya ya daga ya kira ta yace tazo garden ta same shi, hijabi ta ɗora a saman kayan ta fita, gaban ta taji yana faduwa tun da ta doshi wajen, kamar wadda kwai ya fashe wa haka ta karasa, tana ganin shi gaban ta ya fadi, tayi saurin durkusawa a wajen cikin rawar baki tace

"Gani Baba."

"Yawwa auta ta, ga bakon ki nan ki kaishi wajen zaman chan sai kuyi magana ko."

A kunyace ta amsa hakan ya kara dilmiyar da Anas cikin kogin son ta. Shi dinma kunyar yaji ya tashi da kyar yabi bayan ta, kanshi tsaye ya gabatar mata da kansa da abinda ya kawo shi, sosai ta jinjina karfin halinn sa, sai dai hakan ya kara birgeta, nauyin sa ya hanata cewa komai, sai kawai ya karbi number ta yayi mata sallama ya tafi.
  
Sanda Hajiya ta samu labarin har da taka rawar farin ciki, ga aiki me kyau ga mata, amfanin Alkhairi kenan, baya faduwa kasa banza.





****
Bayan shekara daya da rabi

Cikin hukuncin Allah bowayi gagara misali, abubuwa da yawa sun faru, rayuwa ta chanja komai ya cigaba da wakana da wanzuwa kamar yadda yake, sauye-sauyen da aka samu basu sa karaya ko kosawa ba, zaman lafiya kowanne bangare suke cikin so da kaunar juna, Dadah da Mummy komai ya wuce, ba zaka taba tunanin akwai wani abu daya taba faruwa tsakanin su ba, yadda take mutunta ta a da har yaso yafi haka.
   Bangaren masu laifi kuwa kowa ya girbi abinda ya shuka, a zaman gidan yarin ne Adam yayi fada da wani kasurgumin dan bashi, cikin dare kuwa ya biyo shi ya luma mishi wuka a ciki inda ya kashe shi har lahira ya kuma haka rami ya binne shi a wajen, sai da aka tsananta bincike sannan aka gano. Duk da labarin be ma kowa dadi ba, amma sun tabbata hakan shine abinda Allah ya tsara, shiyasa a rayuwa komai kayi me kyau, kuma karka biyewa rudin duniya da zuciya domin zasu kaika su baro ka. Ko babu tsufa akwai mutuwa!

Bangaren Inno tayi nadama sosai inda Aminatu da Kamal suka tsaya mata sosai suka chanja mata komai na gida da rayuwar ta sannan Aminatu ta bata jari me tsoka ta cigaba da juyawa, kasancewar ta mace me zafin nema, nan da nan ta kara bunkasa ta cigaba da juya kudin tana cire riba, duk yadda Kamal ya so share ta ya kasa,dole ya saki jiki ya ke shiga duk wani al'amuran ta,dolen sa ce shiyasa ma da auren Karime ya tashi shine akan komai, yayi uwa yayi uba ta tare a gidan sabon mijinta me kirki da yakana, ba laifi yayi karatun sa na boko dana arabi, matar sa daya suna zaune lafiya da Karimen tunda dama chan bata da matsala. Jarin itama Aminatun ta bata take yan kulle kullen ta a tsakar gida tana siyarwa.

Da bikin ya Anas ya tashi da amaryar sa Rahee da suka dade da daidaita junansu har gida ya kawo wa Aminatu ita ta wuni, ta kuma gayyace ta bikin.
   Da ya dawo daukar ta sai ya kira hajiyan sa ya aika da wayar sukayi magana da Aminatu ta bata hakuri sosai ta kuma gayyace ta bikin da za'a hada dana Ramlah, Aminatu taji dadi sosai ta kuma yi mata alkawarin zuwa idan lokacin yayi, anan sukayi exchanging number da Raheenatun da alƙawarin zata zo koyon hadaddun dishes don ita ɗin k'wararriyar chef ce.

****

Cikin shigar doguwar riga baka me adon pitch ta sauko, babu kowa a kasan ko ina tsaf an gyara shi, Kitchen ta nufa kai tsaye ta tarar da Baba Altine na aiki, a jikin babban freezer dake ajiye gefe guda a Kitchen din ta tsaya tana dora jakar ta a sama gami da files ɗin da  zata buƙata.

"An fito? Ina kwana?!" Baba Altine tace tana goge hannun ta da madaidaicin towel

"Barka da safiya Baba, kin ga naso makara akwai cases da yawa da ya kamata nayi clearing yau, gashi me gayya me aiki yace yana hanya yau, amma zanyi kokarin ganin na dawo da wuri."

"Ah kice yau wajen Hajiya zan gudu maigida zai dawo."

Dariya ta saka bayan ta gama jera abinda zata bukata akan dan karamin tray ta dauka ta wuce falo, a gaggauce ta karya tayi mata sallama ta fito, a baya ta watsa kayan hannun ta ta fada motar ta kirar Camry ja me gadi ya wangale mata gate.
   Sai data daidaita a titi sannan ta daga wayar ta dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login