Showing 87001 words to 90000 words out of 112633 words
Chapter 30 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
asibitn da aka kai shi suka wuce suna zuwa kasar tsaye suka nufi accident and emergency unit.
A lokacin ya riga ya zama unconscious be san wanda yake kansa ba, dukkannin fuskar sa an rufe ta da bandage sai karaya a hannun sa na haggu.
Tsananin tashin hankalin da suka shiga ba zai misaltu ba, sai ga Alhaji Marwan na share hawayen tsananin tausayin dan nasa, ba'a ta Ammi da kowa yasan yadda uwa kan shiga tashin idan abu ya samu danta.
Isowar Daddy ya d'an saukaka abun, kwarai ya tausaya wa aminin nasa yadda yaga ya koma a lokaci daya kamar wanda yayi kwanciyar shekara.
*****
Tun bayan fitar Anas babu wanda ya sake magana a cikin su, kamar kurame sai dai idon sa na kanta duk sanda ta dago sukan hada ido sai yayi saurin basarwa yana maida kallon sa kan yar sa. Fita Baba Altine tayi ta basu waje dan sam bata ji dadin yadda akayi wa Anas ɗin ba, gefn Amal tayi zaman ta tana kallon yadda mutanen asibitin ke kaiwa da komowa.
Kiran wayar Farouk din akayi, kamar bazai daga ba ganin Iman na kokarin farkawa yasa shi dagawa dan kar a tashe ta, Ja'afar ne, baya kasar shima ya tafi karatu sai yanzu yake samun labarin dawowar Farouk din a wajen Dadah da sukayi waya shine ya gwada kiran tsohon layin sa na Mtn aikuwa sai gashi ya shigo.
"Da gaske ka dawo? Wow nayi mamaki wallahi."
"Uhum... Na dawo, kana lafiya?" ya amsa masa
"Lafiya lou, sai dai banji dadin tafiyar ka ba Allah, ina tunanin baka san halin da Mummy ta shiga ba bayan tafiyar ka."
"Ja'afar, kana ji? Ina wani abu yanzu very important, muyi magana anjima."
Be jira amsar sa ba ya katse kiran yana jan dan karamin tsaki. Kallon ta yayi yaga shi take kallo, harara ya sakar mata
"Dan na kori dan iskan chan kike share ni ko?"
Yace yana baro kujerar da yake kai
"Ba haka bane..."
"Yaya ne? Ina lura dake har wani tasowa kikayi da ya kiraki."
Ya zauna kusa da ita sosai a gefen gadon kafadarsa na gogar ta ta, wani iri taji tayi kokarin matsawa ya sake matso ta sosai.
"Ni ba haka bane." Tace tana tashi tsaye, saurin chapko hannun ta yayi ya maida ita ya maida ita wajen da ta tashi yana dora kafadarsa a saman ta ta
"Mesa kike gudu na, bakiyi missing d'ina bane?"
"Ya Farouk?" Ta kira sunan shi
"Ehen ina jinki."
"Dan Allah ka daina wa Ya Anas haka, kaga babu dadi, yayi min kokari sosai a lokacin da na fitar da tsammani da samun wani jin dadi ko cigaba a rayuwa, shine ya rike mu tamkar nasa, ya kula da dukkan al'amuran mu, ya tsaya tsayin daka wajen ganin na samu ilimi me amfani, wanda idan babu shi da tuni rayuwar mu ta lalace, watakila ma da tuni na zama mabaraciya ko na mutu saboda wahala."
Tashi yayi sosai ya kalle ta idon sa na kankancewa
"Kina nufin dai yanzu ya fini wajenki ko? Saboda ya kashe muku kudi ke da Iman, shikenan, Ina so ki tambaye shi nawa ya kashe akan ku tun daga ranar farko zuwa yanzu sai na biya shi, tun da abin ya zama gori..."
"Subhanallah, kar kayi misunderstanding d'ina, ba abinda nake nufi ba kenan."
"Me kike nufi? Shikenan dan yayi wahala daku sai ya bashi damar shiga hurumin da bana saba? Nayi magana kuma kin juya min magana ta, alamun ma ni yanzu bani da wani amfani wajenki."
"Ya Salam!" Tace tana kallon shi,
"Wannan ba Ya Farouk d'ina bane, Ya Farouk d'ina me saurin fahimtar rayuwa ne kuma me yiwa mutum uzuri ne ko da yayi ba dai-dai ba."
Kin tankawa yayi ya sake hade rai shi a dole an bata masa rai, ganin haka yasa tayi shiru itama saboda ta lura neman rigima kawai yake, ba kuma zata biye masa ba balle har ya samu galaba akanta.
Dogon zango suka dauka ba tare da kowa ya sake magana ba, sosai ranta ya ɓaci, dan bata ga abinda tayi masa da zai sashi reacting haka ba, ganin zaman ya ishe ta yasa ta mike don zuwa waje dan ba zata iya cigaba da zama dashi haka yana share ta ba
"Zan koma gida." Tace tana mik'ewa, da sauri ya kalle ta
"Iman din fa?" Yace cike da mamaki
Idon ta ne ya ciko da kwalla tayi saurin sa hannu ta goge
"Ba kana nan ba?" Ta amsa masa kai tsaye
"Akan nace masa dan iska ko?"
Yace yana kura mata ido, kin amsa masa tayi saboda yadda ranta ya ɓaci, ya gaza fuskantar ta s ranaram kishi ya rufe masa ido, gaba tayi kawai tana ji Iman din na kokarin tashi ta bude kofa tayi ficewar ta.
"Ya jikin nata?" Baba Altine tace
"Da sauki, ina ga idan drip din ya kare su sallame ta, muje gida."
"Kamar ya? Muje gida ko naje gida? Na zata zaki zauna a sallame tan ne ko?"
"A ah, zai iya kula da ita ai, muje kawai."
"Fada kukayi?" Baban tace
Gefen da Amal ke zaune Aminatu tayi saurin kallo ganin hankalin ta na wani wajen daban yasa tace
"Ya kasa fahimta ta."
"Shikenan sai kuma kiyi zuciya da yarki? Wannan ai shashanci ne."
"Toh ya zanyi? Tsawon lokaci ina zaman jiran dawowar sa, ya dawo kuma amma ba da halin da na sanshi ba."
"Aminatu ita fa rayuwa da kika gani ba zaki ce mutum ya zama yadda kike sanshi a koyaushe ba, mutane na iya chanjawa, Sai dai chanjawar su ba zai sa kema ki chanja ba."
Jikin ta ne yayi sanyi, ta zauna tana tunanin mafita, suna zaune likita yazo ya wuce su, ya shiga ciki, jim kadan ya fito yayi nasa wuri. Ba'a wani jima ba sai ga Farouk ya fito rike da Iman a kafadarsa ya wuce su, ido Aminatu ta zubawa bayan sa ganin be ko bi ta kansu ba, ji tayi kamar ta tashi tabi bayan sa sai dai bata da wannan karfin halin, tsam Amal ta tashi tabi bayan sa, Baba Altine ta yanka mata harara cikin bacin rai tace
"Me kikayi kenan?"
"Ya zanyi toh?"
"Muje." Tace tana mik'ewa
Fitowa sukayi reception babu alamar su, suna fitowa parking lot suna fita daga asibitin. Wani iri taji ta rasa dalilin da Ya Farouk zai mata haka. Gida suka wuce Baba Altine nata yi mata fada akan abinda tayi, ko gaba kar ta sake irin wannan wautar. Ita dai jin ta kawai take bata iya cewa komai ba.
****Kwata-kwata ta kasa sukuni, tana yi tana duba wayar ta ko zata ga ya kira ta amma shiru kake ji, gashi kwarai tana so taji lafiyar yar ta, wannan shi ake kira a dakeka a hanaka kuka, yayi mata laifi amma ya fita daukar zafi.
Ganin wankin hula na neman kaita dare yasa ta ajiye komai ta kirashi, lokacin ya gama shirya Iman cikin sabon kaya ya bata abinci da chocolate ta gama rigimar ya kaita wajen Ummin ta ya samu tayi shiru bayan ya bata wayar shi yayi mata downloading wani cartoon, shigowar kiran ya katse mata kallon ta, kuka ta saka masa hakan yasa shi saurin rejecting kiran.
Sororo tayi rike da wayar a hannu, mamaki ne ya cika ta , dan son sake tabbatar wa ta kuma kira a take akayi rejecting, Sosai zuciyar ta ta sosu, ta zame ta kwanta ranta na mugun suya.
Shigowar Dadah dakin uku tana son daukar Iman din Amma sam taki yarda, a shigowar ta na karshe ne take ce masa ina Aminatun bata bukatar yarta ne? Duba da rashin ta da tayi kwana biyu? Da yake har yanzu be gama sakin jiki da ita ba yasa yace mata yanzu zai zo ya kai mata ita.
****Ja'afar na ajiye wayar yayi saurin kiran Mummy dan yasan bata san da dawowar Farouk din ba, lokacin tana tsaka da aiki a system ɗin ta, da sauri ta ture komai ta shiga kiran layin Farouk din.
Kura wa kiran ido yayi, a hankali ya zare wayar daga hannun ta ganin har tayi bacci wajen kallon, katse wa kiran yayi ya cigaba da bin wayar da ido har sanda wani kiran ya sake shigowa.
"Farouk!"
"Na'am."
"Yanzu Farouk ka bar kasar nan tsawon lokaci sannan ka dawo duk ban sani ba? Ka kyauta min kenan? Kasan yadda naji dana samu labarin tafiyar ka? Amma shine har ka dawo baka neme Ni ba?"
Shiru yayi duk sai yaji babu dadi, kallon tasa yar yayi ya tuna yanzu shima fa uba ne, idan tasa yar tayi masa haka ya zaiji? Cikin kankan da murya yace
"I'm very sorry, kiyi min afuwa."
Share hawayen fuskar ta tayi cikin dakewa tace
"Ina son ganin ka yaushe zaka zo?"
"Gobe ko jibi in Sha Allah."
"Kazo gobe."
"In sha Allah."
Ajiye wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya, kura wa Iman ido yayi yana jin soyayyar ta na bin kowanne lungu da sako na jikin sa. Tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Aminatu yayi, sai yaji duk be ji dadi ba, atleast idan bazai bi ta a yadda ta ke tunani ba kada ya kuma bata mata rai.
****
Duk sunyi jigum babu wanda yake iya magana da dan uwan sa, gashi har an kwana babu alamun zai farka, dakin likitan ALHAJI Marwan ya shiga ya nemi a basu transfer,zai tsaya yi masa dogon bayani yace shi sam be yarda ba, dole ya amince ya sallame su suka dauke shi suka yi Abuja dashi ba tare da yasan me yake faruwa ba.
A chan gidan kuwa Hajiya Turai ta tada bori bayan ta samu labarin abinda ya faru, gaba daya masu aikin gidan sun taru a kanta tana ta kuka da kururuwa a kaita wajen jikanta, duk sunyi jigum jigum motar su ta shigo gidan, da sauri ta tashi daga zaman dirshan din da tayi ta nufi kan motar tana kuka.
Duk wanda ya ga Kamal a lokacin sai ya masa kuka, tuni Alhaji Marwan yayi nisa a shirye shiryen fitar dashi waje.
Cikin dare ya farka, duk suna kansa, da wani irin abu ya soma kafin ya fara magana da k'yar irin ta wanda ya galabaitu da wahala. Babu wanda yaji me yake cewa saboda yadda maganar tayi kasa, Ammi na kuka Hajiya Turai na yi, cikin yanayin kamar an fuzgo maganar ya furta
"Dad..dy.. A...mm..i.. itace."
"Karka takura ma kanka da magana, dan Allah."
Ammi tace tana kuka sosai, kukan shima yasa yana mika mata hannu, da sauri Daddy ya isa gareshi yana riko hannun sji
"Kamal, look at me, menene? Kayi shiru kaji?"
"Daddy... Ami...natu."
"A kira maka ita?" Yace yana shafa kansa, daga kansa yayi alamun eh
"Toh shikenan, kayi hakuri gobe zatazo kaji?"
Daga kansa yayi yana maida idon sa ya rufe.
"Kaga ni? Yarinyar nan me tayi masa? Yana wannan halin yana kiran sunan ta? Wannan wacce irin masifa ce? Wallahi bazan yarda ta lalata min rayuwar yaro ba."
"Ya kamata ki duba lafiyar shi kafin ki tsaya tunanin komai, ni yanzu ta lafiyar sa nake, ba ta komai ba."
Ran ammi ne ya ɓaci, ta kara jin haushi ta tsanar yarinyar da bata taba gani ba.
Rashin Sani!!!! Yafi dare duhu
Rano 😍: *DG*
*38*
©Hafsat Rano
★★★
*K*amal be sake farkawa ba saboda yadda karfin allurar yake, da safe ya farka amma sai dai har lokacin ba a hayyacin sa yake ba, dole aka sake masa wata allurar saboda ciwukan da ke jikin sa ma.
Abincin kirki Ammi ta kasa ci saboda yadda abin ya dake ta, Hajiya Turai kuwa sai da aka bata magungunan ta na hawan jini sannan aka samu ta dawo daidai, dukkan su sun kasa matsawa daga in da yake, hakan kadai ya isa ka gane irin gata da soyayyar da suke masa.
Babban likitan da aka hada su dashi dake nan Abuja Dr Ahmad (Ruhi Daya) ne ya iso cikin shigar sa data dace da tsari da zubin hallitar sa, tun fari shi Daddy yaso ayi wa magana ganin Alhaji Marwan din ya kafe da son dole sai ya fidda shi waje yasa ya kyale, sai dai tsaikon da za'a samu yanzu kafin a fitan yasa dole ya amince aka kira shi.
Har wajen motar sa Alhaji MD ya k'arasa ya yi masa iso zuwa katafaren part d'insa inda aka ajiya Kamal din, har suka karasa suna tattauna wa akan abinda ya samu Kamal din da kuma abubuwan da Daddyn yake so ya taimaka masa dashi, a nutse ya amsa da zai yi iya yinshi sannan suka karasa ciki.
Cikin kwarewa da sanin makamar aiki na cikakken consultant a bangaren ƙwaƙwalwa ya shiga bincike da son gano ko akwai wani damage a brain d'insa, a haka dai physically babu wani abu da zata nuna ko ya samu wata matsala ,sai dai yana bukatar bincika shi sosai, kai tsaye babban asibitn sa dake Maitama ya umarci a kaishi, anan yayi undergoing several tests kuma Alhamdulillah babu wata matsala internally sai wadda ta bayyana kowa ke ganin ta.
Cire glass din idonsa yayi bayan yasa tsaftacecen handy ya share zufar dake saman goshin sa ya kalli Alhaji MD yace
"Ina ganin zaman sa anan ɗin zai fi samun kulawa fiye da gida, sannan ka bamu dama muyi aiki sosai in Sha Allah zaka ji dadin aikin mu fiye dana kasashen wajen, please let give it a try, for now a ajiye fita dashi."
"Shikenan, na yarda da ingancin aikin ku da asibitin ku, please kayi iya kokarin ka wajen ganin yarona ya samu lafiya, shi kadai nake dashi i can't bear...."
Saurin katse shi yayi
"Babu abinda zai faru dashi in Sha Allah, ya riga yayi passing danger stage din so mu cigaba da addu'a."
"In Sha Allah. Mun gode Dr."
Fita yayi ya samu su Ammi ya sanar dasu abinda ya faru, cikin kankanin lokaci asibitin ya soma cika da yan uwan Ammi da abokan harkar Alhaji Marwan na kusa dana nesa, tuni labari ya game ko ina sai dai ba'a bar kowa ya ganshi ba sai ta window saboda yadda yake bukatar hutu.
****
Hasken ranar daya risketa har inda take kwance yasa ta gane gari ya waye sosai, da sauri ta tashi tana laluben wayar ta da glass din ta da sukayi nasu waje, sakawa tayi tana duba wayar cikin tsananin mamaki take kallon lokacin , karfe bakwai har da mintuna, a zabure ta mike tayi saurin fadawa bandaki ta dauro alwala tazo ta gabatar da sallah tana rokon Allah gafara akan makarar da tayi.
Bayan ya idar ta zauna a wajen tana tunanin abinda Farouk yayi mata na regecting kiran ta da ya dinga yi, a takaice dai yayi fushi, fushin da bashi da dalili ko tushe.
Tashi tayi ba tare da ta cire hijabin jikinta ba ta koma daki ta tashi Baba Altine, zaman dirshan tayi a kasan dakin bayan Baban ta fita ta shiga azkar a nutse, tana cikin yi ne Kamal ya fado mata, jiya ta kirashi babu amsa duk sai taji babu dadi hankalin ta kuma ya gaza kwanciya, be taba tafiya hakan ba ba tare da sallama ba, sannan yanayin daya fita a ranar ya tsaya mata a rai sai dai ta kasa gane dalili ko hujjar da ya sashi aikata hakan.
Gefen gado ta koma ta haye ta kudundune a cikin Hijabin ta shiga kiran layin nasa tana fatan ya daga duk da dai tasan safiya ce. Babu amsa dole ta hakura ta ajiye wayar ta rufe idon ta.
Bata tashi ba sai wajen goma, lokacin Baba Altine ta gama gyaran gidan har ta siyo kokon ta da ya zama mata kamar al'adah tasha abinda. Wanka ta fara yi ta shirya a cikin wata doguwar rigar atamfa koriya wadda Anas yayi mata da sallah sannan ta wuce kitchen ta hado tea da biscuit ta zauna tana ci.
"Kwana biyu Kamalu shiru nace, lafiya kuwa?"
"Wallahi nima abinda ke raina kenan, shirin yayi yawa gashi na kikkirashi baya dagawa."
"Toh, Allah sa lafiya, ki kara gwadawa Allah sa ba kuma sace wayar akayi ba."
"Toh Amin dai, bari na sake kira."
Ta danna kiran tana ajiye cup din hannun ta.
Lokacin wayar na hannun Ammi suna zaune da wasu mata kiran ya shigo, sunan data gani yasa ta jan tsaki ta mike ta dan matsa gefe kafin ta daga
"Ya daga." Tace wa Baba Altine
"Kamal. Ina ka shige kwana nawa ina ta kiran ka, wallahi baka ji yadda muka damu ba."
"Toh munafuka, kin tura min yaro in da zai halaka ba ki masan matsalar da kika saka shi ba ko? Na tabbata abinda ya kaishi Katsina ya gamu da wannan mugun abun ya na da alaƙa dake, tun da kika shigo rayuwar sa shikenan ya chanja, komai ke komai ke, sai ki zuba ruwa kisha tun da kin kassara masa rayuwa." Ta karashe tana share kwallar data zubo mata
"Dan Allah kiyi hakuri, me ya samu Kamal din? Wallahi bani da masaniya."
"Karki sake kiran sa, baya bukatar ki mu iyayen shi kadai mun ishe shi,ki fita daga rayuwar sa ba zan juri rasa shi ba zan kuma iya yin komai akai."
Tana kaiwa ta katse kiran tana komawa wajen zaman ta kamar babu abinda ya faru.
Kuka Aminatu tasa tana fada wa Baba Altine abinda ya faru, duk ta rude idan wani abu ya faru da Kamal ba zata taba yafe wa kanta ba, me ya kaishi Katsina bayan tasan bashi da wani abu da zai kaishi chan din tunda ya taba fada mata tun bayan barowar su Daddy basu sake komawa da sunan zama ba, dama aiki ne ya kai su garin, yan uwan su da sukayi saura basu da yawa a garin ba kuma ma zuwa wajen su suke ba.
Rasa inda zata sa kanta tayi, zaman ma sam ya gagare sai zagaye take,ita kenan duk wanda zai rabe ta sai ya shiga matsala, kamal ɗin da take ganin shi a matsayin dan uwa na jikinta shima ana neman illata masa rayuwa. Dole ta kyale shi kamar yadda mahaifiyar sa ta buƙata amma kuma tana son sanin halin da yake ciki gashi bata san wa zata tuntuba da maganar ba.
***Wanka yayi mata ya chanja mata sannan ya riko hannun ta suka fito falon, Dadah na zaune da anty Safiyya suna hira akan tafiyar da Anty Safiyyan zatayi Kaduna, miƙa hannu Dadah tayi da murnar