Showing 96001 words to 99000 words out of 112633 words

Chapter 33 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7415

rayuwar da tayi,ba karamin girgiza Ammin tayi da labarin ba, tayi kuka sosai sannan kuma ta gode Allah da ya sa yarta bata fada mummunan hannu ba har ta samu tayi karatu irin na yanci. Zata so taga Anas, ya tallafi rayuwar yarta, yayi mata gata. A halin yanzu ita zata tsayawa yarta, ta bata kulawar da zata manta radadin abinda ta kunsa.

****
Duk da bata da tabbacin zai zo kamar yadda yayi mata, sai dai ta gaza aiwatar da dukkan ayyukan ta na ranar tana dakon zuwan sa, ganin da gaske babu alamar shi yasa ta dauki wayar ta kirashi, hakuri ya bata yayi mata alkawarin zuwa gobe da ikon Allah.
   Tashi tayi zata wuce zuwa daki kiran Ja'afar ya shigo, ta so sha'afa da dawowar tasa, sai data ga kiran sannan ta daga a gaggauce

"Son..."

"Mummy yanzu zamu taso, zuwa dare in Sha Allah xamu iso."

"Ok dear, Allah ya kawo ku lafiya, karka manta da kun sauka ka sanar dani, Idris zai jira ka ku taho direct nan Farouk ma zaizo."

"Shikenan, sai mun zo."

"Owk bye."

Ta ajiye wayar tana dan bubbuga bayan ta da ke dan mata ciwo. Tun bayan gano in da yar uwata take ta hau shirye shiryen zuwa takanas wajen ta, bata sanar da kowa ba har dan gaban goshin nata, so take ta basu mamaki kawai, shiyasa ta gama shirya komai take so su je su hudu, ita, Ja'afar, Farouk da babbar yayarsu Anty Lami.
    
    

****Kwanan tsananin wuya Adam yayi, basu raga masa ba ko kaɗan dan Daddy yace kar su saurara masa bayan abinda Alhaji Marwan ɗin ya sanar dashi ya kara tunzura da lamarin Adam ɗin, tabbas babu digon tausayi ko rahma a zuciyar sa, dan haka suma ba zasu raga masa ba.
    A gajiye Daddyn ya tashi kamar wanda aka yi wa duka, kwana yayi yana tunane tunanen yadda abubuwan suka dinga faruwa a karkashin ikon shi, rainin hankalin da adam yayin masa yafi komai taba shi, sai kuma rashin bincike kwakkwara da beyi ba akan case ɗin Mummy, a yanzu babu wadda yake so kusa dashi sama da ita, sai dai yasan taurin kan ta da kafiyar ta ba lallai ta sauko da wuri ba, idan ma ta sakko ɗin, dole ana bukatar ta a yau, ta zama tana wajen komai zai bayyana, amma waye zai kira ta ta yarda tazo? Babu shi. Shiru yayi cikin tunani kafin ya mike da sauri, Safiyya ce kadai zata sata zuwan dole. A gaggauce ya shirya ya fito, Mama na ganin shi ta mike da sauri

"Alhaji, yau lafiya ka shige ciki tun wuri ka rufe kanka, duk hankali na ya tashi ban iya baccin kirki ba."

"Baki da hurumin sanin abinda nake."

Yace yana rabe wa ta gefen ta, baki ta rike cikin tsananin mamaki take kallon sa, sai daya kai kofa sannan yace

"Akwai meeting na gaggawa karfe sha biyu, idan lokacin ya cika ki same mu a gidan MD."

Yasa kai ya karasa fita yana jin kamar ya dawo da baya ya faffasa mata baki da hanci yadda yake jin haushin ta.
   A harabar gidan ya tarar da su a tsaye suna jiran sa, duk suka sara masa da sauri, dakin ya nufa  suna take masa baya daya daga ciki yayi saurin bude masa kofar, kansa ya tura ciki yana kare ma ko ina kallo, yana kwance d'ai-d'ai yana fitar da numfashin wahala, fuskar sa ta haye tayi sumtum kamar bashi ba, babu mask din da yake sawa sai ainihin fuskar sa. Dagowa yayi ya zuba wa Daddyn ido har ya ƙaraso gaban sa, babu digo na sassauci a fuskar tasa

"Iya kar abinda zaka yi min kenan?" Adam ɗin yace yana murmushin karfin hali,

"Damage din da nayi muku kadai aka barku dashi nayi winning, na lalata maka dukiya na kuma cire hakki na daga ciki, sannan na raba ka da matar ka da kafi so, na hada ka danka tillo a duniya na kuma sauya masa tunani akan ka, yana maka kallon mara tausayi, na raba shi da matar sa, abubuwan da na aikata maka suna da yawa, kana tunanin Wannan hukuncin kadai ya ishe ka ramawa?"

Wuya Daddyn ya riko masa ransa a matukar bace

"Menene haɗin ka da Hajara!""

"Matar mu ce da mukayi tarayya akan ta!"

Da wani irin karfi Daddyn yasa hannu ya hankad'a shi, ya bugu da bango ya bishi ya take yana nuna masa hannu

"Sai na kashe ka!"

"Kuna ina!" Ya fada cikin k'araji

Da sauri suka shigo

"Karku raga masa ko kadan, kuyi masa dukan da zai kasa magana, but i want him alive har sai yayi confessing dukkan laifukan sa."

"Yes sir." Suka amsa a tare suna yin kan sa.

****
A yadda ya shigo kadai yasa suka sha jinin jikin su, zama yayi yana dafe kansa da hannu bibbiyu, matsowa Dadah tayi gaban sa ta riko hannun sa

"Lafiya?"

Idon sa da suka soma kadawa ya dago mata cikin dashewar murya yace

"Adam yana cikin gidan nan, za'a hadu da kowa karfe sha biyu na rana, ina rokon ki da ki sanar damu abinda kika sani idan an zauna."

Da baya da baya ta koma ta zauna ba tare da tace komai ba. Girgiza kai kawai yayi ya maida duban sa wajen Anty Safiyya yace

"Safiyya."

"Na'am yaya."

"Dan Aallah ki kira Abidah kiyi convincing din ta tazo yau, idan ni na kira ta ba lallai tazo ba."

"Toh Yaya."

Ta tashi dauko wayar, duk da tana tsoron yadda zasu kwashe idan ta samu labarin tana garin amma bata nemo ta ba, Amma dole ta kira dan ba zata iya ce masa a ah ba.
    Kira tayi ta makala wayar a kunnen ta cike da fargaba

"Rage min volume din chan Ja'afar."

Tace kafin ta daga tana gyara zaman ta,

"Hello Assalamu alaikum." Ta ce kai tsaye,hawaye ne ya taru a idon Anty Safiyya ta kasa magana, sai data sake maimaita sallamar kafin tayi karfin halin furta

"Anty Abidah."

A zabure ta mike shima Ja'afar sai ya mike

"Safiyya, Safiyya kece?"

"Nice." Sai ta sa kuka

"Kina ina? Yaushe kika zo Nigeria, fada min yanzu zan taho innalillah."

"Ina Abuja Anty gidan su Farouk, Please kizo Anty yanzu."

"Wait what! Kina nufin chan Kika tafi? Dadi miji Safiyya,? Suwa ya kamata ki fara nema, tun yaushe ma kike garin kenan? Don't tell me kin kwana biyu sai yanzu kike kirana."

"Kiyi hakuri duk tambayoyin nan idan kika zo zan amsa miki, nidai dan Allah kizo."

"Shikenan, zanzo na dauke ki right away, ba xaki sake zama achan ba kuma, gani nan zamu kamo hanya da Ja'afar yanzu."

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace

"Allah ya kawo ku lafiya."

"Amin."

Juyawa tayi wajen Ja'afar ba tare da ta zauna ba tace

"Tashi Ja'afar, a dauko mota mu wuce Abuja, dole ta baro gidan nan yau yau."

"Mummy wace haka?" Ya tambaya

"Zaka gani idan munje."

"Owk."

****
Maganganun Iman ne ya tashi Aminatu, tana buɗe idon ta abinda ya faru ya dawo mata, kallon dakin ta hau yi zuwa lokacin ta tuna a inda take, kan gadon mahaifiyar ta, sosai taji dadin baccin fiye da wani bacci da ta taɓa yi a rayuwar ta, glasses din ta ta dauka ta saka tana saukowa daga gadon.
  Budo kofar akayi, Ammi ce da Daddy cikin shigar alfarma, kowannen su bakin sa ya gaza rufuwa suka ƙaraso tsakiyar dakin suna duban ta, zamewa tayi da sauri zata sauka Ammi tayi gaggawar riko ta, a kunya ce tace

"Ina kwana Daddy?"

"Lafiya lou yar albarka, wannan amaryar tawa sai data tashe ki kenan."

Dariya suka sa gaba daya, sannan ta gaida Ammi ma. Toilet ta shiga da yake tana fashin sallah, tayi wanka ta fito daure da sabon towel, a gefen gado taga wata haddiyar riga me masifar kyau, hade da sababbin underwears, murmushi tayi ta hau shirya wa cike da dauki.
  Ba karamin kyau kayan sukayi mata ba, ta jima gaban mudubi tana kallon kanta.
   Flat shoe ta zura sabo me kamar slipers ta yane kanta da dan siririn mayafi.
  Idon ta ne ya sarke da nasa sanda ta fito, yana hakimce akan kujera Iman na saman cinyar sa tana masa surutu, zuba mata ido yayi kamar zai lashe ta, tayi k'asa da kanta ta ƙaraso.

"Kinyi kyau sosai."

Yace murya kasa, ta jishi sarai amma sai ta basar ta nemi waje daya ta zauna a hankali tace

"Ina kwana?"

"Lafiya lou princess, ko nace queen, dan yanzu kin zama kamar kwai nasan ni dan kallo zan zama."

Murmushi tayi me aji, tabbas tana jin ta a yanzu ta kai ta isa gogawa da kowa, tunanin Shagari ya fado mata, lokacin komawar ta yayi.
   
"Ya kika ji? Kamar a film ko novel ko?"

"Ina jin kamar I'm the most happiest being on Earth, farin ciki na bazai misaltu ba ya Farouk."

"Alhamdulillah ya Allah! Allah shine kadai abin godiya."

"Haka ne."

"Akwai meeting by 12, komai zai bayyana."

"Allah ya kaimu."

Tashi yayi yana makale hannun sa a baya, ya tako har inda take, sunkuyowa yayi daidai kunnen ta a hankali yace

"Get ready, patience dina ya soma karewa, i need u by my side."

Turo baki tayi, yasa hannu a saman bakin.

"A adana su against next time, yanzu ina gidan surukai ne I have to behave."

"Ya Farouk!!!" Tace tana rufe ido

"Me nayi?

"Ba komai." Tace turo baki.

"Yarinya taji tsoro."

Yace yana murmushi kafin ya juya ya bar falon. Lumshe idon ta tayi ta bude su, kiran Anas ya koma shigowa a karo na uku, jingina tayi sosai da kujerar kafin ta daga.

"Ni kike wulakantawa ?" Yace Muryar shi a shake

"Ba haka bne ya Anas, bana kusa da wayar ne."

"Shikenan kince kina Abuja ko? Ki tura min address din zanzo."

"Naa...am?"

"Sai kin turo." Ya kashe.

"Ya akayi?" Ammi data fito daga wajen Kamal ta tambaye ta

"Wai Ya Anas ne yace na tura mishi address,bansan ya zan ba."

"Tura masa mana dama ina son haduwa dashi, idan har aka tabbatar da babu aure tsakanin ki da Farouk toh fa baki da miji sai shi, dan ni yaron yayi min."

Murmushi tayi, ta rubuta address din Ammin na fada mata, bata son jayayya da ita, amma ita ta riga tasan hakan ba mai yiwu wa bace, Farouk ba zai taba kyale ta ba, gwara ma Ya Anas ɗin yazo ayi ta ta kare.a: *DG*

                       *41*

©Hafsat Rano

*RANAR WANKA....!*
    *Ba'a boyen cibi*

★★★★
Dukka ahalin biyu sun hallara a babban Falon gidan Alhaji Marwan, kowa ka kalli fuskar shi yana cikin zulumin abinda ya tattara su haka waje daya, Mama tafi kowa shiga tashin hankali ko kwakkwaran motsi ta kasa yi sai rarraba ido take kamar tsohuwar munafuka, a gefen kafarta Amal ta zauna, Anty Safiyya da Mummy a kujera two seater Ja'afar da Farouk a kasan su, sai Alhaji Marwan da Uncle Aliiyu, suma a waje daya, Dadah da Hajiya Turai sai Ammi a kujerar ta ita kadai Aminatu zaune daf da ita, Kamal na zaune shima a gefen Ammin yaji karfin jikin sa.
   Shigowar Daddy yasa kowa ya sake nutsuwa, a tsakiyar falon suka wurgar dashi kafin su juya su fice, dafe kirji Mama tayi ganin wanda bata taɓa tunani ba, kuka Amal tasa ta yunkura zata wajen sa Daddyn ya dakatar da ita

"Kar wanda ya motsa daga in da yake."

Komawa tayi ta zauna ta cigaba da kukan ta kasa kasa. Tasowa Dadah tayi, ta tsaya a kansa, yana dagowa ta taska masa mari, ta kuma taska masa kafin tasa kuka

"Tir da kai Adam!"

Komar da ita wajen zaman ta Daddy yayi yana duban kowa na falon

"Alhamdulillah, kamar yadda kuka sani abubuwa da yawa sun faru ba tare da sanin takamaimai abinda yake kawo faruwar hakan ba, toh alhamdulillah, a yau komai zai bayyana kansa, duk wasu kulle kulle zasu warware."

"Adam...Muna so kayi mana bayanin dalilin ka na raba Aminatu da iyayen ta ."

"Cin amana ta suka yi."

"Su waye?"

"Mutanen da ke kokarin binne boyayyen sirrin su, su hau kai su zauna suna rayuwa ingantacciya ba tare da tuna komai ba, Marwan da Fatima kun yaudare ni, yaudara mafi muni...!"

"Babu wanda ya tausaya min balle ya tsaya ya tambayi ba'a sin gaskiyar komai, tabbas nayi kuskuren aminta dakai, na daukake ka fiye da kowa...."

"Soyayya mukayi me tsafta, babu wani abu me kama da rashin kirki a ciki, zuwa lokacin da muka riga muka aminta da juna, kai na fara tuntuba da maganar."

Ya nuna Alhaji Marwan

"Kai na shawarta har ma na baka  wuka da nama wajen neman ta, haɗe da address din gidan su, a matsayin ka na wanda na dauka babban wa, kuma uba! Me kayi? Me kayi min...?"

"Kaje ka bata ni wajen ta, sannan ka nuna musu tarin dukiya, ka aure ta ka raba ni da ita, shin akwai adalci anan?... Tun daga lokacin na fara neman hanyar da zan lalata ma komai daka mallaka, ban samu dama ba."

"Lokacin dana fuskanci Fatima na dauke da juna biyu nayi bakin ciki sosai, na kuma kuduri aniyar daukar fansa ta ko zan mutu a garin haka, hakan da nayi kadai nasan na gama da ku, rayuwar kunci da talauci da kaskanci yar ku tayi, sannan na sa aka rufe mahaifar ta saboda bana bukatar ku cigaba da haihuwa."

"Ni na chanja ya'yan na dauki taku na bada ita a inda nasan ko kare kuke kiwo ba zai yi irin rayuwar nan ba."

"Yanzu wannan dalilin ya isa ka lalata min rayuwar ya?"

"Kai kasan zafin so? Kasan yadda yaudara take da ciwo? Baka sani ba ko?"

Murmushin yayi

"Ban taba dana sanin abinda na aikata muku ba, kun chanchanci fiye da hakan ma."

Kuka ya hana Ammi magana, sam bata taba tunanin hakan zai zama babbar matsala a rayuwar ta ba, yanzu dama rashin haihuwar ta Adam ne? Bayan raba ta da yarta da yayi har da karin wannan, sama da k'asa kawai numfashin ta keyi, duk hankalin kowa ya koma kanta, Kamal duk ya rikice duk dauriyar sa sai yaji yana neman kasa wa.

"Menene alakar auren Aminatu da Farouk da kai?"

"Shiri na ne, ni na kulla komai, ban dauka zai sota ba, sai dana fuskanci yana son ta, sai nayi kokarin dora Amal akan turbar soyayyar sa, mu muka aika mata da takardar saki, mukayi komai cikin tsari, saboda ina so tayi rayuwa cikin kunci har sanda zata mutu!"

Tashi Farouk yayi, Daddy ya sa hannu zai dakatar dashi, sam yaki ma kallon Daddyn har sanda ya damke shi.

"Kai ne kayi min wasa da rayuwa kamar ka sami kwallo, ka bata min lokaci da komai, akan wani banzan dalilin ka mara tushe."

"Sake shi Farouk!"

Daddy ya daka masa tsawa. Sakin sa yayi ya koma ya zauna

"Menene alakar ka da Hajara."

"Ina tunanin na amsa maka wannan tambayar dazu, ko da yake bari na maimaita."

"Zafin ranka yasa nayi amfani dakai wajen kawo maka baragurbi na kuma tabbatar da ka yarda dani, Hajara yarinya tace, ni nake sata komai, kuma da ita muke komai."

"Ita ta taimaka min wajen ganin komai yazo min da sauki, ita ta kai takardar sakin Aminatu ita da Aminiyar ta sai dai bata bari aminatun ta ganta ba saboda bacin rana, haka ma dakikiyar matar data rike Aminatun."

"A takaice dai duk wani abu kaine, kai ne ka raba Aliyu da kasar sa, ka raba ni da Abidah, kaine ka shirya komai."

"Aliyu yayi kokarin shiga abinda babu ruwan sa, ganin zai kawo min cikas yasa na batar dashi ta hanyar da zai dade kafin ya waiwayo gida."

"Ban aikata wa Anty Abidah abinda kake zargin mu ba, nayi amfani da hakan ne wajen saka maka zargin ta don nasan a irin zafin kanka ba zaka taba zama da ita ba. Duk wanda yasan sirri na nayi kokarin ganin na nisanta shi da ku, Anty Abidah ta shiga hurumin da ba nata ba, dole aiki ya biyo ta kanta."

"Wanne irin sirri ne haka?"

Dadah ce ta katse shi

"Zan sanar daku, ina rokon gafara tun kafin kusan komai, zuciya ta cike take da nadama da dana sani, duk da bawa baya gujewa ƙaddarar sa, na dau hakan kuma na rungume ta hannu biyu ina kuma fatan mutane da yawa su dau darasi a cikin labarin da xan bayar amma ina so Amal da Kamal su dan bamu waje,da, idan yaso sai ku duba abinda ya dace."

"Shikenan babu damuwa."

Tashi sukayi suka shiga ciki sannan ta fara

***
"Mu hudu ne a wajen mahaifan mu, mata biyu maza biyu, bayan aure na Allah yayi wa mahaifan mu rasuwa, tun daga lokacin rikon kanwata Habiba ya dawo hannu na da mahaifin ku muka cigaba da rayuwa tare. Bayan wani lokacin kanin mahaifin ku Adamu shima ya dawo gidan da zama, hakan ya bsu damar sabo da juna da kanwata har na fuskanci akwai soyayya tsakanin su.
  A kwana a tashi har sanda zance ya fasu, mukayi murna sosai nida mahaifin ku, sannan aka hau maganar aure gadan-gadan.
   Duk shirye shiryen da ya kamata iyaye suyi wa ya'yan su nida mahaifin ku mun yi, har zuwa lokacin da aka saka biki yazo, daga cikin gidan aka cire musu waje aka gyara musu suka tare abin su.
     Mahaifin ku ya kasance me tafiye-tafiye, hakan ba karamin takura min yake ba, tun da a lokacin ina kan ganiyar kuruciya ta, haihuwa ta biyu kawai, sosai nake cutuwa da tafiyar sa, sai dai kunya da nauyi ya hanani sanar dashi, haka muka cigaba da zama ba tare da na sanar da kowa ba.
     Watarana da daddare bayan kowa ya kwanta, na zabga tagumi ina tunanin abinda ya damen, Habiba ta shigo dauke da leda, kamar ko yaushe idan Adamu ya siyo mata wani abu nima sai sun miko min, hakan yasa na gane ko ledar mecece,a gefe na ajiye dan sam bani da ra'ayin ci a halin da nake. Zama ta danyi muka taba hira kadan kafin tayi min sallama, har taje kofa sai na tsaida ta nace ta turo min Adamu idan ta koma zan aika shi ya siyo min maganin ssuro, da toh ta amsa ta fita, bata jima ba sai gashi ya shigo rik'e da ledar maganin sauron, karba nayi na ajiye sannan na bukaci ya zauna muyi hira, dariya yayi ya zauna muna tattaunawa har zuwa karfe goma ma dare, kamar yadda addini yace, idan mace da namiji suka kebe toh lallai na ukun su shaidan ne, hakan ce ta faru dani da kanin mahaifin ku, bamu farga ba , har sai da mai afkuwa ta afku, shigowar Habiba da ihun da tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login