Showing 90001 words to 93000 words out of 112633 words

Chapter 31 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7422

ta, make kafada Iman din tayi tana buya a jikin baban ta.

"Zo kinji." Tace tana sake gwadawa

"Barka da safiya Anty."

"Barka Farouk, ashe anan ta kwana shine baka miko mana ita ba, ko da yake ba yarda zatayi ba."

Murmushi yayi

"Ni dinma da kyar, zuwa zan na kaita na dawo sai mu wuce, Mummy na son gani na."

"Sannu da gida Dadah."

"Har yanzu fushin ne Baba na? Baka yarda dani ba ko?"

Shiru yayi yana gyara wa iman zama a jikin sa

"Komai yazo karshe in Sha Allah, dani zaku tafi ina so na sanar da kowa abinda baku sani ba, dama dazu baban naku ya kira akan Kamal ya gamu da hatsari yana asibiti ma toh kaga zuwa ya zama dole."

"Subhanallah, accident yayi? Banji ba wallahi."

"Wallahi wai mota ce ta buge shi a Katsina yana tafiya a kafa."

"Ikon Allah, garin yaya? Allah ya bashi lafiya bari na maida ta sai na dawo."

Yace yana tashi, da sauri ta mike tana sake riƙe shi.

"Ja'ira kamar za'a kama ta."

Sukayi dariya gaba daya.

***Da gudu ta bude motar ta shige gidan tana kwala kiran Ummi, da sauri ta goge kukan da take ta fito ran ta fari kal ta rungume yar ta ta cikin wani irin yanayi

"Ummi nah."

"Umm."

"Ina ta neman ki, har kuka nayi."

"Toh gani ai, no more kuka ko?"

Tace tana shafa kanta cikin tsantsar kauna. Hannu ya harde yana kallon su, ji yake kamar ya je garesu ya haɗa su ya rungume su, dagowa tayi ya kanne mata ido daya yana murmushi. Sai ta turo baki tana tashi daga durkusan da tayi.

"Muje ciki." Tace tana rike hannun Iman din. Shigewa sukayi suka bar shi a tsaye, ƙasaitaccen murmushi yayi ya bi bayan su.
Kai tsaye daki suka shiga ta kwantar da ita saman gadon tana zame mata riga, ita kuma tana mata surutai. Budo kofar yayi ya shigo ta dago tayi masa kallo ɗaya ta dauke kanta, ya lura da yadda take share shi duk haushin jiya ne, matsowa yayi har cikin tsakiyar dakin yana karewa ko ina kallo kafin ya sauke idon sa akan kayan ta na lawyers dake ajiye a gefe guda, takawa yayi har wajen ya dauka yana jin sabon nishadi na ziyartar sa.

"Barrister AFS ( Aminatu Farouk Shagari)." Ya furta cikin wani irin shauk'i. Bata kula shi ba ta sauya wa Iman kaya zuwa marasa nauyi ta rike hannun ta suka bar dakin, zaman sa yayi yana sake duba kayan karatun ta yana jin dadi mara misaltuwa.
Wajen Baba Altine ta kaita bayan taje ta rufe gidan da sakata sannan ta komo dakin da niyyar daukar wayar ta.
Ta gaban sa ta wuce ta dauki wayar zata bar dakin yasa mata kafa kadan tayi lu zata fadi yasa hannu ya taro ta, ido ta zaro a tsorace tana kallon sa numfashin sa na yawo a saman fuskar ta. Kici kicin kwacewa ta hau yi ya rik'e ta gam yana sake saka idon sa sosai a cikin nasa domin ya gane irin tasirin da hakan ke dashi..

"Ka kyale ni." Tace tana sake yunkura wa tana kokarin dole sai ta kwace.

"Wai karfi kika fini? Karki manta da soja kike magana, just keep calm babu abinda zan miki."

Juyar da kanta tayi gefe ya sa hannu ya juyo da fuskar yana cije baki kadan kadan

"Fushin ne?"

Sshiru tayi masa

"I'm very sorry, bansan me ya hau kaina bane, bana iya controlling kaina duk sanda na ganshi kusa dake. Nasan yayi min halaccin kula min daku kuma in Sha Allah zanyi kokarin controlling kaina kinji?"

Bata tanka ba.

"Say something."

"Ka daga ni be dace ba." Tace tana hadiye yawu da kyar, murmushi yayi yana sake dora mata nauyin sa sosai

"Babu rashin dacewa dan miji ya kebe da matar sa, zan tabbatar miki da bani da hannu akan wannan takardar bogin da aka kawo miki, ban saki matata ba saboda haka babu wanda ya isa ya hanani kebewa da ita, kinsan yadda nayi kewar ki kuwa?"

"It's still doesn't change anything, please ka kyale ni."

Kura mata ido yayi cikin kankan da murya, ya sa hannu a saman fuskar ta yana bin ko ina kafin yace

"Ba zan taba iya kyale ki ba, ko da ace saki nayi miki ai na uku bane ko? Balle wallahi ban sake ki ba, kuma zan tabbatar miki da haka."

Shiru tayi cikin rashin sanin me zata yi, bata so ta yarda dashi ya zurma ta ta riga tasan hukuncin hakan, motsawa tayi da dan karfi bakin ta ya hadu waje guda nasa, da sauri irin na wanda yake a matuƙar buƙace ya shiga kokarin ganin ya fanshe abinda yake ji game da ita.
Sai daya dau lokaci me tsawo yana aika mata da sakon da yake isa kowanne lungu da sako na zuciya da gangar jikin ta. Bata iya hana shi ba sai ma sakin jikin ta da tayi sosai tana karbar sakon nasa.

"Ummi." Muryar Iman ta dawo dasu daga dogon zangon da suka tafi, da sauri ta ture shi tana sakin kuka, kallon ta yayi ya zura mata ido yana jin ransa fes, kukan me kuma zatayi bayan da gaske tayi enjoying abinda ya faru.

"Ki share hawayen ki kafin ta shigo ta ganki kina kuka, ta zarge ni."

Harara ta balla masa tana goge fuskar ta daidai lokacin Iman ta shigo.

Mik'ewa yayi yana zura hannun sa cikin dogon wandon sa,

"Zanyi tafiya zuwa Abuja, zan dawo gobe ko jibi, daga nan zanzo da kowanne hukunci dake tattare da auren mu."

"Ya jikin Kamal?" Tace tana kallon sa

"Alhamdulillah duk da bansan ya ake ciki ba..." Wayar sa ce tayi kara ya zaro ta yana dubawa

"Barka da warhaka Daddy."

"Barka dai, ya gida?"

"Lafiya lou, ashe kamal be ji dadi ba, Allah ya kara sauki yanzu zamu tawo in Sha Allah."

"Alhamdulillah WallAhi, tsautsayi ya hadu dashi, gashi ya dage da son ganin Aminatu, idan babu damuwa kazo da ita dan Allah, bamu san me yake son fad'a mata ba."

"Babu damuwa, zamu zo tare in Sha Allah."

Ajiye wayar yayi

"Ki shirya baban Kamal ne ya roki alfarmar muzo tare wai Kamal din nason ganin ki."

Dan jim tayi tana tuno warning ɗin maman shi, sai kuma ta tuna tana bukatar ganin shi sosai, gida mishi kai tayi alamar toh



***Kuka ta kwana tana risga cikeda nadamar abinda ta aikata, ganin danta yasa komai ya dawo mata sabo, bata kyauta wa Aminatu ba, bata kyauta ba ta zama daga cikin mutane masu son kansu, da tayi hakuri da duk yanzu babu abinda ya faru, tsantsar kiyayyar data gani a idon sa kadai ya ishe ta gane a wanne bigire a ajiye ta azuciyar sa.
   Dauki da ledar magani Nura ya shigo ya zauna gefen tabarmar dake ajiye a wajen yana duban ta

"Kiyi hakuri Inna, ina kyautata zaton zai sake dawowa."

"Tunanin da kake kenan? Ka kuwa duba banbance banbancen dake tsakanin mu? Kalle mu cikin tsantsar talauci da kauyanci, ka tuna yadda jikin sa yake da ke fitar da tsantsar hutu da jin dadi, me zaiyi dani? Bayan ban zame mishi uwa ta gari ba."

"Duk wannan daban, kasancewar ki mahaifiyar sa ya kore komai."

"Nura kenan."

"Dan Allah Inno mu bar maganar nan haka, karbi ga magungunan nan kisha kin daiji shafi'u me chemis yace jinin ki ya hau sosai, ki sha sai ki kwanta ki huta dan Allah."

Bata sake magana ba ta karbi maganin ta balla tasha ta koma ta kwanta kanta kamar zai rabe biyu saboda azabar ciwon da yake mata.


***Tun daya koma office ya kasa aiwatar da komai, baki daya ya rasa gane inda dai ajiye alakar shi da Aminatu, da kuma billowar Farouk a lokacin da bai dace ba. Ba yaro bane shi dan a ƙalla ya doshi shekaru talatin da biyar, yana bukatar mace a kusa dashi, dan haka ya zama dole ya tuntube ta yaji matsayar sa dan bazai yiwu su dinga yi masa wasa da hankali ba.
  Lambar ta ya lalubo zai kira sai kuma ya fasa ya ajiye yana sake gyara zaman sa sosai, gwara kawai ya bari weekend yaje face to face ayi magana yasan matsayar sa.
   Wulakancin da Farouk yayi masa ya kasa barin ransa, a takaice dai ba'a taba masa abinda ya tsaya masa haka ba irin na Farouk din, ko dan dama tun asali ba wani shiri suke ba oho.
   Kiran Hajiyar sa ne ya shigo masa, ya daga da sauri don wanna zuwan da yayi be samu ya leka su ba bacin ran Farouk yasa ya dawo ba tare da ya shirya ba.

"Barka da safiya Hajiya." Yace cike girmamawa

"Barka dai, ya aikin?"

"Alhamdulillah babu dadi."

"Haka ne dama sai hakuri, Allah ya bada sa'a."

"Amin."

"Na zata zaka shigo wannan satin ina ta jiran ka dan akwai muhimmiyar maganar da zamuyi sai kuma naji shiru."

Sosa kansa yayi

"Abubuwan ne suka sha kaina, satin nan zan shigo in Sha Allah."

Ya samu kansa da boye mata zuwan da yayi wanchan karon.

"Shikenan sai kazo."

Shafa kansa ya dinga yi yana nazarin dalilin kiran mahaifiyar sa, ya santa sarai bata wasa da al'amuran da suka shafe shi, last zuwa da yayi sai data yi masa korafin maganar Aminatun


*****
Wayar da take tayi saurin katsewa saboda shigowar Daddyn da bata yi tunanin a lokacin zai shigo ba.

"Sannu da zuwa." Tace cikin rashin gaskiya, be fuskanci komai ba ya amsa mata a sake yana wucewa dakin sa, dazu da suka tsaya a Kaduna ya hangi Mummy a motar ta, gaba daya sai yaji ya gaza sukuni da ransa, ya rasa dalilin da har yanzu ya kasa mancewa da ita a zuciyar sa, gashi ta kafe sosai ta hanashi rabar ta balle har ya samu nasarar shawo kanta.
Turo kofar tayi dauke da tray din abincin sa, ta ajiye gami da dora wayar ta saman mirror kafin ta juya ta fita. Kallon abincin yayi sam bashi da appetite ya matsar dashi gefe ya saka abin sallah ya gabatar da sallar da ta tsere masa. Yana sallar ta leko ta koma ta cigaba da wasu aikace aikacen
Yana zaune yana addu'oin sa wayar ta dake ta faman kuka ta ishe shi, dan buɗe murya yayi da nufin kiran ta shiru sai kawai ya yanke hukuncin dagawa ba tare da tunanin komai ba. Wanda ya kira ya soma magana kai tsaye ba tare da tunanin tsayawa ya saurari wanda ya daga kiran ba

*"Zan shigo gobe da safe, zanzo kamar yadda na saba zuwa a matsayin Ibrahim, ina so na tabbatar na katse numfashin Kamal kafin ya farfaɗo ya sanar da MD wacece asalin yar tashi, ba yanzu nake bukatar ya sani ba har sai na tabbatar da duk dukiyar sa ta dawo hannu na."*

"Kina jina?"

Yace bayan ya gama maganar, tsaki yaja kadan ya katse kiran yana tunanin network ne

"Adam." Daddy ya furta da karfi

Tsawon wannan lokaci dama shine yake raina masa wayo yana takowa har cikin gidan sa bisa amincewar matar sa? sanin cewa wanda ya riga ya mutu baya dawowa yasa be taba kawo komai ba, ya yarda dashi fiye da yadda ya yarda da kowa har ya amince da tayin auren Maman da yayi masa kai tsaye babu ko dogon bincike, ashe??? Ya zama dole ya shigo hannun sa a goben nan, ba zai taba bari damar ta kubce masa ba. A gaggauce ya rubuta masa text message da wayar Maman sannan yayi saurin gogewa yana ajiye wayar a mazaunin ta.


Rano 😍😍*DG*

                       *39*

©Hafsat Rano

★★★★

Da sauri ya jawo wayar sa ya kira MD, yana dagawa be jira komai ba yace

"Zaman Kamal a asibtin nan akwai hatsari, zan iso asibitin yanzu, kafin zuwa na a tabbata babu wanda ya shiga in da yake."

"Shikenan sai kazo."

Ya ajiye wayar, duba lokcin yayi dare ya soma yi ya fito.

"Lafiya Alhaji?" Ta tsare shi cikin kulawa

"Eh babu komai, wani aiki ne ya taso da yake bukatar fitar tawa."

Yayi gaba dan ko fuskar ta baya son gani.

Yana isa asibitin ya ja MD gefe ya sanar masa da abinda yake faruwa, hankalin sa ya tashi, dole suka tuntubi likita a aka basu sallama a take sannan ya haɗa su da wanda zai kula da Kamal din kafin yazo da safe.
  Dukkan su babu wanda be yi mamakin dalilin da yasa za'a dauke Kamal, haka suka nufi gidan kowa da tunanin sa, matakan tsaro sosai aka kara a kowanne gida sannan Daddy ya samu ya kwanta da tunanin abinda gobe zata haifar.

****
Komawa yayi ya haye gadon ya mike kafa,

"Ku shirya mu wuce toh, amma ya za'a yi da Baba?"

Daga kanta tayi cikin nazari kafin tace

"Ko taje gida?"

"Ummm anya? Why not taje gidan Dadah, idan yaso sai suyi zaman su da mai aikin ta har mu dawo."

"Ok bari na fada mata." Tace

Rakata yayi da ido yana lumshe su kamar na wanda ya sha wani abun, sarai ta ganshi sai ta basar dan ita yanzu ya soma bata tsoro. Jim kadan ta dawo ta sauko da yar karamar trolly dinta ta jera musu kayan su ita da Iman da duk abinda tasan zasu bukata.
  Juyowa tayi tana kallon sa, so take ta chanja kayan jikin ta sai dai ganin yadda ya kafa ya tsare yasa ta fasa ta zaro hijabi ta ɗora a saman doguwar riga, dama chan Iman a shirye take.

"Na gama." Tace tana kallon sa

"Kin fasa chanja kayan jikin naki?"

"Ni nace zan chanja kaya?"

"Na gane ai." Yace yana mik'ewa

"Oya baby muje ko?"  Ya riko Iman din

"Ina?" Ta kalli mahaifiyar ta da sauri tana matsawa kusa da ita

"Ummi ina zamu?" Tace tana kallon jakar dake ajiye

"Unguwa zamu, kije wajen sa Daddyn ki ne babu abinda zai miki kinji"

"Har dake?" Tace tana sake matsawa kusa da ita

"Har dani."

Murna tayi ta kama hannun sa

"Muje uncle."

Shiru yayi duk sai yaji babu dadi, yana bukatar lokaci da zai shaku da yar sa, sai a yanzu yayi dana sanin barin garin da yayi. Kada kansa yayi yaja jakar tare da kama hannun ta suka fita.

"Nace ba, ko zaki kira Anas ki sanar masa kar yazo bama nan?"

Baba Altine tace tana daukar yan kayan ta

"Ok zan kira shi."

Tace sannan suka rufe gidan.

Kai tsaye gidan Dadah suka nufa, Iman ce a gaba sai Baba Altine da Aminatu a baya, suna zuwa suka tarar dasu shirye, da murna Dadah ta tarbe ta ta rungume ta cike da jin dadin ganin ta. Bayanin komai Farouk yayi mata sannan suka fito. Babbar mota ce me kujeru biyu a baya saboda haka basu wani takura ba, Uncle Aliiyu da Farouk ne a gaba, sai Anty Safiyya, Dadah, Aminatu da Amal a baya sai yaran Anty Safiyyan guda uku.' da Iman
  Hira suke tsakanin Dadah da Anty Safiyya, sai Farouk da uncle Aliyu dake tasu a gaba wadda ta shafi siyasar kasar mu ta gado.
  Aminatu da Amal kamar basa motar babu wanda ya bude baki yayi magana duk da kuwa suna manne kusa da juna. Ta gefen ido Amal ke satar kallon Aminatun tana jin wani iri game da ita, tunanin yadda za'a kwashe da maganar auren ta da Farouk da take ganin ya kamata ace akwai mafita a ciki, gashi babu wanda ya kuma daga zancen a cikin su Daddyn sunyi biris kamar basu san da auren ba, gashi ita ba wani take kulawa ba kuma ita sam bata ma yarda da aka ce wai Mummy ta shayar da ita ba, idan har haka ne ba zata yafe wa Mummy ba dan ta cuce ta iya cuta.

***
Daddy be iya bacci ba, jira yayi ta yi gari ya waye kar ma yazo ko yana bacci. Kiran farko a kunnen sa ya yunkura da kyar ya fada toilet ya daura alwala ya fara gabatar da raka'atanil fajr kafin ya wuce masallacin dake kan layin su dan gabatar da sallah.
  Bayan an idar ya dawo gidan, jami'an tsaron dake tsaye a gate gidan ya tattara waje daya ya sanar dasu abin da yake so suyi masa, sun amsa da toh kafin ya koma ciki ya hau shiri dan yana ji a ransa yau komai zai waka na.

Wajajen takwas na safe ya fito harabar gidan ya samu kasan rumfar da ya saba zama musamman da yammaci ya zauna, sannan ya aika aka karbo masa breakfast din sa a wajen.
  Tun yana zaune yana duban lokaci har rana ta soma dagawa da tasa dole ya koma ciki yana tunanin abinda ya katse shi da zuwa bayan yayi masa reply a matsayin Maman ce.
 

****
Yammaci ne me cike da ni'ima, sake fitowa Daddy yayi ya zauna yana kallon ko ina a harabar gidan komai na sake dawo masa kamar a lokacin yake faruwa. Idan bai manta ba, a irin wannan lokacin ya same shi, cikin kankan da murya ya shigar da kansa, be san ya akayi ba,be san me ya faru ba, kawai ya samu kansa da amince masa kai tsaye, ya sakar masa ragamar komai na harkokin sa, a halin yanzu shine yake juya alakar dukiyar sa mafi yawa. Dan karamin tsaki yaja ya shiga shafa kansa, tabbas idan ka biye ma zuciya zata kai ka ta baro ka, gashi shima ya biye wa tasa, ba tare da dogon bincike ba ya afka ga tarkon da yake tunanin fitar sa akwai kalubale babba.
   A daidai lokacin motar su ta kunno kai, duk a gajiye suke saboda tafiyar musamman Aminatu da ba sabawa tayi ba, yaran sunyi bacci yafi sau nawa suna farkawa.
  Da kallo ya shiga bin motar har suka samu waje sukayi parking, Ido ya zura sosai ganin da gaske Dadan ce yasa ya mike da sauri cikin mamaki yace

"Dadah."

Fitowa tayi tana kallon gidan, karo na biyu bayan lokacin ta sake dawowa.

"Barka da zuwa Dadah, ashe kina tafe."

Yace yana bayyana farin cikin sa a waje,

"Barka dai, ya jikin Kamal din?"

"Alhamdulillah."

Hannu ya mika wa uncle Aliyu sannan su Aminatu suka gaishe shi kafin su dunguma zuwa ciki. Duk Aminatu a darare take ta kasa sakin jikin ta, kai tsaye Amal ta wuce dakin ta dan dama a gajiye take da zama waje daya da su.
Farin cikin Mama ya kasa boyuwa, dama haka take chan kirkin masifa ne da ita, haka ta shiga hidima dasu kamar zata goya su, a take ta saka umarnin a gyara tsohon bangaren Dadah daya ke a rufe.
  Dakin Amal maman ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login