Showing 66001 words to 69000 words out of 112633 words
Chapter 23 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
ta makaranta ba,dame zanji?"
"Toh ai ni hakan ma zaifi min farin ciki, yaushe zaki gama da school?"
"Lecture daya ya rage, nan da 30min zamu shiga."
"Shikenan ki kirani idan kin gama."
Yace yana mik'ewa, waya ta dake cikin jakata tayi k'ara, tsayawa yayi ya harde hannu yana jiran yaga mai kiran. Ina ciro ta naga ya kwashe da dariya
"Yanzu zata nutsu kamar wani maka'ika." Yace yana bata fuska, ban bi ta kan shi ba na kara wayar a kunne na gami da sallama. A nutse na shiga amsa masa har ya ajiye wayar, ajiyar zuciya na sauke ina duban KAMAL da shi ma nidin yake kallo
"Ya Anas ne fa."
"Na sani, ai naga sunan, ki rage tsoro kamar zai yanka ki idan ya kira."
"Kai ka sani, aka ce ma tsoron sa nake? Kawai ina respecting d'insa ne."
"Daga baya kenan, ki cigaba da nuna masa tsoro, idan kika aure shi kisha wuya yarinya."
Da sauri na ware ido ina murmushi
"Yanzu Kamal har kasan wani aure? Inyeee."
Dariyar shima yasa yana yin gaba abin sa, sai daya dan d'ara wajen kafin ya ce
"Kinci sa'a ke sirikace zaki bani Iman amma da kinji magana gabza gabza wallahi."
Murmushi kawai nayi ban kuma ce masa uffan ba na hau tattare kayan karatu na ganin lokacin shiga ajin ma ya kusa.
A gaban Hall d'in na tarar dashi tsaye yana jira na, ni har na manta ma munyi maganar zamu tafi tare, babu yadda na iya haka na bishi muka dau hanya, sai dai kamar yadda ya san gidan a dah yau sai yaga mun chanja akalar tafiyar tamu, kallo na yayi yace
"Kun chanja gida ne?"
"Eh." Na amsa mishi a takaice, muna zuwa na shiga na sanar wa Baba Altine zai shigo, cikin daki ta koma na rik'e hannun Iman muka fito, da mamaki yake kallon mu, sai kuma ya ƙaraso ya daga ta sama yana dariya sosai
"Baki da kirki Meena, haka matar tawa ta girma amma baki fada min ba?"
"Shigo ciki dai sarkin zance, sai muyi maganar."
Cikin muka koma, ya zauna a kan dardumar dana shinfida masa, ruwa na dauko masa na ajiye sannan na shiga daki na ajiye jakata na sake fitowa, yana zaune yana wa Iman wasa ita kuma tana ta dariya kamar ta sanshi, Kitchen na wuce na duba, shinkafa da wake Baba tayi, sai salak da tumatir dake yanke an tsaftace shi a cikin mazubi, hadowa nayi na jera komai na kawo masa ina zama.
"Ga abincin gidan talakawa sai kasa albarka."
"Kinci bashi wallahi."
Murmushi kawai nayi, a gefen sa ya ajiye Iman ya bude flask din, ya dauki plate ya zuba abincin sosai ya shiga ci muna hira, sosai yaci dan banyi tunanin zai ci haka ba, ganin yadda yake d'an gayu sai na dauka a komai ma hakan ne, shiyasa Bature yace never judge a book by it's cover, tabbas haka ne, kar kayi saurin yanke wa mutum hukunci ba tare da sanin ainihin waye shi din ba.
Kiran wayar sa akayi, da murna ya daga yana sawa a handfree
"Old Woman kinyi missing d'ina ne hala shisa kika biyo baya."
"Sosai kuwa, sati nawa rabon dana saka ido na? Kana cewa baka son Kano sai gashi kayi luf har kana mancewa dani, ko kayi sabuwar mata ne?"
Dariya ya tuntsire da yace
"Aikuwa dai kin iya saurin gano abu, yanzu ma kin ganni wajen ta, nazo mamanta ta cika min ciki da Rice and beans me shegen dadi."
"Da gaske kake yaron kirki?"
"In bata ku gaisa ne?"
"Eh bata naji."
A kunne ya kara wa Iman wayar yana kunshe dariyar sa
"Oya say hi to my boring Grandma kinji baby."
Gwaranci ta soma yi, kamar yadda ta saba duk sanda Anas ya kira a bata wayar, dariya muka hau yi gaba dayan mu har granny din dake kan waya,
"Ja'iri zaka zo har inda nake ka same ni." Tace tana katse wayar, tallafe fuskata nayi da hannu biyu ina kallon sa
"Baka da dama kamal, Allah shirye ka."
"Amin, naji, itama da gulmar tsiya ai maganin ta."
Mik'ewa yayi ya mana sallama ya tafi, bayan tafiyar sa ina kokarin tattare komai na abincin ya shigo, bakin sa dauke da sallama, ido na cikin nasa nayi saurin yin kasa ina jin faduwar gaba, bai sanar dani zuwan sa ba dazu da mukayi waya, da gudu Iman ta rungume shi tana masa oyoyo, daga ta yayi ya manna ta a jikinshi har lokacin idanun sa na kaina yana yawo dasu.
"Sannu da zuwa." Nace ina cigaba da tattare kayan, da hannu ya amsa min yana nazarin wajen zaman da kayan da nake kwashewa, sallayar na gyara masa ya zauna yana tankwashe kafar sa.
"Bako kikayi ne?"
Yace yana karanta ta, ban amsa na gaishe shi, a gajarce ya amsa daidai lokacin Baba Altine ta fito tana masa sannu da zuwa, da fara'a ya amsa mata ba kamar yadda yayi min ba, ta zauna tana tambayar su Hajiya, tashi nayi na kawo masa ruwa da ragowar abincin na wuce daki, ina jin sa ya jeho ma Baba Altine tambayar da yayi min ɗin, maimakon tace masa eh sai naji tace
"Wata kawarta ce tazo bata jima da tafiya ba ma, ko kun hadu a hanya?"
"No shikenan."
Girgiza kai na nayi ina mamakin halin shi, kayan na sauya na fito na koma kitchen din na dora indomie dan ba karamar yunwa nake ji ba, zama na nayi a Kitchen din ba tare da na koma Falon ba, ina jiyo hirar su ya ware sosai yana wasa da Iman, wannan na daya daga cikin dalilan daya saka nake sake bashi girma, da gasken gaske yake kula damu kamar wanda muka zama masa dolen sa.
Zama na nayi bayan na gama dafa indomie na ci a Kitchen din na zuba ma Iman da Baba Altine tasu a dan flask na fitar da kwanukan na daureye sannan na koma ciki.
"Mu baza'a bamu indomie ɗin ba ne?"
"Za'a baku." Nace ina kokarin komawa kitchen din
"Barshi sai da muka roka, dauko hijabin ki rakani unguwa."
"Baba dauko nake kema kar mu barki ke kadai a gida."
"A ah wallahi, shikenan kuma sai na biku godai godai dani, Aallah kiyaye sai kun dawo."
Murmushi yayi kawai ya rike hannun Iman sukayi waje, ciki na koma na zura hijabin na fito.
A jingine jikin motar na tarar dashi, yana gani na ya bud'e min bangaren mai zaman banza, shiga nayi sannan ya miko min Iman ya rufe mana kofar, zagaya wa yayi yaja muka tafi.
Zagaye ya dinga yi damu daga wannan titin zuwa wannan har zuwa lokacin magriba, tsayawa yayi a wani masallaci yayi Sallah sannan ya kaimu wani wajen cin abinci, nidai duk a takure nake haka yayi mana takeaway muka fito, shopping mall din dake manne da wajen abincin ya shiga, ya ɗan dade a ciki sannan ya dawo hannun sa dauke da manyan ledoji ya zuba a baya muka dau hanya.
Muna zuwa gida ya tsaya jikin motar yana nuna min kayan ciki
"Kwashe kayan ki shiga dasu kizo muyi magana, dare ya fara yi."
Kwashe wa nayi na dawo, na karbi Iman data fara bacci na kaita itama na sake dawowa na tsaya.
"Ya karatun?" Ya tambaye ni
"Alhamdulillah, yasu Hajiya? Kwana biyu bamuyi waya da Raudah ba nasan suna shirye shiryen finals."
"Lafiya lou."
"Ya maganar mu?"
"Na'am?"
"Kinji ai, ina so mu fara fuskantar juna, idan yaso sai nayi kokarin shawo kan Hajiya."
Girgiza kai na nayi a nutse nace
"Maganar iyaye magana ce mai matukar girma, kayi hakuri mu yi abinda tace, bana so ka sami matsala da mahaifiyar ka."
"Zaki jirani zuwa lokacin da zata amince? Zaki jirani?"
"Bani da zabi da rayuwa ta sai abinda Allah ya zaba min, idan kai din Alkhairi ne gare ni, nima kuma alkhairi ce a gareka, Allah ya sa ta amince, idan har ta amince ni bani da zabi."
"Shikenan, in sha Allah zata amince, ki bani lokaci."
Daga masa kai nayi, ya sakar min murmushi ya fada motar yana daga min hannu, sai dana ga fitar sa daga layin sannan na shige ciki ina saka key a kofar.
Da daddare nayi ta juyi ina tunanin maganganun, bani da zabi face amince masa, wacece ni ma da har zai tsaya bata lokacin sa akai na, bani da asali bare tushe, bayan haka wannan ce hanya kawai mafi sauki da zan saka masa da dukkan alkhairin sa.
Sake juyawa nayi zuwa dayan barin ina tuna Farouk, mutum na farko daya so ni duk da karancin shekaru na, ban taba tunanin shi ma zai guje ni ba, haka dama rayuwa take shiyasa na bar wa Allah zabin komai na rayuwa ta, sau tari tunanin sa kan hanani sukuni har naji zuciya ta na zafi, tun ina sa ran haduwa dashi har na hakura na barwa Allah.
Ban cire rai ba amma, kila watarana ya waiwaye mu, ko ba dan ni ba, ko dan yarinyar sa, duk da yace babu komai tsakanin mu, amma ina fatan ganin da zai mata kadai ya isa ya gamsar dashi yar sa ce,shafa kanta nayi ganin yadda yake bacci cike da kwanciyar hankali, bata da damuwa ko matsala, tsoro na daya ranar da zata tambaye ni mahaifin ta, duk da ina fatan kafin ranar na samo gamsasshiyar amsar da zan bata.
***
Shirin fita take taji ana mata knocking, ajiye abinda take tayi ta nufi kofar kai tsaye tana tunanin waye, turus tayi ganin shi, tayi saurin ja baya tana kokarin maida kofar
"Karki rufe min kofa."
Wani kallo tayi masa kafin tayi dariya
"A matsayin ka nawa?"
"A matsayi na na wanda kike jira tsawon shekaru."
"Jira?"
Tayi dariyar rainin hankali
"Karka manta babu auren tsakanin mu."
"Kema karki manta nasan kinyi auren kin fito, kin zata bani da labari?"
Juyawa tayi kawai ciki ya bi bayan ta yana murmushi, falon yabi da ido, yadda aka kawata shi da kayan kawa da komai, sanyin Ac hade da kamshin turaren ta tun na fil'azal ne manne a falon, iska ya shaka ya fesar yana zama cikin jerin manya manyan kujerun da suka kara wa falon kawa.
Ciki tayi ta barshi zaune, sai data dau tsawon lokaci sannan ta dawo ta sauya shigar ta zuwa simple gown ta rufe kanta, zama tayi chan nesa dashi tana kallon screen din wayar ta.
"Me kake bukata?" Ta tambaya kai tsaye kuma a gajarce
"Nazo ne nayi miki wasu yan tambayoyi, nasan tabbas kinsan amsar su."
"Then..." Ta kalle shi cikin ido sosai
"Kin shayar da Amal?" Yayi mata tambayar kai tsayen, kai tsayen itama ta amsa masa
"Eh akwai wani abu ne?"
"Akwai, kinsan auren Farouk dake kanta ko? Kuma kinsan musulunci ya hana auren wanda suka sha nono daya, amma ban manta ba tun a lokacin dana ga take taken ki na hana, saboda irin wannan ranar."
"Na shayar da ita tun kafin kayi min magana, haka zalika na bari daga lokacin da ka hana."
"Mesa baki fada min ba?"
"Me yasa baka fada min da zaka hada auren ba? What is my fault anan? Wait saboda nice karkatacciyar kuka mai dadin hawa ko? Shine bayan komai ya kwabe muku zaka zo wajena."
"Why are you like this? Kin chanja sosai."
Dariya ta shiga yi sosai kafin tace
"Mutane na chanjawa ne daga lokacin da wanda suke tare dasu suka chanja, baka ga komai ba indai nice."
Mik'ewa tayi tana duban agogo
"Ina da abin yi, can you please excuse me?"
"I'm not done yet, ina son sanin ina d'ana?"
"Shine tambayar da ya kamata nayi maka tun zuwan ka, ka sani ba wai nayi shiru bane, ina baka time ne kayi gaggawar fito min dashi duk inda kasa shi ya tafi."
Ransa ne ya ɓaci, ya tashi tsayen shima zai maida mata martani wayar ta dake gefen sa tayi kara, kura wa wayar ido yayi da kuma sunan dake rubuce akan screen din kamar mai nazari, da sauri ta sa hannu ta dauke wayar tana sakata a silent. Shiru ne ya biyo baya ya kasa tantance abinda yake ji game da sunan da ya gani. Ganin ya kasa tunawa yasa ya share yana kokarin tausar zuciyar sa, sai daya dan ja lokaci yana tunanin yadda zai yi maganar kafin ya daure kamar an fuzgo maganar yace
"Abinda ya faru shekarun baya, menene gaskiya? Menene tsakanin ki dashi? Me ya faru a ranar?"
Dagowa tayi a dan zabure, sai kuma tayi saurin saita kanta tana sakin murmushi
"Duk abinda zuciyar ka ta tsara maka, shine abinda ya faru,kuma ya riga ya wuce babu amfanin dawo dashi baya, bani da lokacin wannan maganar."
Tana kaiwa nan tayi shigewar ta daki tana rufo kofar da sauri, kamar wanda aka dasa haka ya kame a wajen yana ayyana abun a ransa, yanayin ta da yadda ya hangi tsantsar tsoro a idanun ta bayan ya kawo mata maganar ta sashi shakku, ko dai ya aikata abu cikin fushi? Ya biye wa dokin zuciya? Yayi mata adalci kuwa a lokacin? Me yasa yanzu yake jin son jin gaskiya duk da tsawon lokacin da aka dauka? Bashi da amsar tambayoyin. Da kyar ya kai kansa mota yana shiga yace
"Kano zamu je."
****
Basu suka isa Kanon ba sai dare, Dadah na zaune saman abin sallah tana karatun Alkur'ani, ya shigo, da kallon mamaki ta bishi har ya dire a gabanta yana jin kamar ana sassara masa kasusuwan jikin sa. Da kyar ya bude baki ya amsa sannu da zuwan da take masa, shiru ne ya biyo baya sai kuma ya tuna yana bukatar suyi magana
"Dadah kinsan Abidah ta shayar da Amal kuwa?"
Kai tsaye tace
"Na sani, amma ina ga ai ta daina tun lokacin daka hanata."
Dafe kansa yayi da dukkan hannayen sa
"Ya akayi duk ban san da haka ba? Kinsan musulunci ya hana aure tsakanin wanda aka shayar dasu nono daya, duk da malamai sunyi sabani, wasu sunce idan har an shayar da nonon sau uku, toh ta haramta ga duk wasu da suke muharraman wadda ta shayar da ita din, wasu suka ce ko sau daya ne idan har an bata tasha ta koshi, toh an haramta auren tsakanin ya'yan matar data shayar da ita, ko kannenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya, ko yayyenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya,ko mahaifinta. Duk dai wasu muharraman da babu aure tsakanin su da ya'yan matar data shayar da ita, toh sun haramta ga wannan wadda aka shayar ɗin.
Wasu malaman suna ganin sai idan har ta shayar da ita na tsawon lokaci ne hakan zai kasance, toh amma dai ko yaya ne, nasan tabbas ta shayar da ita, na tsawon wata guda koma fiye, kinga kenan ta haramta ga Farouk."
"Allahu Akbar, ilimi fadi ne dashi, ban taba sani ko ji ba wallahi, shiyasa ban kawo komai a kaina ba, bayan haka ko da ace na sani,bana ma tunawa da ta shayar da ita din."
Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina kansa da saman kujerar, komai ya chanja masa daga yan da yaso ya kuma tsara.
***
Da baya da baya ta koma ta fada saman gadon ta tana sakin kuka, idan har abinda taji Daddy na fad'a gaskia ne, kenan ita da Ya Farouk shikenan? Kai ina bazai yiwu ba, yadda ta kwallafa ran nan dashi, ace kuma shikenan? Sai ta kara sautin kukan ta sosai.
Da ido tabi wayar da kallo kafin ta shiga share hawayen fuskarta da sauri da sauri, dagawa tayi ta shige toilet bayan ta sawa kofar dakin key.
Tsawon lokaci ta dauka suna magana kafin ta ajiye wayar ta fito, lamo ta kwanta tana tunanin mafita.
***Babu wanda yayi mata maganar daga Dadah har Daddy. Taso tayi ma Dadah maganar taji me zatace amma bata so ta tabbatar mata da gaskiyar hakan, duk abin duniya yabi ya dame ta, gashi ana maganar komawar ta makaranta saboda lokaci na kara tafiya, kamar marainiya haka ta zama, duk farin ciki da take dah idan ta tuno da auren dake kanta yanzu ya kau, tunanin ta yadda za'a samu mafita ace akwai aure tsakaninsu kawai take, idan haka ne Mummy ta cuce ta wallahi. Bata da aiki sai kuka, ranar da sukayi waya da Mama ta fada mata abinda ya faru, kwantar mata da hankali tayi, ta dan ji dama dama kuwa, har ta dan saki ranta.
****
Tun ranar da ta fada mishi abinda ya faru be sake kiran ta ba, ya dai tabbatar mata da yana nan zai san yadda za'a yi.
Sati guda ya dire a kasar, ya wuce kai tsaye Abuja, Daddy na zaune wajen daya saba shan iska ya shigo gidan.
"Saukar yaushe?" Daddy yace yana fadada fara'ar sa, zama yayi kan katon carpet din yana mika masa hannu
"Mun same ku lafiya?"
"Lafiya lou mutanen Turai, Azeema kuwa tasan da zuwan ka?"
"Ina bata sani ba ai, zuwan nawa kenan."
"Lallai sannu da zuwa, ka shiga ciki toh nima yanzu zan shigo ai."
"Ok." Yace kai tsaye ya shiga ciki, tana ganin sa ta rufe baki da hannun ta.
"Ya akayi haka?" Tace tana zaro ido
"Zuwan dole ne, akwai abinda zan duba ne ba jimawa zan koma."
Ajiyar zuciya ta sauke
"Na zata ai ko lokacin da muke jira ne yazo."
"Saura kiris." Yace yana nuna mata hannun sa, dariya ta saka.
Shigowar Daddy yasa su yin shiru, zama yayi suka sake sabuwar gaisuwa,kafin a gabatar masa da abubuwa ci da sha, kadan yaci ya yi musu sallama ya tafi.
Yana fita ya tsura wa gidajen guda biyu ido kafin ya fashe da da dariya, motar sa ya shiga wadda ta kasance a rufe ruf da bakin glass, da karfi yasa hannu ya zare mask din fuskar sa, a razane na saki alkalami na ina sake duban sa da kyau
"Adam!!!" Na furta baki na na rawa.
Murmushin gefen baki ya saki kafin ya maida fuskar ta zama ta wani mutum daban ya ja motar ya bar kofar gidan da mugun gudu.
Ranoa: *DG*
*30*
Kai tsaye garin na Kano ya wuce, yana isa ya mata text kafin ya karasa wajen da zasu haɗu. Tana zaune tana jira sakon ya risketa, dama a shirye take saboda haka mayafi kawai tasa ta fita.
Kafin tazo ya cire mask din fuskar sa ya fito a ainihin kamar sa. Tana zuwa tayi saurin fad'awa jikin sa ta saka mishi kuka, shafa bayan ta ya shiga yi a hankali har ta tsagaita