Showing 12001 words to 15000 words out of 112633 words

Chapter 5 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7413

gama haukan naka zamu wuce."

"Daddy ka taimaka min, maganar karatuna fa dan Allah, wallahi ban aikata abinda kake tunani ba, taimakon ta kawai nayi, wanda na dauke ta tamkar Amal."

Tsaki Daddy yaja, ya gaji da jin wannan shirmen nasa, bashi da lokacin da zai kara batawa ya saurare shi, duk wata hujja tasa bata da amfani tun da be kawo ta a lokacin da ya kamata ba, ko a gaban alkali ne to Tabbas ya tabbata mai laifi tun da har yayi saurin amsawa. Duban shi yayi, baya so ya karya masa zuciya, saboda haka ya nuna shi da hannun sa

"Kai yanzu ai na gama da kai, ba zan iya tsayawa sauraren shirmen ka ba. Maganar karatu kuwa in kana so zaka iya neman admission ka soma karatun anan, kar dai ka manta akwai responsibilities na matar ka kanka, so you have to be very careful."

Hannu ya watsa baya ya juya cikin takun kasaita ya fada mota, Amal ce suka fito da Dada tana kuka sosai akan dole ba zata tafi ba, da sauri ya rarrafa gaban Dadan yana sakin kuka me tsuma rai.

"Dada kiyi min rai dan Allah, Daddy ya dau zafi sosai yaki saurarata."

Dago shi tayi ta bude kofar falon ta tura shi ciki ta rufe, motar ta nufa rike da hannun Amal, daddy na ganin haka ya fito.

"Ka barta ta zauna tare dani har zuwa lokacin da za'ayi resuming makarantar su, sai azo a tafi da ita dan Allah."

"Duk yadda kika ce haka za'a yi, mu zamu wuce."

"Allah ya kiyaye hanya, ka kara nazari akan hukuncin da ka yanke wa Babana, duk abinda ka shirya sai ka sanar min a waya."

"Shikenan in Sha Allah."

Matsawa baya sukayi motocin suka fice daya bayan daya, ajiyar zuciya ta sauke ta kama hannun Amal suka juya ciki.

Kaiwa kawai yake da komowa a tsakiyar falon, yana jin an bude yayi wajen ta da sauri ya fada jikinta yana sakin kuka. Bata hana shi ba, tasan zuciyar sa a cunkushe take kukan kadai zai rage masa radadin da yake ji. Ya dau lokaci sosai yana kokawa da zuciyar sa, yana jin kamar ya hadiye ta ya huta da radadi da zafin da take masa, a hankali ta fara sanyi sakamakon addu'ar da yaji Dadan na tofa masa, da sauri shima ya kama yana karanto innalillah wa inna ilaihi raji'un. Sosai hakan yayi masa tasiri kwarai, zamewa yayi ya zauna akan tiles yana sauke kansa kasa.

"Babana..."

"Tashi ka shiga kayi wanka ka gyara jikin ka, dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma komai zai warware cikin ruwan sanyi. Ka cigaba da addu'a."

Be musa ba, illa mik'ewa da yayi yana nufar dakin sa cikin tafiyar da tafi kama da wanda ya kwanta jinya me tsawo.

***Ina kwance yau ma kamar ko yaushe tun barowar mu asibiti bana iya aiwatar da komai sai abinda Inno tace, komai yimin ake abinci ma sai ta bani a baki, shigowa tayi tana tura kyauren dakin namu, gefen da muke ajiye kayan mu ni dasu Karime ta nufa, ta jawo ledar kayana ta fito dasu, set uku ne an wanke su sai hijabi daya da mayafi yellow, wata ledar sabuwa da alamun ita ta shigo da ita ta bude ta zuba kayan, takalmi na guda daya samfurin sukwal ta jawo shima ta saka min, sai dan kunne da sarka duk suma na sallah ta ne, ina kallon ta har tapp gama tana jan tsaki.

"Tashi kije ki watsa ruwa maza."

Mik'ewa nayi na amsa da toh na nufi bayin dake tsakar gidan mu, su Hanne na gani da su Karime sun cin kwalliya sun sa sababbin kayan su na sallah, kamar na tsaya yi musu magana sai kuma na fasa na shiga wankan. Mintuna kadan na fito na sake wucesu na shige ciki, da hannu Inno ta nuna min kayan dake ajiye a gefen tabarmar dakin. Dauka nayi na saka na koma na zauna ina tunanin inda zamu ake ta wannan shirin. Fita tayi ta barni a nan, ina ta jiyo hayaniyar yaran gidan sama sama, da gudu naji karime ta shigo gidan tana kiran Inno

"Ga motar chan tazo Inno."

"Naji me bakin aku."

Ta katse ta tana hararar ta, mamaki ne ya kamani, yau Inno ce ke cewa karime me bakin aku, lallai ba karamin bacin rai take ciki ba. Shigowar ta dakin ne yasa nayi saurin kallon ta

"Tashi maza ku kama hanya, saura inji ko in gani, ba dadewa zakiyi ba zaki dawo."

Da sauri nace

"Ina zani Inna?"

"Ban sani ba, tashi nace ki wuce suna jiran ki."

Tashi nayi jiki a sanyaye na fito tsakar gidan, Yalwati da Babar su Hanne na gani a tsaye duk sun sha lullubi, kamoni sukayi muka nufi kofar fita daga gidan. Motar dake ajiye a waje aka bude mana muka shiga, sai a lokacin naga Hanne da Karime a gaba, ajiyar zuciya nayi na ɗan ji sauki tun da bani kadai bace. Ina ji aka tashi motar muka dau hanya. Wannan tafiyar tana daya daga cikin shafukan rayuwa ta da bazan taba mantawa ba.

Rano 😍   ©️®️HafsatRano

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
 
                    (7)

***Tafiya kadan mukayi muka isa gidan, da mamaki nake kallon gidan, gidan da nake da muradin zuwa a koyaushe, murna na hau yi Yalwati tayi saurin hararata, da sauri na nutsu, aka bude mana bayan motar ta gama daidaita a harabar gidan da nake wa kallon aljannar duniya. Tsallen murna su Karime suka hau yi Yalwati ta daka musu tsawa, sum sum sum suka dawo bayan ta suka makale, kofar dake kallon mu wanda ya kawo mu ya nuna mana.

"Bismillah hajiyan na ciki ai."

Sake riƙe ni gam sukayi muka nufi kofar, kafin mu karasa aka budo kofar aka fito, matar nan ce ta asibiti, da fara'a ta tarbemu,tayi mana iso cikin falon, wani irin azababben sanyi me hade da sanyayyen kamshi ya kaiwa kofofin hancin mu ziyara, ina kallon Babar su Hanne na sake bude kofofin hancin ta sosai tana shaƙar iskar da tayi mana maraba, duk muka rabe a kasa nida su Karime, aka shiga gaisawa cikin mutuntawa. Nidai ina ta son kallon ko ina a falon amma babu dama saboda yadda Yalwati ke kara rufa min fuskata, bansan dalilin da yasa take min hakan ba, bayan na ga su Karime da Hanne an bar su suna ta shan kallon su. Ina ta hasashen ina ma nice na more kallon nan. Chan na kurawa katotuwar talabijin din dake girke a bango ido ta cikin mayafin duk da ba wani sosai nake gani ba, wasu mutum biyu babba da yar matashiya suka shigo dauke da manya manyan farantai, ina kallo suka dire gaban mu aka sake gaisawa sannan suka juya suka fice.

"Bismillah ga abinci." Matar ta fada tana nuna wa su Yalwati kwanukan da aka jere a gaban mu, wanda tuni kamshin ya fara sawa na manta yanayin dana baro, ina ji na kamar babu sauran damuwa ko takura a cikin rayuwa ta. Kamar su Yalwati ba zasu ci abincin nan ba, ina ta addu'a har sai dana ji matar ta sake musu magana, sannan suka sauko kowa ta hau diba dan dama nasan kawai kara sukayi wanda ni sam ban san su da ita ba.

"Amal!" Ta bud'e muryar ta tana kwala mata kira, da sauri ta shigo, turus tayi ganin baki taki karasowa

"Ƙaraso mana kika tsaya."

Shigowa tayi tana sake kallon mu.

"Ga kawar ki nan rike ta ku shiga ciki."

Hannu na ta kama, muka bar falon, mayafin na cire muna yin gaba, kallo na tayi tace

"Laaaaa Aminatu."

"Na'am." Nace mata ina murmushi

"Yaushe kika zo?"

"Yanzu muka zo, nan ne gidan ku ashe."

Daga min kai tayi

"Zo muje kiga daki na."

Da sauri na bita, muka shiga dakin nata, dan karamin gado sai single wardrobe da toilet, kan gadon muka fada muka saki dariya a tare.

"Dakin ki mai kyau." Nace ina kallon ko ina, a raina ina raya dama nawa ne.

"Thanks." Ta amsa tana murmushi

"Bari na kawo miki chocolate din da Ya Farouk ya siya min."

Ta fita da sauri, tashi nayi na bude kofar toilet din, tsayawa nayi ina kallon mamaki, bansan ina ne nan ba, na dai ga alamun akwai ruwa a ciki. Rufewa nayi na koma gadon na hau, na mike kafata ina murmushi. A raina na shiga raya dama daki na ne dana more.

Dakin Farouk ta nufa tana kwala masa kira, yana zaune da waya a hannun sa suna magana da Ja'afar ta shiga, kallon ta yayi ya mata alamar tayi masa shiru, tura bakin ta tayi ta nufi in da ta bar kayan chocolate din nata ta dauka, har zata fita sai kuma ta dawo ta tsaya a gaban sa tana dariya

"Kawata Aminatu ce tazo, tana dakina."

A dan rikice ya kalle ta

"Ina zuwa zan kira ka."

"Me kika ce? Su waye suka zo?"

Ya fada yana mik'ewa

"Kawata Aminatu."

Da sauri ya dafa kansa, da gaske kenan anyi aure, wani irin yar yaji tun daga kansa har tafin kafarsa, tunanin kalmar auren kadai na sa shi a wani yanayi. Ashe da gaske Daddy yak masa, kwata-kwata yarinyar nawa take, da har za'a yi mata aure. Gaban mirror ɗin dakin ya isa yana kallon kansa. He's to young for that, idan be manta ba next month zai cika 22years chif.

"Ya Salam." Ya furta yana fadawa gadon

"Me nayi wa rayuwa ta ne? Na daure kaina da kaina, yanzu idan Mummy ta samu labari ya zanyi?"

Da sauri ya tashi, farar singlet ce kawai a jikin sa, sai dogon wando, ciwukan jikin sa na nan musamman na fuskar sa, dakin Amal din ya nufa da dan saurin sa, ya bude kofar da karfi. Suna zaune sun baje a saman gadon suna kwasar chocolate. Tsaye yayi yana kare musu kallo, da sauri yaga ta rufe idon ta ta sauke kafarta kasan gadon, kallon kansa yayi ya sake kallon dakin

"Menene?" Amal ta tambaya tana kallon na.

"Tashi ki rakani wajen su Hanne, kar naje ana jirana zamu tafi."

"Kai dan Allah, ki kwana mana."

Make kafada nayi, takowa ya shiga yi har ya ƙaraso gaban gadon, ya sa hannu ya rike ni, zaro ido nayi ina kallon sa, sai kuma nayi saurin rufe ido na

"Tsoro na kike ji?" Ya fada yana kallon saman fuskata

Da sauri na daga kaina, dariya Amal ta kwashe da ita har da tafa hannu

"Tsoron Ya Farouk kike ji, ai baya suka fa."

Bata fuskar sa naga yayi ya saki hannu na, be ce komai ba ya juya ya bar dakin. Ajiyar zuciya na sauke ina kallon Amal din

"Ni dai muje ki rakani."

Tashi taga nayi yasa ta mike itama ba tare da taso ba muka fito wajen Dada. Babu kowa sai ita kadai, kallon ko ina na hau yi da sauri alamun neman abu.

"Kuzo nan yarana, Aminatu me kike nema naga kina ta kalle kalle.?" Ta fada cikin son ta yi min wayo

"Ina su Hanne?"

Nayi narairai da fuska kamar zanyi kuka.

"Kinga ke anan zaki zauna ke da kawarki, kuyi wasa tare, kuyi komai tare har karatu zan sa ana koya muku, idan kika kwana da yawa sai ki koma gida."

"Har karatu ma zamu dinga yi, kuma ba zanyi girkin shinkafa da wake ba ko??" Na tambaye ta ina kallon ta.

"Girki! A ah banda girki, ai kunyi kankanta sai an kwana biyu, sai share dakin ku kawai da wanke toilet, sai kuma sallah."

Washe baki na nayi, cike da murna na ce

"Ni ba sai an maida ni gidan mu ba ma, ki barni ana kawai."

Dariya suka sa gaba dayan su, nima na bisu mukayi ba tare da na gane dalilin dariyar ba. Abincin dazu aka zuba mana, muka hau ci muna kallo, tuni na manta da komai, muna gamawa Dada ta dauko magani ta bani na sha, sannan tace muje muyi sallah, bazan tuna rabon da Inno ta sakamu sallah ba, babu ruwan ta da munyi ko bamuyi ba, muna idar da sallar muka dora kallon mu, ranar gaba daya ji nayi kamar nafi kowa farin ciki a duniya. Sai gaf da magriba sannan muka koma dakin Amal da a yanzu ake masa lakabi da dakin mu.

****
Gidaje biyu ne manya manyan gaske wanda suka cinye kafatanin layin tun daga gaba har baya, iri daya ne sai dai daya yafi daya girma da komai. Da dukkan alamu mamallaka gidan akwai alaka me karfin gaske a tsakanin su, ko ta yan uwan taka ko ta abota. Gidan farko da yake dauke da tafkeken gate me matukar tsawo da fadi aka yi saurin wangalewa sakamakon karar horn, da sauri mutane biyun dake zaune akan dan bencin zaman maigadin gidan suka tashi suka nufi wajen motar. Babban mutum ne dogon gaske, cikin shigar alfarma ya fito daga ciki, hannun sa dauke da wayar sa yana amsawa, yadda yake magana kadai zaka gane yadda arziki ya samu babban matsuguni a wajen, rike yake da murfin motar har ya gama wayar kafin ya maida duban sa bakin yana murmushi

"Sannun da zuwa Alhaji." Suka ambata a tare cike da girmamawa. Amsawa yayi yana duban chan hanyar gate din.

"Wai tun da mukayi waya kuke zaune kenan, sannun ku da zuwa, Bismillah."

Gaba yayi suka bi bayan sa har kofar da zata sadaka da babban  falon gidan, daya daga ciki ne yayi saurin bude masa, godiya yayi sannan ya shiga da sallama, babu kowa a falon nasa, sai sautin  suratul bagra dake tashi daga cikin jerin speakers din da suka karawa falon kawa.

"Bismillah, Ina zuwa."

Wuce su yayi ya haura corridor din da zai maidaka part din matar gidan. Yana shiga yaron dake kwance akan sofa yana kallo ya taso da sauri

"Daddy!" Ya rungume shi,

"Kamal, kana nan kana sana'ar taka ta kallo ko, yau babu islamiyya ne."

"Malam ne yace yau ba zai zo ba zai je garin su."

"Ah lallai, yau ranar hutawa ce."

Kallon ko ina yayi kafin ya sake shi yana cewa

"Ina Mamyn taka ne? Naji gidan tsit."

"Tana daki, wai kanta ne yake ciwo na dame ta da surutu shine ta koroni."

"Toh zauna na dubo ta, kai ɗin ne watarana akwai zuba kamar..."

Buga kafa ya fara yi irin ta shawagabbun yara, dariya kawai yayi ya nufi dakin gimbiyar tasa. Tana kwance ta juya bayan ta ya shiga, yadda yaga yanayin kwanciyar ta ta yasa ya gane da gaske kan nata ke ciwo, dan dama gwanar ciwon kance, fasa tada ta yayi ya juya ya koma wajen bakin sa. Sun jima suna tattaunawa kafin su tafi, daga nan ya bada umarnin kar a bar kowa kuma ranar yana so ya huta sosai.

Watsa ruwa ya fara yi, yaci abincin da ke jere a saman dining din part din nasa, sannan ya nufi bangaren Hajiyar sa.

***
Gaba daya ran Inno a jagule yake, ta rasa yadda zata bullo wa al'amarin, gaba daya ji take dama bata amince da bukatar su ba, da tuni zuciyar ta na nutse bata da wani tashin hankali. Babban matsalar ta ma zuwa da tayi wajen Harira da ta tambaye ta labarin yaron ta, yadda ya amsa mata ya nuna cewa bata san komai akan halin da yake ciki ba. Tun bayan abinda ya faru da Aminatu, kullum bata samun isasshen bacci, bare yanzu da ta koma wani gidan sai take ganin kamar babu ita babu cikar burin ta. Duk da sunyi alkawari da Harira akan haka sai dai bata jin zata samu nutsuwa kenan har idan ba dawowa din tayi ba. Ita da zai yiwu ma da sun hakura da komai ta maida ta wajen iyayen ta, hankalin ta ya kara tashi ne saboda samun ainihin labarin waye iyayen ta, kuma dadin dadawa babu hannun mahaifiyarta ko mahaifinta a bin da ya faru, Harira ta rufe ta, ba ta sanar da ita duk wannan ba, yanzu idan suka ki yarda suka hada su dukka suka kulle su fa, bata tunanin duk duniya akwai wanda zai iya fito dasu. Haka zasu kare rayuwar su a ba wan ba kanin. Ita kam abubuwan sun mata yawa.

***
*Sati Daya*

Wasanmu kawai muke nida Amal, bamu da wata damuwa ko kadan, ina matukar jin dadin zaman gidan. Wajen yanayin jikina kuwa sosai magungunan da nake sha suka taimaka min wajen samun lafiya ta. Har na murmure abu na, kaya kuwa na Amal nake sawa kafin nima a karo min nawa kamar yadda Dada tace. Muna zaune a falon Amal na karanta mana wani story book duk da ba gane wa nake ba, idan ta karanta sai ta fassara min da hausa. Sosai hakan ke min dadi. Shigowa yayi fuskar sa babu walwala kamar ko yaushe ya wuce, duk ya rame yayi baki, ina ji dai ranar Dada na masa fadan ya saukaka wa kansa, damuwa babu inda zata kai shi, duk da hakan be chanja ba. Kullum yana aikin waya, a rana sai ya kira Daddy sau nawa ba tare da ya kosa ba duk da hakan baya dagawa, daga karshe ma sai ya sashi a blacklist.

Har ya gifta mu sai kuma ya dawo da baya ya tsaya a gaban mu. Duk muka kalle shi a lokaci guda dan ba kasafai yake shiga harkar mu ba.

"Me kuke yi?"

Ya tambaya yana zaman a hannun kujerar ta gefen da nake. Mika masa littafin Amal tayi tana matsowa

"Story book muke karantawa."

"Kuna son mu fara lesson?"

Da sauri muka amsa, murmushi yayi ya mika mana littafin

"Shikenan anjima zamu fara idan nayi bacci na tashi."

Murna muka hau yi ya wuce ya bar mu yana girgiza kai. Bayan wani lokaci sai gashi ya fito cikin shigar kananan kaya, yanzun ma wayar ce a kunnen sa suna magana da wani, zama yayi yana wayar yana kallon in da muke, har ya gama be dauke idon sa daga kanmu ba, tashi yayi ya wuce dakin Dadah, yau duk wunin ranar a daki tayi saboda ciwon kafarta da ya matsa mata,daga mu sai masu aiki sai yanzu da Ya Farouk ya dawo. Jim kadan sai gashi ya fito dauke da mukullin mota yana jujjuya shi.

"Kuzo muje ku rakani." Yace yana yin hanyar fita, da gudu muka yi daki, muka sako takalmi muka fito, yana tsaye jikin motar suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login