Showing 102001 words to 105000 words out of 112633 words

Chapter 35 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7414

ta tashi.
  Yana zaune ya kura wa tangamemiyar Tv ido hankalin sa na ga tunanin maganganun Ammin ta fito, sanye take da Hajabi dogo, da ido ya bita har ta samu waje ta zauna.

"Sannu da zuwa Ya Anas."

"Aminatu, idon ki kenan."

"Kayi hakuri, ya aiki?

"Alhamdulillah, gashi muna ta fama."

"Allah ya taimaka."

"Amin."

"Menene alakar ki da gidan nan Aminatu? Kinsan waye me gidan kuwa? Ba karamin me kudi bane karki je kisa kanki a matsala."

Murmushi tayi

"Ya Anas Allah ya amsa addu'a ta, ya haɗa ni da iyaye na."

"What! Kina nufin Alhaji Marwan Dikko mahaifin ki ne?"

Daga mishi kai tayi

"How comes?" Yace cike da mamaki

A nutse ta bashi labarin yadda komai ya kasance, jinjina kansa kawai yake har ta kare,

"Allah mai iko, na tayaki murna sosai, zan sanar wa Hajiya kuwa gobe gobe dama zan je."

"Nagode sosai da karamcin ka gareni."

"Babu komai, wannan labarin yayi min dadi, nasan tabbas Hajiya zata ji dadin labarin."

"So ya maganar mu? Ina muka kwana?"

"Kayi hakuri ya Anas."

"Me ya faru? Karki cemin ba zaki aure ni ba after all this time dana dauka ina jiran ki."

"Ba laifi na bane, a yanzu dana san hukuncin da ke kaina kar mu saba wa Allah, ina da aure a kaina, kayi hakuri na cigaba da kallon ka a matsayin babban ya'ya na."

Mik'ewa yayi da sauri, yayi mata wani irin kallo kafin ya juya kamar zai tashi sama ya fice daga falon.
  Dafe kanta tayi, tasan dama za'a yi haka,sai dai bata so suyi rabuwar rashin dadi dashi, amma tasan fushin sa, dole dama zaiyi abinda yafi haka, zata bashi lokaci har zuwa sanda zai huce.
   Tashi tayi ta koma ciki, tana duba wayar ta ko Farouk ya kira ta, amma babu kiran sa ko daya, gashi Ammi tace kar ta kuskurat ta kirashi, ita abin ma dariya yake bata, yadda Ammin ta dage sosai akan lallai sai ta ja ajinta.

****
Gagarumin taro akayi, duk yan uwan Ammi da kawayen ta matan kushoshin gwamnati sun halarta, gift kuwa Aminatu ta shashi, har sai data daina gane masu bata saboda yawansu.
   Kyautar sabuwar mota dalleliya Ammin tayi mata, Hajiya Turai kuma ta bata wani dankareren gold sarka da da kunne hade da bracelet me kyau. Kamal ma ba'a barshi a baya ba sabuwar waya yayi mata order ya bata,kukan farin ciki ta saka saboda yadda rayuwar ta ta chanja a cikin awanni kadan da a cikin awannin da tayi na rayuwar ta ba komai bane.
   Daddy kuwa ba'a maganar tasa kyautar dan ta musamman ce, kokarin kiran manyan Drs na kashashe daban daban yake akan matsalar idon ta dan yana so ayi mata aiki me kyau, be fada wa kowa ba, so yake sai komai ya kammala ya sanar musu, yawan shakatawa zasu tafi gaba daya gidajen biyu, daga nan sai Aminatun taga likita, suna dawowa sai a hau shirye shiryen gagarumin bikin da suke shirya mata irin na ya'yan gata.

***
Kwanan Farouk uku a Kaduna duk ya gundura, babu abinda yake son gani sai ita, gashi ko ya kira ta wayar da suke kadan ce zata ce Ammi na kira, dole yayi wa Mummy dabara ya lallaba ya taho bayan ya bar Iman din a chan duk kuwa da kashedin da Ammin da kanta ta karbi wayar tayi masa akan lallai idan zai dawo karya kuskura ya dawo babu Iman din, gashi Mummy ma ta kafe shi kam be san ya zai musu ba, abu daya yake ganin shine kawai Mummy tayi hakuri ta dawo gida, in yaso sai su dinga shifting idan tayi kwana biyu ana sai ta koma nan.
   Har ya iso Abuja be daina tunanin yadda zasu kwashe da Ammin ba, sai da yayi wanka ya huta sosai, ya duba Dadah da bata jin dadi tun abinda ya faru,sannan ya nufi gidan kanshi tsaye.
  
Ta window ta hango shigowar shi, tayi saurin tashi daka kwanciyar da take, ta fada toilet, wanka tayi a gurguje ta dauro towel ta fito, kai tsaye wajen mirror tayi ba tare da ta lura da shi ba, ta cikin mirror ta hange shi, gaban tane ya yanke ya fadi ganin mutum a zaune a kan gadon ya zura mata ido ba ko kiftawa, da sauri tayi hanyar toilet din cikin zafin nama ya rigata k'arasa wa ya chapke ta.

"Karki manta soja ne ni, ba zaki fini gudu ba."

"Dan Aallah..."

"Shissh karma ki fara wallahi, ba a isa a hanani abinda Allah ya halatta min ba."

"Ammi zata shigo fa."

"And so? Shine daidai ma ai." Yace yana zagaye hannun sa a saman fuskar ta, runtse idon ta tayi da sauri, ta rike hannun shi.

"Pleee... Please kayi hakuri."

"Please kayi hakuri." Ya kwaikwayi muryar ta yana dariya.

Hannu ta kai chest din sa ta dake shi, ya rike hannun yana ɗorawa a saman kirjin nasa

"Kiji yadda zuciya ta ke bugawa da sauri da sauri, I'm dying to be with you, please do something."

Saurin zare hannun ta tayi, tana juyar da kanta. Zagayo wa yayi bangaren fuskar ta ta

"Bari naji yadda take take bugawa."

Da sauri tasa hannu ta kare saman chest dinta, ta lura so yake sai ya kure ta dole, ga wata masifaffiyar kunyar sa da take ji, Allah yaso ta ma towel din da dan girman shi, duk da haka ana iya ganin fiye da rabin jikin nata.
  Baya ya ja ya harde hannu yana karewa ko ina na jikin ta kallo. He just can't wait...: DG*
                       *44*

©Hafsat Rano

★★★★★★

Maganar Ammi ce ta iso musu tun kafin ta ƙaraso tana bada order, a diririce ya hau neman wajen da zai boye, duk rashin kunyar sa yana tsoron tazo ta ganshi a haka, dariya Aminatu ta shiga yi masa ba kakkautawa, be kula ta ba, yayi saurin samun corridor dake jikin wardrobe ya makale daidai lokacin ta shigo, tsaye tayi tana karewa dakin kallo kafin idanun ta su sauka akan kafafun sa dake bayyana a fili, basarwa tayi ta dubi Aminatun tana hararar ta

"Me kuma kika tsaya kamar wata soja, ko ba wanka kikayi ba?"

Da sauri ta juya ta shige toilet tana kunshe dariyar ta, rigar data cire ta maida ta saka,

"Me haka? Ba sune jikin ki ba dazu?"

"Auw sune." Tace a diririce, wajen wardrobe din tayi ta bude ta dauki kayan ta koma toilet din. 
Sanda ta fito Ammin bata dakin, kallon inda yake a makale tayi ta kwashe da dariya yayi saurin fitowa, rankwashi ya kai mata ta goce tana dariya

"Maganin me satar hanya kenan."
Tace tana masa gwalo,

"Yarinya bashi kika ci, xan dawo ne."

Ya juya ya bar dakin, sai da ya fara tabbatar da babu kowa a falon sannan ya fice daga gidan da sauri yana murmushi.

***Hajiya Turai ce ta aiko aka kira ta, a chan ta tarar da Kamal ta zauna aka cigaba da hirar da ita duk da ba wani sake wa tayi dasu ba amma yadda suke jan ta a jiki yasa ta saki jikin ta itama, har Daddy ya dawo suna wajen,anan suka ci abincin dare gaba dayan su, cikin farin ciki, duk motsin da zatayi sai an samu wanda zai tambaye ta ko akwai wani abu da take bukata? Ta kanyi murmushi tace babu, dan ita a halin yanzu babu kuma abinda zata nema, sai fatan cikawa da duniya lafiya.

Sai data gama shirin kwanciya tsaf, tayi wa Ammin sallama ta haye saman sabon gadon ta, wanda ya kawatu da abubuwa na jin dadi da more rayuwa, cikin kwana biyu aka shirya mata dakin duk kuwa da sun san ba dadewa zatayi ba, babu ce kawai babu a dakin.
  Sama sama taji motsi kamar ana bude kofar, shiru tayi tana sake ji, tunanin ta ko Ammin ce, ta tashi tana kunna bedside lamp, idon ta ya sauka a cikin nasa ya zura hannayen sa cikin aljihun dogon wandon sa, fuskar sa na fitar ta bayyananan murmushi me sanyaya zuciyar wanda ake yi wa shi.

"Yaaa F..."

"Shissh!"

Ya dora hannun sa alamun tai shiru, juyawa yayi ya murza key ɗin dakin sannan ya dawo, ba jiran komai ya haura saman gadon ya kwanta akan bayan sa, ƙafafuwan sa da suke mike sosai ta kalla, ta maida kallon ta kan fuskar sa.

"Kashe wutar nan please bana kwana da haske."

"Kwana? Anan zaka kwana?"

Ware idon sa yai, ya daga mata kai

"Akwai damuwa ne!?"

"Ammi fa..." Tace da sauri,

"Haram na aikata?"

Girgiza masa kai tayi,

"Oya kashe ki kwanta, gudnight."

Ya juya bayan sa, yawu ta hadiye ta kashe wutar tana kwanciya a chan gefe, ƙasa ƙasa yace

" Karfi da yaji an maida mutum gauro."

"Na'am?" Tace tana sake matsawa

"Babu."

Shiru ya sake biyo baya, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa, yadda komai ya sauya daga abun da ba zaka taba tunani ba zuwa me wanzuwa a yanzu a wani bigire na daban, sauyawar akalar rayuwa zuwa wani abu daban abin birgewa da sa farin ciki. Lallai komai ya faru da bawa mukaddari ne, haduwar su da taimakon da yayi mata ya zama wani tsani na rayuwar ta, tsanin da zai yi wuya ta taka shi idan ba wannan dalilin ba.

Mirginawa yayi har ya isa gareta, ya raba hannun sa biyu ya toge dayan da kanta yace

"Bani labari."

Ajiyar zuciya ta sauke kadan, ta gyara kwanciyar ta sosai, a hankali tace

"Gobe zamu je Shagari."

"Daddy ya fada min."

"Owk zaka je? I'm feeling nervous."

"Yes zanje, dole na zama by your side ai, yadda zanji daɗin karya wuyan duk wanda yayi miki kallon da ban gamsu dashi ba."

Murmushi tayi

"Can you do that?"

"Kina mamaki? Zan iya abinda yafi haka ma ai."

"Ummm."

"Allah dai ya kaimu goben.'"

Yace yana sake matsowa jikin ta sosai, hira suka cigaba me dad'i, gaba-daya abinda ya faru a tafiyar sa, da abinda ya faru sai da suka sanar wa juna, wani suyi dariya wani kuma babu dad'i, ba tare da sanin su ba ashe dare yayi sosai, ganin idan suka biye wa hirar zasu kai asubah yasa suka hakura suka kwanta, duk da haka sai da ya tabbatar da ya aika mata sakonnin sa masu tsayawa a zuciya, duk da sakonnin kanana ne ba'a kai ga babban sakon ba,amma hakan yayi tasiri k'warai wajen sake dasa kyakkyawar alaka tsakanin su.
    Kiran asubah ne ya tashe shi, yayi saurin tashi ya gyara mata kwanciya, saboda yasan tana fashin sallah, shiyasa be tashe ta ba ya fice bayan ya tabbatar da babu kowa daya ganshi.

****
Karfe sha daya suka bar Abuja, suka isa Kano cikin yan mintuna da yake a jirgi suka tafi, suna isa suka dauki hanyar Katsina, daga Kamal har Aminatu babu wanda yake magana a cikin su, jifa jifa Farouk ke sako shi a cikin hirar tasu, bashi da kuzarin amsa musu sai dai yayi murmushi kawai.
  Hankalin Ammi ya tafi ne ga kallon hanya, tana fatan su isa lafiya ta samu damar ganin Inno, matar da bata san a wanne bigire zata ajiye alakar su ba, sai dai tana jin ciwo da haushin irin rikon da tayi wa Aminatu, duk kuwa da tasan ba komai Aminatun ta faɗa mata ba. Idan ta tuna wacece a wajen Kamal sai taji tana kokonton irin hukuncin daya dace da ita, ko banza ance uwa uwa ce ba zata so abinda zai bata wa Kamal din ba.
   Haka dai ta cigaba da tunanin abinda take ganin shine, amma bata iya jin zata saurara mata dole ne zata nuna mata kuskuren ta ko dan gaba.
   Shigar bayan azahar sukayi wa garin, kai tsaye gidan suka nufa hakan ya kara tsananta bugun zuciyar Aminatu da take ji kamar zata huda kirjin ta, ta fito, tsoron abinda zata tarar ne dankare a zuciyar ta, bayan tafiyar ta tasan dole abubuwa sun sauya, sai dai ba zata iya daukar rashin wani a cikin mutanen da tayi rayuwa dasu ba ko da kuwa Inno ce.
  
A kasalance ta fito daga motar, rantsattsen lace ne a jikin ta wanda yasha ɗinkin k'warriyar telar nan pink couture, kallo daya ya isa ya gamsar da kai matakin da ta taka ko kuma take shirin takawa a yanzu.
   A sanda Ammi ta bata kayan ita kanta sai data jinjina, dan tasan ba karamin kaya bane, duk sai taji ta kasa sawa tana tantamar wai itace? Sai da Ammin ta sake dawowa sannan ta matsa mata ta saka.
    A waje su dukka suka tsaya, kowa ya zuba mata ido kafin Ammi tace

"Ki shiga muna waje."

Rau-rau tayi da idon ta, ta soma takawa a hankali, duk takun da zatayi sai zuciya da gangar jikin ta sun amsa, idon ta ta wurga gefe, matan dake makwabtaka dasu tuni sun fara lekowa jin tsaiwar mota, sai dai daga kallon da suke mata basu gane wacece ba, kada kanta tayi ta kutsa cikin zauren gidan nasu, yana da tsantsar talauci sunyi wa zauren k'awanya, inda zaka yi tunanin an dauki shekaru masu tsawo ba'a bi ta cikin zauren ba.
  Bakin ta dauke da sallama ta shiga, Karime da tazo ganin gida ta saki tsintsiyar dake hannun ta, idan har ba gizo idanun ta ke mata ba, tabbas Aminatu ce.

"Amin..." Bata karasa ba tayi saurin isa ta rungume ta, kukan da take boye wa ya taso mata gaba daya

"Inna, Inna fito ga Aminatu."

Tace a gigice, da mugun gudu Inno ta fito, sai tayi turus ganin Aminatun cikin shiga ta alfarma, tsoro ne ya kamata, ta tsaya jikin kofa ta kasa karasowa.
  Kallon yadda ta koma Aminatu keyi, idan za'a gaya mata Inno zata zama haka zata iya musawa, babu fiye da rabin jikin ta, ta rame ainun, daga gani tana cikin mawuyacin hali. Da sauri Karime ta dauko tabarma, ta shimfida.
Takowa tayi ta zauna tana kallon dakin Baba, sai ta mike ta isa dakin ta tura kyauren daya gama lalacewa ta shiga, yana kwance akan tsohuwar katitar sa data kara lalacewa, duk yayi baki ya rame abun tausayi, a gaban sa ta durkusa tana sakin kuka me tsuma rai, kukan da take ya farkar dashi daga baccin wahalar da yake, a cikin mawuyacin hali ya kira sunan ta, da ace ma ba a kusa dashi take ba, babu yadda za'a yi taji Hannun shi ta kama ta rike cikin nata, ta cigaba da kuka. Da kyar ta saita kanta tace

"Sannu Baba! Ya jikin?"

"Alhamdulillah."

Shigowa Yalwati ta yi dan tabbatar da abinda aka gaya mata, turus tayi ganin da gaske Aminatun ce

"AMINATU kece?ikon Allah."

"Nice, mun same ku lafiya? Ya jikin Baba?"

"Lafia lou, tare kuke da mutanen dake waje?"

Da sauri ta tashi

"Bari nace su shigo,tare muke."

Tayi waje da sauri, Inno na tsaye in da ta barta, matsawa tayi gaban ta, ta tsuguna har kasa

"Ina wuni Inna?"

"Tsawon lokacin nan kina ina ? Shine kika ki waiwayo wa? Sai yanzu."

"Kiyi hakuri, tare muke da baƙi bari nace su shigo."

Tayi saurin ficewa, suna tsaya tace su shigo, ta juya suka bi bayan ta Ammi jikinta ya gama sanyi dan bata zaci lalacewar ta kai haka ba.
Sallamar su kadai tasa cikin Inno kadawa, bata jira ta gama tantance su ba ta zari buta da sauri tayi banɗaki, zama sukayi akan tabarmar Yalwati ta zo suka gaisa kafin ta tashi ta kawo musu ruwa tana satar kallon Kamal.
Jimawa tayi sosai a ciki, da kyar ta fito, sakin butar tayi ta fadi, ta kwala kiran

"Yalwati, Yalwati! Zo kiga wallahi dana ne, shine yazo ranar zo ki gani karya ƙara tafiya."

"Na ganshi yaya, ki nutsu ku gaisa."

Tsugunnawa tayi a gefe duk jikin ta sai rawa yake kamar mazari. Cikin dakiya Aminatu tace

"Inna wannan itace mahaifiya ta."

Zumbur ta mike ta hau waige waigen inda zata buya dakatar da ita Ammi tayi

"Ki tsaya muyi magana ta fahimta tun da ni dake a yanzu mun hadu akan abu guda, cuta dai kun riga kun cuceni, babu abinda zance muku sai dai na barku da ALLAH."

"Babu abinda ya rage na boye boye,komai ya bayyana, Aminatu ta hadu da iyayenta na asali, cikin mutunci.

Ko ban fada ba kinsan a yauzu ta wuce kallon banza balle a daga mata murya. Ina fatan hakan ya zama izina gare ki dama duk wani me irin wannan tunanin, Kamal da Aminatu dukkannin su yayana ne, ni nan na shayar da shi saboda haka baki da hurumin sake shiga rayuwar mu."

Dagowa tayi da sauri, ta sauke idon ta akan Kamal din, yayi mata nisan da za'a iya misalta shi da tsakanin sama da kasa, ita dama tasan ko da Hajiyan bata ce haka ba, abu mawuyaci ne ya dawo gareta, share hawayen dake faman yawo a fuskar ta tai tace

"Hakika nayi kuskuren da zai cigaba da bibiyata har sanda zan koma ga mahalicci na, ban chanchanci daya daga cikin su ba, na zame masa uwa, ina rokon da ki yafe min, ki dubi halin da muke ciki ko da shi kadai aka barni ya ishe ni ishara."

"Bani zaki roka ba, Aminatu kika cuta, kika batawa rayuwa, idan nace zan daureki akan laifin da kika aikata mata bana jin igiya zatayi saura."

"Aminatu ki yafe min dan Allah!"

"Na yafe miki inna, na jima da yafe miki."

"Idan har ita ta yafe, ni da Daddy ba zamu yafe ba."

Ya fada rai bace

"Kamal?"

"Babu ruwanki Aminatu, wannan ba maganar ki bace."

Tashi yayi ta fita, suka bi bayan shi da kallo, babu wanda yayi magana. Wajen Farouk ya koma yana ta waya, jingina yayi da motar wani abu me daci ya tsaya mishi a makogaro. Tsayuwar motar yan sandan yasa Farouk aje wayar da yake, tuni unguwar ta soma cika jin karar jiniya, Harira, sister Asibi ne a bayan motar kowacce an saka mata handcuf. Durgowa police din yayi, ya tsaya gaban su

"Wacece dyr?" Yace yana kallon shi

Shiru Farouk yayi ganin KAMAL ɗin a tsaye, ganin haka yasa Kamal din yace

"Bismillah, muje na nuna muku ita, dama munyi yawa da Daddy akan haka."

Gaba yayi suka bi bayan shi, yana shiga ya nuna Inno

"Gata nan arrest her."

A zabure Aminatu ta tashi tsaye tana wa Kamal kallon mamaki,

"Menene haka?" Tace rai bace tana duban sa.

"Ku tafi da ita officer." Yace yana dauke kansa.

A gaban sa Aminatu ta tsaya tana masa duba irin na wanda be san abinda yake ba, cikin bacin rai tace

"Me kake shirin yi?"

"Babu ruwan ki."





Kuyi hakuri da short page na aje wayar oga Affan ya dauka yanzu screen din ya tabu da kyar na iya rubutun inayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login