Showing 6001 words to 9000 words out of 112633 words
Chapter 3 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
maana screenshot ta wannan layin๐๐
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*๐๐
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuษi gida masoyan asali๐๐ป๐ฅฐ๐ฅฐ๐๐๐๐๐๐ป๐๐ป๐๐ป_
Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN๐๐๐ป๐ป
*DG*
ยฉ๏ธRano
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*๐๐ฝ
ALKALAMI TV
https://youtu.be/LxY42ErBf_8
ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย (4)
*****
Babu wanda yayi kwakwaran motsi a cikin su, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa. Jin bugun na sake karfi ne yasa shi juyawa da kansa ba tare da yayi magana ba ya nufi hanyar gate din. Budewa yayi yana kallon mutane dake tsaye, wasu dauke da makami, ganin haka yasa sojojin sa suka yo wajen da sauri. Hannu yasa ya dakatar dasu yana bin mutanen daya bayan daya cikin tsananin tashin hankali, sai dai duk da hakan ba zaka tantance yanayin da yake ciki ba, fuskar sa tana nan kamar ko da yaushe.
"A fito mana da yar mu!" Muryar daya daga ciki ta bakunci jin sa, daya bayan daya ya hau kokarin fassara kalmomin acikin yan sakanni.
Take wajen ya kaure da ihun kalmar da yake da bukatar amsar ta cikin gaggawa. Sake daidaita kansa yayi, ya kuma saka dukkan jikin sa ya fito waje sosai yana sake duban su, mutane ne yawancin matasa sai wasu dattijai guda uku daga gefe, kai tsaye ya nufi wajen su, yana me sake daidai ta kansa. Yana isa ya mika musu hannu daya bayan daya, kwarjinin sa ya cika wajen baki daya. Lawan dake niyyar rashin kirki ya ji ba zai iya ba, girma da cikar haibar sa kadai ta isa ka girmama shi. Balle kuma da shigar sa ta nuna ainihin shi din waye ne. A nutse ya kai duban shi wajen sauran yaran kana ya maida kansa garesu
"Me yake faruwa?"
Ya tambaya yana nuna su Garbati,
"Yar mu wadda take cikin gidan nan muka zo tafiya da ita."
"Yar ku? Kuyi hakuri ban gane kan maganar ba, zuwa na kenan."
"Alhaji jiya daya daga cikin yaran gidan nan ya dauke mana yar mu, bayan mun gaji da neman ta muke samun labari ta wajen daya da ga cikin matasan garin da abin ya faru akan idon sa, toh jiya munzo a daren bamu samu ganin kowa na gidan ba sai Maigadi, shiyasa muka shiryo muka zo yanzu, dan har mun sanar wa maigari ma."
Hannu yasa yana shafa kansa, be tsinci komai a bayanin ba, sai dai ya fuskanci suna zargin batan yar su ne a gidan sa, a gidan nasa ma kuma cikin yaran sa, dan jim yayi kadan yana nazari kafin yace
"Ku bani mintina biyu dan Allah ina zuwa."
Juyawa yayi ya nufi cikin gidan, ya zo shiga Garbati ya daga murya yadda zaiji sosai yace
"Wallahi sai an fito da ita, ga Fyade ga sata, haba ai abin yayi yawa."
Chak ya tsaya da tafiyar da yake, wani irin bugu zuciyar sa tayi, babu abu daya daya ki jinin ji kamar kalmar fyade. Maganganun da suka cigaba ne suka shiga maimaita kansu a cikin kwanyar sa, da sauri ya fada gidan, suna nan tsaye duk a in da ya barsu, daya bayan daya ya shiga binsu da kallo kamar me lissafa su, duk sun tsure iya kar tsurewa sun gama sanin me hakan ke nufi.
"Ina Farouk?"
Shiru babu wanda yayi magana, a fusace ya sake tambaya cikin daga murya sosai. Da sauri har suna hada baki suka ce
"Sun...sun fita da Dada da Amal."
" Ina suka tafi da sassafe haka bayan kuma ku da alama ko dukkanku tashin ku kenan."
"Asibiti suka tafi kai wata yarinyar."
Dafe kansa yayi ganin zancen na fitowa.
"Da yaushe suka tafi?"
"Jiya da daddare."
***
Zama Dada tayi tana jiran Amal ta idar da sallah, Farouk na zaune a kan kujerar dakin yayi nisa a tunani, shi kadai yasan me yake tunawa, alluran da ya kamata ayi mata duk anyi mata. Tana idar wa ta tashi ta je gaban gadon tana kallon ta
"Ya Farouk ta samu sauki ko?" Ta tambaya tana nuna masa ita. Daga mata kai yayi yana murmushi
"Amma mene sunan ta?"
Girgiza mata kai yayi alamar shima be sani ba, murmushi tayi tana sake kallon ta.
"Ina son ta da kawa, me kyau kamar ta cikin cartoon din nan."
"Tashi zakiyi mu tafi ba surutu zaki tsaya yi ba."
Sai kuma ta maida kallon ta wajen Farouk
"Kai ma tashi zakayi muje, idan yaso sai a nemi iyayen ta a sanar musu suzo dan yanzu nasan hankalin su a tashe yake."
"Da wai sai na zauna da ita har suzo ษin, kinga be kamata a bar ta ita Kadai ba."
"Farouk!" Ta bude idon ta sosai
"Baka da hankali ko? Kasan abinda hakan zai haifar? Lallai kai yaro ne."
"Dadah ki barmu anan nida Ya Farouk dan Allah, kinga idan ta tashi bata ga kowa ba zatayi kuka."
"Toh uwar iya, wallahi tashi zakuyi mu tafi, ba zan iya da matsalar da zata taso ba, na riga nayi magana da wata nurse zasu shigo suna dubata har suzo iyayen nata."
Kamar ya fashe da kuka haka yaji, shi be ga dalilin da zai sa Dada tace sai sun tafi ba, gashi idan ta kafe babu abinda zai sa ta hakura, tashi yayi tsam yana kallon gadon kafin ya juya ya fice da sauri. Kwafa tayi ta ja hannun Amal suka fito, a tsaye ta hango shi tare da Dr Iman suna magana, karasawa tayi wajen
"Dr Barka da safiya."
"Yawwa Mama, ya me jiki?"
"Alhamdulillah, mungode Allah."
"Allah ya kara sauki, zan shiga sai na duba jikin nata."
"Ok Dr, nima zan dan je gida ne na dawo."
"Ok yayi,ka same ni a office idan na gama round zan yi magana da kai, amma yanzu ka koma dakin karta farka taga babu kowa."
Ta fada tana yin gaba,kallon Dada yayi yana marairaice fuska, ganin yadda tayi kicin kicin da fuska.
"Sai ka zauna ai dama abinda kake so kenan, amma wallahi Babana ina ji maka tsoron abinda zai je ya dawo, ba fata nake ma ba, amma baka san halin mutanen mu ba."
"Babu abinda zai faru sai Alkhairi Dada." Ya fada cikin gamsuwa.
"Shikenan, Allah yasa."
"Amin." Yace yana murmushi.
"Zan tsaya wajen ka Yah."
Kama bakin sa yayi da sauri yana kallon Dadan, tsaki tayi ta juya tana mitar sun raina ta.
Ciki suka koma da sauri, har lokacin bata tashi ba tana sauke numfashi a hankali.
****
Zagaye da hannayen sa yake kaiwa da komowa, wani irin tashin hankali me matukar girma yake hasasowa idan har abinda yaji ya zama gaske, ya zaiyi? Da wacce fuskar zai kalli mutanen kauyen. Tabbas idan hakan ta kasan zai dauki mummunan mataki akan Farouk, baya fatan zargin sa ya zama gaskiya dan zai iya yafe shi ba ma a cikin yayansa ba, a cikin dukkan ahalinsa. Duk kuwa da dimbin soyayyar da yake masa duk cikin ya'yansa.
Jin tsayuwar mota yasa ya juyo da sauri yana kallon gate din da tun zuwan sa yake tsaye wajen ya rasa me zaiyi. Idanun sa akan gate din har aka gama budeshi. Ganin motar gidan yasa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, duk da baya hango cikin motar amma yasan sune suka dawo, a yau da ace ba tare da mahaifiyar sa suka tafi ba be san abinda zai iya aikata mishi ba, sai dai dole ya saita kansa yaji komai a baฦin ta. Hannun sa ya harde a kirji yana jiran daidaituwar motar da yake ganin kamar da gangan driver yake lankan jin ajiye ta a mazaunin ta.
Dada ce ta fito tana me kallon harabar gidan cikin tarardadin abinda yake faruwa, farko mutanen da ke waje tsaye kamar masu jiran a fito musu da gawa su kaita kushewa, sunyi kungiya kungiya suna tattaunawa, yanzu kuma tsayuwar Janar a harabar gidan ya kara tabbatar mata da abinda take tsoro take gudu ne ya faru. Jiki a sabule irin na wanda yayi fama a filin daga ya isa gareta kafin ta ฦaraso.
"Dadah.!
Ya furta muryar sa a bude sosai me nuna yanayin da yake ciki.
"Muje ciki." Ta fada tana kallon sojojin da sukayi dafifi a wajen suna tsaye cikin jiran cika umarnin uban gidan na su. Be musa ba, sai jan kafar sa da yayi da tayi matukar sanyi yabi bayanta.
Ajiye mayafin ta tayi ta zauna tana daidata nutsuwar ta, dan tabbas ta hango tsananin tashin hankali da firgici a idon yaron nata, kasancewar sa babban soja hakan be sashi zamaar mata tamkar yaron goye a duk sanda yake tare da ita ba. Tabbas haka Farouk yake, a duk yayansa shine ya biyo shi, babu abu daya daya bari nasan tun daga dabi'a da yanayin yadda yake daukar a'alamri, abu daya tasani shine Farouk yana da sanyin zuciya da saurin yarda da komai, banbancin sa da mahaifinsa kenan wanda ya kasance mutum me tsauri sosai da rashin yarda a duk sanda abu ya gifta tsakanin ku, duk yadda kake dashi zai bar ka, barwa ta har abadah kamar yadda suka rabu da mata mafi soyuwa a gareshi bisa babban kuskuren data aikata masa.
Ruwan da aka ajiye a gaban ta ta kalla tana kallon Ja'afar daya kawo ruwan. Dauka tayi ta zuba ta mika masa.
"Sha ruwa Muhammadu, ko zaka ji saukin zuciyar ka."
Karba yayi ba tare da yayi magana ba ya kafa kai ya shanye tas yana ajiye kofin.
"Me yake faruwa?" Ta wurgo masa tambayar tana nakaltar nazarin sa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi magana cikin dakiya
"Ni kaina na rasa me yake faruwa, zuwa na kenan, na tarar da wannan tashin hankalin, shin da gaske ne abinda mutanen garin nan ke tuhumar Farouk?."
"Me suke tuhumar shi akai? Maganar yarinya ne ko?"
Ta fada kai tsaye dan tasan kwanan maganar kenan.
"Eh ita Dada, suna zargin Farouk da yi wa yarinyar su fyade sannan kuma ya sace ta, wannan wanne irin tashin hankali ne Dada."
Shiru tayi tana maimaita innalillah wa inna ilaihi raji'un a ranta, abinda take gudar wa Farouk kenan, ya kasa ganewa.
"Dadah dan Allah, ina ya kai yarinyar, kuma shin da gaske abinda suke zargin sa akai ya aikata?"
"Yarinya dai tana asibiti dan yanzu ma daga chan nake, kuma tabbas yazo da yarinya a cikin mayuwacin hali, kuma nayi magana dashi na tambaye shi idan shine ya aikata mata, yayi mun rantsuwar dan musulmi bashi bane."
"Shikenan, Farouk ya gama dani."
"A ah kar kayi saurin yanke hukunci, ka tsaya kaji ta bakin nasa."
"Haba Dadah, yaran yanzu fa sun wuce tunanin mutum, kuma ba'a shaidar su sam, dan wanda kake ganin ba zai aikata abu ba yafi aikatawa."
"Yanzu menene abinyi?"
"Tashi zanyi naje asibitin, gani gashi ga iyayen yarinyar, harda maigari ma."
"Shikenan, amma kabi komai a sannu."
****
Shigar su dakin yayi daidai da sake farkawar ta, a dan tsorace take kallon su, kafin ta maida idon ta da sauri ta kulle su gam. Amal ce tayi saurin karasawa wajen gadon ta rik'e hannun ta, jin an rik'e ta yasa ta bude ido ta sauke su akan ta.
"Ya sunan ki?" Amal ta tambaya dan ta matsu tasan sunan ta.
"AMINATU!"
Da sauri ya juyo, sosai yaji sunan nata har cikin ransa, sauti da amon muryarta ya shiga masa amsa kuwwa, yana jin Amal na fada masa sunan su daya tana murna ya kasa amsa mata, sai ma binsu da ido kawai da yake yi kamar be san me yake faruwa ba.
Hira sosai Amal ta shiga yi mata, kallon ta kawai take yi ba tare da ta gane komai ba, ido kawai tasa mata.
"Zan sha ruwa." Ta furta a hankali, da sauri Amal ta tashi ta dauko mata ruwan, kokarin tashi tayi taji zafi, kuka ta saka yayi saurin tasowa,
"Sannu."
Daga masa kai tayi tana gogen hawayen da bayan idon ta. Ruwan ya bata Amal na tsaye kamar zatayi kuka.
"Gida zan tafi." Tace tana kallon sa.
Zaiyi magana aka turo kofar, wani irin faduwa gaban sa yayi yasa hannu ya rike wajen zuciyar sa da sauri.
"Daddy!"
Amal ta fad'a tayi wajen sa da sauri, rike ta yayi ya matsar da ita gefe bayan ya shafa kanta, Maigari ne ya fara shigowa,sai Baba, Inno na bin bayan sa, sai Lawan Da Yahya. Garbati da Ilu suna take musu baya. Da sauri Inno tayi wajen gadon tana sakin kuka.
Gyaran murya maigari yayi, Inno tayi shiru duk aka nutsu ana kallon sa.
"Garbah!" Ya kira sunan Garbati yana masa alamun ya matso.
"Maimaita abinda kace."
Gyara tsaiwar sa yayi cikin dakiya ya nuna Farouk da hannun sa
"Gashi nan, jiya ana ruwan nan ta gefen daki na naji kamar ana kuka, da har na share sai na kuma jin kukan na tsananta, kamar wasa na dauko toci ta na leko, in haska sai ga tashin hankali, ido na cikin nasa yana aikatawa karamar yarinya, nayi kukan kura na rike shi, muka haure da kokawa, shine fa ya samu yayi min mugun duka, kuma ya dauke ta ya gudu, duk da haka sai dana bisu a baya, naga gidan daya shigar da ita, shine fa nayi gaggawar zuwa sanar da iyayen yarinyar."
Tun da ya fara magana Farouk keย kallon sa, gaba daya jijiyar kansa ta fito, numfashin sa ya shiga fita da sauri da sauri, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, Daddy kuwa kasa yayi da kansa yana jin kamar kasa ta zage ya shige, sai dai bashi da ta cewa, duk abinda gaskiya ta bayyana zai goyi bayan ta, ba zai taba goyon bayan zalunci ba ko da daga dan cikin sa ne.
"Kaji abinda ake tuhumar ka dashi, shin kana da abinda zaka kare kanka, duk da dai ga zahirin ganin ku tare da mukayi anan, amma ko zaka fada mana dalilin da ya jawo hakan."
Maigari ya fada yana duban shi, kokarin magana yake ya kasa, motsa bakin sa yake ya kasa, kallon Garbati kawai yake cikin tsananin bacin rai, bai taba tunanin akwai mutane masu aiki irin na dabbobi kamar shi din ba, kallon Amal yayi yaga ta zuba masa ido kamar me son ganin wani abu, ya sake maida kansa wajen Aminatu, itama shi take kallo, tana share kwallar dake zubo mata. Runtse idon sa yayi ya bude ya maida kallon sa wajen Daddy, yanayin daya ga fuskar sa kawai ta gamsar dashi abin da zai je yazo idan har ya kasa fitar da kanshi daga wannan daurin. Kokarin daidai ta kansa yayi ya shiga kokarin magana a nutse duk kuwa da tarin tashin hankalin da yake ciki
"Allah ne..."
"Kai ne kayi mata Fyade ko ba kai bane!" Daddy ya fada cikin k'araji dan ya gaji so yake kawai ya amsa da a ah ko Eh.
"Daddy Wallahi tallahi Allah ne shaida ta..."
"Will you shut your mouth, amsar ka kawai nake so kai ne ka aikata mata Fyade ko kuwa?"
"Fyade!"
Dr Iman da shigowar ta kenan ta karbi kalmar, duk suka juyo suka kalle ta.
"I'm sorry to interrupt, kuna nufin dama yaron nan ba mijin ta bane, fyade yayi mata suka rufa min yace shi mijin ta ne?"
Da sauri Farouk ya kalle ta zuciyar sa na sake tsinkewa.
DAURIN GORO๐ข๐ข๐ฅ๐ฅ๐
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN๐๐_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin๐๐
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*๐๐
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuษi gida masoyan asali๐๐ป๐ฅฐ๐ฅฐ๐๐๐๐๐๐ป๐๐ป๐๐ป_
: *DG* 5
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*๐๐ฝ
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
ยฉ๏ธ*Rano*
ย ย ย
ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย (5)
****
Duk suka maida kallon sa gare ta, takowa tayi ciki tana kallon fuskar Farouk din.
"Me kike cewa Dr?" Daddy ya tambaya yana kallon fuskar Farouk din
"Nice likitar data karbi case din yarinyar, a yadda mukayi magana na zata matar sa ce, dan shi dinma ya nuna min hakan, duk da cewa akwai karancin shekarun ta da nashin ma kansa, sai dai ya amsa laifin sa kuma ya bada hakuri, amma kuma naji wata maganar daban duk da ba dani ake ba, amma ina da right na sani saboda matsayi na na likitar ta."
"Babu wata matar shi, makaryaci fyade yayi mata kila ma sai daya sha ya bugu sosai sannan."
Garbati ya fada yana huci. Kasa hakuri Farouk yayi ya kalle shi cikin konar rai
"Sharrin da zakayi min kenan, kasan nasan komai shine kake kokarin jona min laifin da ka aikata?"
"Ni? Ni zaka wa sharri, na ganka ido da ido, shine zaka maida abin kai na, na shiga uku, wallahi Maigari karya yake min so yake ya maida abin kaina."
Sake duban sa Farouk yayi yace
"Kaji tsoron Allah, ka sani akwai mutuwa akwai hisabi, kar kaga idon mutane anan, ka fadi gaskiya ko dan rayuwar yarinya karama."
"Wallahi tallahi sharri yake min, shine ya aikata karya yake min wallahi." Garbati ya fada yana karashe wa da fashewa da kuka kamar gaske.
Dafa kai Daddy yayi ya kalli farouk, ya gaji da wasan yaran nan da suke musu, magana daya yake son ji, idan shi ya aikata ya amsa eh ko a'ah. Rike masa riga yayi cikin bacin rai
"I'm asking u for the last time, Kai ne ko ba kai ne ba?"
Kukan Amal da Aminatu ne ya kara karfi a wajen, juyawa Farouk yayi ya dube su daya bayan daya, sosai kukan nasu yake taba masa rai, kallon Daddy yayi ya shiga girgiza kai.
"Alhaji ina ganin tun da ga yarinyar nan a zaune, duk da karama ce amma ba zata kasa tantance wani abu ba, ina ganin a tambaye ta, idan yaso kowa ne ya aikata mata wannan abin, a cikin su, to fa dole ne a aura masa ita bayan hukuncin da shari'a ta gindaya ga wanda ya aikata irin wannan laifin, dan kaf kauyen nan namu babu wanda zai yarda ya karbi aurenta, musamman yanzu da zance ya zagaya ko ina, ina tsoron sai dai ta karasa rayuwar ta a haka."
Maigari ya katse su, sakin sa Daddy yayi ya hankada shi har sai daya kusa bigewa da karfen gadon, dago idon sa