Showing 99001 words to 102000 words out of 112633 words
Chapter 34 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
ne ya ankarar damu kuskuren da muka tafka, lallai wannan itace bakar ranar da bazan taba mantawa da ita ba."
Runtse ido sukayi yadda labarin ya bige su, baki daya kunya ta mamaye su,babu wanda ya iya cewa kala har zuwa sanda ta ɗora
"Bazan iya tantance muku kalar tashin hankalin da muka shiga ba, washegari sai ga mahaifin ku ya diro, daurewa kawai muke muna farin ciki amma babu wanda yake ciki, kwana biyu tsakani Habiba ta hau ciwo me zafi, wanda zallar tashin hankali da firgici ne ya haifar mata dashi.
Haka mukayi ta faman jigilar asibiti da ita har mahaifin ku ya koma, ba laifi ta samu dan sauki sai dai bata umm balle a ah, kullum bata da aiki sai kuka, komai ya tsaya mana, walwala da farin ciki yayi kaura daga gidan mu, kwatsam sai ga ciki ya bullo, wanda bani da tantama cikin Adamu ne, tashin hankalin da ba'a sa maka rana, wannan wanne irin tsautsayi ne? Ashe itama Habiba tana dauke da nata cikin, abin ya hade mana sosai kullum sai dai mu zauna muyi ta kuka, har zuwa lokacin da haihuwa tazo mata, tsananin hawan da jinin ta yayi yasa ta jijjiga, bata kai ga haihuwa ba Allah ya karbi ranta da ga ita har abinda ke cikin ta.
Munyi kuka mun yi nadama mara amfani, kwana bakwai tsakani shima Adamu ya bita, nidai kamar zararriya haka na zama, ciwo ne ya taso min gadan gadan ciki wata bakwai, nayi ta addu'ar Allah yasa ya mutu kafin yazo duniya, sai dai kash, Allah ya ƙaddara sai ya taka doran ƙasa, haka yazo da rai,matsayin dan mahaifin ku.
Nayi nadama mara amfani, na rok'i Allah gafara nayi kuka har sai da idanu na suka kafe, na cigaba da boye gaskiyar saboda gudun kunyar duniya.
Bayan abinda Adam ya aikata ne yasa tsoron Allah ya dada kamani, dama nasan bashi da gadon mahaifin ku, sai dai na kasa sanarwa kowa, ganin lokaci na kure min yasa na yanke shawarar sanar da kowa waye Adam, amma kafin nan sai na fara kiran sa na sanar dashi komai, na kuma nuna masa Lallai kai da Aliyu kuna bukatar ku sani.
Ban sani ba ashe, ba zai taba amincewa ba, a lokacin yayi iya kar kokarin sa wajen roko na akan na bar maganar, ganin na kafe ne yasa shi ya shiga barazana da rayuwar ku.
Sannan abinda ya faru da Abidah sharri yayi mata, kasancewar taji dukkan abinda muka yi magana akai yasa ya bata mata suna, saboda yana so tayi nesa da rayuwar mu, na san komai sai dai ba zan iya budewa kowa ya sani ba, barazanar sa ce ta hanani aiwatar da komai, na cigaba da zama da tabon a zuciya ta.
Dan Aallah ki yafe min Abidah, ban kyauta miki ba na saka Alkhairi da sharri.
To be continued.....*DG*
*42*
©Hafsat Rano
★★★★★★
"Ki yafe min, ban kyauta ba, ban yi halacci ba, sai dai babu yadda zanyi ne shiyasa, hakan shine kadai mafita a garemu baki ɗaya."
"Alhamdulillah." Uncle Aliiyu yace yana murmushi
"Tabbas wannan ranar na jima ina jira, ko a yau Allah ya karbi raina zanyi farin ciki matuka."
Shiru wajen ya dauka kowa da abinda ke masa yawo akai, ta gefen ido Daddy ke kallon Abidah cike da nauyi da kunyar ta, juyowa tayi suka hada ido tayi saurin hade fuska ta mike
"Ina ganin bani da hurumin shiga rayuwar ku, wannan abune da ya shafi family dinku, saboda haka ni zan wuce, Allah kara rufa asiri."
"Haba Anty Abidah, dan Allah kar kiyi haka, kiyi hakuri ki yafe wa Dadah, tabbas ba'a kyauta miki ba, amma nasan ki da hakuri da yafiya, dan Allah kiyi hakuri."
"Aliyu karka damu, ni dama ai na dade da yafe wa duk wanda ya zalunce ni, shi kanshi Adam na yafe masa, saboda ko a yanzu haka aka barshi bashi da wani amfani, kaga kenan tun a duniya ya ga sakamakon sa."
Baro kujerar da take tayi, ta iso gaban ta, ta riko hannun ta,
"Ina neman alfarmar da ki yafe min, ban kasance me adalci ba, amma wallahi bani da zabi ne, kowanne bawa baya wuce ƙaddarar sa."
Zuciyar Mummy tayi sanyi ganin yadda matar da girman ta take hawaye, tunanin rayuwar da sukayi a baya da irin zaman da sukayi na dadi da mutunta juna, ba zata iya fadar aibun ta ba ko ko rashin kyautawar ta, dan adam ajizi ne, kowa kuma nayi laifi. Kasa jurewa tayi, ta riƙe ta sosai tana kokari boye nata kukan tace
"Na yafe miki Dadah, Allah ya yafe mana baki daya."
Sai ta sake ta tana maida fuskar ta gefe ganin Daddy na shirin tasowa
"Safiyya, Ja'afar, Farouk ku tashi mu tafi." Tace tana yin hanya
"Dakata!" Ya tsaida ita
"Ki tsaya a k'arasa komai, abinda ya shafi rayuwar Farouk ne, idan ma ni kike gudu karki damu, ba zan tilasta miki ba ai."
Da wani kallo ta jefe shi, yayi murmushi yana komawa wajen zaman sa, a darare ta koma ta zauna kafin Daddy yace
"Dukkan sirrikun dake rufe sun bayyana, kowanne da musabbin aikata shi, tsakani na da Adam da Hajara sai dai nace Allah yayi min sakayya, sannan maganar 'yayan da muka haifa tare kotu ce kadai zata tabbatar da nawa ne ko nashi ne, sabo..."
"Wallahi tallahi karya yake min, duk abinda ya fada da sa hannu na a ciki, chanja yara, takardar saki da duk wani abu nice me kai masa rahoto, amma wallahi maganar yara naka ne, babu wani abu makamancin haka da ya shiga tsakanin mu tun bayan auren da mukayi."
Ta katse shi cikin kuka, murmushin takaici Daddy yayi ya cigaba da bayanin sa
"Saboda haka na saki Hajara saki uku! Ba zan iya zama da mace irin ta ba. Alhaji Marwan kai akafi yiwa cuta mafi girma da kai da mai dakin ka, ina baka damar bin diddigin duk wanda suke da hannu cikin rayuwar Aminatu, a nemo su ayi musu hukunci daidai dasu."
"Sannan na riga na kirawo yan sanda, su tafi dasu daga nan sai a kai maganar kotu, idan yaso sai ayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata, saboda daukar doka a hannu ya saba ma sharia, Farouk kayii musu magana su shigo."
Yace yana komawa baya, tashi Farouk yayi, ya fita jim kadan suka shigo tare da yan sandan su biyar maza hudu mace daya, suna zuwa suka sara wa Daddy, suka koma gefe daga musu kai kawai yayi sannan yace
"Gasu nan ku tafi dasu." Yaa nuna Adam da Mama.
Tsit wajen yayi sai ihun kukan Mamaa tirje tirje ta hau yi tana magiya, babu wanda ya saurare ta, rike hannun Daddy tayi ya fisge yana dauke kansa, bashi da bukatar ganin ko da me kama da ita ne a yanzu, iyakar cutar wa sun masa, sai dai yace Allah ya saka masa.
Babu wanda ya iya magana har aka fita dasu, Adam nata zage zage da cin mutunci, jikin kowa yayi sanyi musamman Amal data yi tunanin za'a hada da ita, bata taɓa sanin mahaifin nata ya kai haka ba, he used her ya samu abinda yake so, ya kuma nuna mata shi aka cuta, bata san abubuwan daya aikata sun kai haka ba, hatta sharrin data yi wa Dadah da Ja'afar akan maganar sakin shi ya sakata, bayan babu sanin su duk dan ya riga ya gama juya mata tunani. Kunya da nauyin mutumin daya riƙe ta da amana take, Daddy yayi mata halacci be nuna banbanci tsakanin ta da ya'yan shi ba.
Ganin shirun yayi yawa yasa Alhaji Marwan daurewa duk da baya jin dadin komai yace
"Ina bawa kowa hakuri bisa abinda ya faru, lallai akwai rashin kyautawa ga kowanne bangare, sai dai hakan ba zai hana hukunta masu laifi ba,ina fatan duk wanda hukunci ya biyo ta kansa yayi hakuri, mu dukka abu daya ne, kuma zamu cigaba da rike juna da mutunci. Sannan ina sanar da dawowar ya ta, duk da wasu a cikin ku sun santa, sai dai wannan sanin yasha banban dana baya, Aminatu yata ce ta cikina, kowa yaji yadda aka chanja mana ita, ina fatan kowa ya karbe ta hannu bibbiyu, ba wai a matsayin matar Farouk ba, a matsayi 'ya ga Marwan Dikko!"
Da sauri Mummy ta dubi Aminatun, duba na tsanaki kafin ta dauke kanta tana mamakin yadda abin ya zama.
Hajiya Turai tafi kowa shiga farin ciki, takanas ta taso ta dawo wajen Aminatu, ta sata jikin ta tana murna, tabbas jinin tace, babu tantama ko shakku. Duk da kasancewar Dadah tayi farin cikin samun labarin, sai dai bata da kuzarin nuna hakan duba da yadda kunya da nauyin ahalin ta mamaye ta, saboda haka bata iya cewa komai ba sai kokarin danne abinda ke taso mata na nauyi da kunya kawai take.
Amal kanta sai da maganar ta girgiza ta, ta shiga duban Aminatun da wata kama daban ba wadda tasan ta a baya ba,duk da amintar dake tsakanin Alhaji Marwan da Daddy, sai dai nisa da tazarar dake tsakanin su ta fannin arziki ba abu bane karami, ta ko ina MD ya yaga wa Daddy. Gashi ita bata ma da tudun dafawa kasancewar uban da take tunkaho dashi da babu duk daya, hakan ne yasa ta jin shakku, tabbas Aminatu ta yaga mata ta ko ina, tayi mata nisan da har abadah ba zata taba kamo ta ba, gashi ita yanzu bata ma san makomarta ba,ko Daddy zai cigaba da rike ta kamar yadda ya fara? Shine bata sani ba.
Duk da Ammi ta kadu sosai jin cewa Adam na da hannu a rashin haihuwar ta, sai dai taji dadi, atleast ta samu hanyar da zata nemi maganin matsalar ta a addinance. A kasan ranta ta tausaya masa, duk abinda yayi a dalilin son da yake mata ne, wanda ita kanta tasan bata kyauta masa ba, amma kuma abinda yai mata yayi tsauri sosai, sai dai tana fatan hakan ya zama izina ga yan baya, wani zai iya jure ma yaudara amma wani ba haka ba, zai iya salwantar da rayuwar wadda ta yaudare shi kamar yadda Adam yayi mata ko ma fiye da haka.
Ganin an tafi wata maganar daban yasa Farouk daurewa yace
"Am...am... Daddy dama maganar da kace na bari a zauna..."
"Auw kaga naso na manta." Alhaji Marwan yace yana murmushi
"Game da maganar auren su, ya kamata asan halin da ake ciki, tun da dukkan bincike ya nuna bashi da masaniya akan komai, dukkan abin da ya faru plan ne babu abu daya daya kasance gaskiya, bayan haka ma ko da ya kasance da gaske ya aikata sakin a bisa tirsasawa aka gusar masa da tunani, ko bisa rashin sani toh akwai maslaha akai kamar yadda yazo idan har ya tabbata bashi ya sha kayan mayen da kansa ba kuma ba'a cikin hanyacinsa yayi haka ba, to hakika sakin baiyi ba domin alkhalami ya sauka daga kansa sakamakon baya hayyacinsa, Sannan ya tabbata acikin hadisi Manzo s,a,w yana cewa:_
*ان الله تجاوز عن امتي الخطا والنسيان وماستكرهواعليه*
_Ma'ana Allah ya daukewa al-ummah ta laifuka guda uku (3) Na farko: Abinda sukayi bisa rashin sani. Na biyu: Abinda sukayi bisa Mantuwa. Na uku: Abinda sukayi bisa tilastawa Abinda aka tilasta mutum yayi kenan ba'a Son ransa ba.
Sai dai dukkan shaidu sun nuna bai aikata ba, bashi da masaniya ma akan abinda ya faru, hakan ya tabbatar da auren su yana nan, da ace dai tayi wani auren ne toh fa tabbas ta kubce masa.
*WALLAHU A'ALAM*👏🏻
Ina fatan hakan zai wanke duk wani kokonto daga zuciyar kowa.
Aminatu ta koma dakin ta su cigaba da zaman su.
Kasa Aminatu tayi da kanta tsananin kunya duk ta rufe ta, babu wanda maganar batayi wa dadi ba in ka cire Amal, Ammi da Mummy da ba zaka iya tantance abinda ke ransu ba.
Mik'ewa Ammin tayi tana kama hannun Aminatun kafin tace
"Ayi min afuwa, ina bukatar yarinya ta a tare dani, saboda haka sai na sake bincike sosai akai, ba zanyi saurin saka rayuwar ta a matsala ba."
Tana kaiwa nan ta jata suka shige ciki,rai bace Alhaji Marwan ya mike Daddy ya dakatar dashi
"Tana bukatar yar ta, karka manta shekara ashirin da doriya ba kwana ashirin bane, ka kyale ta dan Allah."
"Shikenan."
Ya koma ya zauna, kasan zuciyar shi farin ciki ne dan shima yana bukatar hakan, yana so ya nuna mata gatan data rasa, ya sa mata sabo dashi kafin ta koma wajen Farouk din.
Ita dai Mummy bata ce komai akai ba, ta umarci Anty Safiyya, Ja'afar da Farouk da su tashi su tafi tun da an kare maganar, zancen zuwa kotu kuwa ita ta yafe, bata bukatar komai idan aka tsaya a haka ma Adam yaga ishara.
Farouk be so ba, yaso ko ganin Aminatu ne yayi kafin su tafi, amma baya so Mummy ta ga kamar baya damuwa da ita da lamarin ta, haka suka dunguma har Uncle Aliiyu da yaransu suka bita zuwa Kadunan.
Har sun dau hanya uncle Aliyu ya dakatar dasu yace yayi mantuwa, Iman yaje ya dauko ya fito da ita, da ido Mummy ta dinga bin sa har ya ƙaraso ya bude saitin da take zaune a mota ya mika mata ita
"Ya kamata kiga jikata kafin mu tafi."
Kallon Iman din tayi kai tsaye ta gane wace, duban Farouk tayi daya gaza boye farin cikin sa tace
"Son?"
"Yes Mum."
Murmushi tayi ta kura wa yarinyar ido tana jin kaunar ta a cikin zuciyar ta.
"Very cute, Masha Allah."
"Uncle Aliyu ka bar min ita mana." Tace tana murmushi
"Anty ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, sai dai da kyar idan Hajiya Fatima zata bar miki dan naga take taken ta."
"Waye yafi kusa da ita?" Tace tana bata fuska.
"Kece."
"Shikenan na kwace ta, hakan zai sa tayi gaggawar dawowa da Son matar sa, dan nagano ta so take ta wahalar min da shi."
Dariya suka sa baki daya, har Iman din da zuwa yanzu ta saba dasu.
"Zaki bini na baki chocolate?"
Tace tana shafa kanta, make kafada tayi tana kallon Farouk
"Tare zamu tafi na riga na tambayi Ummin ki kinji dota."
Yace dan yasan me take so tace masa, a tambayi Ummin ta, bata kara magana ba ta kwanta a jikin Mummyn, dadi ne ya lullube ta, har bata san sanda ta rungume ta a jikin ta ba.
Dole Uncle Aliiyu ya koma ya sanar wa Daddy sun tafi da Iman kafin ya dawo su dauki hanya.*DG*
*43*
©Hafsat Rano
★★★★★★
Shiga daki sukayi, Aminatu ta zauna a gefen gadon tana sunkuyar da kanta, zama Ammin tayi tana daukar wayar ta, mita take tayi tun dazu, hakan ba karamin dad'i yake wa Aminatu ba, wai itace yau ta samu me tsaya mata, lallai uwa me dad'i, tana jin Ammin tana ta waya da yan uwan ta na jiki, tana sanar dasu taron da ta shirya na murnar dawowar Aminatun wanda sai a lokacin Aminatun ke samun labari, ita dai bata ce komai ba har ta gama ta ajiye wayar kafin ta zauna gefen ta
"Kinsan dalilin da yasa naki amincewa da komawar ki? Ba wai bana son Farouk bane,ina tunanin nafi kowa son ki dashi, sai dai ba zan yarda da abinda ya faru a baya ba, dole ne yanzu ya zama kamar sanda zan aurar dake na farko, sai na gyara ki, yadda babu raini tsakanin ki da miji ko kuma uwar miji, zaki fito a cikakkiyar ya ga Marwan Dikko, zan shirya miki gagarumin bikin da kowanne lungu da sako na kasar nan zai dauka, ina fatan kin fahimce ni?"
"Na fahimta Ammi."
"Good."
Tace tana tashi,
"Ammi..." Ta dakatar da ita
"Umm??"
"Ina so muje Shagari dukkan mu, nayi wa kaina alkawarin ba zanje ba har sai sanda na hadu da iyaye na."
"Yaushe kike so muje? Duk da nasan dole binciken da za'a yi yabi ta kansu, dole ne za'a kama ita matar da ta rike ki, da duk wanda yake da hannu, amma dole sai zuwa sanda aka tura case ɗin Adam ɗin kotu, so yanzu kike so muje ko bayan nan?"
"Yanzu dai."
"Shikenan, bayan taron sai muje, ina da bukatar ganin ta nima."
****
Kamal na kwance duk da yaji dadin yadda abubuwan suka kasance, amma ya kasa manta fuskar Inno sanda ta biyo shi tana kiran shi, dukkan motsin da zai yi sai ya tuna, ransa babu dad'i amma kuma kasan zuciyar shi na kwadaita masa sake ganin ta. Shigowar Ammi yasa ya saita kansa ya k'ak'alo murmushi.
"Ya jikin naka?" Tace tana zama a gefen sa
"Da sauki Ammi."
"Sannu."
"Ina ganin zamu je chan garin, nan da kwana uku, zuwa lokacin ka kara samun karfin jikin ka, sannan akwai taron da za'a yi gobe a gidan nan na murnar dawowar Aminatu."
"Owk Allah ya kaimu."
"Amin." Tace tana mik'ewa.
"Ammi..."
"Kana bukatar wani abu ne?"
"A ah, babu komai."
Yace yana had'iye wani abu, dawowa tayi ta zauna tana duban sa
"Menene?"
"Nagode Allah ya saka da Alkhairi Ammi, duk da kun gano bani da wata alaƙa daku amma baku chanja min ba, kun cigaba da kula dani kamar..."
"Ya isa!" Ta daka mishi tsawa
"Yanzu Kamal ni kake wa godiya? Har kake cewa baka da alaƙa dani? Kasan me kake cewa kuwa? Haihuwar kace kawai banyi ba amma baka da maraba da dan dana haifa da cikina, ni nan na shayar dakai, nayi maka tarbiyya, duk wani abu tsakanin uwa da d'a Kamal kai nayi wa, ko musulunci ya tabbatar da ni ɗin mahaifiyar kace ta shayarwa, saboda haka ka zama muharramina, kai dana ne, har duniya ta nade ba zaka daina amsa sunana a matsayin mahaifiyar ka ba."
Tashi tayi ta fice daga dakin da sauri dan bata so tayi kuka a gaban sa, kukan ya saka shima, dan ba karamin tabashi maganganun sukayi ba, da yasan haka zai bata mata rai da be ma fara ba.
****
Da daddare sai ga Anas ya iso, tana ganin kiran sa ta sanar wa Ammin, shigo dashi falon tasa akayi, ta fita da kanta wajen sa, cike da girmamawa ya gaishe ta, ta amsa a sake dan tun kafin zuwan sa take daukin haduwa dashi, bayanin kanta tayi masa a matsayin mahaifiyar Aminatu, wanda hakan ya ɗan sashi zama shock, ta lura da hakan sai kawai tayi murmushi