Showing 54001 words to 57000 words out of 112633 words

Chapter 19 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt

07 Aug 2025

7435

gidan nan ma baki daya duk babu dadi ayi ta yimin iyaka da abinda ya zama mallaki na."

"Yo dama uwar ka ai ba sonka take ba, ka rabu dasu duk zanyi maganin su dan uban su, kaji shalele na, ka daure ka fara chan din tunda ya kafe."

"Old Woman..." Ya kafe ta da ido

"Wai bake kika haifi Dad bane?"

"Nice mana, me ka gani."

"Kawai ki tilasta masa kice kin gama magana ya kaini waje nayi karatu."

"Ba za'a kai ka ba, dan gidan ku."

Da sauri ya mike yana sosa kai, yayi wuri wuri da ido yana neman hanyar fecewa daga falon, matsowa yayi har gaban sa kafin ya sakar mishi rankwashi a tsakiyar kai, da karfi yasa ka ihu kamar karamin yaro, hakan yasa Hajiya Turai yin salati tana tafa hannu

"Karka kashe min shi, rankwashin nan sai ya juya masa kwakwalwa ai."

Kunkuni ya saka ya bar falon da sauri.

"Hajiya duk ke kike biye masa wallahi, yanzu Kamal shekara nawa yake? Amma bai san abinda ya dace da wanda be dace ba, gashi kinga ni shekaru na kara hawa suke, yaushe zai yi hankalin da zai kular min da dukiya? Ya kula da mahaifiyar sa dani? Lokaci fa tafiya yake."

"Ka kaishi wajen daya ke kulafuci mana, chan anfi saurin karatun nan danan sai yayi ya gama ya dawo."

Girgiza kansa yayi

"Hajiya dan Allah, mu bar wannan maganar, Kamal zan dauka na kai waje? A gaban mu ma ya yakare? No bazan taba wannan gangancin ba."

Juya masa baya tayi, tana magana kasa-kasa, sallama yayi mata ya fita dan yasan idan ya biye mata rigimar da zata sashi a gaba tayi ba kadan bace. Bayan motar sa ya fada yana addu'ar shiriya ga tilon dan nasa, duk kuwa da yasan laifin na mahaifiyar sa ne, taki barin su sam suyi masa nagartacciyar tarbiyyar data dace dashi.

Niko Nace hmm, Allah sarki su malam Kamalu an zake da yawa😂😂

***
Gaisuwa ta musamman gareki Oum Iman me comment da readmore😍😍 Allah ya bar kauna. Muna gani kuma muna godia.

Sannu sannu dai bata hana zuwa sai dai a dade baje ba, kuyi hakuri a hankali zamu warware komai, *Daurin Goro* labari ne me rassa da zaruruka da yawa. A hankali zamu kawo inda muke son zuwa.🙋

Comments dinku na kara mana kwarin guiwa sosai, mungode.: DG
             23

★★★
Tun daga kan zauren gidan zaka tabbatar da san samu chanji ta kowanne bangare, tana zaune gaban kofar dakin ta, ta yi tagumi tana tunanin rayuwar baki daya, idan aka ce mata komai zai chanja rayuwar ta juya mata baya cikin dan kankanin lokaci zata musa.
Tun bayan fitowar su daga police station bata sake samun nutsuwa ba, magana ta zagaye kowanne lungu da sako na kauyen nasu, bata da damar fita nan da chan, sai kaji ana yar mata da magana. Dalilin haka ta hana kanta fita, gashi komai ya tsaya mata na abinda ya danganci sana'ar ta.
Jikin Baba ya sake matsawa sosai, haka dai suke jinyarsa ita da yalwati duk da karfin jinyar ma ta Yalwatin ce, ita kanta tana bukatar a kula da ita dan kuwa ba isashiyar lafiyar ce da ita ba.
Karime ce ke dan lekowa lokaci zuwa lokaci tana duba su, ta tafi, da haka ake rayuwar cikin kankanin lokaci dan jarin nata ya kare sai yan dabbobin da suka rage mata. Tabbas ko a haka aka barta ta gane kuskurenta, tana ji a ranta bata kyauta wa Aminatu ba, duk da a tunanin ta ta aikata hakan ne don taimaka mata, amma tabbbas tayi kuskure, ta ina ma zata fara neman ta, ta haifi abinda yake cikin ta ko yaya! Wannan tunanin biyu ke sata sake shiga cikin matsanancin tashin hankali.
Cikin dare jikin Baba ya sake rikicewa, babu wanda ya runtsa a gidan, wani irin abu yake fitar wa daga bakin sa, ala tilis da safe suka nufi asibiti bayan ta barwa Nura sallawun daukar guda cikin dabbobin ta ya kai kasuwa wajen mahauta su siya saboda kudin asibitin da za'a bukata.
Ba'a karbe shi ba, har sai da Nuran ya kawo kudin,sannan aka bude masa file aka karbe shi, kafin kuma asan abun da za'a bukata a gaba.

***
Duk hanyar da take tunanin zata same shi ta bi, tayi dukkan kokarin ta amma babu wani labari. Sosai zuciya da ruhin ta suka kosa da abubuwan, tana bukatar wanda zata fadawa damuwar ta, tun bayan rabuwar su da Daddy ta zama mace me matukar tsauri, bata barin kowa ya rabe ta, bata sabo da kowa balle ta saki jiki , agogo ta mayar da kanta,ko yaushe cikin aiki take ba dare ba rana, duk don son ganin ta manta komai. Sai dai a halin yanzu ta karaya, zuciyar ta tayi laushi ainun, tana son wani a kusa da ita, da zai jibanci al'amuran ta, ya saurari kukan ta, amma waye? Bata da kowa a halin yanzu sai babbar yayarsu data rage dake zaune a cikin garin na Kaduna, wadda itama girma da dawainiyar yaya da jikokinta kadai ya ishe ta, ranar data bar wajen meeting dinsu chan ta nufa, da niyyar ta sanar da ita kukan ta, sai kuma ta tarar da ita ma da tata matsalar, dole ta hakura ta boye natan har ta baro gidan.
Kwanan ta kusan hudu bata sake leka waje ba, jinya take sosai, jiki da ruhi, komai baya mata dadi, tana jin ta kamar a yanzu komai yake faruwa, duk abubuwan data shafe su a babin rayuwar ta a baya, yanzu sun dawo mata suna mata amsa kuwwa a kanta.
Rashin uzurin Daddy da yadda yake rufe idon sa ya kasa gano gaskiya komai,ya sake jefa rayuwar d'an su a wani hali. Ba zata taba bari rayuwar dan nata ta salwanta kamar yadda komai ya chanja mata a rana daya tak!

****
Bai taba tunanin zai shiga damuwa kamar haka ba, sai gashi komai ya kakare masa, tafiyar Dadah ta kara sashi a wani yanayi, maganganun ta ne ke kai kawo a cikin ransa, babu abu daya data fada masa da bai zama gaskiya ba, sai gashi yana jin son sanin abinda ya faru a bayan, duk da ya rufe babin nan a rayuwar sa, amma kuma wani bangare na zuciyar sa na son sanin komai, watakila hakan zai taimaka wajen samun haske a wannan sabuwar matsalar data same su.
Ita kadai ce zata sanar dashi komai, sai dai yasan ba zata taba sauraran sa ba, duk da kasan zuciyar shi na nan akan bakan sa na abinda ya aikata mata shine daidai da ita, amma kuma yana jin kamar bai mata adalci ba, kamar yayi tsauri wajen yanke mata hukunci, duk da abu ne daya shafi mahaifiyar sa da d'an uwan sa shakikinsa, amma kuma da ya bata dama, yaji wani bangare na labarin ta, sai dai kash, bai yi hakan ba, a lokacin ma sam baijin zai iya bata wannan damar, yadda zuciya da ruhin sa suka azabtu da abinda ta aikata masa. Bata kyauta masa ba, bata kyauta ba!
Mirginawa yayi yana gyara kwanciyar sa, zai dora tunanin sa Mama ta turo kofar dauke da wayoyin sa da ya baro su yashe a saman teburin falon sa. Mika masa tayi ya duba kiran, misscals ɗin MD ne, shaf ya manta sunyi zasu hadu a yau din, tashi yayi ya shirya kansa ya sauya shigar sa daga doguwar jallabiya zuwa farar shadda da hula ya fita. Kai tsaye gidan sa ya nufa, ya shiga ya nufi babban Falon sa da yake ajiye duk wani bako mai muhimmanci a wajen sa.



★★★

Rayuwa ta a gidan bayin Allah nan rayuwa ce me cike da kyautatawa da mutuntawa. Na gama gane halin kowa a gidan naci kuma alwashin zama da su da halin su, zuwa ranar da zamu rabu, tunda nasan ba zamu taba dawwama a haka ba, dole watarana xan tafi.
Iman bata da matsalar komai, girma da wayo kawai take karawa abin ta, duk wani abinda za'a bukata nata Anas na samar mata shi tun kafin a nema. Kunsan ance me d'a wawa, hakan ya kara mishi matsayi babba a zuciya ta, ina jin sa kamar wani uba ko babban wa a garemu, ina jin sa kamar wanda aka aiko shi dan ya taimaka wa maraicin mu nida ita a lokacin da muka rasa madafa.
Ina zaune ina ninke kayan ta da na wanke da rana Ramlah ta shigo a gajiya ta fada saman gado tana sakin nishin gajiya

"Makaranta akwai wahala wallahi."

"Bayan wuya?" Nace mata ina dariya

"Kafin dadin fa? Aiko kinga naji labarin ance Post Utme ta fito fa."

"Innalillah, kinji yadda naji, Allah sa muna da rabo, karatun nan shine kadai hope d'ina."

Na faɗa a sanyaye,

"In Sha Allah zaki samu, akwai abokin Baban mu wani professor kuma nasan Ya Anas yayi masa magana, nima dan cut-off mark d'ina na jamb be kai na buk ba shiyasa na chanja northwest."

"Toh Allah yasa,kinga har naji kamar bani da lafiya wallahi."

"Allah sa muji Alkhairi."

Amin nace ina cigaba da aikin da nake, sauya kayan jikin ta tayi ta nufi Kitchen dan samo abinda zata ci.
Da daddare kamar yadda muka tsara Ramlah na koya min karatun daya shafi addini, ba laifi ina karuwa sosai da ita, duk abinda kake da interest akai kana tsayawa ka koya sosai, hakan ce ta faru dani, zama na dasu na gane bansan komai daya danganci addinin ba, daga karatun sallah sai dan abinda ba za'a rasa ba, bana mantawa a makaranta na koyi yadda zan kula da kaina yayin lokacin al'adah. Shiyasa na dage nake takura ta a kullum tana karamin sani a abinda ya shige min duhu.
Da hannun sa rataye a bayansa abinda ya zama masa dabi'a ya shigo dakin namu da sallama, kusan sati guda kenan baya zama sosai a gidan aiki ya masa yawa kamar yadda naji Ramlah na fada, daina karatun mukayi muka maida hankalin mu wajen sa, be ƙaraso ciki ba ya tsaya yana kallon mu, a tare muka hada baki muka gaishe shi, ya amsa a sake kafin yace

"Congratulations, sai jiran admission kinci postutme."

"Alhamdulillah." Na shiga jerantawa, cikin tsananin farin ciki na hau yi masa godiya, rana ta farko dana ga babu wannan cunkushewar a fuskar sa, a sake yake amsa min yana yi yana min wani kallo.
Yana fita muka rufe karatun muka yi dakin Hajiya, dan sanar mata, tayi murna sosai ta saka albarka. Daren ranar ban iya runtsawa ba, tunanin Farouk da yadda zaiji idan yana tare dani kawai nake, tun bayan tsawon lokaci yau naji alamun ina da rabo a rayuwar nan.
Haka na tashi da safe cike da farin ciki da walwala, tsokana ta su Hajiya da Altine sukayi tayi ina dariya. Da wuri muka gama aikin mu da zamuyi ranar na bi Altine kitchen ina kara koyon abubuwan da ban taba sanin ma suna existing ba sai yanzun.
Cikin hukuncin Allah Admission ya fito, sunana na jerin sunayen farko da suka samu, nayi farin ciki ranar nayi kuka sosai na kuma godewa Allah, saboda nasan ba wayo na bane ko dabara ta. Tun daga lokacin na tattara dukkAn damuwa ta na watsa ta a bayana na shiga shirye shiryen sabuwar rayuwar makaranta.
Yadda Ya Anas ya soma chanja min ne ya shiga daure min kai, duk lokacin da yake gida ya kan tabbata da ina falon a zaune, duk hirar da za'a yi sai ya sako ni a ciki, ta karfi da yaji yake kokarin ganin sai na sake dashi, ina lura da yanayin Hajiya kamar bata son hakan, duk sanda zai min wata magana sai ta kawo abinda zai sauya akalar maganar zuwa wata daban da bata shafe ni ba. A haka aka fara registration da screening, shine dai wannan karon ma ya shige min gaba akan komai, sannan duk kudin da aka bukata shi ne ya bada su, duk da naso yin wani abun da kaina sai dai sanin halin sa yasa na hakura na zuba masa ido.
Kwana wajen uku sannan na samu nayi screening din, na gama ina zaune karkashin wata bishiya me dauke da zagayayyun kujeru naji an zauna a gefe na, dagowa nayi da nufin ganin waye, hannu yasa ya nuna ni cike da mamaki yace

"You!" Sai nayi kamar ban gane shi ba na juya kaina gefe. Gefen dana koma ya dawo ya sake zama yana leken fuska ta.

"Ji mana."

"Wa kake nema ne Please?" Na watsa mishi wani kallo, dan tsaf na karance shi dan rainin wayo ne na ajin karshe, sosa kansa yayi kafin yace

"Shit! Kin iya rainin wayo wannan beb ɗin wallahi, kece dai ta ranar Exams din nan na gane ki."

"And so?"

"And so? And so?"

Ya shiga nanatawa kamar karatu , sai kuma ya bigi gefen kujerar yana fitar da yar karamar iska daga bakin sa, sai kuma yayi murmushi m d'an sauti

"Can we be friends?" Yace yana miko min hannun sa,bin hannun nayi da kallo, kafin na girgiza kaina ina sake matsawa kadan

"Bana ƙawance da maza, infact ban ma tab'a ganin ka ba sai yanzu, sai kawai na saki jiki da kai?"

"Kaji matsalar yan matan garin nan kenan, kauyancin masifa. Go to hell!!."

Yace yana mik'ewa, da ido na rakashi har ya bar wajen cikin tafiyar sa ta ya'yan da suka jiku da hutu, murmushi na saki kadan ina mamakin sa. Gefe na kalla ina sake sakin murmushi, ido na ya sauka a cikin na Ya Anas, yana tsaye ya harde hannun sa, fuskar nan tasa a gimtse, da sauri na dauki tarkacen kaya na na nufi wajen sa, bansan tsawon lokacin daya dauka a wajen ba, ina karasawa yaja dan karamin tsaki yayi gaba, na bishi.
Tada motar yayi muka fita daga makarantar, gefen window nake kallo ina ganin yanayin garin, tsaki yake tayi tun da muka fito, ban kulashi ba, haka ban kalli inda yake ba ma balle na san halin da fuskar sa take ciki. Murya a cunkushe ya soma magana

"Idan har kinsan irin wannan ƙananan yaran zaki tsaya kulawa ba karatu ba, sai ki sanar dani tun farko na daina wahalar da kaina."

Juyowa nayi da mamaki na kalle shi, idon sa na kan titi ya hade girar sama da ta k'asa, sai nayi shiru kawai na maida kaina waje ina mamakin fushin sa. Har muka isa gida be sake magana ba, fita nayi na barshi a motar don naga bashi da niyyar fitowa.
Ina shiga na tarar da Altine na ta faman zagaye goye da iman, murmushi nayi na gaishe ta, ba karamin girman matar nake gani ba, kunto min ita tayi na karbe ta na shige ciki.
Dakin Hajiya na leka, na sanar da ita mun dawo, kadaran kadahan ta amsa ta cigaba da abinda take, kwana biyu akwai chanji sosai a yadda take min, sai dai na dau hakan a matsayin wani ɓangare na dan adam, ba lallai ne koyaushe ya zama kamar yadda ka san shi ba, idan ma babu wata matsala ai akwai lalura, zata iya yiwuwa bata jin dadi ne. Sai ban wani damu ba, na cigaba da al'amura na yadda na saba su.

***
*Bayan wata biyu*

Cikin nasara na soma zuwa makaranta, bani da matsala da iman dan lokacin ta fara shan ceareal, wajen Altine nake barin ta bayan na tabbatar da tasha ta koshi, sauƙin ta ma babu ranar da muke wuni a makarantar, duk inda azahar tayi mun dawo, hakan shi yasa nake jin dadin karatun ina kokarin ganin na samu abinda naje nema.
Bangaren Hajiya bani da wata matsala tun bayan rage shige min ɗin da Anas yake, sai ta sake muka koma kamar da, duk ban kawo komai ba.
Ranar wata talata na sauka a titi na shigo layin namu ina tafiya a nutse, nazo daidai wajen wani me dan kiaosk na saida katin waya naji maganar ta, bazan taba mantawa da muryar ba,muryar da zan iya cewa na daya daga cikin abinda ke makale a raina na yarinta ta, da sauri na isa wajen, ido bude nake kallon ta da tsantsar mamaki, idan har idona ba gizo yake min ba, kunnuwa na ba karya suke min ba,toh tabbas Amal ce. A bayan ta na tsaya cikin tsananin farin ciki ina jiran su gama, juyowa tayi da nufin barin wajen, taci karo dani, da wani irin tashin hankali ta ja baya, kamar zata koma cikin kiaosk ɗin

"Amal." Na kira sunan ta cike da farin ciki sai naga ta hau jujjuyawa kamar me neman wani abu

"Amal baki gane ni ba? Aminatu ce fa."

Gaba tayi da sauri har kamar zata fadi, nabi ta da sauri na cimmata ina kwala kiran sunan ta, ja tayi ta tsaya tana juyowa a fusace tace

"Wai lafiya kike bina?"

"Nice fa Amal, baki gane ni ba?"

"Na gane ki, sai akayi yaya?"

Washe baki na nayi ina tunanin matsala ta tazo karshe nace

"Nasan dama zaki gane ni ai, ina su Dadah da Ya Farouk, Allah Nagode ma daka hada mu."

Dariya ta tuntsire da, kafin ta hade fuskar ta cikin isa tace

"Ke wai har yanzu baki manta da su ba, bayan sun manta da kina existing a duniyar nan, kinga karki takura min dan Allah, kar ma ki kuma nuna kinsan ni wallahi, ke da su kuma sai dai idan ana haduwa a lahira."

"Me kike cewa Amal, kina nufin Ya Farouk ya manta dani, Dadah ma haka, idan kowa zai manta dani nasan su ba zasu taba mantawa dani ba,dan Allah ina Ya Farouk ina son haduwa dashi ko dan yar sa dake tsakaninmu?"

Na fada murya ta na rawa, daga min kai tayi, sosai naga yanayin fuskar ta ya sake sauyawa, ambaton yar sa da nayi, ja baya tayi

"Ya manta dake mana, tun da har ya aure ni, nice matar sa a yanzu saboda haka bana bukatar ki kusa da mijina da yan'uwa na, batun ya kuwa ke da kanki kinsan ya ƙaryata tun lokacin rabuwar ku, sai kije can ki nemi uban yar ki, idan kuma shegiya ce sai mu sani."

Jiri ne ya soma dauka ta, na kalle ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login