Showing 33001 words to 36000 words out of 112633 words
Chapter 12 - DAURIN GORO COMPLET book 1 by Hafsat Rano.txt
Inno ce ta daga labule tace ya shigo, a gefen tabarmar da Dada ke kai ya zauna yana gaida Inno din, amsawa tayi kafin Dadah tace
"Kana da hoton Abidah a wayar ka ko?"
"Ina dashi."
"Yawwa mu gani."
Budowa yayi ya mika mata, ta kalla ta mika wa inno,
"Wannan fa?"
Girgiza kai Inno tayi tace
"Gaskiya ba ita bace."
"Owk shikenan Ja'afar, zaka iya tafiya."
Tashi yayi ya fita, Dadah ta cigaba da nuna wa Inno dukkan hotunan data ke tunani, amma sam Inno bata ga matar ba, a dole Dadah ta hakura da tunani shin wacece? Ganin ta kasa gane wacece yasa ta yi mana sallama bayan ta sa yara sun shigo da kayan data kawo min ta tafi, da nufin zata dawo gobe idan Allah ya kaimu. Har waje na rakata ina jin kamar na bita, sai dai nasan hakan ba mai yiwu wa bane.
***
Sosai Dadah ta shiga damuwa, babu abinda yafi daga mata hankali sama da abubuwan da takardun nan guda biyu suka kunsa, abubuwa biyu dake da alaƙa da juna da siga daban, idan har ya tabbata Farouk shine yayi sakin ya kenan za'a yi? Bin Ja'afar tayi da ido har ya karasa shigowa cikin falon.
"Wash." Yace yana fadawa saman kujerar.
"Daga ina kake haka kai kuma?"
"Wallahi Dadah zagaye nayi a gonar nan, sai naga girman ta ya karu sosai fiye da dah, ko dan na jima banzo bane ba oho."
"Sai dai hakan, amma ai yadda take haka take, kawai son jikine irin naka."
"Yawwa kai, nace yaushe rabon ka da Babana ne wai?"
"Wai ya Farouk?"
"Bansani ba."
"Sorry, a satin nan ma munyi magana ai."
"Da gaske ko da wasa?"
"Wallahi, kinsan baya kasar sannan inda yake babu wani network me kyau, nima Amal ce ta bani number tasa lokacin da Mummy ta kirani akan bata samun shi a waya, shine na kirashi, wajen kwana huɗu ma ina gwada kiran kafin ta shiga."
"Ina number, maza bani ita."
"Owk bari na dauko wayata a ciki na barta."
Mik'ewa sukayi a tare ya nufi dakin sa, a tsaye Dadah take har ya dauko ya dawo, hannun ta rike da wayar ta. Number ya karanto mata ta saka sannan tayi dialing, bugu daya ta shiga, zama tayi da sauri tana saka ta a handfree, sai dai har ta gama ringing din bai daga ba, cigaba tayi da kira, babu alamun za'a daga ɗin, haka ta hakura ta bari anjima ta sake gwadawa.
"Be d'aga ba."
"Kila baya kusa ne, idan ya gani zai kira nasan."
"Ina ita Abidar take, tana Kaduna ne ko Abuja?"
"Wai Mummy, ina ga tana Lagos, yanzu tafi zama a can ai saboda bussiness ɗin nata yafi a chan haka."
"'Owk yayi, ka gwada kira min shi zuwa anjima idan ya dauka ka haɗa ni dashi."
"Ok Tam, bari na shiga na huta."
Barin falon yayi itama ta wuce dakin ta tana samun magana da Farouk din kafin wayewar gari. Tun tana saka ran zai kira har ta hakura ta kwanta, da safe wajen karfe goma Daddy ya iso, dama shi akwai shi da sammako saboda yanayin abubuwan nasa, zuwa sha-daya suka isa gidan Maigari, ciki maigari ya shiga dasu ya tura kiran su Inno. Lokacin ina zaune muna yar hira da Karime sakon kiran yazo, Hjabi na kawai na dora a saman kayan jiki na muna tafi gabana na ta faduwa. Cikin gidan muka shiga, yanayin takalman da na gani a kofar dakin tasa jikina ya ɗan soma rawa, rike ni Inno tayi muka shiga da sallama, duk suka zubo mana ido, a darare na zauna gefen Inno kaina a kasa na gaishe su, sannan suka gaisa da Kawu kanin Baba da Inno. Kamar wanchan karon yanzu ma maigari ne ya sake sabon jawabi, sannan ya bawa Daddy damar jin ta bakin sa. Wayar Dadah ce ta dau burari alamun kira ya shigo, dan dakatawa Daddy yayi ta ciro wayar, da sauri ta furta
"Alhamdulillah."
Ta daga ta saka ta a handfree
"Assalamu alaikum."
Muryar sa ta daki dodan kunne na, wani irin zabura nayi daga zaune, kowa ya zuba wa wayar ido kamar shi din ne a wajen. Daddy ne ya mika hannu ya karbi wayar
"Kana jina?"
"Daddy barka da warhaka, ina kwana?"
"Lafiya, kana jina, ba wani dogon bayani muke bukata ba, ina fatan kana hayyacin ka dai ko?"
"Eh daddy, a hayyacina nake."
"Good, menene hakikanin gaskiyar takardar sakin daka aiko wa matar ka?"
Shiru yayi, kamar baya kan layin, har sai da Daddy yace
"Kaji abinda nace ko?"
"Naji Daddy."
"Toh ina jinka, me ya faru ka sake ta? Wani laifin tayi maka ne ko menene?"
Kai tsaye yace
"Babu laifin komai, kawai zaman mu ne ya kare."
Da sauri na dago, Ina son sake tabbatar wa kaina wannan ba Farouk d'ina bane.
"Haka kawai kenan ka sake ta ba tare da laifin komai ba ko me?"
"Eh haka nan ne, babu laifin da tayi mun."
Share zufa naga Dadah nayi, Inno kuwa kamar bata wajen, kuma baka isa ka gane yanayin da take ciki ba, ni kuwa sai naji kamar yanzu ne komai yake faruwa, jikina har rawa yake, na kasa yarda da abinda kunnuwa na ke jiye min, ina kallo Dadah ta karbi wayar cikin bacin rai tace
"Babana kaine kuwa? Kasan me kake cewa? Kana nufin duk abinda ke jikin takardar kaine ka rubuta shi? Kuma shine gaskiyar abinda yake faruwa?"
Babu ko digon tsoro balle damuwa a cikin muryar sa, kai tsaye yace
"Ni ne da kaina, kuma duk abinda ke rubuce a ciki shine gaskiyar magana, kuyi hakuri idan na bata muku, Allah ya huci zuciyar kowa."
Kafin ta samu damar sake wata magana kiran ya katse, da sauri tayi kokarin sake kira Daddy ya dakatar da ita.
"Karki kirashi Dadah, barshi kawai, ni ya wulakanta ya nunawa duniya ban isa dashi ba, babu komai amma.."
"Kayi hakuri Alhaji, yaran yanzu ne sai addu'a, idan ka biye tasu sai kayi musu mugun baki."
Mai gari ya katse shi, sannan ya maida kallon sa wajen da muke zaune
"Toh kun ji dai daga bakin yaron, duk da dukkannin mu babu wanda zancen nasa yayi wa dadi, amma dole haka zamu hakura, aure ya riga ya kare, dama shi raine dashi, idan kwanan sa ya kare ko ana so ko ba'a so dole a hakura."
"Amma ba wai na katse ka bane, yarinyar nan fa tana dauke da juna biyu, ya kamata a duba lamarin nan."
Kawu yace yana duban maigari da Daddy,
"Juna biyu !" Suka hada baki a tare cikin tsananin mamaki
"Tabbas tana dauke da juna biyu, ni da kaina naga sakamakon gwajin da akayi mata."
A cewar Dadah tana duban Daddy.
"Amma shine yaron nan zai maida mu yan iska? Lallai ma wallahi, dani yake magana."
Yayi maganar a fusace
"Mubi komai a sannu Alhaji, idan yaso sai a sake tuntubar shi yaron kan maganar cikin."
A cewar maigari.
"Babu bukatar hakan dan yaro ya riga ya nuna baro-baro babu wani abu da ya hada shi da ita, dan haka magana ta kare."
Duk muka juyo da sauri, Mummy ce tana tsaye tayi kyau ainun cikin shigar alfarma, kallon juna sukayi ita da Dadah, kafin cikin bacin rai Daddy yace
"Me kike yi anan Abidah?"
A gadarance tace
"Abinda ya kawo ka, shi ya kawo ni,kasan dai ina da hakki akan Farouk ko? Wanchan lokacin na kyale ka da kayi kokarin bata min rayuwar yaro, akayi masa sharrin da kai kanka kasan ba shine ya aikata ba. Shine yanzu za'a sake ruguza min rayuwar sa bayan Allah ya taimake ni ya gane gaskiya, naji komai a wajen Ja'afar tun ranar da abin ya faru, har zuwa zaman da zakuyi anan ɗin, dalilin zuwa na kenan saboda na karba wa d'ana yanci."
"Danki? Ashe dama kina da d'a?"
"Kafi kowa sani ai, bani da lokacin amsa maka wannan tambayar, maganar d'ana nazo, babu kuma uban da ya isa ya tilasta masa aikata abinda beyi niyya ba."
Kasa magana Daddy yayi saboda tsananin kunyar data rufe shi, kasa yayi da kansa kawai yana jin kamar kasa ta tsage ya shige, jawabi ta shiga korawa maigari, a karshe tace Farouk ba zai karbi cikin jikina ba dan ba nashi bane. Tun da ake maganganun nan jikina yake rawa kamar mazari, tuni zuciya ta ta kekashe, hawayen dake faman kai kawo a saman fuskata ya bushe, cikin dakiya na tashi, na isa tsakiyar wajen, hannu na biyu na hada waje daya cikin wani irin yanayi nace
"Ina rokon duk wanda yake wajen nan, da yayi hakuri, da abinda yake faruwa, ni kaina bansan menene matsalar ba, sannan ina neman wa Ya Farouk afwa wajen ku iyayensa, tabbas bashi da laifi ko daya a cikin duk wani abu da ake tuhumar sa, hasalima shi taimako na yayi. Daga rana irin ta yau na bar maganar nan, zan cigaba da rayuwa ta a matsayin wadda bata taba sanin shi ba, zan manta dashi, zan cigaba da rainon abinda ke cikina, har zuwa ranar da zai zo duniya, ina fatan hakan ya faranta wa kowa."
Ina kaiwa nan na juya da sauri, zuciya ta na tafasa na bar dakin, ina ji suna kwala min kira, ban saurara ba, dan bana jin zan iya sauraron duk wani abu da zasu ce min, maganar da akayi da ya Farouk a waya kadai ta isheni, bana bukatar jin sauran wani bayani, a yau na tabbatar da na rasa shi, rashi na har abadah, zan sake sabuwar rayuwa, duk da bazan ce zan manta dashi a rayuwa ta ba, amma tabbas zan ajiye dukkan shafukan rayuwar mu tare a baya, zan bude sabon shafin rayuwar da bani da masaniyar in da zata kaini.
_"Aminatu ina so kiyi karatu, ina so ki zama abar alfahari sanda zaki sadu da sanyin idaniyar ki."_
Wadannan sune maganganun sa a kullum gareni, wanda bani da masaniyar hakikanin abinda suke nufi, sai dai yau nayi wa kaina alkawarin, zan dauke su a matsayin wani tsani na matakin rayuwar da zan shiga anan gaba.
Hanya kawai nake haɗawa da taimakon Allah na isa gida, da sauri Karime ta tare ni, tana kokarin rikeni na raba ta gefen ta, na shiga daki na hada kaina da guiwa ta cikin rashin sanin makomata. A kaina tazo ta tsaya tana min magiyar na sanar da ita abinda yake faruwa, ban iya ce mata kala ba, har ta gaji ta samu gefe na ta zauna tana rafka tagumi.
A tare suka shigo gidan, kai tsaye dakin Inno suka shigo, Dadah ta ƙaraso gareni tana daga ni.
"Aminatu tashi zakiyi mu tafi, mun gama magana da Maman ki, ba zan iya kyale ki ki raini cikin nan ke kadai ba, maza tashi kinji."
Janye jikina nayi a hankali na matsa gefe ina kallon ta
"Kiyi hakuri Dadah, ba zan biki ba, na gode da hallacin da kuka nuna min, sai dai na yanke shawarar nesantar duk wani abu daya danganci Ya Farouk, ina ganin hakan da zanyi shine kawai mafita a garemu, kiyi hakuri."
"Ya zaki ce haka, kina nufin kin karaya, kin hakura kenan? Ni sam ban yarda da Farouk zai aikata ba, akwai dai matsala, ki bini muje in Sha Allah zamu gani bakin zaren."
"Kiyi hakuri dan Allah, ba zan iya binki ba, hakan na iya haifar da matsala gagaruma a cikin ahlinki, sannan Mummy, ba zata taba karba ta ba, zan yi rayuwa ta, zan zauna anan, tare da yan uwa na dan Allah."
"Aminatu..."
K'asa na tsuguna ina kama kafarta
"Kiyi hakuri Dadah, kiyi hakuri."
Kuka ta saka, ba tare da tayi magana ba ta juya da sauri ta bar dakin.
"Ya Allah!" Na furta da karfi ina zama a kasa, kaina kamar zai rabe biyu saboda tsananin ciwo. Matsowa Inno tayi tana kallo na
"Kin tabbata ba zaki bita ba, zaman nan ba zai miki dadi ba, kinga yanzu da dah ba daya bace."
Girgiza kai na nayi,
"Kiyi hakuri, amma bazan bita ba."
"Shikenan, ki daina kuka kar kanki yayi ciwo, tashi ki kwanta a saman gadon, zanje na yi mata bayani yadda zata gane."
Tashi nayi jikina na rawa na hau gadon na kwanta ina lunshe ido na.
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
8/a: ©️ Hafsat Rano
15
****
Duk hidimar da ake a gidan ban mik'e daga kwanciyar da nayi ba, sake juyawa nayi na maida kaina dayan barin, daga daren jiya zuwa yau na riga na gama yanke wa kaina hukuncin da nake ganin shine zaiyi daidai da rayuwata. Tsawon lokaci na dauka Ina kwancen har lokacin da Inno ta shigo dauke da kwano, a kusa da kafata ta ajiye ta.
"Tashi maza, kici abinci sai kuje chan gidan ki dauko abinda zaki dauka."
"Toh." Nace ina tashi, ajiyar zuciya na sauke na jawo kwanon, fara fita nayi na wanke hannu na da bakina na dawo na zauna na shiga cin abincin a hankali, ina gamawa na chanja kayan jikina, na zura hijabi da takalmi na fito. Dakin Baba na shiga na gaida shi na duba jikin shi sannan muka tafi nida Yalwati. Da yake safiya ce bamu hadu da wasu mutane masu yawa ba muka isa gidan, sojoji ne tsaye a gate din, sai Ja'afar dake magana da daya daga cikin su,yana hango mu ya taho yana fad'ad'a fara'ar fuskar sa.
"Sannun ku da zuwa."
Yace yana tsayawa a gabana, sai dana dan ji wani iri dan sosai suke yanayi da Ya Farouk, dakewa nayi muga gaisa, yanayin yadda yake kallo na yasa na dan ji babu dadi, nayi kasa da kaina har muka shiga gidan ban dago ba. Daddy na zaune suna magana da Dadah muka shigo, da sauri ta mike tana riko ni fuskar ta kamar zatayi ne saboda tsananin farin cikin ganin mu
"Aminatu, kin chanja shawara ko?" .
Yadda tayi maganar cikin farin ciki yasa naji kunya, a hankali na zame jikina na tsuguna a kasa na furta
"Ina kwana Dadah?"
"Lafiya lou Aminatu, nasan dama zaki chanja shawara, Nagode sosai da kika yarda zaki bini." Sai ta maida hankalin ta kan Yalwati cikin fara'a tace
"Sannun ku da zuwa."
"Yawwa ina kwana Hajiya."
"Lafiya lou, ku zauna mana."
Zama tayi a kujerar dake hanya ni kuma na sake gyara zamana a kasan da nake.Sabuwar gaisuwa suka sake sannan suka gaisa da Daddy da ya gama waya. A hankali na dago kaina na cikin girmamawa na gaishe shi, a sake ya amsa yana nazarina. Komawa Dadah tayi ta zauna sannan tace
"Aminatu, zo matso kinji'
Jan jiki nayi na matsa gaban ta, cikin rashin sanin yadda zata dauke abin nace
"Dadah zan dau kayana ne, da abubuwan makaranta."
"Ba zaki bini ba kenan?" Tayi tambayar tana bata rai
Zanyi magana Daddy ya katse ni
"Kiyi hakuri Dadah, tabbas tana da babban uzurin ta na kin amincewa ɗin, Aminatu, kiyi hakuri kinji, kowacce rayuwa cike take da kalubale, idan kayi hakuri sai kaga kaci riba, tabbas nasan ba'a kyauta miki ba, amma bani da yadda zanyi, kiyi hakuri kinji."
Ban iya magana ba sai daga kai kawai da nake kamar kadangaruwa, nasiha ya shiga yi min sosai, sannan ya bani tabbacin duk yadda zaiyi zai nemi Farouk, yaji komai sannan magana ciki sun karba, sun tabbata bazan taba yin wani abu da zai bata sunana ba. Ɗorawa tayi
"Zanyi kokarin ganin na kula da komai naki har zuwa lokacin da zaki sauka lafiya, mun riga munyi maganar jiya. Yanzu ki cire duk wata damuwa a ranki, ki fawwala Allah komai."
"In Sha Allah, Nagode Allah ya kara girma."
Wayar sa ce tayi kara, ya mike ya bar falon, hawaye naji ya zubo min, nayi saurin maida su ina bawa kaina k'warin guiwar bazan yi kuka ba, musanman a gaban Dadah. Bata ce min kala ba, sai kawai ta maida hankalin ta wajen Yalwati tana mata yan tambayoyi. Mik'ewa nayi tsam, suka bini da ido,a hankali na nufin dakin, cikin tarardadin abinda zan tarar ɗin. Turawa nayi, kamshin turaren sa ya daki kofofin hanci na, babu abu daya na dakin daya chanja, yananan tun ranar da muka bar shi, ba tare da sanin cewa na barshi har abadah ba. Kaina ne ya hau juyawa, nayi saurin dafe wa, na shiga har haɗa duk abubuwan dana san nawa ne, cikin dan kankanin lokaci na hada komai waje daya. Kallon wardrobe d'insa nayi, zuciya ta ta kasa hakuri, hannu nasa na bud'e, babban album din sa ya fado, tsugunawa nayi na dauka a hankali na shiga budewa, daya bayan daya nake bin hotunan da kallo, kwalla na taruwa a ido na. Jin takun tafiya yasa nayi saurin tashi, na ciri guda daya na tura cikin jakata na maida sauran tare da rufe wardrobe din. Juyowa nayi da nufin tafiya muka hada ido, tana tsaye ta zuba min ido tana murmushi, murmushi me dauke da ma'anoni da yawa Dauke kaina nayi na tattare kayana zan bar dakin, ta gefen ta nazo wucewa a hankali nace
"Ina kwana?"
Bata amsa ba, dama nasan ba zata amsa din ba, sai dai har lokacin idon ta na kaina, kallon da na rasa na menene, rab'ewa nayi na wuce kawai ba tare da na sake cewa komai ba. Ina zuwa falon na tarar da Dadah, tana zaune tana juya wayar hannun ta, kasa na tsuguna cikin dakiya nace
"Na gama zan tafi Dadah." Girgiza kai naga tayi, ta miko min har karamar jakar hannu. Ajiye kayan hannu na nayi na karba ina kallon ta
"Karbi ki ajiye wajen ki, in Sha Allah zan dinga zuwa ina duba ki lokaci zuwa lokaci, ki kula da kanki kinji? Allah yana tare dake."
"Nagode sosai Dadah, bansan da wanne bakin zan gode miki ba, Ubangiji ya sake miki da mafificin Alkhairi."
Da sauri ta tashi, ta shige dakin ta ba tare da tace komai ba, jiki na a matukar sanyaye na mike, ina karewa ko ina kallo, Yalwati ta tayani daukar kayan, muka fito. Da sauri ya tare mu, ya karbi kayan hannu na har lokacin idanun sa na kaina.
"Daddy yace na mika ku saboda mutane."
Ba musu muka bi bayan sa, ya saka kayan a booth muka tafi. Har kofar gida ya kaimu, sannan ya tayamu sauke kayan yara suka dauka muka shige ciki.
Daki na wuce kai tsaye, na ajiye kayan na jawo jakar Dadah na bude, waya ce yar karama,