Showing 30001 words to 33000 words out of 262509 words

Chapter 11 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21421

ƙasa ta ce "Ina yini." Sadik da yake ta binta da kallo ya ce "Lafiya k'alau ya aiki." Neehal ta ce "Alhamdulillah." Sadik ya gyara zama cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya ne na ganki wani iri.?" Neehal ta ce "Lafiya ta k'alau." Sadik ya ce "Uhm, ko ki tambaye ni yau ina shiga.?" Neehal ta ce "Ai zan tambaye ka, dafatan dai Lafiya.?" Sadik ya ce "Lafiya lau, sha'anin aiki ne ya kawo haka." Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Sadik ya yi murmushi cikin tsokana ya ce "Fushin me ki ke yi to.?" A shagwab'e ta ce "Ni ba fushi nake ba."




"Uhm rigimar autanci ce ta motsa kenan."


Neehal ta yi murmushi saboda yanda yay maganar ya bata dariya. Hirar su suka cigaba da yi cikin nishad'i, wani irin daɗi take ji saboda ganin Sadik, cikin lokaci kaɗan ta ware suka shiga hirarsu. Sadiƙ mutum ne da ya san takan bi da duk wanda yake mu'amala da shi, mutum ne mai tsananin kirki da hak'uri, gashi da sanyi kamar ba lawyer ba, sai dai akwai kaifin tunani da saurin fahimtar abu, ga uwa uba nutsuwa da addini. Abun da yake ƙara burge Neehal da shi nasiha da faɗin gaskiya a kodayaushe, ko yaya kuka ɗan zauna dashi sai ya tunatar da kai wani abu na addini da mu'amalar rayuwa. Mama ma yaron ya na burgeta, ta yaba da hankalinsa da nutsuwarsa, shi yasa ba ta hana mu'amalar su da Neehal.




Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah, yau gashi bikin Ameen ya matso saura satittika, shirye-shiryen biki ake ba kama ƙafar yaro, ɓangaren gidan amarya da gidan Ango, ba yama kamar gidan su Amarya, dan su yanda suke tsara bikin ma sai anfi sati ana shagali, ango ne yake neman ba su cikas dan shi ya ce bashi da lokacin ɓatawa a yawon zuwa events, amarya dai ta na ta lallab'ashi a kan ya amince amma ya ƙi. Su Mama shirin su suke sosai ita da 'yan'uwanta, Ameen ya saki kuɗi an haɗa lefe na gani na faɗa, Aunty Sadiya da Aunty A'isha ne suka haɗo masa. Ƴan'uwan Dad ma masu murna da auren ba a barsu a baya ba gurin nasu shirin.








Yau Saturday Misalin ƙarfe goma na safe Neehal ta na kwance a kan gadonta ta na bacci ta ji ana tashin ta, a hankali ta buɗe idanunta dake cike da barci ta na karanta addu'ar tashi daga bacci a zuciyarta. Ameerah 'yar gidan Uncle Mahmud ta gani tsaye a kanta, yunk'urawa ta yi ta tashi zaune ta na mutsitstsika ido, Ameerah ta na murmushi ta zauna a bakin gadon ta na faɗin. "Bacci har wannan ranar Yaya Neehal." Cikin murya mai cike da bacci Neehal ta ce "Kin san jiya muka gama exam, baccin da ban yi ba ne kwana 2 saboda karatu nake ramawa, yaushe ku ka zo?." Ameerah ta ce "Yanzun nan, Mama ta ce in shigo in tashe ki." Neehal ta ce "Welcome, ke da Ammi ku ka zo.?" Ameerah ta ce "Ehh, suna falo suna kallon lefe." Neehal ta sauka daga kan gadon ta na faɗin, "Kin san nima har yau ban samu nutsuwar ganin lefen nan ba, saboda exams d'in da muke, gashi har za a kai gobe." Ameerah ta ce "Ai dama exam akwai caza wa mutum kai, Allah dai ya ba da sa'a." Neehal ta amsa da "Amin" tare da shigewa toilet.






Bayan ta shirya suka sauko ƙasa inda suka tarar da Mama,Hajiya,Ammi,Aunty Sadiya da Aunty A'isha sun baje kayan lefen a falon suna kalla, Ammin su Ameerah sai yaba kayan take ta na faɗin "Masha Allah kaya sun yi sosai". Neehal ta ƙarasa ta rungume Hajiya cikin murnar ganinta ta ce "Hajiyata Oyoyo na yi miseed ɗinki." Hajiya ta ce "Kamar da gaske, ina ja'irar k'awarki.?" Neehal ta ce "Daɗina dake ba'a miki gwaninta sai ki gwale mutum." Hajiya ta ce "Na ji ɗin." Neehal ta sake ta ta ƙarasa kusa da Amminsu Ameerah ta rungume ta tare da gaishe ta, Ammi ta amsa mata cikin fara'a da kulawa. Gaishe da su Mama da Aunties ɗinta ta yi. Mama ta dubeta ta ce "Ki je ki haɗa break fast ki kaiwa Yayanki, kema ki haɗa ki ci." Neehal ta ce "Mama bari na ga kayan nan sai na kai masa." Hajiya ta tari numfashinta da faɗin "Kayan da sun kusa sati a gidan nan, mak'ota da ƴan'uwa duk sun zo sun gani amma ke ki na kwana a gidan baki gani ba." Mama ta bata amsa da faɗin "Ba ta wani gani sosai ba saboda ta na exam, kin san Neehal idan ta na exam ba ta da nutsuwa." Aunty Sadiya ta ce "Yanzu dai an gama, sai a bita da addu'a Allah ya ba da sa'a." Suka amsa gabad'aya da "Amin." Neehal bayan ta gama ganin kayan ta mik'e ta shiga kitchen ta haɗawa Ameen break fast kamar yadda Mama ta bata umarni, tunda Ameen ɗin a gida ya kwana yau. Ta ɗauki kayan ta na duban Ameerah da ta taya ta haɗa kayan ta ce "Mu je ki raka ni na kaiwa Yayan." Ameerah ta riƙe hab'a tare fito da idanunta waje ta ce "Wa? ki je ke kaɗai dai, kin san halin kayanki fa." Neehal ta ce "Kar ki je ɗin, kuma sai na faɗa masa in ce kince masa masifaffe." Ameerah ta ce "Allah ya na gani dai." Ammi ta bi Neehal da kallo bayan sun fito harta fice daga falon, Ammi ta sauke Numfashi ta ce "Neehal har yanzu ba ta maida jikinta ba tun ramar da tayi lokacin rasuwar Anwar." Mama ta ce "To bata son cin abinci, ba dole tai ta rama ba." Ammi ta ce "Duk da rashin cin abincin ma, amma mutuwar na damunta a rai har yanzu." "Ai dole ne ta damu Aunty Bilki, Samari har biyu sai an kusa bikinku duk su mutu." Cewar Aunty Sadiya cikin jimantawa. Mama ta ce "Wlh nima abun na damuna ina tsoron kar ace sanadin Neehal ake kisan nan." Cikin tarar numfashi Hajiya ta ce "Ashsha, faɗima ba na hanaki wannan zancen ba, yanzu idan wani ya ji ba sai ya samu abun ɗorarwa ba, tunda kema uwarta ki na faɗa, kun san mutane ba sa rasa abun fad'i, yanzu sai a gogawa yarinya baƙin fenti aita jifanta da sharruka kala_kala." Mama ta sauke numfashi ta ce "Shikenan Hajiya Insha Allahu na dena faɗar haka, shima Dad ranar da na faɗa masa haka sai ya hauni da faɗa wai a kan me zance haka, Neehal ɗin me taiwa wani da zai dinga bibiyarta ya na kashe mata samarinta?" Aunty A'isha da ba ta ce komai ba tunda suka fara maganar sai yanzu ta ce. "To mu dai muna ga Allah, kuma shi zai warware mana gaskiyar al'amari, duk ma mai nufin wani da sharri Allah ya mayar masa kansa." Suka amsa gabad'aya da "Amin."




Ameen ya na cikin bedroom ɗinsa ya na shiryawa ya ji a na knocking k'ofar falo, sai da ya ƙarasa shirinsa a tsanake sannan ya fito dan zuwa ya buɗe, zuwa lokacin Neehal ta gaji da tsaiwa ga kaya a hannunta. Ya buɗe k'ofar tare da yin baya dan bata damar shigowa, Neehal ta yi sallama sannan ta shiga. "Yaya a ina zan ajiye maka?" Ta tambaye shi bayan ya amsa mata sallamar. Kan carpet d'in dake tsakiyar falon ya nuna mata, ajiyewa ta yi ta na sauke numfashi. Juyowa ta yi Ameen dake kallonta yay saurin ɗauke kansa tare da zama a kan kujera 2 seater. Neehal ta zauna a kusa da shi ta na kallonsa a ranta ta na gulmarsa ganin kamar ƙara kyau yake ya yi wani fresh abinsa, Neehal a ranta ta ce "Tun kafin a yi auren, wannan ina ga anyi auren." "Ina kwana Yaya" ta faɗa cikin nutsuwarta. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Lafiya, Ya exams.?" Neehal ta ce "Mun gama jiya." Ameen ya jinjina kai ya na dubanta ya ce "Allah ya ba da sa'a." Neehal ta ce "Ameen." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta na son ta tambaye shi abu amma ta kasa saboda sanin halin halinsa, wannan ƴar sakewar da ta samu ya mata yanzu sai ta nemeta ta rasa. Wayarta dake cikin aljihun rigarta ce ta fara vibrate, hannu ta zira ta ɗauko a tunanin Mama ta ce amma sai ta ga Sadik ne. D'agawa ta yi ta na murmushi ta kara a kunnenta. "Wa'alaikassalam Yaya Sadik ɗina." Ta fad'i haka cikin murmushi mai sauti alamun ta na cikin nishad'in kiran da a ka mata. Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Lafiya k'alau and you." Ameen dake kallonta ya tab'e ɗan ƙaramin bakinsa tare da ɗauke kansa daga kallon nata, da sauri kuma ya juyo amma cikin basarwarshi yanda ba za a gane saurin nashi ba jin ta na magana cikin shagwab'a "Dan Allah da gaske kake Ya Sadik? Kar fa kasa na fito kuma ba ka zo ba." Sosai Ameen yake kallonta, Ƴar dariya ta yi sannan ta mik'e ta na faɗin "Gani nan to." Kallon Ameen ta yi ta ce "Yaya ina zuwa, bari in je in dawo." Ba ta jira amsarshi ba ta fara tafiya. Bin ta da kallo kawai ya yi cikin ransa ya na ƙissima abubuwa, har ta kai bakin k'ofa ya tsayar da ita ta hanyar faɗin...........✍️










*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:34] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_












*1️⃣4️⃣*














........... Neehal duk da ta ga irin kallon da Hafsat ta mata amma ta danne zuciyarta ta rungume ta, sai dai jikinta ya yi sanyi ba kaɗan ba. Kamar yadda ta rungume Hafsat haka ta rungume Fadeelah. Fadeelah da ba ta ji daɗin abun da Hafsat ta yi ba ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Ai na yi fushi, tunda Aunty'nki kawai ki ka sani ita ki ka fara tarb'a." Neehal ta yi murmushin yaƙe ta ce "Sorry ai kema Auntyna ce." Fadeelah ta yi murmushi dan sosai ta ji ta na son Neehal, yarinyar ta burgeta daga gani ba ta da d'abi'ar wulak'anta mutane duk da kasancewar ta celebrity. Neehal ta ce "Mama ta na sama mu ƙarasa." Fadeelah ce kawai ta amsa mata suka mik'e suka bi bayanta, Hafsat sai hararar bayan Neehal take. Neehal ta shiga d'akin Mama ta sanar mata da isowarsu sannan ta fito ta wuce ɗakinta. Kafin Mama ta fito Fadeelah ta ce wa Hafsat "Haba Hafsah, gaskiya ban ji daɗin abun da ki ka yi wa yarinyar nan ba ko kaɗan wlh." Hafsat ta mata wani kallo ta ce "Yarinyar ba ta mun ba ne shi ya sa." Fadeelah ta ce "Hmmmmm, me yarinyar nan ta yi da za ki ce ba ta miki ba? Yarinya ta taho da murnarta da ɗokin ganin ki ka amma ki mata wannan wulak'ancin, gaskiya ban ji dad'i ba." Hafsat ta tab'e baki ba ta ce komai ba, domin ita kaɗai ta san baƙin cikin dake cin ranta na ganin Neehal, ashe duk kyawunta da mutane suke faɗa na ganin da suke mata a TV a fili tafi haka, yarinya ga dirin jiki kamar ita ta yi kanta, tafiyar ta ma kaɗai abun kallo ce ga zazzak'ar murya.... Fitowar Mama ya katse mata tunanin da take. Cikin girmamawa suka ɗan zamo daga kan kujerar da suke suna amsa sallamar da Mama ta musu. Mama ta zauna ta na faɗin "Sannun ku da zuwa." Suka amsa da yawwa tare da gaisheta, Mama ta amsa musu cikin fara'a ta ƙara da faɗin. Ya mutanen gida.?" "Suna lafiya, suna gaishe ku." Cewar Fadeelah. Mama ta ce "Masha Allah, muna amsawa." Hafsat dai kanta na ƙasa ta na satar kallon Mama, domin Maman kamar ba ta tsufa, a 'yan shekarun da ta yi ba ta ganta ba sai ta ga ta ƙara kyau da gayu, ba za ka taɓa cewa ta haifi Ameen ba. Mama ta mik'e ta na faɗin "Bismillah ku ƙarasa dinning ku ci abinci, bari na kira Neehal ta yi sarving ɗinku."




Neehal ta na shiga ɗakinta ta zauna a bakin gado hannunta dafe da kanta, mamaki take sosai a kan abun da Hafsat ta mata, dan ta ji haushi ba kaɗan ba kawai ta danne zuciyarta ne, domin ita mutum ce wadda bata son wulak'anci ko kaɗan kuma ba ta son a yi mata, hakan ya sa itama ba ta yi. Kawar da tunanin Hafsah ta yi daga ranta ta na ƙoƙarin tashi kira ya shigo wayarta, ta daga tare da karawa a kunnenta. Cikin daddad'ar muryarshi ya mata sallama, Neehal ta amsa tare da faɗin "Ina yini Yaya." Ameen ya ce "Lafiya k'alau, su Hafsat sun zo kuwa.?" Neehal ta ce "Ehh." Ya ce "Ok" tare da kashe wayar, ya bar Neehal da mitar faɗin ya kira Hafsan mana ya tambaye ta.




Su Hafsat sun ɗan jima a gidan Mama kafin su tafi, sosai Neehal suka sha hirarsu ita da Fadeelah, dan da ta fito ma ko ƙara kallon inda Hafsat take ba ta yi ba, hakan kuwa ya burge Fadeelah dan ko ba komai Neehal ta nunawa Hafsah tafi ƙarfin raini. Da za su tafi Mama ta basu turaruka da kayan kwalliya. Suna Mota Hafsat ta dinga yi wa Fadeelah masifa a kan wai me yasa ta sakarwa Neehal fuska su ka yi ta hira kamar wata sa'arta salon ta jawo ta rainasu. Fadeelah kallon Hafsat kawai ta tsaya ta na yi cike da mamakinta, kawai daga ganin mutum sai ka ɗauki k'iyayya ka ɗora masa ba tare da wani dalili ba.?"






Bayan Magriba Mama ta na kitchen Dije ta zo ta sanar mata ta yi bak'o, Mama ta ce ta je ta shigo da shi gata nan zuwa. Ta na fitowa falon ta ga ashe Sadik ne. Ta na dubansa ta ce "Sadik ashe kai ne?" Ya ɗan sosa kai kansa na ƙasa ya ce "Ni ne Mama." Mama ta ce "Shine kuma ka tsaya a waje ba za ka shigo ba, sai ka ce wani bak'o.? Sadik ya yi murmushi kawai tare da gaishe da Mama, Mama ta amsa cikin fara'a sannan ta mik'e ta hau sama dan ta kira masa Neehal. Neehal ta na duba abu a system Mama ta shigo d'akin ta ce "Ba ki gama abun da ki ke ba har yanzu?" Neehal ta ce "Ehh, amma na kusa." Mama ta ce "To ki sauko ƙasa kin yi bak'o." Neehal ta d'ago da sauri ta na duban Mama da mamaki ta ce "Mama bak'o kuma?" Mama ta ce "Eh, ya na ƙasa ya na jiran ki." Ba ta jira amsar Neehal ɗin ba ta juya ta fice. Neehal ta mik'e ta na turo baki ta ɗauki Hijabinta ta zira ta sauka ƙasan. Babu kowa sai shi kaɗai ya na latsa wayarsa, Neehal ta ƙaraso cikin falon ta na kallonsa, a hankali ya d'ago kansa suka haɗa ido, gaban Neehal ya yanke ya fadi. Ƙasa ta yi da kanta da sauri bugun zuciyarta na sauyawa, dama tun da ta shigo falon ta ji kamar tasan baƙon k'amshin da ta ji a falon, ashe shine. Zama ta yi a kujerar dake fuskantar sa kanta na ƙasa ta ce "Ina yini." Ba tare da ya ɗauke idonsa daga kanta ba ya ce "Lafiyar k'alau, ya aiki." Neehal ta ce "Alhamdulillah." Shiru suka yi na tsawon mintuna biyu, Sadiƙ ya katse shirun nasu da faɗin "Kun kusa komawa school ko?" Neehal ta ce "Ehh." Ya ce "Yaushe." Cikin k'osawa ta ce "This coming Monday." Sadiƙ ya jinjina kai ya ce "Allah ya taimaka." Suka ƙara yin shiru na wasu mintuna, Sadik ya na lura da Neehal gabad'aya a takure take sai turo baki gaba take. Neehal ganin bashi da niyyar tafiya ta ɗan d'ago kanta ta ce "Gashi kuma ka zo k'anwar taka ba ta nan." Sadik ya yi murmushi ya ce "Ok, you mean Ke ba k'anwata ba ce.?" Neehal ta yi shiru tare da ƙara mai da kanta ƙasa, Sadik ya ƙara yin murmushi ya ce "Shikenan bari in tashi in tafi." Neehal cikin shagwab'arta da ta zame jiki ta ce "Am sorry ba haka nake nufi ba." Ya ce "To ya.?" Ta yi shiru ta na wasa da yatsun hannunta dan ba ta da abun cewa. Mama ce ta sakko ƙasa za ta ɗauki abu, da mamaki a kan fuskarta ta ce "Neehal ya ba a kawo masa ruwa da abinci ba.?" Kafin Neehal ta yi magana ya riga ta da faɗin "Ba komai Mama a k'oshe nake ma." Mama ta ce "No, ba za a yi haka ba, Neehal tashi ki kawo masa abinci." Neehal ta mik'e a hankali ta nufi kitchen, Mama kuma ta ɗauki abun da za ta ɗauka a falon ta koma sama. Neehal ta fito da k'aton tire a hannunta ta ajiye a gaban Sadik, sannan ta koma ta ɗakko drinks ta kawo masa. Shi dai kawai bin ta yake da ido. Neehal ta koma ta zauna, ganin bashi da niyyar taɓa abincin ta ce "Ka ci mana." Ya ce "Na k'oshi." Neehal ta marairaice ta ce "Dan Allah Ya Sadik ka ci, idan ba ka ci ba Mama faɗa za ta mun." Ya yi murmushi a karo da yawa ya ce "Shikenan zan ci." Neehal ta yi murmushin itama. Ruwa kawai ya tsayaya ya sha, Neehal tayi_tayi ya ci abincin amma ya ƙi, dole ta hak'ura ta k'yale shi. Jin an fara kiran Sallah ya mik'e ya na faɗin "Ni zan wuce." Neehal ta ce "Bari na kira Mama ku yi sallama." Ya ce "A'a ki ce mata na wuce kawai." Neehal ta ce "Sai da safe ka gaida gida." Daga haka ta wuce sama. Ɗakin Mama ta leƙa ta sanar mata ya tafi. Mama ta ce "Ok, zan kira shi, kema ya kamata later ki kira shi ki ji ya ya koma gida." Neehal ta ce "To" kawai, amma ita Mama ba ta ma san ko Number'nsa ba ta da shi ba. Ɗakinta ta koma domin yin Sallah.




Bayan ta idar da Sallar, ta ɗakko wayarta da niyyar kiran Haneefah ta faɗa mata Sadik ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login